Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 2 Page 12

hehu 2

12.

Muhammad Bello be bari sun yi sallama da Usman ba sai da ya tabbatar ya ma sa alkawarin zai kara tunani akan lamaran.
Rahila kuwa ko da ta shedawa Tanko sakon Zainab, Tanko ya dara ya na mai jinjinawa


matar shi akan makircin da ta iya kulkawa, haka kuma ya na mamakin rashin dabara irin na Zainab, Dan kuwa ko shi da ba ya cikin Rugar Shehu ya sheda da irin soyayyar da Shehu ya ke yiwa Zainab. Tanko ya ce dama shi ma a shirye ya ke, abu daya sa ya ke so Zainab za ta ma sa, shi ne ta tabbatar ta ja Usman bakin ruwan da ke makota da gidan gona lokacin da ake tsaka da bikin sharo, shi kuma ya mata alkawarin matukar ta masa wannan to zai mata hanyar da za ta koma gida a ranar.

Rahila ta ba ta yi kasa a gwiwa ba ta koma Rugar Shehu in da ta bar Tanko ya na shirin yanda goben za ta kasance ta hanyar aika sako ga yaran sa wanda dama suna nan cikin Taraba suna jira.

Jin sakon Tanko Zainab ta fara shirya kayan ta a boye. Sai da ta hade kayan ta tsaf cikin akwati sannan ta haye gadon karfe yayinda kirjin ta ke bugun uku uku, gaba daya hankalin ta ya kasa kwanciya. Sai bayan Ishai’i Usman ya nufi gida, bayan ya gama hidimar sa kaf, ya tsaya kogi yayi wankan sa na musammam dan kuwa so ya ke ya raya daren ranar suna soyayya da Zainab, sannan ya sheda mata burin sa na mayar da ita birni su karasa rayuwar su a can.

Ko da ya ga fitilar bukkar a kashe be damu da ya kunna ta ba, kai tsaye ya nufi gadon su ya na mai lalube har hannun sa ya sauka jikin Zainab wacce ta dan firgita ta na kokarin tashi yayi saurin janyo ta jikin sa tare da fadin

“Shhhh Abu….Ni ne”

Ya kara rungume ta sosai kamar mai kokarin mayar da ita cikin jikin sa, hakan ya sanya Zainab narkewa ba ta san sanda hawaye ya fara fita daga idanun ta ba, sai saukar su da Usman ya ji a kirjin sa, ya furta

“Subhabanallahi me ya faru? Ba ki da lafiya ne? Bari na dauko haske Abu”

Ya yi yunkurin tashi, amma Zainab ta kamkame shi ta hana shi tashi

“Menene Abu?”

“Babu komai”

Ta bashi amsa cikin rawar murya. Shiru ne ya biyu baya, inda Usman ya ke tuntuni, ya san ko Zainab ba ta fada ma sa ba tunanin gida da su Ammy ne ya sanya ta kuka, dan haka ya furta

“Kin ga Abu, na san dalilin kukan ki, kada ki damu dama akwai maganar da na ke so mu yi……”

“Ba yanzu ba dan Allah, please…”

Zainab ta katse shi, babu abin da ta ke so a lokacin fyace tarayyar ta da Usman, dan kowa komai da ta ke masa na bankwana ne. Yanda ta ke dada kamkame shi ne ya sanya Usman ya fahimci abin da ta ke bukata, tuni ya aje maganar da ya ke so su yi, shi ma ya bi yarema a sha kida. Yanda Zainab ta saki jiki ta nuna masa salo iri iri ne ya kara jaddawa Usman irin san da ta ke masa, nan kuwa be san duka na bankwana ba ne.

