Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 1 Page 8

*khadija SidiAUREN SHEHU
8.

Da sauri su Jauro ka karasa wajen, su na haske Zainab su ke tambayar ko lafiya? Menene ke faruwa?


“Wannan yarinyar mu ka kama wani mai bakar mota ya sauke ta, dadin dadawa kuma mun ga sanda ta diro daga kan katangar gidan Malam! Ba tun yau ta saba yi ba, yau duban ta ya cika! Wallahi sai ta cire wannan nikabin na munafunci mun ga kowacece!”

Cewar Uzairu yayinda ya ke bin Zainab da kallan banza. Jauro wanda kallo daya ya mata ya san uwargijiyar ta shi ce, tuni ya hakikan ce ya ce

“Wannan maganar banza ne! Ina ruwan ku da matar mutane? Dan sharri har za ku ce daga gidan Malam ta diro? Ke malama kama hanya ki tafi!”

Jin haka Zainab ta dan motsa da niyar wucewa, su ka yi saurin dada tare hanyar.

“Idan har ta bar wajan nan toh ban isa dan halas ba! Idan ma za ta tafi sai ta fada mana ita wacece kuma daga ina take! A wannan marra ta masifar duniya ba za mu ga haka mu bari ba!”

Cewar Khalifa, shi kuma Uzairu cewa yayi

“Me ku ke jira? Ku fizge tsinannayir abar mana ko ta fi karfin ku ne?”

Jin haka Zainab ta sa hannun ta ruke nikaf din da ya jike jagab da hawaye, Ganin haka Jauro ya yi saurin shiga tsakani ya na fadin

“Kul! Kar wani dan iska ya kai hannun jikin ta!”

“Toh ka san wacece kenan, idan ka san wacece ka fada mana mu dena bata lokacin mu!”

Daya daga cikin jama’ar da su Uzairu su ka tara ma Zainab ne ke maganar cike da rashin kunya

“Zan ci uban ka ka min rashin kunya anan! Sakarai mara tarbiya!”

“Mara tarbiya ga ta nan bayan ka Malam, kuma wallahi ba wani wane wane! Sai ta bude fuskar ta mun gani!”

Tuni hayaniya ta kara kaurewa a wajan, in da kowa ke fadin albarkacin bakin sa, Jauro kuwa be fasa kare Zainab ba, ya tsaya tsayin daka babu mai ganin fuskar ta, shi kan sa Isa mamakin yanda Jauro ya hakikance ya ke. Jin an furta

“Me ka faruwa a nan? Hayaniyar me ku ke haka? Dare mahutar bawa amma ba za ku bari mu huta ba?”

Kowa yayi tsit saboda kwarjini da Malam ya ke da shi a idanun jama’a. Zainab kuwa ganin shi tsaye tare da Usman ji ta yi dama kasa ta bude ta shige tsabagen tsoro da firgici. Hayaniyar su da haushin karnuka ya sanya Malam fitowa, Usman kuwa da kyar ya samu ya dan ja hankalin karnukan ciki kafin shi ma ya biyo bayan Malam.

“Kai Jauro wacece wannan matar da ke tsaye bayan ka?”

Malam ya kara tambaya, in da hankalin Jauro ya tashi dan be so Malam ya fito ba, ya so a yi ta ta kare ba tare da Malam ya sani ba. Kafin Jauro ya iya tunanin amsar da zai bawa Malam, sai ji su ka yi an furta

“Mata ta ce…..”

Hankalin kowa ya koma kan Usman, yayinda cecekuce ya dada kaurewa, da daga mai cewa

“Kar ka rena mana hankali!”

Sai me cewa

“Karya ne wallahi! Akan wani dalili za a sauke matar ka daga wannan bakin daren? Kuma a kan idanun mu ta diro daga katanga! Ba kuma tun yau ta fara ba!”

“Malam mu fatan mu kawai a tuntubi wacece, kuma ta bude fuskar ta mu ga wacece kar mu na zaune a cutar da mu”

Jin wannan batu kan Malam ba karamin kullewa yayi ba, ya furta

“Daga wani katanga kenan? Kai Usman ta Yaya ta zama matar ka? Dama ka na da aure? Me zai sa matar ka fitowa da tsakar dare haka?”

Malam ya tambaya yayinda gaban sa ya shiga faduwa ya na mai haske Zainab ta hasken tocilit. Tuni ta dada sunkuyar da kan ta, cike da dana sanin fitar ta a daren ranar. Usman ne ya shiga tsakani, ya na mai kare Zainab daga haske ta da Malam ya ke, ya ce

“Na yi kuskure, duka wannan laifi na ne Malam, kamar yanda na fada wannan mata matata ce, Sam ba ma zaman lafiya, wannan dalili ya sanya ban sheda ma ka ina tare da ita ba, dan kuwa na san tabbas idan ka sani ba lalle ka bari mu zauna a gidan ka ba Malam…..”

