Auren Shehu Book 1 Page 18
18
Anty Sauda na Mai duban Zainab ta ce
“Yakura ni fa ganin yanda wannan ke kwance rai a hannun Allah gwara a sake shi kafin ya mace mu su a nan”
Cikin nuna rashin tausayin Muhamad Bello Zainab ta zunbura baki tare da fadin
” A sake shi? Idan aka sake shi sai a je a dauko shi almajirin ko Anty Sauda? Wallahi ni auren nan gaba ?aya na tsana har rai na!”
“Ah ah ba sai an dauko shi ba, wannan horon da aka yiwa dan uwan sa ma ya isa ya sake ki muddin ya na da hankali”
Cewar Anty Sauda, ba ta gushe ba ta kara da
“Su dauke shi yanda ya ke su kai mayar da shi Kano…”
“Anty Sauda……”
Zainab ta katse ta cike da damuwa. Murmusawa Anty Sauda ta yi, ba ta gushe ba ta kara da
“In dai almajirin nan ne wallahi sai ya sake ki, yanzu dai a mayar da wannan kada ashahadun mutuwar shi ya rataya kan mu!”
Haka ba a son ran Zainab ba ta na ji ta na gani kafin su tafi, Anty Sauda ta ba da umarni a mayar da Bello Kano gidan Malam in da aka dauko shi.
A ranar aka wuce da Bello Kano, hajaran majaran, gaban gidan Malam su ka ajiye shi a wulakance, su ka juya su ka yi tafiyar su. Hayaniyar mutane ne ya sanya su Jauro bude kofa, ganin mutane sun yi cincirindon ya sa Jauro kutsawa cikin su domin ganewa idunun sa abin da ke faruwa, masu salati na yi, ma su Allah wadar da kasar nan na yi.
Kallo daya Jauro ya masa ya san ko shakka babu wannan bafulatani na da dangantaka Usman, dan haka da sauri ya koma ya yi kiran Usman, wanda jin abinda kr faruwa ya sanya shi fitowa kafa ko takalmi babu.
“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Bello? Bello!!!”
Cewar Usman yayinda idanun sa su ka sauka kan Bello. Tuni idanun sa su ka kada su ka yi jajur tamkar garwashi, cikin kankanin lokaci gaba daya ya sauya kamanni. Tsugunnawa yayi gaban sa tare da daura hannu bisa kirjin Bello, jin ya na bugawa be tsaya bata lokaci ba ya dauke shi cak ya daura a bisa kafada, Haka kafa babu takalmi, Isa biye da shi su ka dauki hanyar da zai sada su da titi, Allah ya so kafin su karasa sai ga dan sahu, Isa ne ya tsayar mu su da shi, su ka shige, Usman na mai umartar dan sahu ya kai su asibiti mafi kusa.
Sun je asibitoci ya kai biyar, Amma duka sun ki karbar su, cewar su halin da Bello ya ke ciki ya kamata su zo da police report. Da kyar su ka samu aka karbe su wani karamin private hospital da ke cikin Tarauni, me suna Iklima Clinic, su ma din sai da Isa ya koma ya hado gaba daya abin da ya mallaka na kudi tare da wanda Usman ke da shi, su ka ba su sannan su ka yarda aka ba su gado, likita ya shiga duba Muhamadu Bello.
Bayan wasu mintina Likita ya fito, Nan ya ke yiwa su Usman bayanin yanayi yunwa da kishin ruwa da Bello ya ke ciki, bayan haka ga dukkan alamu an bashi kashi sosai, jikin sa zane ya ke da alamun shatin belt. Allah ya sa be sami karaya ba ko daya ba.
“Yanzu likita ya za a yi? Dan Allah ka taimaka ka ceto ran dan uwana”
Cewar Usman, cikin ran sa ya na mai cin alwashin ramuwar gayya ga duk wanda ya aikatawa Bello tsananin azaba haka, ko da kuwa wanene.
“Ka da ka damu, in Sha Allah za mu yi iyakar kokarin mu”
Cewar likita, wanda tun shigowar Usman Allah ya dora masa tausayin sa, musammam ganin yanda hankalin Usman ya tashi akan abin da ya sami Bello.