Sanda su ka sami nutsuwa Usman ya kara kokarin zayyanawa Zainab abin da ke ran sa, Amma be an kara ba sai ji yayi ta kara nauyi a jikin sa, Ashe bacci yayi awan gaba da ita. Dan haka a dole ya hakura, ya na mai sumbatar da a goshi ya furta

“Ina kaunar ki Abu, so na tsakani da Allah, da fatan za ki yafe min ki karbi soyayya ta”

******

Washagari sassafe aka tashi da girkin bikin sharo, masu daka fura na yi, masu tuka tuwo ma haka, haka ma masu tatsa da dafa nono ba a bar su baya ba. Zainab kuwa tun da garin Allah ya waye ba ta saka Usman a idon ta ba, haka shi ma Usman wanda tun fitar shi sallar asuba be sami damar dawowa ba bare ya samu yayi magana da Zainab. Cikin dabara ta ja Rahila gefe, ta fada mata cewa da zarar an fara sharo ta saci jiki ta dawo gida ta tafi mata da dan akwatin ta can inda su ka yi za su hadu da Tanko, ta duba girman Allah kada ta bari a ganna ta, Rahila ta amsa da an gama.

Sai wajan sha biyu sai gashi ya shigo gidan, ya tadda Zainab sai kai kawo ta ke cikin bukka domin kuwa lokacin da su ka yi da Tanko sai gabatowa ya ke, dan kuwa ana idar da sallar azahar za a fara bikin.

Jawo ta yayi bangaran jikin sa na dama, tare da sumbatar ta a goshi, sam be lura da yanda Zainab ta kasa daga ido ta kalle shi ba, ya na mai damka mata ledar da ya ke dauke da shi ya ce

“Ga kayan fitar Sharon ki, na so ace kin taba gani da ba zan yarda ki je wajan ba dan kar a kalle min ke, toh amma dan Allah idan kin je kada ki jima….”

Jin haka Zainab ta yi saurin fadin

“Toh idan na bar wajan ina zani? Sai na dawo gida na zauna ni kadai kamar mayya bayan an ce kowa can zai tafi…”

Usman na dariyar tsiwa irin na Zainab ya furta

“Ba fa kowa ba, ko kowa zai tafi ai ban da Iyalle..”

Zainab na mai buga kafa cikin shagwaba ta furta

“Ni dai ban yarda ba, Ni dai sai dai za ka biyo ni mu je yawo, dama ka ce akwai maganar da za mu yi, ka ga sai mu cikin annushuwa daga ni sai kai”

Kalmar daga ” ni sai kai ne” ya sa Usman cin dadi har cikin ran sa, Wai yau shi ne Zainab ke san kebewa da shi, da ga ita sai shi yanda babu wanda zai dame su.

“Kamar dai yanda ya kasance a gidan gona?”

Ya tambaya ya na mai kokarin kallan idanun Zainab. Yanda kwayar idanun sa ke rawa ya sanya tsigad jikin Zainab tashi, ta yi saurin kawar da kai gefe, ta furta

“Ko ma ka kai ni wajan ruwan nan, ban taba ganin shi ba sai dai na ji labari”

“An gama gimbiya Abu, in Sha Allah za mu je, sai kuma tafiyar ta mu za mu yi ta da dabara, idan an fara da minti talatin haka sai na miki alama ni zan fara yin gaba, sai ki bi sahu na, ai dai za ki gane hanya ko? Ba nisa zan mi ki sosai ba”

Zainab ta gyada masa kai alamar “eh”. Sallamar da aka yi ana neman Usman ne ya sa ta sake ta ya fita. Nan ya barta jiki na rawa, in da ta sami gefan gado ta zauna. Sai da ta yi kusan minti goma zaune sannan ta iya bude ledar da ya ba ta. Atamfa ce koriya da ja, dinkin riga da zani, rigar an dinka ta doguwa sosai dan za ta kaiwa Zainab har gwiwa, ga fadi ko ado babu jiki, sai kuma mayafi shi kuma shudi da ruwan dorawa. da ka gani ka ga kalar fulanin kauye, sai kuma sifas shi ma din ruwan dorawa ne. Ko da ta gama dagawa sai ta ja tsaki, a zahiri ta ce

“Yau dai Allah zai raba ni da wannan gidadanci! Dan ji wani jahilin kaya da ya kawo min! Macuci azzalumi!”

Da kamar ba za ta saka kayan ba, Amma da ta tuna da hudubar Rahila haka ta rufe idanu ta sanya kaya, tun da ta zo duniya ba ta taba muni irin na ranar ba, ita kan ta sai da ta tsargu da kan ta.

