Soldiers Family 63-64
Page 63&64
__”suna taka kafarsu aperlon Yana fara wata irin girgiza kamar za,ayi girgizar kasa, cikin sauri Alyasat yak’ara matse mama ajikinshi gam, suko way’anda kewaje kallon tsantsar mamaki su kema gidan kamun sukama jabaya domin har k’asa kamar zata tsage hakan takeyi.
Didi kuwa tanacan cikin d’akin tasafinta taga abubuwa sunfara tarwatsewa gamun d’akin yahau girgiza,,arazane yamik’e tafito perlon tana fine, dubemu meke shirin faruwane? tana Kiran aljanunta tamanta ko kayan tsafin bata cire ba, tanayin Ido hud’u da mama ganta yayanke ya fad’i sai da ta dafe kirjinta, magana suka faraji cikin wani irin sauti marar dad’in sauraro ake fad’ar.
“Kinyi yase meenat kinyi sake shindama ban gayamiki wannan ranar zatazoba? Dama na fad’a akwai lokacin da zaki tarwatsamu zaki hallakamu muddin bakidena bibuyar rayuwar ma,Isha da ahalintaba? shin bangamiki watarana surukar na,Isha zatakawo karshenkiba? Shin bangayamiki ki guji hafuwarki da wannan yarinyar ba? Tuntana jinjirarta saida nunamiki ita,,Amma kikayi birisda zancena saboda jaguss da dodo sun goya miki baya kika fad’ar Yar Nigeria zatazonan hartazama barazana agarekiko? To ai yau gaki gata ayau Kam alkadarinki ya karye ba wani sauran tsafi ko sihiri dazai yimiki tasiri Kuma tabbas wannan gidan Nanda wasu Yan lokuta zezama tarihi kinga tafiyata ba ruwana meenat baruwanaaa na haneku da aikata hakan bakujibaaaa yanzu ka sakamako yazooooo,yana gama fad’ar hakan kuma sai wurin yayi tsit.
Gabaki d’aya way’annan bayin Allah sunyi mutuwar tsaye Jin wannan sauti dazantukan da,akeyi kowa zuciyarshi fall tambayoyine acikinsu, Zeenah Tal’udu kusan Yar uwar tata cikin taraddadin abunda zataji tace “Didi me wannan zantukan ke nufi? Mekikeyi da wannan kayan dake jikinki? Waye wannan me wannan zancen? Kaddai kikayayyar dakikeyiwa ma,Isha takai ga hallaka? Kiyimun bayanin da hankalina ze iya d’auka Dan Allah.
Didi kuwa idonta dake bushe tawatsawa ammy batare da tacewa Zeenah komai ba tak’arasa kusan ammy gab da gab yadda zasu iya jiyo numfashin juna tace”na tsaneki ma,Isha kad’ai ce yarda nahaifa Kika zamemin matsala arayuwata tundaga haihuwarki nake samun matsala har kawo yanzu baka barni na huta ba yanzu kinzamo sanadiyar rasa komai nawa,,shiru yad’anyi kamun taci gabada fad’ar, “ni cenan na kwantar dake jinya kikakoma kamar gawa nice Nan na b’atar da mijinki kuma nice na mayarda mahaifin mijinki sak’aho Kuma na mantarwa da kowashi acikin zuciya hakan Kuma nicenan na kashe mahaifinki saboda shine sanadin faruwar komai yanzu gashi duk wannan abubuwan danasha wahala nayi surukarki ta kakata komai itada way’annan hasararrun…”kul meganah karki kuskura kikira yarana da hasararru domin Kece babbar asararriya wadda tayi asarar duniya data lahira kin tsani Yar cikinki kin wulakanta rayuwarta saboda wani banzan dalilinki akwai asararre aduniya Wanda yawuceki tsohuwar najadu kawai,,cewar ummansu maheer tana nunata da yatsa.
Shiru duk wurin yad’auka kowa da abunda keransa yayinda Alyasat ya cika yayi fam kamar zaifashe hakama twins abbe kuwa inbanda hayawaye Babu abunda yakeyi yayinda ammy tayi mutuwar tsaye tunani takeyi anya didi ce mahaifiyarta kodai akwai abunda Bata saniba? Shin metayiwa mahaifiyarta take kiyayya da ita hakan? Itadai a,iya saninta tasan cewa lafiya kalau take da Didi dukda Bata sake Mata kamar yadda kowacce uwa keyiwa y’arta Amma sanadin wannan kiyayyar aurenta da Habibullah ko maye silar hakan?
