Tabarmar Kashi Book 2 Page 45
Book 02Page 45
“Na dawo daga office a gajiye, ina jin yunwa,inaso nayi wanka,amma duk baki lura ba, sai kawai ki bini da wata sannu da zuwanki me kama da bada umarni umarni?” Ya qarashe maganar yana lashe lips dinsa,hankalinsa na fusga akan nata lips din zuwa qirjinta da yaketa son rudar masa da tunani, rigar jikinta din doguwace sakakkiya,amma duk da haka akwai wata tattara a qirjinta data sake yiwa halittunta mazauni da kyau. Sake fincikota yayi sosai zuwa cikin jikinsa yana ci gaba da ifanta da wani narkakken kallo cikin qwayar idonsa
“You know what?” Ya fada yana hadiye yawu,ba tare da ya jira amsarta ba ya bata amsa yana sake jawota cikin jikinsa da kyau
“I swear i straight up forget my name for a second duk
sanda na kalli wadannan qwayar idanun” ya qarasa fada yana sanya yatsarsa tare da yi mata yawo dasu softly saman idanun nata, abinda ya tilasta mata lumshesu, tana jin tsigar jikinta na neman fara tashi
“Hold me so close for some minutes your breath already become my oxygen” ya fada yana kama hannuwanta ya kuma sanyata ta zagaye bayansa da su,sannan ya kama fuskarta a tausashe ya rige suna musayar numfashi me dumi dake fita daga hancin kowannensu.
Qafafunta ne suka fara rawa, ta fara gogarin zamewa,bai hanata ba ya barta ta janye,saidai bai barta ta matsa duka daga jikinsa ba ya rige hannunta
“Wannan shine kalan gaisuwar da nakeso bayan na dawo a office,zan shiga nayi wanka, kafin na fito please i want something to eat….am starving” tuntuni ta juya masa baya,a haka ta gyada masa kai tana addu’ar ya fita a kitchen din, tana tunanin zai fitanne tunda ya gama abinda ya kawoshi saita tsinci muryarsa cikin karyar da murva a shagwabe
“Please,my lips are so lonely one kiss please” har cikin bargonta taji tasirin muryar tasa. Qarasa rudata yayi,har spoon din hannunta na faduwa qasa,ya tsugunna ya dauka yana miga mata
“Matsiyaciya” ya fadi yana sakin wani tattausan murmushi hadi da soma takawa a nutse yana fita a kitchen din.
Bayan ta tabbatar ya fita din sai data samu guri ta zauna saboda ta daidaita bugun zuciyarta,idonta ta lumshe tana mamakin yadda yake yawan sanyata faduwar gaba da rudewa, abinda a baya Sam ba dabi’arta bane?.
Komai ta zubawa fadeelan har furar ma tace tanaso, sanann ta dawo ta shirya masa nasa saman wani kyakkyawan tray bisa tsari,sai taji kaman ta aikata fadeelan takai masa,amma kuma tunda ya fuskanci ya zama dan garari me neman dalili galilan ya moreta son ranshi,sai ta haqura ta zura hijabinta ta dauki tray din ta wuce dakin nasa tabar fadeela na kallo a parlor.
A nutse ta bude bedroom din ta shiga gamshin da yake fitarwa da sanyi suka buso mata,first night dinta da tayi da ranar Allah shi ya fara dawo mata fes a kai,ta dauke kai daga kan bed din ta soma takawa da gaggawa,tanason ajiye masa ta fice kafin yakai ga fitowa daga toilet din da take jiyo qarar ruwa. Har ta kusa isa qofar fita ya bude qofar bandakin ya fito
“Wait mana” ya furta yana dubanta, kamar ta zura da gudu haka taja ta tsaya sannan ta waiwayo da nufin ta samu gurin zama. Kadan ya rage bata fadi ba saboda tsabar rudewa,murdadden jikin nan nasa dake dauke da curarrun muscle ya bayyana muraran, gargasar dake lullube da jikinsa da damatsensa da suke fadin yadda mamallakinsu ke yawan daga qarfe, ba komai a jikinsa sai wani gajeran towel da ko cinyarsa bai gama rufewa ba don tabbas idan yace zaya zauna ne to kana iya hangen jikinsa sosai.