Ya dan nisa, ganin irin kallan da Malam ya ke ma sa ne ya sanya shi tsugannawa, dan shi kan sa be taba tsammanin ya iya shirya karya haka ba, ganin hakan shi ne sutura ga Malam da iyalan sa, Usman be gushe ba, ya cigaba da fadin

“Na sama mata haya can kasan unguwa, ta yi gta yi na kawo ta gidan nan, kuma fitinar ta ya sanya na kasa. Hakan ya ke sanya ta haura katanga duk sanda ta so gani na, Ni kuma na nuna mata rashin yiyuwar haka sai dai kawai na gan ta cikin gidan ba dan komai ba sai dan kawai ta tayar min da hankali ta tafi. Kasancewar amana aka ba ni ita babu damar na sake ta, duk da ta nemi hakan daga gare ni, haushin hakan ya sanya ta shan alwashin bata ni a idanun ka Malam, ban taba tunanin za ta aikata wannan tozarcin a gare ni ba, haka kuma wanda ya sauke ta a mota ban da masiya akan shi, ka yafe min…..”

Jin kalaman Usman idan ran Malam yayi dubu ya baci, dan takaici kasa magana yayi, shi kuwa Jauro kallan Usman ya ke cike da mamakin yanda ya iya sharara karya har haka dan kare Zainab. Isa kuwa mamakin rashin adalci irin na Usman ya ke, gani ya ke duk lalacewar da matar shi ta ke shi ya jawo, da kakkausar murya ya ce

“Lalle ka cika azzalumi! Mahainci! Kai Usman ka bani kunya, ka ci amanar aure, domin kuwa wannan halin da matar ka ke ciki kai ne ummul abaisi, da ka killece ta in da kake da duk haka be faru ba, maza irin ku azzulumai ke jawo mana zagi kwarai da gaske”

“Mu dai ko ma wacece ta bude mu ga fuskar ta!”

Cewar wasu daga cikin samarin wanda su har lokacin ba su gamsu da jawabin Usman ba. Cikin nuna bacin rai Usman ya ce

“Mata ta ce, akwai hakkin kare darajar ta, dan haka ba za ta cire nikabin fuskar ta ba, babu mai bude min fuskar ta….”

“Ashe? Shin ka san darajar matar ta ka ka sake ta sakaka har ta fada ga mummunar halaka haka? Na ji takaicin kasancewar ka dalibi a gare ni, na yi danasanin karbar wanda be san darajar mata ba a matsayin dalibi, Allah ya wadar da azzaluman maza irin ka!”

Cewar Malam wanda ya ke maganar a fusace tsabagen yanda zuciyar shi ki radadin danasanin karbar Usman, kallan jama’ar wajen yayi, kana ya ce

“Ina mai neman afuwan hakkin ku da aka shiga ta sanadiyar wannan dalibi nawa, ban da masaniya akan wannan zalunci da ya ke aikatawa wannan baiwar Allah, bare na san da haurawa gida na da take, so dayawa mu kan yi zaton ko dai barayi me ke son hauro min, dan haka ne ma masu gadin gidan su ke har su uku ga su nan, Ashe matar dayan su ce mai aikata barnar, ku yafe mana, zancen sai kun ga fuskar ta be taso ba, shi addinin musulunci ya na san rufin asiri, ya zabi ya rufa asirin iyalin sa, dan haka ku rabu da su kada ku tsanan ta bincike! Ina fatan kowa zai koma gidan sa, Allah ya tashe mu lafiya”

Daga mai cewa

“Amen Malam”

Sai masu

“Amen Allah ya kyauta”

“Amen amman dai ba haka mu ka so ba”

Haka su ka ja jiki, kowa yayi na sa wajan, su Uzairu da har lokacin gani su ke rufa rufa kawai aka mu su, suna tafe cewa su ke

“Yau an rufa, Amma a juri zuwa rafi dai, mu na nan mu na sa ido wallahi”

Zainab ta yi tsuru tsuru da idanu, so ta ke ta shige gida amma ta na tsoran yanda za ta samu ta shige ba tare da Usman ba, gashi dai ya kira ta matar shi.

“Kai kuma Usman daga yau na sallame ka daga aji na, haka kuma kar na kara ganin ka saka kafa a gida na!”

Cewar Malam ya na mai nuna Usman da yatsa, shi kuwa Usman da maganar ta masa bazata kasa cewa komai yayi, dan kuwa dai sam be yi zatan Malam zai yanke hukuncin akan sa haka ba. Ita kuwa Zainab farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta jin Malam ya ce

“Me ka ke jira nan tsugunne? Ka dauki matar ka ku tafi kar na sake ganin ka gida na!”

