Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 1 Page 16

*Khadija Sidi*
Auren Shehu

16

Cike da ladabi ta gaishe da Shiek, Wanda ya amsa cikin ran sa ya na mai yabawa da nutsuwar Halitta. Ta’aziya ya mata, sannan ya kara da


“Ga dukkan alamu wannan ce matar da Malam ya bawa Sudais”

Halitta ta sunkuyar da kai yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan tun da ta dunfaro falon ta ji kamar ana mata kallan kurulla, haka kuma jikin ta ya bata wannan da Shiek ya ke magana ne duk da ita ba ta daga ido ta kalle shi ba. Zainab kuwa wani irin bakin kishi ne ya dasu cikin ran ta, ai dama ita Malam ya yi niyar ya bawa Sudais ba Halitta ba, dan haka sai in da karfin ta ya kare.

“Halitta ba, eh ita ce, ya ko yi dace da diya mai mutunci, Halitta ta san darajar manya”

Cewar Hajja Kilish iya gaskiyar ta, hakan ya sa Zainab watsa ma Halitta harara ta wutsiyar idanu.
“Ai daga gani ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa, ya sa a yi damu, in Sha Allah lokacin da mu ka saka da Malam ba za mu saba ba”

Duka su ka ce “Amen” ban da Zainab wacce ta ke ta sakar yanda za a yi Sudais ya zama mamallakin ta.

“Halitta ban ji kun gaisa da angon na ki ba”
Hajja Kilish ta fada ta na mai duban Sudais wanda ya saka ma Halitta idanu ba tare da ya ji kunyar kowa ba. Cike da kunya Halitta ta kai kallan ta gare shi, sai ga idanun ta cikin nasa, ta yi saurin yin kasa da na ta idanun sannan ta furta

“Ina wuni?”

Zainab ta kauda kai dan kishi ji take kamar ta tashi ta bar mu su wajan. Babu abinda ya dada kona mata rai fyace yanda Sudais ke washewa Halitta baki sa’ad da ya amsa gaisuwar ta, tare da mata ta’aziya, dan kuwa rabin fara’ar da ya ke yiyiwa Halitta be yi mata ba. Kasa daurewa ta yi, ita ta fara tashi ta mu su sallama ta shige ciki. Shigar ta ba da dadewa ba Shiek ya mu su sallama, har sun fita sai ga Zara ta dawo, gun Halitta ta je ta dan tsugunna cikin rada ta furta

“Ya Sudais ya ce na karba masa number dinki”

Ta mika mata wayar, da kamar ba za ta karba ba, ganin yanda Ammy ke kallan ta ya sa ta karba ta saka numbar. Cikin jin dadi Zara ta karba tare da fadin

“Na gode Anty Halitta, Allah ya ba mu alkhairin sa”

Ta tashi ta fita. Kamar yanda su Zara su ka tafi da Halitta a baki, haka ma su Falmat da Kori su ka ta yaban Sudais. Har daki Falmat ta bi Halitta. Da ke tun tafiyar Shiek da iyalan sa ta komawar ta daki ta kwanta. Falmat ta shiga da gudun ta, ta fada kanta

“Alhamdulillah wani hani ga Allah baiwa, Allah ya hana ki Usman dan ya ba ki mafi alkhairin sa!”

A hankali ta dago ta na kallan Falmat, sai a sannan ta lura da jajayen idanun Halitta da hakuma hawayen da ke kwance kunci ta. Cike da mamaki Falmat ta ce

“Ya salam! Kukan na menene? Ina dai fatan na rashin Dady ne a wannan rana ta farin ciki”

“Na komai ne Falmat, komai ya cushe min, komai babu dadi, rayuwa babu dadi, rayuwa ta chanza, rayuwa ta zo min ba yanda na ke tsammani ba! Falmat ba na san shi….”

Halitta ta fada ta na mai zubda hawaye, baki Falmat ta bude ta na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da

“Kin fi kowa sanin burin rai na miji ne gurin yaya ta, ina ji ina gani aka sanya tazara a tsakanin mu. Na daukar wa Dady alkawarin auran zabin shi, kuma ba zan saba alkawarin ba ko da kuwa hakan na nufin rasa farin ciki na, gashi yau an wayi gari babu Dady Falmat……”

Ta karasa ta na mai fashewa da kuka. Tausayin Halitta ne ya rufe Falmat. Rungume ta ta yi cikin rarrashi ta ke magana, ta na fadin

“Ki yi hakuri Halitta, rashin abin da rai ke so ba karamin rashi ba ne, sai dai kuma wani sa’in hakan shi ya fi alkhairi a gare mu, daga ganin Sudais alkhairi ne Halitta, wallahi hankalin kowa ya kwanta da shi, darajar biyayya Allah ba zai bari ki tabe ba Halitta”
“Allah ya sa Falmat, Allah ya sa”

Cewar Halitta ta na mai kokarin tsayar da hawayen da ke zuba daga idanun ta. Haka Falmat ta cigaba da ba ta baki har sai da ta sami nutsuwa ta dena kuka.