“Come and serve me masallaci zaki shiga ne haka na ganki da hijabi?” Ya fada cikin gatse, don ba haka yaso ganinta ba,yaso ya morewa kallonta ne sosai. Bata tankasa ba ta dawo gaban tray din
“Stop madam,ki cire wanann hijab din kada kiyimin gazanta” magana ce fal bakinta takeson maida masa, amma kuma tana tsoron kada allura ya tono garma,abisa dole ta hadiye ta zare hijabin yadda ya bugata ta fara saving nasa pancake
“Furar is enough” ya fada yana duba wayarsa da ya samu da tarin miscalls
Gida biyu hankalinsa ya rabu,rabi yana kan wayarsa rabi kuma tana ta fusgar hankalin nasa,so samu ace yanzun tana jikinsa yana shan duminta bai taba tunanin akwai ranar da wata mace zata dinga wasa da hankalinsa haka ba.
A nutse ta mige ta isa gareshi, dai dai sanda ya daga kiran dava shigo wayar tasa, miqa masa cup din tayi,ya miga hannu da zummar karba, kawai sai ya hade hannuwansu guri daya ya kuma jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinvarsa tare da manneta da qirjinsa ya riqeta tsam. Ko motsi hanata yayi,cikin tattausar muryarsa din nan da yau tayi kusanci sosai da kunnenta taii ya ambaci sunan maji yana kuma gaidata.
A galla ya kusa minti talatin suna magana da majin,ita kuma tana zaune zaman cinyarsa,wata muguwar kunya na dawainiya da ita,duk sanda ta motsa zai zake maidata jikinsa va manneta gam, har ya kammala wayar sukayi sallama,ya aje wayar gefansa sannan ya tattara hankalinsa a kanta. Tallafo hannayensu dake riqe da cup din yayi ya matso dashi saitin bakinsa,sannan ya kamo daya hannun nata ya aza saman cokalin dake cikin furar, murvarsa gasa gasa cakude da alamun damuwa yace
“Oya…feed me please” ya furta kamar wanda ke tsoron wani ya jishi. Shi ya taimakawa hannun nata ta hanyar rigeshi, yana tayashi debowa tare kaiwa bakinsa. Wani irin shiru ya ratsa tsakaninsu,ba wanda ke cewa komai a tsakaninsu,sai jikkunansu dake hade,dumin fatar cinyarsa da towel din bai gama rufewa ba tana ratsa
saahar tare da haifar mata da wani irin vanayi a cikin jikinta. Shima baice komai ba har suka gama,sai ya sanya daya hannun ya sake dafe tafukan hannayenta yana kallon cikin idanunta tare da sauke wata ajiyar zuciya me nauyin gaske
“Na gode, Allah yayi miki albarka” har ciki tsakiyar ranta tali dadin addu’ar, batasan cewa shi ya fita jin dadin samun wannan kulawar ba, duk da sai daya tilastata kusan ya samar da ita
“Ameen” ta furta can gasan ranta amma kuma labbanta sun motsa
“Amma….kin saka an dakeni kuma an hanani kuka?” Ya fada yana langabe kai cikin wata shagwababbiyar murya data sanyata daga kai ba shiri, idanunsu kuwa suka hade guri daya,sai ya dage mata gira abinda ya sanyata saurin mai da kanta qasa
“Yes maji tace zakuyi tafiya tana neman alfarmata na barki ki tafi, batason kuma doguwar tambaya ita tasan inda zakin keda angel” ya qarasa fadi cikin yanayi na nazari.
