Tabarmar Kashi Book 2 Page 44
*_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 44
Karon farko ta isa gidan aminiyar dake gaunarta dason qawancensu,ta shiga baqinciki da tashin hankali itama tayita roqon maji ta zauna dasu tace a’ah, tabar nigeria kenan har abada daga lokaci irin wannan, alfarma daya take nema tayi mata magana a landline phone dinsu da yayanta ya siya mata ticket na komawa
“Allah ya sawwage ace har saikin nemi yanuwanki” a aljihunta ta siya mata ticket din, kwana biyu kacal maji ta qara ta koma Algeria,wanda tunda tabar nigeria bata gara waiwayarta ba sai a wannan lokacin.
Kawa ga maji ita taci gaba da bibiyar al ‘amarin su toufeeq kafin fauziyya ta ganota ta hanata shigowa gidan da ganinsu gaba daya. Cikin ikon Allah ta shiga neman mai aiki saboda a lokacin ta soma bungasa kasuwancinta da tafiye tafiye,ta kuma qulla aure tsakanin yayanta da daya daga cikin qawayenta,auren da sukayi yarjejeniya tsakaninta da qawarta ta.
tata. Ruqayya qawar maji ita tayi wuf ta aika da baaba ramatu,saboda yadda da amintar da tayi da ita,ta kuma tabbatar zata bawa yaran dukkan wata kulawa tare da kula da lamarinsu. A hankali baaba ramatu ta fuskanci yadda fauziyya ta kawar da hankalin yaran gaba daya daga ganin kima da jin maganar kowa,duk abinda ta shimfida ya zauna daram. Da farko maji na kiransu,idan aka kwana bivu bata kira ba zasu nemi babansu ya kira musu ita suyi magana sannu sannu sai gashi gaba daya daga yaran har babansun sun soma mantawa da wata mai suna MAJI sam cikin gidan,duk wata kewa da qulafucinta da sukeyi ta sanya anzareshi tsaf daga ransu,sai abinda tace sai abinda takeso.
Tun ba’a ie ko ina ba ta raba auren maryam qawarta da dr jarma,ta sake kutun kutun ta aura masa murja itama bayan wasu shekaru ta raba auren da salon kissa da kuma asiri. Cikin shakarun sai data aura masa mata hudu tana sanyawa yana sakinsu, mace ta garshe da ta aura masa mansura. Mansura itace babbar aminiya cikin gawaventa, kuma ta kashe aurenta ne don kawai tazo fauziyya ta aura mata Dr jarma,ta fito daga gidan baban labiba ta baro yara hudu labiba auta ta biyar,can qasan zuciyar mansura itama danqare fal da buri da nata qudurin na mallakar Dr jarma da uban dukiyar da ya fara tarawa a dare daya.
Mafarin rashin gaunar da toufeeq yake yiwa mansura din ya samo asali ne da zuwansa gidan wata rana,a lokacin duka duka shekararsa sha biyar ya samu tana yiwa Dr jarma barbaden magani, wanda kusan maganin nata ne data fauziyya,yawanci mansura ita ke sabuntawa fauziyya aikinta,saboda komai yana tafiya mata dai dai,rayuwa tana mata yadda takeso,bata bugatar Dr jarma ya koma Mahmud dinsa, ta tabbatar inda har yanzu maji na cikin rayuwarsa babu lallai takai matsayin da take kai yanzu a rayuwarta.
Komai yana iskar maji ta hanyar ruqayya,co sau daya bata taba sassautawa wajen yiwa yaranta addu’a ba,tasha hana idanunta bacci saboda sallah,ta sha hana cikinta abinci saboda azumi, duka tana yine saboda nemawa yaranta kariya,a kullum idan ta kwanta babu abinda ke mata yawo a kunne sai kukan nadeeya dana toufeeq, wani irin kuka me karyar da zuciyar me imani suna kiran sunanta,kukansu na qarshe da taji bata kuma sake ji ba saidai tayi hasashe.
