Auren Shehu Book 2 Page 11
AUREN SHEHU 2
11
Rahila ba ta iya jiran dare yayi ba ta yi amfani da damar annushuwar da Usman ya ke ciki ta tambaye shi ko ya na da labarin in da Tanko ya ke ba tare da ta nuna dama ta san in da ya ke ba bare ma a gano ta saba satar hanya.
Tausayin Rahila ne ya kama Usman musammam yanzu da ya san darajar soyayya, Dan haka ya ce da Muhammad Bello ya raka Rahila ta ga mijin ta, idan ma ta na so ta koma wajen shi ne gaba daya ta na iya komawa babu laifi in ya so duk sanda ta ke da bukatar shigowa Rugar Shehu neman abinci ko wata bukatar mai muhummanci kofa a bude ta ke gare ta. Ta na murna ta yi bankwana da jama’ar rugar, in da ta yiwa Zainab alkawari cewar tafiyar ta ba ya na nufin lalacewar maganar su bane, shi ne ma dalilin da ya sa za ta wajan Tanko, duk yanda su ka yi da Tanko za ta dawo ta fada mata, haka kuma za ta na kawo mata ziyara a kan kari.
Cike da farin ciki ta riski mijin ta Tanko wanda sam be nuna farin cikin sa na ganin Rahila dauke da kaya niki niki ba, a tunanin sa Usman ya karota ne, sai da ta masa bayani tare da albishir da ta zo masa da shi sannan ya dan saki ran sa.
Bayan Bello ya masa sallama ya juya ne Tanko ya kada baki ya ce
“Ban so dawowar ki waje na ba, kamata yayi ki zauna can in da za ki fi ganin duk abin da ya ke faruwa, yanzu da ki ka kwaso kafa ki ka dawo uwar me za ki min a nan?”
Cikin sosuwar rai Rahila ta furta
“Kai kuwa Tanko ai zato na farin ciki za ka yi da zuwa na, na ga kowani namiji burin shi ya kasance tare da iyali saboda jiki da jini….”
“Toh yar jaraba! Jaraba ce dai ta dawo da ke! Ke jikin ki ma duk ya sake amma ba za ki hakura ba?”
Jiki sanyeye Rahila ta furta
“Haba kai kuwa, ai sai ana son ka ake mararin ka..”
“Toh uwar jaraba wuce mu je na mi ki abin da ki ke so, Amma dai zaman ki a nan ba zai yiyu ba! Dole ki koma Rugar Shehu!”
Rahila ba ta yi zuciya ba ta bi bayan Tanko, sai da ya ba ta hakkin ta sannan ya shiga zayyana mata yanda za a yi su cafke daga Usman har Zainab, in da ya ce ta shedawa Zainab yanda ta yi yayi daidai, ta kara dagewa wajan samin yardar Usman, hakan ne kadai zai sa su iya cin nasara. Su ka yi sallama Tanko na farin cikin burin su ya kusa cika, dadin dadawa kuma ya kusa samun Zainab, wacce tun da ya gan ta be da mafarki sai na ta, duniyar nan kab be da buri da ya wuce samin Zainab ko da kuwa na wuni daya ne.
Babu wanda be yi mamakin dawowar Rahila ba, cike da bakin cikin Tanko ya hana ta zama da shi, ta mu su karyar ga mata yan uwan ta me zai sa ta je can gefe ta ware kan ta, zaman cikin Rugar Shehu shi ya fi mata alkhairi. Sai da ta faki idanun matan Rugar sannan ta iske Zainab a daki, ta kwashe yanda ta yi da Tanko na game da Usman ta sheda ma ta, tare da sakon Tanko gare ta, kana ta kara da
“Kin ga kenan yanda ki ka yi ba karamin dabara ba ne, yanzu ki dada jan shi jiki, ki sa ya yarda da ke sosai ya saki jiki da ke, kya iya nuna masa ma kin kamu da son shi…..”
“Mtswww Allah ya sauwake na kamu da san wannan bagidaje!”
Zainab ta katse ta a fusace. Jin haka Rahila ta dada godewa Allah, kenan hasashen ta ba daidai ba ne, Zainab dai ba ta fadama san Usman ba, gudun kar daga baya ta ba su matsala.