“‘Nima ina sake neman alfarma tare da rogon kauda duk wata tambaya daga ranka shakka ko kokwanto, khairan in sha Allah” har cikin bargonsa sautinta ya ratsashi, karon farko data masa magana da irin wannan salon, hashi kuma kusancin dake tsakaninsu ya bashi damar jin tone dinta tarrr
“Oh my god,repeat please,sake fadi” fuska ta tsuke,ta kuma shammaceshi ta mige da zafin nama,saidai ya rigata ta hanyar cafko hannunta
“Waye yace ki tashi?, haka kawai kin ciremin towel,oya mayarmin da abuna” sulalewa kawai tayi a wajen ta tsugunna tana curewa guri guda,ko kallonsa a haka ba zata iya sake yi ba bare ta gyara masa munafukin towel din daya dauro. Magiya ta hau masa
“Tashi kije” ya fada yana danne dariyar dake qasan ransa,da gaske yarinyar ta horu yadda ya kamata,inda dane da tuni yasha tsiwa da musu sau babu adadi. Koda ta fita waiwayawa tayi ta ballawa dakin harara tana jan awafa sannan tayi gaba
_niko nace a banza,ihu bayan hari kenan,idan yarinya ta isa tayi a gabansa mana ????
[04/10, 8:52 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*
* TABARMAR KASHI *
Book 02Page 46
_assalamu alaikum,barkanmu da dare,jiya an samu typing error,zakuga na sana matsiyaciya a maimakon matsoraciya,ina fatan kun fahimci kuskuren dake gurin,na gode_
Tun daga ranar data fuskanci ina ya sanya gaba take rufe dakinta da wuri su kwanta ita da fadeela,idan yazo ya gani saidai ya koma ranshi babu dadiyaso ya sake wasata da kyau ya kuma more kafin lokacin tafiyar kamar yadda maji ta gaya masa. Amma a kwanaki itace take shirya musu breakfast tayi musu abincin da zasuci idan sun dawo,ta kuma hada lafiyayyen dinner. Sai a lokacin ya vadda da zancan hausawa da sukance a rashin uwa akanyi uwar daki, tabbas a rashin samun girkinta yake yaba abincin Jacob, bai taba tunanin akwai wani da yakai
Jacob iya girki ba sai gashi ya samu wadda ta fishi nesa ba kusa ba.
Hankali kwance säahar keyin shirin tafiyarta,shiru da meenal da hajiyan sukayi da al’ amuransu jikin säahar ya bata tabbas ba a banza ba,saidai ita kanta cikin satin baccinta ragagge ne, don addu’ar neman nasara tuquru takeyl.
Qarfe biyu na dare yana zaune cikin dakin nasa yana sarrafa CCTV camera din dake cikin dakin nata,duk da ta haramta kwanansu tare amma hakan bai haramta masa ganinta ba ta hanyar CCTV camera din, abinda ya zame masa kamar ibada,a kullum idan ya dawo daga aÃki ya kammala komai sai ya zauna yayi bitar wuninta na ranar a cikin dakin,saidai daukar kadan yake samu,duk da cewa yawanci zazzafar dauka ce dake yawan dagula lissafinsa,don a nan ne yake samun damar ganinta sosai, abubuwan da bata iya barinsa ya kalla yadda ya kamata a nan yake samun dama.
Kwanakin data dauka tana sallar daren duka yana sane da su,ko a yanzun da tafiyarsu ta kama jibi ne yana bibiye da komai,amma har yanzu baici karo da inda tayi maganar tafiyar ko wani abu daya danganceshi ba.
Ajiyar zuciya ya sauke,ya tabbatar gobe zai tafka mata tsiya ne,bazai iya bari tayi tafiya me nisa haka ba ba tare da sunyi kyakkyawar gaisuwa ba,sai ya maida daukar ya rufe ya koma duba history na jiya da daukan da camera din ta yiwa sashen hajiya qarama. Bude video din yayi yana sake nazari,hajiya mansura ce ita da hajiya qaraman,kowacce fuskarsa cikin bacin rai,kuma magana suke da juna cikin fushi, saidai har yanzu ya kasa tantance me suke gayawa junansu saboda sunyi nisa da ma’ajiyar camera din tsaron. Ya jima yana duban fuskokinsu su biyun,yadda suke a haka a hakan ake nuna masa su cikin mafarkinsa,ya dade sosai yana sake bibiyar wasu motsinta na baya dake ajjiye sannan ya kashe yana sauke ajiyar zuciya
“Akwai gagarumin abu a qasa” ya furta a hankali, gaba daya zuciyarsa da gangar jikinsa suna bashi akwai babban al’ amarin dake tunkaroshi, saidar ya rasa meya wannan?.