Shekararta biyar da rabuwa da DR JARMA sannan tayi wani auren,saidai auren duka duka shekara biyar mijin ya rasu, bata kuma sake sha’awar sake wani auren ba,ko wancan matsantawa ce ta yayanta guda daya daya rage, shekara biyu kadai da yin auren kuma ya rasu.
Sau biyar hajiya qarama na yin aure bayan aurenta na fari da ya’aqoub, amma auren baya wani lasting sal ta fahimci ba don komai suke aurenta ba sai don abinda ta tara,saita sallami mutum tunda yawanci auren dauki sandarka ne. Allah ya jarabceta da sha’awar auren amma haka ta tattara ta haqura saboda tsoron kada abinda ta Jima tana yaqi akan tarashi ya salwanta. A karo na shidda ne taga DR GIREMA(mahaifin säahar), a lokacin suna abota sosai da Dr jarma kafin rayuwa ta cilla kowa wani sashe na daban. Ta mutu sosai akan dan mutanen borno shuwa arab na asali dake da kyau na burgewa,irin kyan da take ganin yayi dai dai da nata kyan. Ta soma shiga da fita akan a jawo mata hankalinsa,cikin ikon Allah duk inda take tunanin nasara babu ita,a hankali ta fahimci matarsa tsayayya ce,ta tsayawa kanta da mijinta da addu’o’in tsari,sannan gwanace kuma qwararriyar mace wadda ta amsa sunanta wajen iya kula da miji tare da dasa soyayyarta me zafi a zuciyarsa,don duk inda ka zauna dashi zama ya danyi tsaho sai yayi maka zancan AMINATOUnsa. Tayi barnar kudi akan dr girema kamar ba gobe amma kusan a banza za’a ce,don babu wani ci gaba ko nasara data samu,tana ji tana gani haka ta haqura da shi, don ta fahimci kallon ganwa kawai yakeyi mata, daga gaisuwa kuma babu abinda yake qara shiga tsakaninsu.
Abinda maji ta mallaka daga gadon iyayenta da tumunin takabarta data samu shi ya shiga kasuwanci dashi babu kama hannun yaro. Family dinsu babban family ne kuma sananne da suke da mutane masu tarin muqamai kala daban daban,wannan yasa bata wani sha wahala ba kasuwancinta ya samu karbuwa daga gurin matan manyan qasar ta Algeria, a hankali kuma sai ya fadada zuwa qasashen qetare maqwabta,harma da
Nigeria din kanta, amma bata taba yarda ta saka qafarta Nigeria ba saidai aike, duk da cewa Zuciyarta da gangar jikinta ko da yaushe tana kan yaranta,tana kuma bibiye da dukkan wata nasara ko faduwa tasu.
Taso zuwa auren toufeeq na farko amma hajiya qarama ta aike mata da saqon basa gayyatarta. A sanda sagon ya isketa tana asibiti bata da lafiya,saita saki murmushi kawai tana girgiza kai. Ta sani tabbas addu’a babu abinda ya kaita kaif,ta jima ta fahimtar wata muguwar shakkarta da tsoronta ya shigi hajiya qarama,gamuwarsu kuma shine abu na qarshe da bataso. Ciwonta shi ya hanata zuwa bawai barazanar banza da wofi ta hajiy qarama ba,ta barwa ranta akwai lokaci na gaba,akwai kuma dama ta gaba,don tana ji a jikinta dama lokaci yayi da zata tabbatarwa da fauziyya yaranta data bar mata,ta bar mata su raino ne kawai,ta gama yanzun kuma zata karbi ajiyarta.