****
Can birnin Kano kuwa anyi cigiya da shelar neman Zainab, haka kuma an bi sahunta har Mambila amma an kasa gano takamamman in da ta ke, musammam yanda Jama’ar garin su ka yi kyameme su ka nuna ba su taba ganin Usman ba bare Zainab, hatta dajin Rugar Shehu sun shiga, amma gajen hakuri ya sa su ka juyo saboda yanda dajin ke da ban so tsoro, gani su ke bil’adama ba zai iya rayuwa ciki ba.
Kudin da Ammy ta kashe na sadaka da sauka ba adadi, tun tana sa rai ta na yarda da maganar yaran General da Anty Sauda, har ta fara karaya, ta yanke hukunci ziyartar kasa mai girma dakin Allah ta yi addua, idan har. Zainab na raye Allah ya bayyana ta, idan kuma ta mutu Allah ya nuna mata kabarin ta ko ta sami kwanciyar hankali.
Da wannan niyya, da kuma burin ganin Halitta Ammy da Falmat su ka tashi zuwa kasa mai tsarki.
***
Cikin kankanin lokaci jama’ar Rugar Shehu su ka kamu da kaunar Kado kamar yanda su ke kiran zainab, daga manyan su har zuwa yara. Ya kasance ko magana ta yi ya zaunu ba a mata musu, haka ma ta shige cikin zuciyar Usman ta zauna daram, Dan kuwa shawarar Rahila ta dauka, jan shi ta ke a jiki ta na masa soyayya irin ta yan birni musammam Zainab ta gama gogewa a wannan fanni.
Wani sabon al’amari shi ne yanda Usman ya tashi tsaye kan Muhammad Bello, duk wata hidima da ilimin tafiya da Rugar Shehu kokari ya ke ya koyawa Bello, haka kuma ya sanya ranar auren Bello da Raqeeba wata daya kacal, Allah ya so dama Bello ya jima ya na muradin Raqeeba duk da ya fahimci ba shi ne gaban ta ba, shi din ne ya ke san maso wani sai kuma faduwa to zo daidai da zama.
In da Bello da jama’ar Rugar Shehu aka shiga shirye shiryen biki, Amarya Raqeeba a nata bangaran bakin ciki ne ya mamaye zuciyar ta, ta na ji ta na ana gani za a daura mata Bello bayan Usman ta ke so, Kuma mahaifiyar ta ta san da haka amma ta ce ko da wasa kar da ta sake wani mahaluki ya ji zancen nan in ba haka ba sai ta tsine mata.
Rahila ce ta fara gano halin da Raqeeba ta ke ciki ana gobe Bikin Sharon da aka shirya musammam dan auren Bello, in da sati daya ya rage auren na Bello. Rahila ta yi ta bugun cikin ta har yarinyar ta hakura ta sheda mata soyayyar da ta ke yiwa Usman, da kuma maganar mahaifiyar ta na kar ta bari kowa ya sani.
Hakan yayiwa Rahila dadi, dan kuwa kwana biyu ko maganar Usman Zainab ba ta yi mata, ta na ganin hashashen ta dai zai kasance gaskiya, Zainab ta fara san Usman, dan haka ta yi amfani da damar ta shiryawa Raqeeba duk yanda za ta yi, sai da ta tabbatar Usman ba ya nan sannan ta tura ta dakin.
Zainab kwance bisa gadon kara, tunanin Ammy da su Falmat ta ke, ta na mamaki ace har ta yi wata hudu wani uwa duniya amma a kasa samin wanda zai biyo sahun ta? Wani zuciyar kuma ta raya mata kila an bi ba su same ta ba ne. Kamar daga sama ta juyo sallamar Raqeeba, Zainab ta tashi zaune tare da amsa sallamar, da fara’ar ta ta bata izinin shigowa, Raqeeba ta shigo kan ta a kasa ta zube gaban Zainab.
Cike da fara’a Zainab ta furta
“Ha’a Amarya ta shi zauna gado mana, kya zauna a kasa?”
Maimakon ta tashi sai ta fashe da kuka har da shassheka. Hankalin Zainab ya tashi, cikin sauri ta sauko kasa gurin Raqeeba yayinda ta shiga rarrashin ta tare da tambayar ba’asi. Da kyar ta iya lallaba Raqeeba ta yi shiru, cikin lallami da lumana Zainab ta ce da Raqeeba
“Me ya faru? Me ya sa ki kuka haka? Auren ne ba ki so?”