In da Usman ke zirga zirgan nemawa Bello lafiya, Zainab kuma a na ta bangaran tunanin yanda za ta kawo karshen auren ta da Usman ta ke, dan kuwa yanda ta ga ana maganar auren Halitta Sudais ba karamin daga mata hankali ya ke ba. Gashi duk wani dabarar da za ta ja hankalin Sudais ta yi, Amma ina kamar ta shuka dusa dan kuwa dai ha?onta ya kasa cimma ruwa.
Bayan sati ?aya da sakin Muhammad Bello Anty Sauda ta zo gidan Malam. Ta yi rashin sa’a Ammy ba ta nan, Halitta da Falmat sun raka ta asibiti a gwada jinin ta, dan ta na yawan fama da ciwon kai. Zainab ce ta saka Anty Sauda gaba a kan auren ta da Usman. Cike da Mamaki Anty Sauda ta ce
“Wai ke wannan saurin ina zai kai ki ne? Na ga ke kan ki makaranta za ki koma, ki fita harkar almajirin nan, ki hada na ki ya na ki ki koma makaranta, duk ran da ya gaji zai sake ki, Ni na san bayan abin da ya faru da dan uwan sa zai sake ki Yakura, dolen sa ma”
Zainab na kallan Anty Sauda ta kada baki ta ce
“Anty Sauda idan kuma na sami mijin aure fa? Shikenan ina ji ina gani sai na bari ya wuce ni?”
“Ina ki ka taba jin mijin wata ya wuce ta?ai matar mutum kabarin sa, toh tunda abin haka ne bari Hajja Aleesha ta dawo sai ki fada mana dan gidan wanene, in ya so duk yanda za a yi almajiri ya sake ki sai a yi, wancan din ya fito a hada auren da na Halitta”
Cewar Anty Sauda hankali kwance. Kamar daga sama ta ji Zainab ta ce
“Ba fa kowa ba ne face Sudais, dama ni Dady ya ce zai daurawa tun farko, kuma dani ya fi dacewa……”
“Zancen banza zancen hofi!”
Ammy ce ta katse ta a fusace, dawowar su kenan biye da ita Falmat da Halitta ne. Idan aka dauke Halitta babu wanda be tsorata da furucin Zainab ba. Ammy ba ta gushe ba ta kara da
“Wannan bakin hali na ki Yakura ba guna ki ka dauka ba, haka kuma ba halin Malam ba ne….!”
“Akwai bakin Hali da ya wuce na shalelen ta ki Halitta? Ace ta rasa wanda za ta yiwa hassada da bakin ciki sai yar uwar ta wacce ta sha nono ta sakar mata? Yarinya bakin hali kamar cinnaka ai muna sane da duk wani tuggu da ta ke shiryawa Yakura a gidan nan!”
Anty Sauda ce ta ara ta yafa ta na mai watsawa Halitta wacce ta bude baki ta na kallan ta harara. Jin haka Ammy ta sami waje ta zauna, murya kasa kasa ta ce
“In akwai wacce ta ke cinnaka kaf gidan nan Yakura ce! Ita da kan ta take kullawa kan ta koma menene! Nan ai ita aka ce za a aurawa Sudais din ta nuna mana iyakar mu ta hanyar haurawa katanga, haka Halitta ta na ji ta na gani Malam ya musayan ta a madadin Yakura, ta masa biyayya, komai na tafiya dai dai sai ta zo mana da yashesahen zance? Wallahi ko ita ce sarkin shedanun duniya ta yi kadan!”
Zainab na mai zunburo baki, cikin neman doki ta ke duban Anty Sauda, wacce gaba daya ita ma din jikin ta ne yayi sanyi. Kai ta girgiza ta ce
“Ah ah Yakura, kin yi kuskure nan kam, Ni ma ba zan goyi bayan ki a nan ba, Kuma na ji wannan yaron na kaunar yar uwar ki…”
“Ita fa ba ta son shi, wannan almajirin da Dady ya daura min ta ke so! Ku tambaye ta mana!”
Shiru ne ya biyo baya yayinda Halitta ke duban Zainab cike da mamakin halin ta.
“Karya ki ke mata!”