Sanda taji matar toufeeq ta haihu sai taji kowacce soyayya tata ta tattara akan FADEELA, tun tana jaririyarta har kawo shekarun da take kai a yanzu,sai taji tamkar itace ta yiwa nadeeya qanwa. Wata iriyar soyayya ce da bata boyuwa sam sam,wannan ya sanya hajiya qarama karkade makaman yaqinta data binne,ta kuma tabbatarwa kanta lokaci yayi da zata dawwamar da hajiya qarama cikin toro firgici da kuma zulumi
_wannan kenan_*
_sauran warwarar lamuran suna nan a gaba kadan zakuji komai filla filla_*
“sauran duka abinda fauziyya ta aikatawa rayuwata data su moha wanda idanu basa iya gani ita daya ta sani,sai kuma ubangijin sama da qasa,wanda idan yaso bayyana komai zai bayyana shi ba tare da wani jinkiri ba,wannan itace fauziyya,wanann itace hajiya qarama, kina tunanin akwai yanayin da zaizo wanda zai sanya na manta wacece ita?,na baki goyon baya dari bisa dari ki fita da fadeela,ba’asan abinda Allah ya hukunta ba,zama ba shine mafita ba tunda har akwai chance na yiwuwar warkewarta” gaba daya jikin säahar ya gama yin sanyi,duk gwiwarta ta mutu,cikin ranta tsoron Allah yana sake kamata,ashe ire irensu adam da momee suna da yawa a duniya? ‚ashe har yanzu mutane basa ji a jikinsu bisa yarda da imanin akwai ranar sakamako?,a yanzun bata ko shakka ko kokwanto,hajiya qarama zata iya aikata komai ma,sannan qarfinta ya karkata dari bisa dari akan sanya hannunta da ta’azzarar ciwon fadeela,ta sake imanin akwai wata boyayyar manufa tata data sanya take matsa qaimi akan duk wanda yace zaiyi maganar a yiwa fadeela aiki,ita ta cusa toro da fargabar surgery na fadeela a zuciyar mahaifinta,hakan na nufin shi dinma yana kan wani TARKO nata ne kenan ba tare da ya sani ba?. A karon farko wani tausayinsa ya sauka ya lullube zuciyarta, idanunta da suketa zub da qwalla
suka saka tara sabon hawaye tana jin radadinsu dikin
idanunta,da gasken gaske maji taga rayuwa,ta hadiyi
abinda ba kowacce maca ce zata iya hadiyarsa ba
“Ki ajjiyemin account number dinki, zan saka miki duk iya
adadin abinda zaku kashe da wanda zaku buqata,wacceqasa ce?”
“Germany ne maji,bonn, amma don Allah mai, inason nayi wannan aikin da kudina ne, ko da duk abinda nake dashi zai qare, ina kwadayin ladan” kai ta gyada
“Bansan wanne lokaci zaya daukeni kafin na samu visa
din can ba,tunda ban taba shiga ba,amma zanyi iyakar
bakin goqari na,ina matuqar alfahari da wanzuwarki cikin ahalina khadijatu,banzan kuma da kalar bakin da zan miki godiya ba”.
Hirarsu da maji a ranar ta maqale mata a wuya,ta yini
tana juya abinda suka tattauna da ita. Yau gaba daya sai ta kasa fita a sashen,saidai duk wani motsi idan akayi cikin gidan yana kan kunnenta,sai ta dinga jin taron data baiwa fadeela a baya ma kamar yayi kadan, kamar hajiya qarama zata iya yin wani motsi don ta cutar da fadeela,don haka a idanunta da kunnuwanta motarsu ta shigo gidan,cikin motar toufeeq jarma wanda a yanzun ya zamana vadda suke fita tare tare suke dawowa.
Labulen ta sauke tana sakin ajiyar zuciya sanda ta tabbatar sune tanason taje ta tari fadeelan amman kuma tasan suna tare ne da toufeeq. Har yanzu wani matsanancin kunya ce take lullubeta idan ta tuna abubuwan da suka faru a dazun,wuni tayi abin yana dawo mata tana mamakin kanta na vadda ya sanyata ta saki layi haka lokaci daya, sai ta juya a nutse ta koma kitchen din,ranar farko da zata girka wani cikakken abinci a ciki.