Shikenan za ta samu ta gudu ba tare da Malam ya san ita kowacece ba, Usman ne ya sa murnar ta ta koma ciki, Wanda batun ya tafi da Zainab ba karamin kaduwa zuciyar shi ta yi ba, A tsorace ya ke kallan Zainab, Fadi ya ke

“Kamin afuwa Malam mu dan kwana, sai mu tafi ido na ganin ido, ina tsoran dare da masifun da ke cikin sa, ba mu san me zai mu tarar a hanya ba!”

Kara tunzura Malam yayi, cikin nuna bacin rai ya ce

“Ka na tsoran dare ka bar iyalin ka ta ke yawan dare?”

“Malam ba wai ina goyan bayan sa ba ne, amma ni ma ina ga zai fi ya bari sai goben, ko dan jama’ar da su ka tara mana kofar gidan nan, babu mamaki akwai wanda su ke nan labe su na jira su taho su ci mutuncin wannan baiwar Allah, ba shi ake ji ba, matar ta sa ake ji”

Isa ne ya saka baki, wanda tausayin matar da Usman ya kira tashi ya mamaye zuciyar sa. Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Malam ya juya, ya na fadin

“Ka ci darajar iyalin ka, amma gari na wayewa ka tattara na ka ya na ka ka bar min gida!”

Ya na tafiya Jauro da Isa biye da shi su ka shige aka bar sa daga shi sai Zainab nan waje, babu wanda ya motsa cikin su bare su tankawa junan su, Isa ne ya kara lekowa tare da fadin

“Malam za ka tsaya nan kuna kallan juna ne mu rufe gida? Allah ya wadar na ka ya lalace! Ilimi dai be yi amfani ba!”

Jin haka sim sim Zainab ta wuce gaba, Usman na biye da ita su ka shiga farfajiyar gidan Malam. Har lokacin Malam be shige cikin gidan ba, mitar tashin hankali da tozarcin da Usman ya ma sa ya ke, Ashe duk wannan lokacin da ake hauro ma sa gida matar Usman ce amma ya na ji yayi shiru.

Karnukan gidan ba su fasa haushi sama sama ba, Amma ganin shigowar Zainab be sa sun harzuka kamar yanda su ka saba ba duk sanda su ka ga baki ba, sai ma zuwa da su ka yi su ka tsaya in da Zainab da Usman ke tsaye. Yanda hasken fitulun gidan ya haske su sosai ya bawa Malam damar kallan ta da kyau, sai a sannan ya lura da yanayin ta, hakan ya sa shi kaguwa ya ga fuskar ta a karo na farko,

“Usman wannan matar ta ka ya sunan ta? Yar wani gari ce? An ya kuwa ban taba ganin ta ba?”

Dam gaban Zainab ya fadi, shi kuwa Usman ganin an shigo gida dama ya rufa asiri ne ba dan komai ba sai dan darajar Malam, shiru yayi kawai ya na duban Malam. Ganin haka Malam ya dube ta ya ce

“Ke bude fuskar ki!”

Zainab na mai girgiza kai ta ke duban Usman cikin neman dauki, shi kuwa Usman ya kawar da kai gefe guda.

“Ba da ke na ke magana! Ki daga wannan nikabin na ce!”

Cewar Malam karo na biyu cikin tsawa domin kuwa hakan nan ya ji gaban sa na faduwa. Zainab ba ta san sanda ta ruko hannun Usman ba, cikin rada ta dada matsawa kusa da shi, karo na farko da ta yi magana kenan tun sanda Mike ya gudu ya bar ta, cewa ta yi

“Dan Allah ka rufa min asiri, dan Allah, dan Allah…….”

“Usman ina so na ga fuskar matar ka! Ka bude min fuskar ta na gani yanzun nan!”

Cewar Malam wanda ganin yanayin da Zainab ta shiga ya kara kyautata zatan shi akan ta na rashin gaskiya, ganin Usman be da niyar motsawa bare ya aikata umarnin Malam ya sanya Malam karasawa gaban su, tare da fadin

“Ko dai ku bude fuskar nan, ko kuma na mika ku ga hukuma a daren nan!”

Jin haka Usman ya tsinci kan sa ya na fadin
“Diyar ka ce Malam, daya daga cikin ‘ya’yan ka……..!”

Kamar takobi haka maganar ta soki zuciyar Malam, hannu ya sa ya yaye nikabin yayinda fuskar diyar sa, diyar ta sa ma wacce ya ke mata mafi kyakkyawan zato ya bayyana gare shi. Kuka ta ke sosai ta na fadin

” Dan Allah dady ka yafe min, dan Allah dadi ka yafe min……sharrin shedan ne”

Malam yayi baya tsabagen firgici sai gashi zai fadi, Jauro da Isa ne su ka yi saurin taro shi, yayinda hawaye bibbiyu ke fita daga idanun sa.

*Khadija Sidi**Auren Shehu

Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 8"