*********Washegari tun bayan sallar isha’i da sukaci abincin dare ya kafa ya tsare a falon, wanda kusan wannan ba al’adarsa bace yafi zama a balcony dinsa study room ko cikin dakinsa,kasancewar shi din mutum ne maras son hayaniya ko a shiga al’ amarinsa. Fadeela na lafe a jikinsa tana ta masa hira,yayin da nashi idanun kekan säahar duk wani shiga da fita da taketa yi tana sake kammala musu kayansu na tafiyar da zasuyi a gobe saman idanunsa ne. Tun a yanzun ya dinga jin wata kewa tana ratsashi.
Bai tashi a gurin ba har fadeela tayi bacci a jikinsa,sai ya gyara mata kwanciya yana canza tasha zuwa News channel.
Sai data tabbatar komai ya kammala,ta canza kayan bacci fadeela kawai zata dauka su kwanta sai ta zura hilabinta ta sanya slippers dinta ta fito falon don dauke fadeelan su kwanta.
Takunta ya sanyashi waiwayawa,kallo daya tak yayi mata ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana harbawa,cikin baby hijab din jikinta fuskarta tavi wani mugun kyau,tattausar rigar baccinta me gajeran hannu ta fidda qirarta ta coca-cola shape, duk da idanunsa baya kanta amma idanun zuciyarsa yana tattare da ita,ya kuma qididdige takunta har ta iso gareshi,ta kuma duqa zata dauki fadeelan
“¡dan kin kwantar da ita ki kawomin coffee daki”
“Tom” tace da shi ba tare data kawo komai cikin ranta ba, don zuwa lokacin ta fannin abinci bata ayashi ta data ta bashi. Ba abinda take tunawa a duk sanda ya bugaci abinci sai yadda yayi missing mahaifiyarsa a shekarun da yake da buqatar kulawarta,hajiya qarama ta shiga tsakaninsu,ta tarwatsa soyayyar da Allah ya ginata,sannan ita din bata zauna ta basu irin kulawar da uwa ke bawa danta ba.
Kasancewar sai ta tsaya ta dafa ya dan ja lokaci wannan ya bashi damar gama nasa shirin baccin.
Yana zaune saman gado rabin gafafunsa lullube da duvet ta shigo dakin da sallama. Bata lura ds kallon da yake binta da shi ba,saboda ta qagu ta gama dashi taje ta kwanta ta samu isashen baccin da zata farka tsakiyar dare tayi addu’a ta musamman saboda samun dacewa da nasara.
“Migo min” ya fada a nutse yana lumshe ido, sassanyan qamshinta yana hautsina tunaninsa tare da qara masa kwadayinta.
Hannunsa cikin nata kamar yadd ya saba mata duk sanda zata bashi wani abun sha ya riqeta tsam. Duk zafin coffee din haka ya dinga kurbarsa da zafi zafi saboda wata wuta ce ke ruruwa cikin ruhinsa da zuciya,dama kowanne sashe na gangar jikinsa.
Kurba hudu kacal ya gama dashi,ya zare cup din da daya hannun yayi wurgi dashi cikin zafinsa, saboda ji da yakeyi cikin jikinsa yakai maqura. Gaba dayanta ya fincikota jikinsa,ta samu kyakkyawan masauki tsakanin girjinsa da tsakiyar qafafunsa,yayi mata wata zazzafar runguma yana laluben bakinta da nasa bakin dake dauke da dumin coffee.
