Auren Shehu Book 1 Page 5
AUREN SHEHU
5.
Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta saki, ta na mai duban Halitta murya kasa kasa ta ce
“daga ina na ke kuwa? Dage exercise mana!
”
“Exercise din tun karfe 4:45 na dare Yakura? Ki ji tsoran Allah! Ammy ta turo ni tashin ki sallah Yakura, na san ba gidan nan ki ka kwana ba, daga ina ki ke?”
Halitta ta kara tambaya ta na mai tsare ta da idanu.
“Daga yawon ta zubar na ke ko da yanda za ki iya ne? Ki na da abin yi ne? Kuma Allah ya mana katangar karfe da saidawa!”
Kafin Halitta ta bata amsa ta yi saurin kwasar takalman ta, ta yi wuf ta shige dakin ta. Jim ta yi ta na maimaita kalaman Zainab cikin ran ta
“Daga yawon ta zubar na ke……”
Ta kara maimaita.
“Shin anya kuwa shirun nan da na ke akan abin da Yakura ta ke yi Allah ba zai tambaye ni ba? Ko dai Ammy zan fadawa? Ko da ya ke in har na fadawa Ammy kamar na fadawa Dady ne, Allah kadai ya san halin da Dady zai shiga muddin ya sani, Allah ka ga zuciya ta, Allah ka mana magani”
Kitchen ta wuce, ganin Iya har lokacin ba ta fito ba sai ta wuce dakin Iya domin ta ga ko lafiya.
Zainab kuwa ta na shiga bandaki ta shige ta yi wanka, fitowar ta daga wanka ta tarar Ammy tsaye tsakar dakin, abin ku da mara gaskiya sai da zuciyar ta ta dan yi rawa. Ta na kame kame ta ce
“Ammy, aw ashe ke ce”
“Ni ce jiki yayi sauki kenan, ai na turo Halitta ta tashe ki sallah da asuba….”
“Eh mun hadu ai”
Ta yi saurin katse ta. Kallon ta Ammy ta ke kamar mai nazari, kafin daga bisani ta ce
“Me ki ke cewa ne? Kamar yaya kun hadu?”
Zainab na mai sosa kyeya ta ce
“Ah ah ina nufin na gan ta, da ta zo tashi na, eh ta tashe ni din”
“Oh toh, Ni ce min ta yi ba ta gan ki ba, ta na tunanin kin tashi tuni har kin shiga toilet”
“Eh ai ina toilet din na jiyo shigowar ta, haka na ke nufi Ammy”
Kai Ammy ta gyada, sa’annan ta kara da
“Ya ciwon kai?”
“Ciwon kai? Aw Alhamdulillah na sami sauki, Ina kwana Ammy?”
Cewar Zainab yayin da ta zauna bakin gado, Allah Allah ta ke Ammy ta fita ko ta samu gaban ta ya bar faduwa.
“Lafiya lau Alhamdulillah, ashe ba mu gaisa ba, Allah ya kara sauki, sai ki yi maza ki fito mu karya ko?
“Wallahi Ammy ba zan iya cin abinci yanzu ba, wani irin bacci na ke ji, rabona da bacci tun jiya da safe, kin san bacci ba a cin bashin sa ”
Ta na mai duban ta cikin nazari ta ce
“Wannan baccin na ki kuwa anya Yakura? Me ya hana ki bacci? Nan fa na shigo na tarar ki na ta bacci?”
“Ah ah, wai ina nufin ban yi ishasshe ba, ina yi ina tashi saboda ciwan kai”
“Toh Allah ya sauke, ki daure dai ki ci wani abu kafin ki kwanta”
Zainab ta amsa mata da toh, dan dai kuwa ba ta da buri da ya wuce Ammy ta fita ta samu ta ji hakarkarin ta bisa katifa. Illai kuwa ta na fita ko mai ba ta iya shafawa, ta dauko wata yar riga iya gwiwa ta sanya, ba batun sallar asubahi ta bi lafiyan gado abin ta. Nan da nan bacci ya dauke ta.