Murmushin bakin ciki Didi tayi kamun tace aikobaki fad’aba nasanda hakan sedai Kinga shugabar asararrinan tafad’a tana nuna ammy…cikin tafasar zuciya Alyasat yace, “uwata ba asararriya bace kece dai babbar asararriya kuma na rantse da wanda raina ke hannunshi Idan kika k’ara aibatamun uwa saina ajiye tsufanki agefe nak’arasaki lahira domin barin irinku aduniya had’ari ne”ya isa Alyasat karka k’ara cewa komai abbe ya fad’a daÆ™yar.
Suhaif da tund’azu bece komai ba sai tafasar da zuciyarshi keyi msa yake saurare shine yazo wurin yadubeta Ido cikin Ido yace “meganah mi ummynmu tayimi Kika tsaneta hakan? Har kike iya cutar da ita da abbenmu? Dukkanmu Nan munaso musani domin zukatamun susamu salamar akan kokwanto da mukeyi akan bakece mahaifiyar ammy ba.
“Abunda tayimun kukeso kusani? Yanzuko zakuji.
Shekaru 42 baya
Lokacin da Ina budurwa banyi aure ba akwai saurayin da nakeso shikuma mahaifina akwai Wanda yakeso na,aura wato mahaifin ma,Isha,,anbuga Dani Masa da k’asa na aureshi naki sai kawai wata Rana yabiyo dare yayimun fyad’e yarabanida mutincina, nayi kuka nayi bak’in cikin wannan Al,amari sanadin hakan abbana yace dolene shizan aura domin Wanda nakeso yagujeni bashibama duk wani me rab’ata yagujeni saboda hakan,,haka aka had’amun aure dashi akakaini gidansa abun mamaki Ashe wancan fyad’en dayayimun nasamu cikin ma,Isha har ciki yakai wata ukku kana akayi Mana aure ba Wanda yasani
Lokacin da cikin yabayyana bak’aramun bakin ciki najiba nayi yunk’urin zubardashi sau ba adad’i Amma hakan Bata samuba,Ina cikin wannan halinne wata k’awata tasameni inda takaini inda za,azubda cikin sai dai Muna zuwa shugaban wurin yace, “bazasu zubadda cikiba domin suna buk’atar jinin y’arda Zan Haifa Idan zanbasu” na ce, “kuwa nama basu mizanyida Yar shegiya Kuma jinin mak’iyina”,mukabar zancen ahakan nacigabada renon cikinta har lokacin haihuwa yayi bayan na haihu akasake d’aura muna wani auren tinda wancan anyishi abisa rashin sanin akwai ciki saida akayi komai nasuna kana nad’auketa bakai gun shugaba,,Amma seyacemun sunfasa Shan jininta aureta yakeso Idan ta girma zasu samu d’aukaka sosai ak’ungiyarsu Zan kasance shugaba acikinsu..wannan abun bakaramin dad’i yayimunba hakan yasa nakoma da ita gida Ina kulawada ita sosai,,kuma sukabani babban matsayi acikin gungiyarsu tareda manyan aljanu way’anda kemun hidima da duk abunda nakeso.
Bayan ma,Isha tagirmane muka fara Shirin aurenta da shugaba kawai se Habibullah ya bullo duk kiyayyar Dana nuna akan auren hakan beyi tasiri ba hankalina yatashi matuk’a inda muka shiryayin aurenta kamunna habibullah Wai kwatsam se sweet d’in d’auren auren ma,Isha da habibullah Wanda bakowane yabada wannan shawararba Kuma yakafe akan hakan face shuraim.
To kaji abunda sukayimun wannan dalilinne yasa na aikata koma miye nayi musu Kuma wannan shedaniyar tazo takaryamun komai narantse sai nayi aljalinki, tafad’a taredayin kan mama…!
*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700₦ Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124
Autar Alheri ✍️
*S F*
Post a Comment for "Soldiers Family 63-64"