Soldiers Family 9-10
Page 9&10
__”tana me hantsilowa daga k’asa kamar wata aljana hakan tadira gunda eggo tafad’i juyo da ita tayi, tana kallon yadda jini ya
b’atawa tsohuwar fuska cikin tashin hankali, ta shiga girgizata tana fad’ar sunanta Amma ko gezau eggo batayiba…abunda mama Bata saniba tuni eggo takarb’i Kiran mahaliccinmu….
Shiko wannan banzan mutumin wurinta yadawo tare da zabga mata marin da saida ta ga wasu taurari, Babu Imani balle tausayin ganin ya kashe mata mahaifiya hakan yak’ara fisgarta tareda wullarda ita awurin….Amma ni k’ememe mama taki kai k’asa gata dai ta tafi kad’an ya rage bayanta ya tab’i kasan tinda jefata yayi Amma be tab’a ba Kuma bata ta soba….duk Wanda kewurin kallonsu yakeyi cikin mamkin wannan abun ciki kuwa hadda sauran Y’an ta,addan Yan uwanshi.
Kuma yazo zai turata dak’arfi…kamun hannunshi yakai jikinta yayi Bala,in Jada baya saka makon idonta data bud’e hawanyen jini nafita bako k’ak’k’au tawa sun wani birkice kamar ba nata ba….duk Ido suka zaro suna kallonta…itako ahakan ta taso tana mik’ewa tsaye kamar ana turo icce ko saÆ™aho.
Baya sukaja dukkansu suna Kara kallonta amutukar tsorace suna neman fecewa…itako mama cikin k’ank’anin lokaci kamannin ya sauya kamar aljana.
Wani daga cikinsu ne ya yarda bindigar hannunshi, tare da rugawa aguje domin ya gama sadak’arwa yau aljana ce suka Æ™wamuso ba mutum ba….ai beyi aune ba yaji anfin cikoshi tare da makashi akan wani dutse atake kansa yatarwatse ko shurawa beyiba yace, “Ga garinku nan”
Ihun sauran suka saka ganin mama ko daga inda take bata motsa ba Amma Tamik’arda hannunta tacimma wannan mutumin harta kamoshi….ba,iya Yan ta addaba duk da sauran mutanen da aka kamosu tare ahalin yanzu amugun tsorace suke fiyeda Wanda sukeji daga farko…..tsayetake kawai tana k’arewa duk Wanda ke wurin kalllo kamun tashiga d’aukarsu d’aya bayan d’aya tana makasu afuk inda tasamu wasu akan dutse wasu akan manyan bishiyun dake wurin wasu Kuma kasa seta tabbatarda ta karairayawa mutin kasusuwan jiki kana tayi masa d’aya Wanda baze Kara numfashi ba…..iya tashin hankali yan ta,addan Nan sunshiga domin izuwa wannan lokacin sun riga da sun yadda da aljana ce suka sato domin duk ya wansu gashi tana neman karardasu Kuma Kara Yar Loma figigiya da ita.
Ahakan mama tayitayin tamaula dasu seda taga bayansu Wanda yakashe yarinya kuwa biyu tarabashi domin kafawanshi tarik’a tareda yageshi gida biyu duk Wanda ke wurin seda yarufe idonshi….datazo kan Wanda yakashe eggo kuwa kisan wulakanci tayi masa domin seda tagama ragargaza kasusuwan jikinshi kana tashiga É“allahsu gab’a gab’a tana jefarwa seda taga yagama nakassa da galabaita yasuma Babu adad’i azaba na farfad’o dashi kana ta cire mashi kai tawulgar…..dubawa tashigayi ko Ina tananeman taga ko akwai Wanda yarage Amma ba ko d’aya…suko sauran bayin Allah da,asatosu tare gabaki d’aya sun cure wuri d’aya wasu duk sun suma sabida firgita wasu kuwa kamar zukatansu subuga saboda razana….ganin Babu saura b’atagari awurin sekawai tasamu gefen bishiya tazauna tareda rufe idanuwanta.
Ganin hakan yasa sauran bayin Allah sukad’an samu natsuwa acikin ransu domin sunyi tunanin daga ta gama da Yan bindigar gunsu tayo…..sund’au tsawon lokaci ahakan kamun wani daga dattijuwan wurin yayi k’arfin halin nufar wurinda gawar eggo take seda yaduk’a Yana kallanta yaga tabbas Bata numfashi d’agowar dazeyi yaga mama tabud’e idanuwanta da har yanzu basu sauyaba tana kallanshi seda yad’an zabura da kallon datayi nasa domin ya razana sosai sekawai yaga tamayarda idonta ta lumshe ajiyar zuciya ya sauke mek’arfi kana sauran Mata dake wurin sukazo suka d’auketa daganan kana wani dattijo Daban yaje kusan mama cikin tsoro da fargabar abunda zuwan nashi ze haifar yafa fad’ar y’ata Dan Allah kiyi hak’uri kitashe muje cikin gari kekaigun dankinku akai gawar baiwar allarnan…shru mama tayi kamar bazayi maganaba sekuma tabud’e Baki dakyar cikin wani voice me ban tsoro tace bansan inda danginta sukeba kawai kuyimata sitira kamar yadda addini yatanadar.