Cewar Ammy bayan ta farfado daga rudanin da ta shiga, ba ta gushe ba ta kara da
“Karya ki ke ma ta, ke ko ma da gaske ki ke wallahilazim ba za ki auri yaron nan ba, matukar ina raye Halitta za a daura masa, idan kin so ki kashe auren ki, ki zauna ba aure har a bada, kai Yakura haihuwar ki ko haihuwar asara……!”
“Kayya!! Kayya!! Na fa ce ki dena yiwa yarinyar nan baki”
Anty Sauda ta katse Ammy. Cike da jimami ta ce
“Toh ba dole ki sami hawan jini ba yanda ki ke daga hankalin ki aka abu kankani haka, kin fa san yarinta ke damun Yakura, Yakura yarinya ce har yanzu ba ta san ciwan kan ta ba. Kuma yaran nan fa duka na ki ne, ina laifi idan kin nusar da ita kin gyara ma ta Aleesha?”
” Yakura ba yarinya ba ce tunda har ta san bin maza da busa hayaki! Babu wani nusar da ita da zan yi akan wannan maganar, magana daya ce dal, aure ne dai sai an daura shi tsakanin Sudais da Halitta da yardar Allah, na kuma sake jin kin furta wani abu akan auren nan wanda ya ke kishiyar alkhairi da zaman lafiyar Halitta wallahi sai na tsine mi ki Yakura! Tashi ki ba mu waje shashasha wacce ba ta san ciwan kan ta ba!!”
Zainab ta tashi fuuu, saura kiris ta buge Halitta Allah ya sa ta yi maza ta kauce mata daga hanya. Duk yanda Anty Sauda ta so Ammy ta huci zuciyar ta ta duba lamarin ki ta yi, ta ce babu wanda ya isa ya saba alkawarin da Malam ya dauka na auran Halitta da Sudais, aure ne an daura shi an gama da yardar Allah.
***
Muhamadu Bello kuwa sai da yayi sati a asibiti sannan ya dawo hayyacin sa. Duk yanda ya so ya bawa Usman amsar tambayoyin da ya ke ta jera masa kasawa yayi domin kuwa rashin lafiyar Iyar su ne kadai gaban sa.
“Iya…..Iya na kwance rai a hannun Allah, ita ta ce na yi maza na kira ka, ta ce lalle ka zo”
Ganin abin da Bello ya rubuta masa da rubutun ajami jikin takarda ya sanya Usman gigicewa.
“Me ya sami Iya? Tun yaushe ta aiko ka? Su waye su ka aikata ma ka wannan abun?”
Usman ya jera masa tambayoyi ya na duban Bello da ke zaune bisa gadon asibiti. Takardar ya dauka ya kara rubuta
“Kwana na nawa a kwance a nan?”
“Sati guda….”
“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Mun bata lokaci da yawa Allah ya sa Iya na raye.”
“Ta na raye! Babu abin da zai sami Iya ta!”
Cewar Usman a fusace bayan ya karanta amsar da Bello ya bashi. Idanun sa ne su ka fiffito gani Bello ya rubuta
“Dama ka yi aure ne? Mutanen da su ka kama ni suna ta duka na wai sai na saki matar da aka daura min, sai da wasu su ka zo, ina jin su duk da ba na iya ko da kwakkwarar motsi ne, na ji sun ce ba ni ba ne, a nan na gane kai su ke nema…..”
Cikin zafin nama ya fizgi takardar, ya na mai kara dubawa da kyau yayinda idanun sa su ka yi jajur tsabagen bacin rai. A fusace ya mayar masa da takardar tare da fadin
“Ka fada min komai da komai! Me ya faru? Yaya mutanen su ke? A ina su ke?”
Ji yake ina ma Bello na da baki ya fada masa dan kuwa rubutun na Bello ya masa rashin sauri da yawa a yau. A haka Bello ya zayyana masa komai. Ran Usman yayi baki sosai, zuciyar shi ba karamin ?aci ta yi ba akan abin da Zainab ta sa aka aikatawa dan uwan sa. Lalle za ta ji a jikin ta, sai ta gwammaci ba ta zo duniya ba…. tunanin da yake a ran sa kenan kafin Bello ya sake rubuta masa wata tambayar
“Wacece ita?”