***
Haka rayuwa ta cigaba da gudana. Zainab ta kasa hakura da club ta bari sai ta koma makaranta kamar yanda ta saba, saboda sabon saurayin ta Mike, shi ne ke zuwa daukar ta ya dawo da ita.
Ba komai ne ya bata lasisin wannan shagalin na ta ba face shawarar Mike da ta bi na siye daya daga cikin masu gadin gidan. Cikin masu gadin uku ta san Isa da tsattsauran ra’ayi ko da wasa ba zai amince da ita ba, Usman kuwa shi tsoran sa ma ta ke ji, dan haka sai ta kama Jauro ta rike gam. A kulli yaumin ta kan tabbatar ta masa alkhari na safe daban na yamma da daban, ta haka ta samo hanyar shawo kan sa. Ta masa karyar cewa akwai kungiyar bitan karatu da su ka hada ne ita da yan makarantar su da ke zaune Kano, kafin su koma makaranta, Amma da daddare ake yi, ta na tsoran kar ta fadawa su Ammy ne su hana ta gabadaya, shi ya sa ta yanke hukuncin ta na bi ta bayan kasa, har su koma makaranta.
Duk da Jauro ya san maganar Zainab yashesshen zance ne, da ke ido a kabo ne da ta bashi sai ya sa hannu ya karfe, idan dare yayi sai ya tabbatar Usman da Isa ba sa kusa sai ya bude mata kofa, haka idan ta dawo shi ne ke bude mata.
Duk wannan hidimar da ya ke yi akan idanun Usman, tun ya na ?auke kai har ya gaji wata ranar Juma’a da yamma, ana saura sati daya Malam ya dawo Usman ya sami Jauro kishingide karkashin bishiya ya na shan rake, dan kuwa tunda Zainab ta fara bashi kudi kullum cikin kudi ya ke.
Sallama ya masa tare da zama kusa da shi. Tayin rake Jauro ya masa bayan ya amsa sallamar. Usman na mai godiya, cikin maganar sa mai cike da nutsuwa, yanayin yanda ya ke fito da kalmomin hausa daga bakin sa ne ki kara jaddada kasancewar sa na kabilar fulani, ya ce
“Alhamdulillah, na gode Jauro ka sha raken ka, dama akwai yar magana da na ke so mu yi da kai”
“Toh Madallah dan cirani, da me ka zo”
Cewar Jauro bai fasa shan raken sa ba. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Usman ya ce
“Ka yi hakuri zan ma ka shisshigi, wala’alla za ka fahimce ni”
Jauro na mai fuzar da totuwar rake daga bakin sa ya ce
“Uhum, ina sauraron ka.
“Zancen fitar dare da Bingel din nan ke yi, diyar wajan Malam”
Cikin halin ko in kula Jauro ya ce
“Uhum? Menene na ka a ciki?”
“Akwai, Malam ya ba mu gadin gidan sa bisa amana, ni da na ke gani ina dauke kai ba tare da fadawa mahaifan ta ba, ina da alhaki, bare kai kuma da ka ke ba da gudunmawa Jauro!”
Jauro na mai tashi zaune ya ce
“oho! Ashe dai ka na gani, kuma ka san ka na da alhaki! Tun da ka ke gani ba ka san ka na da alhaki ba sai yanzu da ka ga ina dan samu ko fillo? Ni za ka yiwa halin na ku na fulanin daji ko? Dan bakin ciki!”
Usman na mai dafe kai ya ce
“Ya ilahi! Ba ka fahimce ni ba Jauro! Ba dan komai ya sa ban iya fuskantar Malam akan wannan batun ba sai dai dan kunya da nauyin sa da na ke ji! Da wani ido ko baki zan iya kallan Malam na ce masa diyar sa na haura katanga? Ko kuma duk dare ana zuwa ana daukar ta? A dawo da ita da safe?”