Amma ko da lokacin tafiya yayi ta fito waje, hankalin kowa kan ta ya koma, in da ake ta yaba kyan ta da koma kyan kayan jikin ta. Ita kan ta Rahila kasa shiru ta yi ta furta

“Kai wannan ko ke ce amaryar sai haka! Gaskiya kin fito ziza da ke, ko da shi ke ai matar Shehu guda!”

Wani malulun bakin ciki ne ya tsaya makoshin Zainab, Amma daga baya da ta lura da irin shigar da sauran jama’ar su ka yi, daga matan har mazan wani irin farin takalmin roba su ka sanya sau ciki, inda yawanci matan atamfa ne jikin su irin wannan ma su kalar rambatsau din nan, yan matan cikin su sun ci gilashin roba kala kala, haka ma samarin wajan wanda ba za su ba da gudunmawa wajan Shadin ba dauke da rediyo a kafada, sai bada iska su ke a dole gayu su ka sha.

Tun Zainab na daurewa har ta fara dariya musammam da su ka isa filin Sharon, ta ga shigar da Bello yayi, kan sa har da gashi da wata irin hula na angwanci. Amarya Raqeeba kuwa can ta hango cikin kawayen ta, tabbas babu wani bambamcin shigar ta da na Zainab idan aka dauke gilashin robar da ta sanya da kuma farin takalmin robar da ke kafar ta. Kallo daya Zainab ta mata ta dauke kai dan kuwa ji ta ke ta yi mugun tsanar Raqeeba.

Daira aka yi yayinda aka bar fili a tsakiya, samari masu jini a jika su ka tsaya daga su sai gajeran wando hannun su dauke da sandar gora su na mai yiwa kan su kirara, ganin haka Bello ma ya kwabe rigar jikin sa, ya ja gora shi ma ya fada fili, tuni waje ya dau sowa da tafi. Hakan yayi daidai da isowar Usman cikin shigar sa na fararin yadi yar shara, yau din ma hula ne kan sa ba rawani ba, kallo daya za ka masa ka tabbatar da jin dadin da ke tattare da shi.

Dage gefe ya tsaya yanda zai na hango Zainab. Ita ma din kallan sa ta ke ta ya kiyas ta lokacin da ya kamata su bar wajan. Usman be jima da isowa ba aka fara bikin sharo, wani matashin saurayi ya na mai kuwa ya furta
“In dai ka kai namiji wanda zai daga hannun sa haka a bashi itace! In Allah ya so ya yarda zai yi farin jinin yan mata a dandali kayyasa!”

Ya na gama fadin haka daya daga cikin samarin ya daka wani katan sanda ya zuba masa a gadan baya, in da shi kuma ya cije cike da jarumta ya na mai taka rawa. Ganin haka Zainab ta ja tsaki cikin ran ta, ta na mai fadin ‘jahili dai jahili ne!’

Haka su ka ta bugun junan su wani har jini na fita, tuni abin ya hau kan Zainab ta na tunanin yanda za ta ja Usman su yi gaba ta ga ya janye cikin sa da kan sa ya tafi, can gefe ta hangi Rahila ta dan mata alama da idanu sannan ta bi bayan Usman.

Karkashin wata bishiya ta tarar da shi ya na tsimayin ta, in da su ka nufi hanyar kogin Usman na jan ta da hira, Zainab na kokarin amsa ma sa duk da sam hankalin ta ba ya gare shi, lissafin ko Rahila ta dauko mata kayan ta? Za su tarar da Tanko wajan?

Tun da su ka isa bakin ruwan Zainab ke dan waige waige har Usman ya gane ya tambaye ta tana tsammanin wata ne?

Ta girgiza kai alamar ah ah ba tare da ta iya tanka masa ba. Daga bakin ruwan su ka zauna. Yanayin yanda ruwan ke zuba daga dutse ya na mai gangarowa kasa, da kuwa kukan tsuntsaye da ke tashi wajan ba karamin karawa wajan annushuwa yayi ba. Usman na mai janyo Zainab kusa da shi ta hanyar sanya hannun sa ta cikin ta ya zagayo ta kugun ta ya furta

“Abu mata ta ta kai na, kin yi kyau kwarai”

Zainab ta murmusa kawai yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa musammam da ta ji Usman ya kara da

“Ki yafe min Abu, na yi kuskure, idona ya rufe akan ramuwar gayya, ba komai ya sa na dauko ki daga birni na kawo ki nan kauye ba fyace sanadiyar rashin ganawa da mahaifiya ta da ki ka yi har ta rasu, ta hanyar kame Muhammad Bello da ki ka sa aka yi . ….”