Kyarma jikinta ya fara yi ganin yadda gaba daya yake a gigice yadan dakata kadan yana duban idanuntà da jirkitattun idanunsa tamkar wanda yasha abun maye
“Baki d imani wallahi, kin sani sarai yadda na jigata a kwanakin nan, amma kin dauke kanki kamar baki sani ba,har yanzu baki sona ne?, ko irin dan kadan din nan ki soni mana don Allah” ya furta kamar zai shide saboda yadda qamshinta da dumin jikinta ke sake birkitashi,ga abubuwan dake tone masa ido yau din suma cikin yancinsu suke, don rigar baccin ne kawai a jikinta
“farewell mee…” Kasa garasawa yayi saboda
muryarsa gaba daya ta sarqe, sai ya lalubi bakinta ya fara aike mata da wani zazzafan kiss kamar zai cinye bakin, saidal kuma cikin taushi da laushi.
Duk yadda take zaton jikinta zaiqi karbar abun sai zancan yasha banban,a duk wani saqo da ya aiketa masa sai ta samu jikinta ya karbeshi da kyau har fiye da yadda ya kamata. Yaqi ta dinga yi da zuciyarta saidai itama zuciyar tako ina lugiguita yakeyi cikin salo da qwarewa,duk da haka saboda qi fadi bata fasa yunqurin tureshi ba.
Cak ya dakata da abinda yakeyi, sanann a zafafe ya kama hannuwanta yayi musu kyakkyawan rigo yana kallon tsakiyar qwayar idanunta fuskarsa a dinke tsaf. Bai shirya ba wata qaramar dariya ta kufce masa yana sake ci gaba da kallon idanunta da suka sauya launi, tabbacio ko ta ina itama sagon yana isar mata
“Malama you are just pretending fa,amma tun daga zuciya gangar jiki dama ko ina na jikin sun nuna suna karban saqo,so stop please,let’s enjoy our selves”
kunya ce ta sanvata tattarashi ta tureshi da sauran garfin da ya rage mata, baiyi musu ba ya fada gefe,sai yayi rigingine idanunsa a lumshe yana sakin boyayyen murmushi
“Okay,baki buqata ko?‚am sorry you can go” ya fada yana jan duvet ya lulluba har kansa. Minti daya biyu sannan yaji ta motsa tana shirin sauka,ya birkitota da sauri ya aza mata nauyinsa yana dariya
“Ki daina pretending din nan,ki fada kanki tsaye, kina bugatar mijinki simple and easy” bai bata damar yin magana ba ya hade bakinsu guri guda.
Bata sake turje masa ba,saidai cikin ranta ta cika da mamakin yadda komai yake kai mata inda bata zata ba. Da wannan damar shima yayi amfani ya kwance mata lissafinta tasss fiye da wancan ranar, shima dai daga
baya kukan kunya ta saki,ya biye mata yana bata haquri dariya kuma na cinsa,yayi mata kyakkyawan masauki a faffadan qirjinsa ta boye fuskarta da kyau tana kula
“Kiyi haquri,tsautsayi ne ko? ‚kuma baya wuce ranarsa” ta fahimci gatse yake mata,saita tattarashi ta ture tana sauka a gadon ta nufi qofa bayan ta lalubi rigarta da ayar. Baiko motsa ba saima gyara kwanciyarsa da yayi yana dariya qasa qasa,ya fuskanci idan ba sauketa yaci gaba da yi daga kan layi ba ba zai taba sauke mata zafin kanta a nan kusa ba
“Idan aka shiga turaka ba’a fita sai da asuba koma da safe” dole ta dakata, kamar zata saki kuka ta dawo da baya ta zauna bakin sofa bed. Kusan minti sha biyar tana zaune,har ya miqe ya shiga toilet yayi wanka ya fito.