“Dan sa ido! Da Idon da bakin da ka zo ka tinkare ni yanzu mana! Yarinya na fita bitar digiri(Degree) din da ta ke yi a jami’a, ko da yake kai fa ko zo na kashe ka da turanci ba ka sani ba bare ka san kalmar Degree! Kai Allah dai ya raba mu da jahilci!”
Duk zuciya irin na Usman sai ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa, ka na ya ce
“Ban da cin fuska mana Malam Jauro, na zaci za mu iya samin fahimtar juna shi ya sa ma na tunkare ka da maganar, amma tun da abin haka ne, Allah ya ba ka hakuri!”
“Ni kuma na taimaka da Aameen! Eh amen, kuma Allah ya raba mu da munafukai da yan bakin ciki”
Usman na murmushi ya amsa da amen, tashi yayi tare da yiwa Jauro sallama duk da dai be ji dadin yanda Jauro ya kasa fahimtar ta shi, sam be ruke shi a rai ba, shi dai fatan sa Allah ya bashi ikon kawo karshen wannan masifar da ke faruwa gidan Malam, duk da kamar yanda Jauro ya fada be san “digiri” ba, Amma koma menene wannan digirin in dai haka ake yin sa toh lalle ba alkhairi ba ne.
***
In da Usman ke kokarin neman mafita akan iftilakin da ke faruwa gidan Malam, ita kuma Halita soyayyar Usman ce ta sami wajan zama cikin zuciyar ta. Zaune su ke a falo, sun gama cin abinci kenan su ka zauna zaman hira. Falmat sanye da atamfa koriya dinkin doguwar riga, Halita kuwa kananan kaya ne cikin ta, riga da sikit jajaye, kanta daure da jan mayafi.
“Ni kuwa Halitta ina mamakin yanda ki ke kaunar Usman din nan, dan kuwa dai sai dai na kira shi kauna dan ya fi karfin so”
Cewar Falmat yayinda yanayin fuskar ta ke gasgata lafazan ta. Sanyayyar ajiyar zuciya Halitta ta saki kafin ta ce
“Daga Allah ne Falmat, Ni dai kawai ki taya ni addua”
“Toh zan taya ki, Amma duk randa Ammy ta san Usman ki ke so Halitta, I mean not just Usman o, but Maigadin gidan nan wallahi akwai kura….”
“Shhhhh”
Halitta ta katse ta, ta na mai kasa da murya ta ce
“Ke fa matsala ta da ke Falmat handsfree! Ki rufa min asiri kar Yakura ta ji…..”
“Ji kuma na nawa?”
Da sauri su ka juya su na kallon ta, ba wanda ya san da shigowar ta bare ya san adadin mintunan da ta yi tsaye ta na sauraran su. Sanye ta ke cikin bakin material, doguwar riga ta yi daurin nan da ake Kira tura ka tsiya. Idanun ta kan Halitta wacce har ga Allah ba ta so maganar ya je kunnan ta ba ta ce
“Yanzu ke Halitta ki rasa wanda za ki so sai wannan Maigadin? Yo to menene abin so a wannan kazamin bafulatanin hammata fal gashi?”
In da Halitta ta fusata, ita kuwa Falmat mamakin yanda aka yi Zainab ta ga hammatar, ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba, wanda hakan ba karamin tunzura Halitta yayi ba. Yakura ba ta gushe ba ta kara
“Ke anya kuwa bakin wannan ya san brush? As in kafin na so mutum I first imagine things people do when they’re in love, as in can you imagine yourself with him? Like imagine kissing wannan dagageggen bakin na shi?”
“Wayyo Allah Ammy!”