“Sannin wacece ita be da muhummanci Bello! Ka huta idan ka sami sauki sosai zuwa gobe in Sha Allahu za mu tafi Rugar Shehu wajen Iya”
Ya na gama fadin haka ya fice. Shi kan shi Muhamadu Bello ya tsorata da ganin yanayin Usman, rokan shi Allah ya kiyaye kar ya aikata wani abun da za su zo su yi dana sani a gaba.
*****
Kamar yanda Usman ya fada, washaegari da sassafe aka sallami Bello. Bayan ya biya sauran kudin da ake bin su, ya dauki yan kayan sa tare da yiwa su Jauro sallama, ya sa Bello gaba su ka nufi Rugar Shehu duk da jikin Bello be yi kwari sosai ba.
Da yake Bus su ka shiga, ana ta tsaye tsaye ba su suka shiga rugar Shehu ba sai yamma likis. Tun da su ka nufi Rugar gaban Usman ke faduwa. Kafin su kai ga shiga rugar su ka fara kacibus da matasa da magidan ta wanda yawancin su dawowar su daga kiwo kenan, suna kada shanu gida, sanye su ke cikim kayan saki, wasu daga cikin matasan kitso ne kan su, wasun su kuma hular kaba ce bisa kan su, magidan tan ne ke sanye da hular saki.
Ganin Bello tare da wani mai kama da yayan sa ya sa kowa ya bar hidimar gaban sa, su ka tasan ma su. Ko da su ka karaso dab da su, su ka duba da kyau su ka ga Usman din ne ko shakka babu tuni matasa su ka dau sowa su na mai jefa gora sama suna cafewa suna mai zagaye Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin
“Maraba da magajin Rugar Shehu na kwarai! Ashe Rugar Shehu na da raban arziki har gobe!”
Magidantan kuwa duk da sun yi maraba ba da ganin Usman, ba su fasa tambayar
“Kai kuwa Shehu Magaji ina ka je ka juyawa tsatsun ka baya haka? Ashe rai kan ga rai?”
Shauki da jimami ya sa Usman kasa fadin komai, hawayen farin ciki ne ke fita daga idanun sa, Allah Allah ya ke su karasa cikin Rugar ya ga Iyar sa.
“Iya ta? Mu karasa ciki na ga Iya ta sai na mu ku bayanin komai!”
Tuni matasa su ka tsaya da sowa, yayinda kowa ya sha jinin jikin sa.
“Iyar ka? Ashe ka na da Iya? Ka damu da ita? Ya ka zo mu je na kai ka gun iyar ta ka ta na nan kwance ta na jiran ka!”
Cewar wani magidanci ya ke kani wajan mahaifiyar Usman. Ya na magana ne da harshen fulatanci
“Kawu Iliya….”
“Shiiiiiii! Kar ka damu, biyo ni kawai!”
Cewar Kawu Iliya yayinda ya fizgi hannun Usman, Bello na biye da su, sauran jama’a babu wanda ya biyo su. Usman be tsorata ba sosai sai da ya ga sun gifta Rugar Shehu ba su shiga ba, Kawu Iliya ya wuce da su can jeji in da ake rufe matattu. Gaban wani saban kabari ya tsaya, idanun sa na fidda kwalla ya ce
“Ga iyar ka nan kwance! Yau kwana bakwai kenan da ?asa ya rufe ta, ta mutu da sunan ka bakin ta, ta kira ka Usman, ta kira ka, ba ka zo sanda ta ke bukatar ka ba, yanzu ga ta kwance sai ka mata addua”
Ihu da kururuwa Bello ya saka yayinda ya zube kan kabarin Maihaifiyar su ya na mai rungumo kasar. Wani irin tsawa Usman ya daka masa wanda ya sa shi tashi a firgice tare da shiga hayyacin sa.
Hakan ya bawa Usman damar tsugunnawa gaban kabarin Iyar su, ya na mai dafawa ya mata addua sannan ya debo kasar kabarin da hannun shi, a hankali ya ke sakin kasar yayinda iska ke kadawa har duka kasar ya bi iska ya rage sai kura hannun sa.
“Wallahi! Wallahi!! Wallahi!! Billahil azi! Na rantse da Allah kamar yanda wannan kasar ta baje a iska, haka farin ciki zai baje a rayuwar ki Zainab……wannan shi ne sakayya mafi dacewa da ke!”
Cewar Usman ya na mai fitar da kwalla, daya na bin daya.
Alhamdulillah.
Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 18"