Auren Shehu Book 1 Page 6
*Khadija Sidi*
AUREN SHEHU
6.
Ranar da Malam ya koma gida ya sanarwa Hajja Aleesha maganar auren Zainab da Sudais. Zaune su ke a daki, Ammy ta na yi
Malam wanda ke sanye cikin jallabiya ya gyara zama, sannan ya ce
“Hakkun, ya na ga kin yi jim maganar ta yi mi ki bazata ko? Ki yi hakuri abin ne ya zo ba shiri, kwana uku da su ka wuce Shiekh Ahmad ya zo mun da kyakkyawan labari na gama makarantar Sudais, ya kuma nemi a ba shi auren ?aya daga cikin ‘ya’ya na mata, Ni kuma na masa alkawarin zan ba shi diya ta mafi soyuwa cikin rai na, na tabbata idan na zo mata da maganar za ta karba hannun bibbiyu dan kuwa Yakura ba ta taba yi min musu ba”
Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, kafin daga bisani Ammy ta nisa ta ce
“Allah ya tabbatar da alkhairi Malam, ya nuna mana, Amma zan so ka dena wannan furucin na cewa Yakura ce mafi soyuwa cikin ranka, sauran ‘ya’yan su ka ji ba za su ji dadi ba, na tabbatar ba ma ‘ya’ya na kadai ba, hatta ‘ya’ya Hajja kulu babu wanda za ka zartar da hukunci ya ma ka musu da yardar Allah”
Murmushi Malam yake yayinda ya jawo hannun ta, ya motso da ita kusa da shi, ya ce
“Dadi na da ke adalci Hajja ta, in Sha Allah zan kula da furuci na, Amma kin san cikin ‘ya’ya da iyali dole akwai wanda zai fi shiga ranka, ina alfahari da Yakura ba dan komai ba sai dan halin ta na gari, ga nutsuwa, ga hankali dadin dadawa ga kamun kai, ace yarinya ta gama secondary, ta shiga jami’a ko saurayi ba ta da shi? Ta taba kawo mi ki maganar wani ko kuwa kin ji ta na maganar wani da yan uwan ta?”
Kai Ammy ta girgiza alamar ‘ah ah’
“Kin gani shi ne ai, kunya irin na Yakura ai ba zai iya bari ta tsaya da wani da namiji ba, Allah ya mata albarka, Allah ya sa yan uwan ta su yi koyi da ita”
Ammy ta amsa da ‘amen’
Nan su ka cigaba da hirar yanda za a tsara daurin auren ba tare da bidi’a ba, in da Malam ke da shirin shedawa amaryar abinda ake ciki a washagari.
*****
Washegari bayan sallar la’asar Malam ya nemi ganin su Zainab. A falon shi su ka tarar da shi zaune tare da Ammy. Dukkannin su cikin fargaban dalilin kiran su ke, musammam Halitta wacce ta ke zargin ko dai Zainab ta sake zagayawa ta tuna mata asiri gurin Malam. Zainab kuwa fargaban kar dai Usman ya tona mata asiri. Falmat kuwa tunanin duniyar na ta rasa laifin da za a iya cewa ta yi, Amma hakan be sanya hankalin ta kwanciya ba.
Kamar yanda Malam ya saba duk sanda ya zauna tare da iyalin sa, nasiha ya mu su akan tsoran Allah da yanayin rayuwa, ya kare da kalamin da ya sanya dodon kunan Zainab toshewa
“Alhamdulillah na zabawa Yakura mijin aure, Sudais babban dan aboki na Shiekh Ahmad, mun sanya ranar daurin aure, shabiyu ga watan Juli…..”