Falmat ce ta saka ihu ta na mai dariyar mugunta, ita kuwa Halitta iya kulewa ta kule. A fusace ta ce
“Malama ina ruwan ki? Kin manta ba kiss ba! Abin da ya fi kiss! Idan ma auren shi na ce zan yi ina ruwan ki!”
Ta na mai daga hannu sama yayinda ta zagaya ta shigo falon sosai, kujerar da ke kusa da Falmat ta zauna, sannan ta ce
“Babu fa, babu ruwa na ko kadan, aw kin san abin da ya fi kiss ashe, yo ai na zaci uztazanci ya hana ki sani, Sha it’s your life, Bari na ja baki na!”
“Alhamdulillah tunda kin san haka, da fatan za ki yi aiki da shi….”
“Ke fa ba kunya gare ki ba Halitta!”
Zainab ta katse ta cikin tsawa, ta kara da
“Kar ki ga kin yi tsayin kafa wallahi ina iya doke ki, mara kunya fitsararriya”
“Toh sarkin tsiwa! Tun daga daki na ke jiyo hayanoyar ku! Anya kuwa Yakura? Ke da waye kuma?”
Ammy ce wacce ihun Falmat ya sanya ta fito da sauri ta ke tambaya.
“Babu komai Ammy”
Halitta ta fada gudun kar Yakura ta mata tunan asiri, ilekuwa sai cewa ta yi
“Da komai fa Ammy, ai dai gaban ki yarinyar nan ta gama azazzabi da rawan jiki wajan jaddada bayani akan wannan dan bokon haram din, toh dai ruwa ba ya tsami banza, ga shi nan na ji tana managanar son shi ya kamata…”
Ta karasa maganar ta na yar dariya tare da girgiza kai. Daga Falmat har Halitta mutuwar zaune su ka yi, sun san Zainab da barin zance amma ba su taba zatan za ta tonawa Halitta asiri hakan nan kara zube ba.
Ammy na dariyar yake ta ce
“Ke kuwa Yakura ba dai zolaya ba, ina Halitta ina kula wani da namiji? Har kuma ki ce Maigadi? No wonder na jiyo ku tun daga daki, ah ah ni ma ban goyi bayan wannan wasan ba!”
“Atoh Ammy ke dai kya fada”
Cewar Falmat ta na mai fatan rufe asirin Halitta. Zainab kuwa ba ta damu da irin sakon da Halitta ke aika mata ta ido ba, sake cewa ta yi
“Wallahi Ammy ba wasa na ke ba, Halitta soyayya ta ke da Maigadin gidan nan”
“Lailaha ilallahu Muhammad a rasulillahi!”
Cewar Ammy ta na mai tafa hannu cikin tashin hankali ta ke duban Halitta wacce ita ma din kallo daya za ka mata ka tabbatar da damuwan da ta shiga.
“Halitta me na ke ji haka? Wannan wani irin mummunar labari na ke ji Halitta? Duka tarbiya, kulawa da soyayyar da mu ke baki abin da za ki saka mana da shi kenan Halitta?”
Tuni hawaye ya shiga fita daga idanun Halitta, ta na girgiza kai ta ke fadin
“Ah ah Ammy, wallahi ba haka ba ne Ammy….”
Cikin bambami Ammy ta ce
“Ba haka ba ne uban ki ne? Yi min shiru! Wallahi kin ba ni kunya kin yi asara Halitta! Yanzu idan Malam ya ji wannan tozarcin da cin amana ya ki ke tunanin zai ji. Dama aka ce tsintacciyar mage ba ta mage! Hakan nan mutum daga sama ya zo gidan ka ka karbe shi har da bashi wajan kwana, gashi nan zai masa sakayya ta hanyar hure ma diyar sa kunne ai! Toh kuwa zaman shi a gidan nan ya zo karshe”
Jin Ammy na batun zai bar gidan wani dadi ne ya mamaye Zainab, dan kuwa burin ta ke nan.