Da tunanin Sudais Zainab ta kwana cikin ran ta, washagari da safe ta kasa dakewa, sai ga ta dakin su Halitta ta ci sa’a Halitta ce kadai zaune bisa gado ta amsa wayar Sudais kenan, ta zauna tunani.

Ganin Zainab da yanda ta zo mata mamaki ya rufe Halitta, musammam da ta ga ta zauna kusa da ita har da riko hannun ta, ta ce

“Halitta, dama wani shawara na zo da shii”

Kallan ta ta yi na wani dan sakanni, sannan ta ba ta amsa da

“Toh Yakura, ina jin ki”

“Dama batun Sudais ne, na san ba kya san shi, Kuma idan har ba kuskure na yi ba, na san kin jima da saka wannan almajirin da Dady ya aura min a ran ki…..”

Daf! gaban Halitta yayi mummunar faduwa, ta yi saurin zare hannun ta daga cikin na Zainab ta na fadin

“Auzubillallah! Wannan wani irin magana ne Yakura!”

Murmushi Zainab ta sakar mata, kana ta ce

“No kwantar da hankalin ki, ba wani abu ba ne dan kin so shi, ni yanzu ma hakan rahama ya za me min, domin kuwa Allah ya sa min san Sudais, wallahilazim Sudais shi ne mijin da na ke burin samu a rayuwa ta, sam be dace da ke ba, Kuma duka kwamacalar nan Dady ya hada, Allah ya masa rasuwa, kin ga kenan hankali kwance za a iya warware komai. shi wancan almajirin sai ya sake ni, in ya so ya aure ki, ni kuma na auri Sudais…..”

“Allah ya sauwake mi ki Yakura, tur da tunani irin na ki!”

Halitta ta katse ta cikin dakiya duk da har ga Allah zuciyar ta ta kwadaitu da zance Zainab. Ba ta damu da irin kallan da ta ke mata ba, ta kara da

“Ina hankalin ki ya tafi ne? Wai yaushe za ki gyara hali ne? Toh ki saurara ki ji ni da kyau, zabin Dady shi ne zabi na, hawainiyar ki ta kiyayi rama na, Sudais miji na ne In Sha Allah, gwara ma ki ruke mijin ki ko Allah ya sa ki dace….”

“Ke dallah malama rufa mana baki! Yen! Yen! Yen!”

Zainab ta daka mata tsawa ta na mai kwatanta yanda Halitta ta yi maganar, ba ta gushe ba ta kara da

“Har ke kin sa! Wani rama gare ki! Ki asuwa cikon benci da ke? Na tabbatar aka jera mu ni da ke ba Sudais ba ko wani da namiji a duniyar nan sai ya dauke ni sau dubu kafin ya dube ki! Ki na nan banza a banza kashi a leda! Nunan rana da ke har kin samu ina shawara da ke! Toh ki saurara ki ji Halitta idan har ban mallaki Sudais ba ban cika diya mace ba! ”

Ta tashi fuuu ta fice ta na mai buga kofa. Tagumi Halitta ta yi idanun ta na kallan kofa, tun da take a duniya ba ta taba ganin mutum irin Zainab ba, in dai san kai da san zuciya ne, a komai ita kan ta ta sani sam ba ta tunanin kowa a cikin lamarin ta fyace abin da zai dada mata.

Dakin Ammy ta nufa, ta tarar da Ammy ta fito daga wanka kenan ta zauna za ta shafa mai. Babu gaisuwa babu komai kai tsaye ta ce

“Ammy akwai maganar da na ke so mu yi”

Fasa shafa man ta yi, ta na duban Zainab ta ce

“Ina sauraran ki”

Zainab ta matso gaban Ammy ta zauna, hannayen ta bisa cinyar Ammy, hawaye na zuba daga idanun ta ta ce

“Ammy dan Allah ki yafe min, na yi kuskure, dan Allah ki yafe min, Ammy dan Allah….”

“Na yafe mi ki Zainab, na yafe mi ki duniya da lahira, bayan rasuwar Malam Zainab idan ban yafe mi ki ba me ya rage min a rayuwa? Na yafe mi ki”

Zainab na murmushin jin dadi ta furta
“Ammy na gode, Ammy dan Allah ina neman alfarma”

“Ina jin ki”
Cewar Ammy yayinda ta fara shafa mai.