Cikin faduwar gaba ba ta san sanda ta dago ta kalli Malam ba, har su ka hada ido, in da ta yi saurin yin kasa da na ta idanun yayinda zuciyar ta ke tafasa kamar ruwan zafi. Halitta da Falmat da su kan su maganar ta zo mu su a bazata idanun su akan Zainab ya ke, in da wani sanyi ya sauka zuciyar Halitta, dan ta tabbata Allah ne ya karbi adduar ta ya kawo hanyar shiriyar yar uwar ta. Malam be gushe ba ya kara da
“Ba komai ya sa na yanke hukunci haka kai tsaye ba, sai dai dan mun san mun Isa da ku, ba ni da haufi a kan ku, Yakura ba ki taba min mu su ba, na san ki da ladabi da biyayya, ina fatan za ki yi na’am da wannan hadi na alkhairi da mu ka kulla, za ki cigaba da zama abin alfahari a gare mu”
Murya can kasa ta na kokarin makale kwallan da ke shirin fara zarya daga idanun ta ta ce
“In Sha Allahu Dady, zan kasance mai biyayya a gare ku a ko da yaushe”
Cikin jindadi duk da ya lura da sauyin yanayin da Zainab ta samu sanadiyar jin furucin auren ta, Malam ya ce
“Allah ya mi ki albarka, yanda ki ka mana Allah ya baki ma su yi mana”
“Amen”
Ta amsa can kasan makogoro. Malam ya kara da
“Ku ma Allah ya mu ku albarka, Allah ya ba ni ikon zaba mu ku mazaje na gari kamar yanda na zaba ma yar uwar ku, bisa sunnah, ku tafi na sallame ku”
Falmat da Halitta su ka amsa da
“Ameeen ameen”
Jiki sanyaye su ka tashi su ka tafi. Zainab kuwa su na shiga bangaran su da gudu ta wuce dakin ta yayinda kuka mai karfi ya kwace mata. A falo Halitta da Falmat su ka zauna jigum, kowa ya na sakar zuciya.
“Ki na ga….”
“Ni a gani na….”
Falmat da Halitta su ka fara magana a tare, gannin haka sai duka su ka sake yin shiru, Halitta ce ta sake fadin
“Ni a gani na wannan aure na Zainab alkhairi ne Falmat, ko ba komai Allah zai kare Daddy daga halin Yakura!”
“Halin Yakura? Me ki ke nufi? Shin Yakura na da wani hali mara kyau da ban sani ba? Har ki ke tunanin zai iya cutar da Daddy?”
Shiru Halitta ta yi cikin wasiwasi da auna fadawa Falmat ko kuwa rashin fada mata a mizani, dan kuwa ko Instagram Falmat ba ta yi bare a ce ta san account din Zainab, ita dai a bar ta da WhatsApp din ta da Facebook.
“Ke na ke sauraro Halitta, kin yi shiru?”
Kai Halitta ta girgiza sannan ta ce
“Kar ki damu ba wani hali ba ne, kawai kin san yanayin Yakura da rawan kan ta ne sai a hankali”
Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ce
“Kai har kin sa hankali na ya tashi, ki na gani hukuncin da Dady ya yanke be yi tsauri ba? Ina ma laifi ya tambaye ta ko ta na da manemi, idan ta ce babu ne sai ya bawa dan abokin na sa dama ya dan zo su gana su kuma fahimci juna, idan mai yiyuwa ne sai a kai ga maganar auren, ba hakan nan tashi guda kamar yankar wuka ba, sai ka ce a zamanin da!”
Ta kare maganar cikin nuna rashin jin dadi.
“Etoh kin yi gaskiya, Amma dai a musulunce iyaye ke da alhakin zabarwa ‘ya’ya mata mazaje a auren su na fari, kuma dai kin san Dady ba zai cutar da mu ba”
“Eh ba zai cutar da mu ba, but at least ya kamata ya duba lamarin nan, wallahi na ji tausayin Yakura, haba mana, yanzu idan ke ce aka yiwa haka Allah kadai ya san halin da za ki shiga”
“Zan damu na sani, Amma zan yi tawassali na auri duk wanda Dady ya zaba min, na mi ki wannan alkawarin Falmat”
Ta fada cikin jaddawa
“Toh kuwa ni dai ba zan iya ba wallahi, haba mana ai an sami cigaba, Sudais din da ko ganin shi ba mu taba yi ba, kawai a ce wani za a aura mata shi, gaskiya ba a kyautawa Yakura ba!”