Raqeeba ta gyada mata kai alamar
“Eh”
“Auren dole za su mi ki?”
Ta gyada mata kai. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ta furta
“Kin fadawa Usman ba kya so?”
Ta girgiza mata kai alamar
“Ah ah”
“Me ya sa ba ki fada masa ba? Kin fadawa Hansai?”
Nan ma sai ta sa mata kuka, da kyar ta samu ta yi shiru har ta sheda mata abin da maifiyar ta ta ke so. Cikin jimami Zainab ta furta
“Shi wanda ki ka ce ki na so, wanene shi?”
Budar bakin Raqeeba sai cewa ta yi
“Shehu….”
Dam! Maganar ya doki kunnan Zainab yayinda gaban ta ya yi mummunar faduwa, kishi ne ya taso ya tsaya mata kahon zuci, ba ta san sanda ta furta
“Shehu? Usman miji na ki ke so?”
Raqeeba ta gyada kai, ta lura sarai da halin da Zainab ta shiga kamar yanda Raheela ta ce mata zai faru, haka kuma ta ce kada ta sake ta nuna ta san abin da ta ke, dan haka Raheela ta yi burus ta kara da
“Idan babu shi ba zan iya rayuwa ba, ya san ina san shi ba tun yau ba, Amma ya ce na auri Bello, mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki……”
Kamar takobi haka maganar ta soki zuciyar Zainab, musammam da ta ji Raqeeba ta kara da
“Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire shi ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai……!”
“Shut up!”
Zainab ta dakawa Raqeeba tsawar da sai da jikin Raqeeba ya dau rawa tsabagen firgita. Ita kan ta Zainab din jikin ta rawa ya ke saboda bacin rai, ta na mai nuna mata hanya ta ce
“Tashi ki fita”
Maimakon Raqeeba ta fita, sai ta yi kamar yanda Rahila ta ce ta yi duk da ta tsora ta ainun, ta na mai ruqo kafar Zainab ta furta
“Dan Allah ki taimaka min kada ki bari Shehu ya san na mi ki wannan maganar, matukar ya san na fada mi ki ya na sawa a daure ni, koma a kar ni har lahira shiya sa ma mahaifiya ta ta haneni ga fadawa kowa, ki min rai ki taimake ni”
Ganin yanda ta marairaice sai tausayin ta da tausayin kan ta ya kamata, lalle Raqeeba abar tausayi ce tunda har ta fada soyayyar azzalumi kamar Usman. Cikin sanyin murya ta furta
“Na ji, ki sakar min kafa ki kuma fitar min daga daki, in dai Usman ne na kusa barin rayuwar shi har abada!”
Jin haka Raqeeba ta tashi da sauri ta fice gudun kar Zainab ta gane shara ta take.
Nan bakin gado Zainab ta zube, so ta ke ta yi kuka amma ta nemi hawayen ta rasa.
“…..mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki……”
Maganganun Raqeeba da ke yawo cikin ran Zainab kenan. Ko da ta tuna
“Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai……!”
Ta yi saurin shafa cikin ta, nan ta ke wani tunani ya bugi kan ta, tun da tazo Rugar Shehu ba ta taba yin al’ada ba, duk da dai nata mai wuyar sha’ani ne ba kowani wata ta ke yi ba, Wani lokacin kuma ta kan yi sau biyu a wata. Haka kuma tun da ta fara sakarwa Usman jikin ta kusan kullum sai ya kusance ta, Tuni ta fashe da kuka ta na fadin
“Allah ya isa! Allah ya isa ba zan taba yafe ma ka ba Usman duniya da lahira! Allah ya isa!”
Babban tashin hankalin ta shi ne gaba daya ta manta zuciya ba ta da kashi, kamar yanda ta ke kokarin sace zuciyar Usman, tuni na ta zuciyar ta yi rauni, ba ta iya yin cikakken minti goma ba tare da ta yi tunanin Usman ba, haka har Allah Allah ta ke dare yayi su kebe, dama ga ta Allah yayi ta mace mai yawan bukatar mijin ta.