Cikin sauri tsohonnan yace, “to shikenan yarnan tashimuje cikin gari ayimata suturar”….”kuje zanzo ta fad’a atak’aice”… Tun Bata rufe baki ba yace, “to shikenan sekin k’araso” Yana gama fad’ar hakan yabar wurin domin shikanshi da basin mama yayi ba Adan zaman da sukayi yasan ba muryartace ba tunda yanaji tana yiwa mamarta magana wani lokacin.!
Yana zuwa tasanarda Yan uwanshi Aiko suka d’auki eggo akayi cikin gari da ita duk da sunci bak’ar wuya kafin sufita saboda nisanda kenan…bayan sunfitone Allah yakawo musu wata mota babba kamar boss duk sukashi bayan sunyiwa memotar bayanin inda zekaisu..
Basu tsaya ko ina ba seki dan wani daga cikin dattijuwan suna Isa ba suka Sami mama zaune ak’ofar gidan ba wanda yayi mmkin ganinta Idan sukayi duba da abunda ya faru b’ata lokaci akashiga yiwa eggo sutura domin sadata da gidanta na gaskiya…sai da duk aka gama yimata komai za,afitada ita kana d’aya daga cikinsu yazo domin ya kira mama taganta kafin su fita da ita…Amma seya samu tana bacci mamaki sosai abun yabashi harzetafi yabarta sekuma sekuma wata zuciyar tace yatadata hakan yashiga tadata yad’an jima Yana Dan buga k’afarta kamun tayi firgigit tamik’e zaune tana rarraba Ido tareda doba inda take atake atake abunda yafaru yashiga dawo mata tun inda wannan mutumin yafincikota har hankad’e eggo dayayi wani irin zaro Ido mama tayi tareda mik’ewa tana fad’ar, “eggo eggo kina inane Ina mahaifiyata? Me mukeyi anan? Misuka Mata? Dan Allah Ina sukaimun eggo ta?” K’wallah wannan bawan Allah yashare kamun ya janyo hannunta izuwa inda gawar eggo take kwance..Yana zuwa wani ya bud’ewa mama fuskar eggo daketa fitadda anuri cikin suturarta kamarba matacciyaba…wani irin jaa baya mama tayi tana k’walalo duka idanuwanta kafin ta k’wall k’ara tana Kiran eggoooooo innalillahi wa innailaihhiraji un nashiga ukku 🙆 Ni mama sunkashemun mahaifiyata ba tare da takaini garinsu ba sun rabani da farin ciki na na shiga ukku Ni mama…. kuka takeyi sosai akan gawar eggo dakyar aka d’aga ta wata mata tayi cikin gida da ita kana aka tafi kai eggo gidanta na gaskiya….ansha fama da mama awannan wunin domin in banda kuka ba abunda takeyi ahakan har dare yayi duk me Imani Idan yakalli mama dolene ya tausaya mama Inka duba karancin shekarunta Babu uwa Babu uba bawani takamme ko jigo arayuwarta😥….cikin dare Mama nazaune tana rusar kuka kowa yayi bacci itace kawai Ido biyu…dafata taji anyi Koda tad’ago taga wata mata tayi shigar fararen Kaya da murmushi kwance a fuskarta…cikin kuka tafad’a jikinta tareda cewa k’awata Ina kikaje sunkashemun eggo ta sunkashet….kasa K’arasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta be hanata ba sai da tayime isarta kana yad’ago ta tana share Mata hawaye kamun tace ba k’awarki bace mama yayartace k’awarki da bibibo basanan sunyi tafiya me Nisan gaske domin cika umurnin me martaba nikaina bansan abunda kefaruwa dakeba sai da abokin bibibo d’inki yasanar dani kiyi hak’uri mama munkasa Baki farin ciki kamar yadda muka d’auke alkawari munkasa tare Miki faruwar wannan abunda yasameki Amma kiyi hak’uri komai na duniya me wucewa ne watarana sai labari, ki d’auka wannan abunda yasameki k’addara ce daga ubangiji insha Allah komai zai zo ya wuce kinji.