“Usman……”
Zainab ta furta cikin rawan murya. Usman na mai daura yatsa bisa leban ta ya furta

“Shhhhhhh, ban gama ba ai. Akan wannan dokin fushin na rabo ki da komai na kawo ki dajin nan, ki yafe min Abu, Allah ya jarabce ni da soyayyar ki, Kuma ina da yakinin ki na so na….”

“Dan Allah Usman ka dena fadin haka”

Cewar Zainab ta na mai zare hannun Usman daga jikin ta yayinda ta mi ke tsaye, shi ma din tashi yayi yayi saurin shan gaban ta ya na fadin

“Ki yi hakuri ki saurare ni Zainab, na san na yi kuskure, Kuma na san ni ba sa’an auran ki ba ne, Amma tunda kiga ga haka ya faru da mu toh kaddarar mu kenan, Zainab na dade ina istigifari akan abun da na mi ki, haka kuma na yi nadama, Kuma shirye na ke na gyara komai, za mu koma birni, in akwai makarantar da zan shiga na dan sami wayewar kai Zainab zan shiga saboda ke, duk abin da ki ke so Zainab zan yi….dan Allah Kar da ki juya min baya….”

“Toh tantabarar sarkin soyayya!”
Muryar Tanko da dariyar yaran sa ne ya daki kunnan Usman da Zainab. Sam ba su lura da zuwan su ba, su goma ne idan aka hada da Rahila wacce ke dauke da akwatin Zainab. Daga Tanko har yaran sa dauke su ke da bindiga irin dogwayen nan da ake kira AK 47, kasancewar sun rufe fuskokin su be hana Usman gane Tanko ba. Can kasan makogaranta Zainab ta furta

“Ya Allahu me na yi ni Zainab!”

“Me ya kawo ka cikin Ruga ta? Ban ma ka tazara da Rugar Shehu ba?”

Cewar Usman a fusace ya na mai tsayawa gaban Zainab yanda zai kare ta daga ganin Tanko da yaran sa domin kuwa ya lura da yanda jikin Zainab ya dau kakkaura. Dariyar mugunta Tanko ya saki ya na mai jefa kai baya, sai da yayi mai isar ta ya ce

“Matar Shehu ga mu mun iso kamar yanda ki ka umarce mu, ga kuma jakar ki nan Rahila ta dauko mi ki, kamar yanda ki ka sa ta”

Kamar wanda aka kwarawa ruwan sanyi haka Usman ya yi mutuwar tsaye na wani dan sakanni, sai a sannan ya lura da Rahila, haka kuma ya kai kallan sa ga akwatin da Rahila ke dauke da shi, ko shakka babu akwaitin Zainab din ne. kwakwalwar sa ta tsaya har sai da ya din yi jim kafin ya juya a hankali ya dubi Zainab wacce tuni idanun ta ya cika da hawaye, ta kasa magana sai kai ta ke girgiza masa.

“Fito mana! Ko ba ki gama ban kwana da Shehun ba ne, Malam dan matsa mata hanya mana!”

Ga mamakin kowa sai kuwa Usman ya matsa, amma Zainab ta kasa motsawa bare ta karasa wajan su Tanko, kallan Usman ta ke yayinda idanun shi ke aika mata sako kala kala. Ganin haka Tanko ya furta

“Usman ka sani cewa yau zan raba ka da abubuwa uku kamar yanda ka so ka raba mahaifina da ….. Na farko zan raba ka da sarautar Rugar Shehu kamar yanda ka yiwa mahaifina, haka kuma na raba ka da farin cikin ka ta hanyar raba ka da matar ka, kamar yanda ka raba mahaifina da farin cikin sa, na uku kuma zan kashe ka, duk da dai shi mahaifin nawa ya na nan raye”

Jin haka hankalin Zainab ya tashi, murya na rawa ta ce

“Ba mu yi haka da kai ba! Ke Rahila ba mu yi haka da ke ba! Ba ku ce za ku kashe shi ba! Ba za ku kashe shi ba! Gida kuka ce za ku mayar da ni ba ki ce za ku kashe shi ba!”