“Akan auren da Dady ya daura min Ammy, Ammy dan Allah ki raba aure na da…. ”

“Ba zai yiyu ba! Auren ki Malam ya daura shi, ba zan taba kashe shi ba Yakura, idan har kin ga auren nan ya mutu toh Usman ne ya sake ki da kan shi….”

“Ammy dan Allah….”

“Yakura!”

Ammy ta katse ta cikin nuna bacin rai, ta kara da

“Kada ki tsaya jayayya da ni!”

Jiki sanyaye Yakura ta amsa da

“Toh Ammy, Allah ya huci zuciyar ki”

Tashi ta yi ta fita ran ta na radidi ba ta taba zaton Ammy za ta juya mata baya haka ba. Ta kasa zaune ta kasa kwance daga karshe hukunci kai maganar dangin Ammy wanda ta tabbatar za su mara mata baya akan kashe auren na ta tayi, dan kuwa babu wanda ya goyi bayan auren, duka sun nuna bakin cikin su karara akan auren Zainab da Usman.

Jin za ta tafi gidan Babbar yayar su Ammy, Anty Sauda. Ammy ba ta hana ta ba, ta dai ce mata kada ta yi dare.

Ta ci sa’a ta tarar da kanwar Ammy wacce su ke kira Anty Hannah ma ta je gidan. Nan Zainab ta saka mu su kuka, ta hada karya da gaskiya duka ta fada mu su. Cike da takaici Anty Hannah ta ce

“Toh shi Malam ma fisabilillahi ya ma zai dauki yar sa, jinin mu ya aurar da ita ga almajirin sa! Dan ruga! Ai ya san tsadar mu, kila ya manta wahalar da ya sha kafin ya auri Hajja Aleesha ne!”

“Toh da ke Allah ba azzalumin bawan sa ba ne ai gashi ya dauke Malam a doran kasa, ke bar kuka wallahi babu wanda ya isa ya sa ki zama da almajiri! Dangin mu ko talaka ba su taba aure ba bare almajiri!”

Anty Saude ta ara ta yafa. Cikin jin dadi Zainab ta shiga share hawayen ta, ta kara da

“Ammy ta ce matukar ba shi ya sake ni da kan shi, ita ba za ta kashe auren ba, Kuma wallahi na san da kyar ya sake ni Anty….”

“Ke rabu da wannan Ammyn ta ki, kila zafin mutuwar mijin na ta ne ya toshe mata kwakwalwa, in ba haka ba ya sha giyar wake ne da za a aura masa kyalleliyar diya, jinin shuwa da Kanuri kuma ya sake ki dan kan sa? Mu nan za mu sa a kawo mana shi tun daga Kano har barracks, dan uban shi sai ya sake ki!”

Cewar Anty Saude da ke mijin ta soja ne mai babban matsayi “General”. Anty Hannah da Zainab su ka sa sowa, su na mai fadin

“Yayi matar General”

Zainab ta kara da

“Wallahi shi ya sa na ke kaunar ki Anty Sauda, Allah ya ja da tsayin rai!”

Anty Sauda na mai darawa ta furta

“Ku ji yarinya fa! Ai yiwa akai ne! Yanzu ki na diyar mu sai mu bar ki da auren almajiri? Allah ya mana sutura! Ai ke din matar manya ce, san kowa kin wanda ya rasa, babu talauci a jinin mu, Kuma in Sha Allah ba za mu gan shi ba, ina ki ka ce shi almajirin ya ke yanzu”

“Amen Anty Saude, ai ya na nan gidan mu, shi dan masu gida ba! Wai fa BQ Dady ya ce na koma, wai nan ya ce Ina kwana da shi….”

“Lailahailallah! BQ!”
Su ka fada a tare, Anty Hannah ta kara da

“Yanzu ita Hajja Aleesha sai ta mike kafa ta na bacci diyar ta na kwance da almajiri a BQ?”

Zainab ta rangwabar da kai ta ce

“Wallahi Anty, har ma ta sa na kwashe kaya na, ana gobe Dady zai yi accident ma fa can na kwana….”

“Kin kwana da shi???”

Anty Hannah ta tambaya cikin tsawa.

“Ah ah kofa na rufe ina zan yarda na kwana da shi”

“Atoh yanzu na ji batu, yar tselan uwa da kin yabawa aya zakin ta ki ka shiga hannun wannan gardin!”

Cewar Anty Saude ta na mai hango Usman a idanun ta sanda ya zo ta’aziyar Malam. Sai da Anty Saude ta yiwa Zainab alkawarin za a yi duk yanda za a yi Usman ya sake ta, ko da kuwa hakan ya na nufin za a je har kanon a dauko Usman ne, sannan Zainab ta dawo gida zuciyar tas, dan ta san auren ta da Usman ya kare, sai kuma batun soyayyar da ta ke shirin kullawa tsakanin ta da Sudais.

Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 16"