Auren Shehu Book 1 Page 4
AUREN SHEHU
4.
Jin kalmar “Boko Haram” jiki na rawa Bobo ya figi motar ya na mai tayar da kura, fadi ya ke
“How? Ya aka yi ki ka san dan Boko Haram ne?”
Karar yanda Bobo ya figi motar ne ya sanya su Isa da Jauro fitowa a guje suna fadin
“Su waye nan! A tare! A tare!”
Ina sai sahun tayar motor Bobo su ka gani, idan shi kan shi Usman da ke tsaye kamar mutum mutumi Jauro ya ce
“Yo kai ?an cirani kana nan tsaye ashe, me ke faruwa ne?”
Isa ya kara da
“Wacce mota ce ta tashi a guje yanzu? Su waye?”
Maimakon ya ba su amsa, sai ya juya abin sa yayi ciki, suna tafe bayan sa, su ka koma ciki, daki yayi wucewar sa ba tare da ya tanka mu su ba.
Isa da Jauro su ka tsaya jugum jugum suna duban juna, Jauro ne ya gyara tsayuwa ya ce
“Ina Isa? Ni fa Allah na gani ban yarda da wancan dan ciranin ba! Ga fa karar tashin motar da mu ka ji! Mu ka tashi mu ka ga gidan nan bude, shi kuma mu ka taras waje tsaye kamar gunki, Anya kuwa Isa?”
Isa wanda kamar Jauro ya shiga ransa, ya dan yi ta maza ya dake, ya na mai yamutsa fuska ya ce
“Anya kuwa me?”
“Anya kuwa lafiyayyan mutum ne?”
Jauro ya fada cike da damuwa.
“Ka gan shi da wata rashin lafiya ne?”
Cewar Isa cikin dakiya dan ya san in da Jauro ya dosa. Jauro na mai girgiza kai ya sake cewa
“Ka san abin da na ke nufi Isa, dan kuwa na san kai ma zuciyar ka ta yi rawa akan lamarin Usman…..”
“Na raba ka Jauro, na raba ka! Kar ka manta Malam ya karantar da mu akan zato, ya ce zato zunubi ne ko da kowa ya kasance gaskiya, Ni ka ga tafiya ta kunto karnukan nan, da bacci be dauke mu ba ai duk da ba haka ba!”
Isa ya tafi ya na mita, Amma cikin ransa tunanin da Jauro ya ke shi ma din shi ya addabi zuciyar sa.
Usman kuwa can lambu ya shige in da ya saba raba dare, wata yar doguwar kujera ta hutawa ya samu yayi kwance idanun sa na kallan sararin samaniya. Kamanin Zainab ke masa gizo, haka kuma kan sa ya dada kullewa akan lamarin ta,
“Shin ita wannan diyar Malam din ina za ta je da tsohon daren nan? Shin mahaifiyarta ta san da fitar ta? Shi wannan da ya ?auke ta a bakar mota mai bakin gilashi wanene shi?’
Tambayoyin da ya ke yi cikin ran sa ke, wanda ya kagu ya samu amsar su.
Ita kuwa Zainab tun da su ka tafi Bobo ke tambayar ta ya aka yi ta san mutumin nan dan boko haram ne? Wanene shi? Sai da ta nutsu sannan ta iya amsa masa da
“Daya daga cikin daliban Dady ne, kuma ya na mana gadi, haka kawai jinina be hadu da shi ba wallahi, ka ga jiya ma shi ya kama ni, gashi yau ma an kuma! Allah dai ya tushe bakin sa….”
“Wa ya ce mi ki dan boko haram ne?”
Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.
“Haaaaa’a! Are you even listening?”
Zainab ta fada cike da tsiwa, ba ta gushe ba ta kara da
“Dallah waye zai yarda dan boko haram ya zauna gidan su? Na ce da kai dalibin Dady ne!”
“Toh Zeeee ke ce na ji kin kira shi da boko haram…..”
“Saboda ya na min kama da su ba! Ba wai ina nufin shi din ba ne, ko da ya ke it’s possible shi din ne tunda ba wai kwakkwarar bincike aka yi ba….”
Ta fada ta na kallan Bobo wanda ya fara hada zufa. Dariya ne ya kwace mata, ta ce
“Sai shegen tsora, dallah wasa na ke ma”
Bobo na mai goge zufa da hankaci ya ce
“Ai dai mutanan ne abun tsoro, Allah ya mana tsari da su, mugu be da kama Zee”
Cikin faduwar gaba yayin da kamannin Usman su ka bayyana a zuciyar ta, ya fito mata sak a kamannin mugu, ta na mai saurin kawar da tunanin ta ce
“Amen, Allah ya min tsari da shi!”
“Wa fa?”
“Dan Boko haram mana, Maigadin gidan mu!”
Ta fada kai tsaye.
“Ki ka ce ba dan boko haram ba ne?”
Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.
“Aaaarrrrghhhh Bobo don’t spoil my mood!”
Ta fada cikin tsawa. Hannun ya daka tare da fadin
“Allah ya baki hakuri Zeee Mama!”
“Ba Allah ya ba ni hakuri ba, you better take me to a nice club!”
“I got you, kafin nan bari na baki sauti mai dadi”
Cewar Bobo yayinda kunna waka ya na mai kure karar.