Usman kuwa cewa yayi
“Zainab me ya sa? Duk zaman nan da mu ka yi da ke, duk kwanciyar hankalin da mu ka samu…. Zainab… Zainab me ya sa…? Dama kin yi ne dan ki cutar da ni?”

“Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!”

Cewar Tanko, be gushe ba ya mayar da kallan sa ga Zainab ya na mata irin kallan nan na kurulli ya furta

“Ke kuma zan mayar da ke gida amma sai na karfi kudi makudai daga wajen iyayen ki sannan na more jikin ki san rai na…..”

Be san sanda Usman ya matsa gaban sa ba sai saukar mari ya ji kawai, ya ja da baya ya na mai dura zagi. In da yaran sa su ka yo kan Usman a fusace su na Shirin bugun sa, Tanko na mai huci ya furta

“Ah ah kada ma ku soma, Ni nan ni zan jibgi dan bantan uba! Ku daure min shi!”

Nan su ka fara yunkurin daure Usman in da shi kuma ya ke kokarin bubbuge su musammam da ya ga Tanko ya kai hannun sa jikin Zainab wacce ke kuka da ihu ya ja ta gefe, fadi ta ke

“Dan Allah ku rabu da shi, duk abin da ku ke so za a baku, kada ku kashe shi”

Sai da su ka sa igiya suka daure Usman tun daga kafadar sa har zuwa kafafun sa, sai gashi kwance tamkar gawa. Tanko na mai duban Zainab ya furta

“Abu uku na ke so, kuma duka sai na dauka, sarautar Rugar Shehu! Jikin ki! Sai kuma raba mijin ki da ran san sa!”

Ba Zainab ba, ita kan ta Rahila sai da gaban ta ya fadi jin har da jikin Zainab cikin lissafi. Zainab kuwa yawu da kaki ta tofa fuskar Tanko, tare da fadin
“Sai dai gawa ta kaskantacce mara mutunci! Za ka sake shi ko sai na bata ma ka rai!”

Tanko ya tunzura saboda sam ba ya iya jure tsiwa, bare kuma ga yawu Zainab ta tofa masa. A fusace ya dauke ta da marin da sai da Usman ya motsa ya na kokarin kuncewa, Zainab kuwa sai ta ga wuta a idanun ta ba, ba ta gama warewa daga zafin marin ba Tanko ya soma jibgar Usman da bakin bindigar sa har ya kai ga fasa ma sa kai. Kuka sosai Zainab ta ke yayinda ta ke kokarin shigar masa, Tanko ya hankada ta gefe, ya durkusa gaban shi ya furta

“Ka san dalilin da ya sa na ce a daure min kai haka dan uwa na? Saboda ba zan kashe ka da bindiga ba gudun kar yan sharo su ji karar ta, haka kuma ba zan kashe ka da wuka ba, mutuwar za ta ma ka sauki da yawa, yanda ka ke haka haka zan jefa ka cikin kogi, ka sha ruwa ka koshi har ka sheka barzawu, ni kuwa ina can ina morewa da matar ka, sai na tabbatar dukkanin tudun jikin ta ya saki sannan na mayar da ita ga iyayan ta, Rugar Shehu kuwa ka tabbatar ta zama tawa yanda na yi ma ka, haka zan wa Bello! Bissalam”

Ya tashi tsaye yayinda ya bawa yaran sa Umarnin su dau Usman su jefa shi ruwa. Akan idan ta su ka dau Usman gadan gadan, idanun sa wanda su ke rabi a rufe a kan ta, ta fara ihu kamar wacce ke shirin zarewa fadi ta ke

“Dan Allah ku yi hakuri kar ku kashe shi! Dan Allah Rahila ki sa baki kar su saka Usman cikin ruwan nan!”

Karar saukar Usman cikin ruwa da yanda ruwan ya tashi daboda yanda su ka jefa shi da karfi ne ya sanya Zainab saka ihu mai tsananin kara kafin ta zube kasa sumammiya.

 

 

Post a Comment for "Auren Shehu Book 2 Page 12"