Sai da ta yi mai isar ta, sannan ta share hawaye bayan ta gama yanke hukunci ta kwallawa Rahila Kira, wacce dama ta yi lamo ta na tsammanin kiran. Da saurin ta ta shigo, ganin yanda idanun Zainab ya kumbura su ka yi suntun ta fara tambayar ko lafiya. Murya shake Zainab ta furta
“Ki ce da mijin ki Tanko na shirya tsaf, ya gaggauta kawo mafita idan ba haka ba zan yi gaban kai na!”
Cike da munafunci Rahila ta shiga doka salati ta na tambayar Zainab shin ko menene ya faru. Zainab ta ce ita yar sako ce ta tafi ta kai sakon ta. Rahila ta amsa da toh ta fice jiki na rawa kamar wacce za ta yi tsuntsu dan sauri.
Nan cikin gonar Bello ta wuce Usman da Bello, yanda ba ta lura da su ba haka su ma ba su ga giftawar ta ba. Musammam Bello wanda maganar Usman ta sa kan shi yayi tsawa. Cikin jinjinawa ya ke maimaita
“Za ka bar min sarautar Rugar Shehu?”
Usman na mai murmushi ya gyada masa kai, in da Bello ke masa kallan zararre. Zaune su ke karkashin bishiya da ta mu su lema, dukkanin su sanye cikin fararen ruguna yar shara. Bello na kallan fuskar Usman wanda tun da ya gane yanda Zainab ta ke satar kallan sa duk sanda be daura rawani ba ya dena saka rawanin gaba daya sai dai hula, Bello ya furta
“Akan wani dalili zan gaje ka bayan kana raye?”
“Murabus na ke so na yi”
Usman ya ba shi amsa a takaice, ya kara da
“Shi ya sa na ke ta sa ka a hanya, ban dawo Rugar Shehu dan na zauna ba, na dawo ne sanadiyar kiran Iya, Iya kuma ta kwanta dama mun kuma baro kabarin ta can falgore, bakin cikin haka ya sanya ni dauko Abu daga birni, na kawo ta daji dan kuwa a nawa wautar hakan ne zai sa na rama babban asarar da ta ja min, da zalincin da ta ma ka, Amma na huce yanzu Bello, ba zan iya jure ganin Abu cikin wahala haka ba, ba ta saba da rayuwa irin ta mu ba….”
“Toh ka sake ta mana…”
Bello ya katse shi da iya gaskiyar sa. Murmusawa Usman yayi, kana ya ce
“Ai ko da da Allah be jarrabe ni da soyayyar Abu ba ba zan iya sakin ta ba saboda alkawari mai girma da na daukarwa mahaifin ta, bare yanzu da son ta ya bi jiki na jini da tsokana, ina san mata ta Muhamadu, ina san ta lillahi warasulihi, ba zan iya rayuwa babu Abu ba”
Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Bello ya nisa ya ce
“Shin ita maidakin ta ka ka ji ta bakin ta? Idan ita kuma ba ta da wannan ra’ayin fa? Shi fa kado ba shi da tabbas…”
“Ko ban yarda da komai ba, na sheda Abu ta na kauna ta, Abu na ta na so na, daren yau zan sheda mata soyayyar da na ke mata, Zan nemi yafiyar ta akan dauko ta da na yi daga birni duk da dai ni banyi dana sanin hakan ba, Rugar Shehu shi ne tsatson soyayyar mu”
“Yanzu Shehu akan mace za ka bar sarauta? Ka bar shanu? Ka bar yan uwa ka tai birni?”
“In ka dauke yan uwa duka sauran abubuwan da ka lissafa na dade da barin su, sai dai wannan karan zan yi amfani da dama ta na gina gidan gona cikin birni, yanda za mu bunkasa tattalin arzikin Rugar Shehu a can birni, in Sha Allah ko ban iya yin yanda Shugaban kasa ke da hashashen kawo cigaba birni ba, zan kwantata, haka kuma zan sayar da wasu daga cikin shanu wanda su ke mallaki na domin ginawa Abu gida irin na yan birni”
Ya kare maganar ya na murmushi yayinda ya ke ayyana irin gidan da zai gina mata cikin ran sa. Jikin Bello sanyaye ya ke duban sa, ya sha ji ana cewa asiri ba ya kama Usman, Amma ko shakka babu wanda Zainab ta yiwa Usman bakara min asiri ba ne. Cewar Bello cikin ran sa.
Aure s
Post a Comment for "Auren Shehu Book 2 Page 11"