Cewar falmata ta na mai kara nuna bacin ran ta, ita kuwa Halitta ta shi ta yi, kana ta ce
“Hajiya Falmat ai sai ki je ki fadawa Dady kin ji uwar Yakura? Ni dai na yi gaba, ko a tafin kafa ta”
“Wallahi ba dan kar na mi ki fata ba da na ce Allah ya sa Dady ya canza da ke Halitta yanda ki ke son Usman din nan na ki sai mu ga yanda za ki yi!”
Cikin nuna ko in kula ta ce
“Ai Allah na duba izuwa zuciyoyin mu ne, Allah ya sani ba dan komai na goyi bayan wannan aure na Yakura ba, sai dai dan ina gani shi ne mafi alkhairi ga rayuwar mu duka, Allah dai ya sa mu dace”
Ta na gama magana ta wuce ciki inda Falmat ta bi ta da kallo cike da mamakin lafuzzan ta, da kuma halin ko in kula da ta ke nunawa akan tashin hankalin da yar uwar su ke ciki.
Zainab kuwa kuka ta ci ta koshi, tuni manyan idanun ta su ka kumbura su ka yi rubu rubu. Cikin wannan hali Ammy ta zo ta same ta, ganin yanda ta fita daga hayyacin ta ya sa Ammy salati ta na mai tafa hannu ta ce
“Yanzu duk yabon nan na ki da Malam ya ke akan ladabi da biyayya ashe ke kina nan kina kuka kamar wacce aka turowa da sakon mutuwa? Menene dalilin wannan kuka haka Yakura?”
Cikin shassheka Zainab ta ce
“Ammy ya ma Dady zai min haka dan Allah, ya Dady zai saka min ranar aure da wanda tun da na zo duniya ban taba ganin shi ba Ammy, ban san halin shi ba, be san hali na ba, be san ya na ke ba, ban san ya yake ba, tashi guda ku hada mu rayuwar aure Ammy…..”
Ta karasa cikin kuka. Jiki sanyaye Ammy ta zauna kusa da ita, har ga Allah ta ji sanyi a cikin ran ta jin Zainab ba ta furta ta na da wanda su ke soyayya ba, kenan hashashen Malam akan Zainab gaskiya ne, ba ta da wani saurayi, dan kuwa shi ne babban fargaban Ammy, dan ta san rabuwa da masoyi abu ne mai wuya matuka. Ta na mai kamo hannun ta tace
“Ki yi hakuri Yakura, ki sani da nufin alkhairi Malam ya ke so ya kulla wannan dangantakar, ki tuna ba ke kadai ba ce diyar shi, ba kuma mu kadai ba ne iyalan sa, Amma ya tsallake kowa ya zabe ki, ba dan komai sai dan ganin kin fi kowa cancan ta, kuma ya isa da ke…..”
Nan ta cigaba da bata baki, amma ta inda ya ke shiganta nan take ya ke fita, sai da ta bari Ammy ta gama jawaban ta kaf sanan ta ce
“Ammy duka na ji, na yarda kuma na gode, Amma Allah na gani ba na san auren nan, dan Allah ki saka baki Dady ya fasa”
A fusace Ammy ta tashi, cikin nuna fushi ta ke nuna ta da dan yatsa, ta ce
“Ba zan saka baki ba Yakura, idan kin isa yar halak, Ni Aleesha ni na haife ki toh kuwa kar na kara ji kin yi musu akan maganar auren nan ba!”