“Atoh ai tun da na fara ganin sa na san ba za a wanye lafiya ba, na yi magana a ce na fiya kyaman yan kauye, ga dai irin ta nan!”
Cewar Zainab ta na mai daga kafada tare da saukewa. Falmat ce ta saka baki ta ce
“Ammy ba ki fahimta ba, wallahi ba haka ba ne, shi wannan bawan Allah sam be ma san da Halitta ba, bare ma ya hure mata kunne, ba soyayya su ke ba, kawai dai Halitta na yawan maganar sa ne ya sa ke tsokanar ta da shi, Amma babu komai tsakanin su Ammy!”
“Ki ji wani yashesahen zance idan babu rami me ya kawo rami?”
Ammy ta tambaya a fusace, in da Zainab ta taya ta da atoh. Halitta kuwa ta ma kasa magana sai hawayen takaici da ge gangarowa daga idanun ta.
“Allah Ammy gaskiya na ke fada mi ki, in kuma ya kama a kira shi ne ki tambaye shi ki kira shi Ammy”
Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, Zainab sai adduar Allah ya sa kar Ammy ta yarda da zancen Falmat ta ke cikin zuciyar ta. Jin abin da Ammy ke fadi ne ya sanya ran Zainab yin baki. Tana mai ajiyar zuci ta ke fadin
“Toh ni fa in ce, jinina ba za ta taba san Maigadi mara asali ba, haba har na dan ji sanyi cikin rai na, toh wallahi kar na sake jin maganar nan ko da wasa!”
Ta na mai duban Halitta ta kara da
“Ke kuma Halitta na kara jin maganar Maigadin nan bakin ki sai na sabar mi ki”
Kai Halitta ta gyada kafin ta tashi ta fice da ga falon, dan kuwa gani ta ke muddin ta cigaba da zama zafin rai zai sa ta iya tonawa Zainab asiri akan yawan daren da ta ke, ita kuwa ba ta so ta biye mata garin ramuwar gayya su jawa mahaifiyar su matsalar hawan jini.
Ta na jiyo Zainab na cigaba da sukar zaman Usaman a gidan. Ita kuwa Falmat mamakin yanda Zainab ta hakikance ta na bata Usman da karya da gaskiya wajan Ammy, har ta kai ga ta na tunanin shin me ya taba hada su ta ke masa wannan tsana haka?
Duk yanda ta so a kori Usman a gidan, ranar ha?on ta ya kasa cimma ruwa, duk da dai ta ci nasarar tusawa Ammy kiyayyar sa cikin zuciyar ta, ko ba komai yau da gobe in dai Ammy ta tsane shi tabbas sai zaman gidan ya gagare shi. Ta sha alwashin sai ta san yanda za ta yi ta sa Malam ya kori Usman daga gidan.
****
Ana sauran kwana biyu Malam ya dawo Kano, haka kuma wata daya ya rage a fara azumin watan ramadan, bayan sun idar da sallar isha’i gidan Malam da ke Maiduguri, Malam ya karbi bakwancin aminin shi, Shiek Ahmad Suraj.
Kamar yanda Malam ya ke babban Malami haka ma Shiek Ahmad ya ke sananne a cikin garin Maiduguri, ba dan malamtakan sa kadai ba, har dama tarin dukiya da Allah ya ba shi. Duk da dai shi asalin sa dan Chad ne. Ba karamin farin ciki masa tarba na ban girma kamar yanda ya saba masa duk sanda ya zo.