Ranar club yayi ma Zainab dadi, ta hadu da sabon saurayi wanda tare su ka cashe a daren ranar har ta shagala da lokaci, dan kuwa dai ba ita ta ankara ba sai da shida ta wuce. A kidime ta azalzali Bobo wanda ta janyo shi tsakiyar kedaru su na cashewa. Sabon saurayin da ya Kira kan sa Mike ne ya nuna dacewar ya aje ta gida, hakan ba karamin dadi yayiwa Bobo ba, amma Zainab ta hana, ta dai ce ya bari sa yi magana daga baya. Haka su ka yi sallama Bobo na mitar ta katse masa shagali su ka dauki hanyar gida.
Dab da za su shiga unguwar ya kalle ta ya ce
“Babe kin katse min runs wallahi”
“Mtswww”
Ta ja tsaki ba tare da tanka ma sa ba, gaba daya hankalin ta ba ya tare da ita, shikenan yau kam asirinta ya tono, tun da take zuwa club ba ta taba kaiwa haka a waje ba, har a idar da sallar asuba ba ta koma gida ba? shin me za ta ce da Ammy idan har ta shiga dakin ta tashin ta sallar asuba ta ga ba ta dakin? Ya ma za ta yi ta shiga gida gari waye haka babu daman ta haura? Kuma ta san su Isa da Jauro ba lalle sun bude gidan ba in ba dai dan boko haram din nan ya kwana nan in da ta barshi tsaye ba ne, wanda ko jikin ta kunne ne ta san ba abu ba ne mai yiyuwa ba, kila ma ya riga ya fadawa Ammy fitar ta…..
Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa, a zahiri kuma fadi ta ke
“Ya Ilahi…..”
“Kai Zeeena ashe kin iya ambaton Allah!”
Cewar Bobo cike da zolaye. Harara ta watsa masa, tare da fadin
“Dadi na da kai Bobo rashin sanin ciwon kai! Ba ka ga halin da na ke ciki ba ne wai?”
Dariya ya ke yayin da ya sami waje ya faka, suna hango gidan Malam ya ce
“Come na, stop panicking! Kwantar da hankalin ki babe, calm down, ki fita ki je gate din gidan ku, idan bude ya ke ki shigewar ki kai tsaye, ba kya bin masu gadin ku bashin bayani, idan rufe ya ke ki buga mu su su bude mi ki, gidan uban ki ne, idan Momcy ta gan ki tell her kin fita exercises ne, shikenan!”
“Yen yen yen yen! Ni na rasa yanda aka yi na ke mu’amala da kai Bobo! Duk randa na fita da kai sai ka jawo min matsala!”
Ta na gama fadin haka ta fice a fusace tare da buga masa murfin mota. Zuciyar ta na bugu ko wani taku ta yi, wayar Halitta ta shiga kira, ta yi ringing ta gama ba ta daga ba, hannu na rawa ta kira Falmat, ita ma din ba ta daga ba, isar ta gate din ta dan tura ta ji a rufe, sai da ta dan yi jim sannan ta yi karfin halin bugawa. Har ta fitar da rai da bude gate din, ta na shirin juyawa sai ta ga an bude hujun da aka yi jikin gate din domin ganin na waje.
Idanun ta ta tsinta cikin na sa, tuni ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba, yayin da bugun zuciyar ta ya karu, sai da yayi sakanni ya na kallan ta, ta na mai cuna kumatu cike da tsiwa ta ke mayar masa da martanin kallan, dan kuwa tsoro baya hana Zainab rashin kunya..
“Malam dalla ka bude min gate! Ka zuba min na mujiya ba ka taba ganina ba ne?”
Ga mamakin ta sai kuwa ya bude, shigar nan dai da ta gan shi da ita jiya da daddare, shi ne jikin sa, Goran nan dai be aje ba, ta na rike hannun sa na hagu, hannun sa na dama kuma ruke da rediyo ya na jin labarai.
Ko kallan sa ba ta kara yarda ta yi ba, bare su hada idanu kai tsaye ta wuce ciki kamar dai yanda Bobo ya ce ta yi, addua ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ta hadu da Isa ko Jauro, sa’ar da ta yi da an idar da sallar asubahi su ke komawa su yi baccin su tun zuwa Usman gidan, shi kadai su ke bari da gadin safe, karnuka kuwa ana kiran sallar farko ake daure su, saboda kar su dami masu sallah masallacin gidan da haushi, duk da dai ta waje masallacin ya ke.
Sai da ta kurewa ganin sa, zuciyar sa cike da tunani kalala wanda duk yanda ya so ya cire daga zuciyar sa ya gagara, ya mayar da gate ya rufe.
“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Babu shakka Allah ya jarabci Malam da diya kamar yanda ya ke jarafta salihan bayin sa cikin ikon sa! Ya Allah ka kare Malam daga sharrin wannan Bingel!”
Cewar shi a zahiri, yayinda ya koma mazaunin shi bisa benci, ya kishingida ya na mai cigaba da sauraron labaran shi a tashar BBC hausa.
Cikin sanda takalman ta a hannu ta ke tafiya, ta kitchen ta bi ta shiga falon, dab da zata karasa dakin ta muryar Halitta ya daki kunnan ta
“Yakura daga ina ki ke?”
Jiki na rawa ta saki takalman su ka zubi kasa, Kallan Halitta ta ke ta na mai waige waige ta ga ko ita kaidai ce. Ita kadai din ce sanye cikin hijab har kasa, hannun ta ruke ta carbi dan Halitta ba ta komawa bacci bayan sallar asuba, zama ta ke ta yi zikiri da adduo’i har gari ya waye rana ta fito, sannan ta shiga kitchen ta taya iya abin karin kumallo. Ta fito za ta kitchen din kenan su ka yi kacibus da Zainab ta na sanda za ta shige dakin ta.
Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 4"