*ZARAAH* d’agowa mama tayi dasauri tana kallan matar Jin ta fad’i asalin sunanta…itako murmushi kawai tayimata tare da shafa kanta tace nizan tafi kinji kirika yiwa mamarki addu,a kidena wannan kinjiko? Kai mama tad’aga cikin sauri kana tace zanbiki kikaini gun bibibo na bazan iya zama ananba Idan narufe Ido eggo nake gani kamar zata dawo tak’arasa zancen ciki kuka…”shikenan ya,Isa mama zanjeda ke Amma bibibo bayanan sedai Idan yadawo Zaki ganshi Zaki iya zama,inda nake? Daga matakai mama tayi cikin sauri..tace to shikenan rufe idonki…ba musu mama tarufe idanuwanta wannan matar ta b’ace b’at daga ita har mama kamar Basu tab’a wanzuwa awurinba..!
Tofa 🤔 wayannan bayin Allah wasukayiwa alkawarin zasu bawa mama farin ciki? Shin meyema had’inta dasu? Dasuka kasance wani gefe na rayuwarta?
Koda safiya tawaye mutanen gidan suka nemi mama sama da k’asa suka rasa abun kamar wasa har dare Babu mama abubu Alamarta megidanne yace sukwantarda hankalinsu kila mutanen datake taredasune suka d’auke ta tindadai ba wanda yashigo gidan balle ayi wani tunanin daban….sai a lokacin hankalinsu yad’an kwanta dudda basuji dad’iba Sam domin sunso rike mama tsakanida Allah domin tabasu tausayi matuk’a sai dai ba yadda za suyi da k’addarar rayuwarta..!
London
Wata baturiyace tsaye bakin k’ofar office d’in alyasat tana rike da wani abun ahannuta me kama da babyn roba (y’ar tsana) sedai kallo d’aya zakama abun kasan ba alkhairi a tare dashi duk’awa tayi wurin tana k’ok’arin daga carpet d’inda ke wurin sekawai muyar lateep Yana fad’ar leamtair mikijeyi ananne? Cikin sauri tatura abun cikin kasan wandonta tashiga k’ok’arin zuge igiyar takallminta tana fad’ar takalmanane yakwance Sr shine Zan d’ora…. kallonta yatsayayi kamar me nazarin wani abun domin Sam be yadda da itaba Kuma lateep be,iya b’oyoba Kuma nuk’u2 shiyasa yace ba gaskiya bane leamtair akwai dai wani abun Amma kasani ko miye nagani atare da brother na hummm….Yana gama fad’ar hakan yashige nashi office d’in…da kallo tabishi tana tinanin Hali irin nashi cikin ranta kuwa fad’ar takeyi koza,a mutu saita samu abunda takeso atareda alyasat..
Yau Thursday tun safe alyasat ke kiran k’annenshi domin suhashi da mahaifiyarsu Amma besamu ba kum. Ya tashi da k’ulafucin San yaganta domin hakan kawai gabanshi ke fad’uwa….wayarsa yajanyo tareda Kiran yusif Yana d’auka yace “”bro I will go to Dubai now? “What happened Satt?” Cewar Yusuf… nothing just I love see my mom….”ok wait I’m coming now….okay kawai yace tare da yanke wayar yatashi yashiga wanka bayan minti 15 yafito d’aure da towel akugunshi d’aya Kuma ahanunshi Yana tsane kanshi wurin mirror yanufa yashafa mayukanshi masu kamshin dad’i kana yafesa titare wurin kala ukku kamun yad’auko kayanahi yasaka kananun kayane wando blue Riga Marron gaskiya bakaramin kyau suka mishiba sufitida asalin kyawun farar fatarshi wayoyinshi yakwasa da jakar computer d’inshi kana yafita aperlo yaci karo da Yusuf da lateep suma duk cikin shigar kananun kayane ajikinsu Masha Allah dukkansu kyawawane ajin farko Amma alyasat yafisu kyau domin kyawunshi na dabanne Kuma da shi da Yusuf sun É—an fi lateep tsayi shiko yafisu jiki… alyasat kuwa yafisu mird’ad’d’in jiki duk da suna ko wannensu ba baya ba…ahakan suka fita daga gidan cikin tafiya irinta majiya k’arfi masujida kansu way’anda hutu da nera suka gama ratsajinin jikinsu….suna fitowa kowanne yaranshi ya shiga suka taso tareda bud’e musu motocinsu suka shiga ahakan suma duk suka shiga tare da barin gidan tsiyace kamar yadda suka saba tare da d’aukar hanyar filin jirgi…!
*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 kokuma kikira wannan number 👉 08107819124
Autar Alheri ✍️
🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)
*By Dr Yasmeen Ahmed*
Autar alheri ✍️
Post a Comment for "Soldiers Family 9-10"