Gajeran wando ya sanya wani cotton fari qal,ya shammaceta ya isa gabanta. Hannu ya sanya ya lakuce dogon hancinta
“Indai kikaci gaba da wannan abun bayan kun dawo daga tafiya tabbas aure zan gara” daga haka bai jira komai ba ya sunkuceta ya wuce gado da ita. Tas ya tube rigar data sanya ya kuma matseta cikin jikinsa yana lullubesu da duvet tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya. A duk sanda ya samu wani mu’ amala tsakaninsa da ita yanajin duniyarsa kamar ta banbanta datà kowanne dan adam,wata mahaukaciyar soyayyarta da kullum yake goqarin ya saisaita kansa da ita kada ya wuce gona da iri qara ninkuwa takeyi cikin ransa. Yayi imanin batasan me yakeji tattare da ita bane,da duka ta sauke abinda takeji din akansa. Can qasan maqoshi tsakiyar kunnuwanta ya furta a hankali
“| always sleep better with you by my side,gobe da sauran kwanakin bansan ta yadda zanyi bacci me dadi har haka ba,to be honest,at this point in my life, i just need one women to love me hard, and never leave me alone” ya furta da alama har cikin zuciyarsa abinda ke ciki din kenan. Kashe mata jiki kawai yayi gaba daya,saita lumshe ido kawai ba tare data sake motsawa ko tace komai ba.
Da asuba ma bai ayaleta ba,kiran sallar farko taji ya sake cewa
“I want to water the plants” bata sake tunani na biyu ba ya sake wurgata wata duniyar,yayi alqawarin sai ya bar mata abun tunawa tun daga tafiyarta har dawowarta,muddin baiyi hakan ba ya tabbata looser,bai kuma amsa sunansa na Muhammad toufeeq ba,yaci alwashin goge mata haddarta fes da duk wani daagiya tata da qi fadinta.
****Qarfe tara na safiyar ranar suna a filin sauka
da tashin jiragen sama na mallam aminu kano.
Yana rige da hannun fadeela,fuskarsa da safiyar yau din ke cike da annuri cikin shigar farin yadi na maza me taushi wanda yake da shara shara har kana iya hangen fara qal din vest din jikinsa,ginannen jikinsa dake a tsaye qyam ya zauna cikin dinkin ya kuma dace dashi.
Sassanyan kyansa me cakude da kwarini ne shimfide akan fuskarsa,zubin halitta da kyansa kuma yana ci gaba da fusgar hankalin duk wata diya mace.
Sãahar na tsaye a gefe cikin doguwar riga sakakkiya sosai wadda ta yiwa rolling da mayafin da ya sauka har mazaunanta ya rufesu sosai,shiga ta biyar kenan da tayi a safiyar kafin ya danne zuciyarsa ya haqura aka taho a hakan.
Haka kawai yau din ta samun kanta da satar kallonsa,kyakkyawan murmushin sa da wani irin aji cikin maganarsa da aikinsa. Karo na barkatai idanunta ya sauka akan fuskar ‘yammatan dake facing dinsu,ta sake samu idanunsu a kansa dukka su biyun. Janye dubanta tayi daga kansu tana jin wani abu yana tsaye mata a wuya. Sake maida kallonta tayi kansa a sace,sai takejin babu dadi cikin ranta, tunda suka fito cikakkiyar magana bata hadasu ba,yayi ma kamae baya ta tata, dukka attention dinsa na kan fadeela.
Zaman gaba daya taji baiyi mata ba,kallon da matan dake gurin suke masa taji ya fara hawa kanta,duk da wani sashe na zuciyarta nason qaryata hakan, amma tabbas tasan she’s not comfortable. Ajiyar zuciya ta sauke sanda lokaci da zasu wuce zuwa ciki yayi. Sai a sannan ya waiwayo suka hada ido,sai ta janye idanun nata gefe tana tura baki gaba wanda ita kanta batasan tayi ba,a qasan ranta tana cewa
“Dan rainin hankali sai yanzu yasan ina wajen” shi da fadeelan suka qaraso gurin,ya miga hannu a tausashe ya rigo nata hannun yayi kissing sannan ya dage hannun sama alamun yanason miqar da ita. Kamar ba zata tashin ba, amma idanun mutum biyun nan da sukafi kowa baci a gurin ta fahimci yana kansu,sai ta samu confidence sosai na miqewar, tana kuma miqewar ta fada jikinsa tayi hugging nasa tightly.
Zafafa biyar
??????????????????
??????????????????
[04/10, 8:52 am] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 45"