Babban Falon Malam su ke zaune, falo ne ya kayatu kwaran gaske. Bayan sun gaisa tare da hirar bayan saduwa, Shiek Ahmad ya ce
“Ya Shiek dan wajan ka Sudais fa ya hada karatu, mu na sa ran dawowar shi gida Nigeria farkon shauwal da an kammala azumi”
Malam na mai washe baki ya furta
“Toh Alhamdulillah, ka ce Sudais ya zama cikakken likita, kuma mahaddaci wannan labari abin alfahari ne, Allah ya masa albarka, ya albarkaci ilimin da aka samu, ya sa a yi aiki da shi, ya kawo abokiyar rayuwa ta gari”
“Allahumma amen, abokiyar zaman kuwa Ya Shiek gidan ka na ke so a samu, dan kuwa sami ‘ya’ya masu tarbiya irin ‘ya’yan ka mata sai an duba akaramallah”
Cewar Shiek Ahmad wanda ke maganar har cikin ran sa da zuciya daya. Hakan ya sanya farin ciki bayyana a fuskar Malam, idanun sa har sheki su ke, ya na mai ruko hannun Shiek Ahmad ya ce
“Jazakallahu khair, jazakallahu khair, jazakallahu bi jannah da wannan sheda ta ka Shiek, Ni kuwa na maka alkawarin bawa Sudais diya ta mafi soyuwa a rai na, cikin su tafi kuwa nutsuwa, ga ladabi da biyayya, ga rukon addini, ga kunya, ga…ga…ga….sai Zainab! Ta na aji uku a matakin karatun jami’a, in da take karantar Microbiology anan American university of nigeria da ke Yola”
Cikin gamsuwa da jin dadi Shiek Ahmad ya ce
“Madallah da wannan diya da ta sami shaida mafi daraja daga wajan mahaifin ta, muna so”
Malam na mai murmushi ya ce
“An ba ku”
Hannun Malam Shiek ya rike cikin musabaha ya ce
“Mun karba, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, in Sha Allah da yaron nan ya dawo sai a turo a sa ranar daurin auren ko?”
“Su waye za su saka rana da ya wuce mu? Ai kawai tsaya ka gani ya Shiek”
Malam ya dauko calendar ya na dubawa, ranar Juma’a ya zagaye wanda ya kama shabiyu ga watan juli Malam ya ce
“Ga rana nan duba ka ga, idan har ya maka, sai mu yi fatan Allah ya kai mu da rai da lafiya”
Shiek Ahmad na duba calendar da Malam ya nuna masa ya ce
“Hamdan ya yi Ya Shiek, Allah ya nuna mana da rai da lafiya”
Malam ya amsa da Allahumma amen.
AUREN SHEHU
Biyu
***
Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce
“Falmat na yarda da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama..”
Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin
“Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?”
Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta
“Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na ?an gan shi…”
Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da
“Haba mana yar ?anwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so”
Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce
“Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta…”
“Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba”
Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta ?auko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya.
Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa’a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya.
Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki
“Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa’ar ki da sai na tsawatar masa!”
“Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima………..”
“Hajiyoyi za a fita ne?”
Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa.
“Eh sannun ku da aiki”
Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke ?auke da fara’a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa.
“Toh Allah ya dawo da ku lafiya”
Ya fada sa’ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara’ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin
“Amen Isa, godiya mu ke”
Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin
“Ina ruwan Falmat, ‘ya’yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba”
Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta
“Isa ina da wata tambaya domin Allah”
“Ina jin ka”
Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki.
“Shin Malam ya na da ‘ya’ya mata da yawa ne,?”
“‘ya’yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami’ar kwana ta ke ai”
Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga.
‘ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?’
Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam.
Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa’a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki.
Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta.
Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando “bump short”, da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta
“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?”
Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta.
“Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?”
“Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji….?”
“It’s not meant for Daddy’s view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?”
Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da
“Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske….”
“Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah”
Halitta ta katse ta. Komawa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce
“An yi rashin sa’a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?”
Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce
“Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?”
Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce
“Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It’s my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I’m the person I chose to be, I don’t use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!”
Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce
“Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!”
Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce
“Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da ‘ya’ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?……”
“Get out of my room! Ba na bukatar wa’azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!”
Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce
“Ba zan fasa mi ki wa’azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki”
“Mtswww”
Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri.
*Khadija Sidi
Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 5"