Ta juya ta fice a fusace, hakan ba karamin tunzura zuciyar Zainab yayi ba, Nan ta fara wani saban kukan. Kuka ta yi mai isar ta, har magrib ta yi. Da kyar ta iya tashi ta yi sallah. Ta na idarwa ta fara neman number sabon saurayin ta Mike, amma ba ya shiga, sai ta tura masa sako kamar haka
“Hello Mike, I need you, I need to talk to you it’s an emergency, call me ASAP”
Ta na tura masa ta aje wayar gefe in da ta kara haurawa gado ta kwanta, tsabagen ta yi kukan mai isar ta sam sai ta nemi kukan ta rasa, sai ajiyar zuci. Sau biyu Falmat da Yakura su na lekowa dan su kira ta su ci abinci, Amma ta ki kula su bare ma ta tashi ta fito su ci abinci, har Ammy ta yi fushi ta ce kada wanda ya sake kiran ta, su bar ta ai yunwa ba kanin uban kowa ba ne.
Wajan karfe goman dare har fitar da ran Mike zai kira ta, sai ga Kiran shi. Hannun ta na rawa ta daga, Amma ta kasa magana sai kuka, yayi juyin duniyar nan ta masa bayanin abun da ke faruwa amma ina sai kuka kawai. Har ya gaji ya aje wayar.
Bayan minti arbain ya sake kiran ta, ta na dagawa ya ce
“Ina waje, come out”
Murya dashe tsabagen kuka ta furta
“Mike….I can’t, Dady ya na nan”
“I don’t care, just come out, bazan iya jure kukan ki ba Zeee, kin daga min hankali, I need to see you right now!”
Shiru ta yi ta na tunanin yanda za a yi fita, daga bisani ta nisa ta ce
“Ka koma gefen gidan mu, ta side din da bishiyoyi su ka yi yawa, zan hauro yanzu”
“Alright babe, ina jiran ki”
Cewar Mike yayinda ya aje wayar yana mai kokarin yin ribus ya koma in da ta kwatanta masa.
A gurguje ta shiga bandaki ta wanke fuska, kayan jikin ta ta sauya, ta sanya shudin riga mai haske tare da shudin wando wanda ya kamata sosai ya bi jikin ta. Hijabi ta jawo yanda ta saba ta sanya har kasa, har ta kai kofa ta dawo ta dauki nikabin ta ta saka, wayar ta kawai ta dauka, takalmi a hannu ta zaga ta bayan dakin su, ta na jiyo muryar su Falmat a parlour ko tsoran kar su kamata ba ta ji ba tsabagen yau zuciyar a dake ta ke, kai tsaye garden ta wuce.
Da ya ke yau Malam ya na nan, Usman na can wajan shi suna daukar karatu bare ma su hadu yanda aka saba, dan haka ta sami damar taka wani rashe na bishiya da ya mata tsani zuwa katanga, da ke sababbiya ce tuni ta haura, da taimakon Mike, hannun sa bisa kugun ta ya dire ta kasa. Ya na dire ta ya rungume cikin rarrashi ya ke fadin
“Oh my baby, me ya faru?”
Cikin tashi hankali ta ke waige waige gudun idanun jama’a duk da dai wajan akwai duhu amma dare be yi sosai ba, mutane na dan wucewa ta ce
“Mike let’s just get out of here”
Hanun ta cikin na shi da sauri ya bude mata gaban mota, sai da ta zauna ya rufe motar sannan ya zaga da sauri shi ma ya shiga motar, hannun ta ya kara rukewa yayinda ya tashi motar. Duk wannab abun da su ke yi akan idan wani dan saurayi matashi da ya zo wucewa ta layin. Cike da mamaki ya ke jinjina kai, wato dai rade radin da ake a unguwa na ana daukar wata a cikin bakar mota daga gidan Malam gaskiya ne, yau ya ga zahiri dan kuwa akan idan shi Miki ya riko kugun Zainab ya dire ta kasa, kuma ya rungume ta. Jiki na rawa yayi gaba zuwa majalisa domin ya kunsawa abokan sa abin da ya gani.
Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 6"