Yadda jilkinta vake a sanyaye yau tasan ba lallai ta gama abinci da wuri don haka tun bata dora ba ta fara yiwa fadeela pancakes da smoothie ta ajiye mata,sai fura data dama daban Incase ko batason smoothie din.
Tana aikin yayyanka vegetables amma hankalinta yana cikin gidan. Tana jin lokacin da suka bude gofar suka shigo,fadeela ta rada mata kira da kyau. Tanason ta amsa amma idan ta tuna da toufeeq na gurin sai ta kasa. Har zuwa sanda fadeela ta kalleshi
“Abby,ko anty N na wajen baaba ramatu?” Kafada ya maqale yana murmushi tare da dan tabe baki
“Muje na rakaki ki gani” ya fadi can qasan ransa yana jin zumudin ganinta.
Sallamar yarinyar cikin kitchen din ya sanyata sakin abinda takeyi tana amsawa ba tare data juyo ba
“Anty,yau bakiyi welcoming dina ba” fadeelan ta fada tana togewa daga bakin qofar gami da qin qarasowa ciki.
Qaramin murmushi ya saki yana jin farinciki na saukar masa a zuciyar ,kamar fadeela tasan muradinsa a yanzun na kallon qwayar idanun säahar din,wanda ya tabbatar ko zai narke a banza ba zata bari ya gani ba.
Gyara tsaiwarsa yayi sosai yana sake zube idanunsa a kanta,tana sanye da high tummy skirt na yadin chiffon wanda aka yiwa qananun tattara ainun,hakan ya santa qugunta fita das a jikina,ya kuma fitar da shape dinta.
Rigar jikinta ta plain chiffon din ce wadda ta dace da skirt din jikinta, gashinta na nannade a boye cikin dankwalin kayan. Idanunsa ya lumshe yana fitar da iska tun daga hunhunsa,hancinsa na dawo masa da sassanyan qamshin gashinta wanda yake jinsa kamar yanzun yake nutsa kansa cikin sumar sa. Tana takowa idanunsa nakan lips dinta,baya gajiya dasu sam, akwai sirri me yawa da wani irin softness samansu
“‘Faddee rigima” ta furta a hankali, abinda ya bawa lips din nata damar motsawa da juyawa a hankali, wannan ya sanyashi sake fidda wata iska me nauyi ta hancinsa.
Duqawa tayi tana karbar lunch bag da school bag din
fadeelan
“Sannu da zuwa” ta fadi ba tare data dubi sashen da
yake ba. Banza yayi da ita kamar baiji ba
“Sannu da zuwa” ta sake fada still da yanayin dazu,sai a sannan ya saki hannayensa yana dan waiwayawa,kamar me neman da wanda take magana
“Da wa kike?” Yayi mata tambayar da ta sanyata daga
kanta zuwa gareshi cikin mamaki, don dai ita bataga
kowa a kitchen din ba saishi da ita sai kuma fadeela
“My angel, karba kayanki ki qarasa dasu daki,oya” ya fadi yana duban fadeelan. Bata musa ba ta miga hannu ta karba komai nata da sãahar din ta cire, ta kuma fella da gudu ta fice ta barsu a tsaye.
Da kallo säahar tab fadeela duk data qule, gabanta na
faduwa kadan kadan,tana tsoron kada ya zamana wata muguntar ya sake hada mata,har yanzu bata warke daga mikin jiya ba. Bata gama tunanin ba kuwa tattausan gamshinsa ya ya soma ratsata qofofin hancinsa,ta daga idanunta ta kalleshi, karon farko da yaga karaya da tsoro a cikinsu. Taku ta fara yi da baya yana biye da ita,cikin zafin nama ya sanya hannu ya rigo qugunta ya tsaidasu cak shi da ita tsakiyar kitchen din yana jifanta da wani shu’umin kallo da narkakkun idanunsa
*HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI*
Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 44"