Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Soldiers Family 61-62


  • Page 61&62

 

__”takasa K’arasawa inda Tanufa,,Masha Allah sun,isone? Zeenah tafad’a tana nufar k’ofar..acan waje kuwa dukkansu fitowa sukayi daga cikin motocinda su sayetkan da ameesh sukaje d’aukarsu kowannensu Ido fik’i,fik’i kamar way’anda aka k’wato abakin Kura😂

 

K’arasowa zeenah tayi Tana tarbarsu cikin farin ciki tarungume ammy Tana sunbatarta a goshi,,itama Amma rungumeta tayi tanamejin k’aunar k’anwar mahaifiyar tata,,gaidata su jalaludeen sukayi cikin girmamawa abbe ma yagaidata,,ta,amsa cikin kulawa kana tarik’o hannun ammy suku nufi k’ofar shiga gidan,,tsayuwar motarda sukajine yakasu tsayawa,,wata arniyar motace tafaka me shegen kyau da girma kamar motar shugaban k’asar America 😂 babbar motace mekamada girgin k’asa,, dukkansu kallon mutar sukeyi domin ba k’arya tatafida imaninsu dagani base anfad’aba kasan nera tayi kuka awurin.

 

Wasu matansan yammata ne kyawawa sukabud’e motar sukafito cikin sauri suka zagayo d’aya gefen suka bud’e kofofin…wata dattijuwace tafito dashiga ta alfarma cikin kayan sarauta sebaza kamshi takeyi,,gabaki d’aya su alhassan da kallo sukabi wannan matar domin Basu tab’a ganin tsohuwa me kyau irin nataba,,,d’aya gefen kuwa mama ce tafito itama cikin shiga ta alfarma abayace ajikinta tanad’o mayafinta akanta   kamar balarabiya tak’ara kyau da cika jikinta kuwa kamar ka k’wanta jini yafito gacikinta yafito sosai yayimata d’ass agabanta abun gwanin Sha,awa,,kowa awurin kallon mmki suke Mata Dan bawanda yasanda cikinta inba abbe ba se jalaludeen dakuma alyasat d’in shiko bema lurada itaba kawaidai yaji bugun zuciyarshi nasauyawa.

 

Ido jalaludeen yawaro Yana fad’ar k’anwata kece haka? Masha Allah,,wata irin jiyowa alyasat yayijin abunda jalaludeen yafad’a Aiko karab idonshi suka sark’e cikin nata,,Ido yawaro tareda sake hannun yusif dake rik’edanashi Yana fad’ar”my sweet lifeeee dak’arfin gaske tareda rugawa aguje yayi kanta,,juye fuskarta tayi cikin sauri tana had’e girar sama dak’asa,, alyasat Kuma dagudu yak’araso wurinta Yana zuwa yazube a akan kafafunshi tareda rik’o nata kafafun yad’ago Yana kallon yadda tagame fuska kamar wadda aka aikowa mala,ikar mutuwa.

 

Suko su alhassan da lateep dukkansu Ido suka zaro suna kallon yadda jarimin soja yazube akasan mace kamar yaronta zenemi kafara awurinta.

 

“Fishi kikeyidani ko my sweet life? Taji muryarshi tadaki dodon kunnenta lumshe idanuwanta kawai tayi batareda tace komaiba,,,cigaba yayida fad’in Dan Allah karkiyi fishidani zaraah bazan iya jurar wannan horonba  kiyafemun abunda nayimiki badasan Raina natafi nabarkiba Amma Dan Allah kiyafemun nasan duk nine sanadin faruwar koma miye Daban barkiba bayadda za,ayi wani yayi yunk’urin cutardake I’m so sorry please zaraah I’m so sorry pls

 

“don’t forget me  please zaraahh wlh I love you so very much I really love you my sweet life love you more and more my happiness please for give me my wife 👏😥 yak’arasa Yana zubda k’wallar idonshi..Ido mama ta runtse dak’arfi tanajin wani irin rauni nashigarta tabbas seyau ta tabbatar tana Bala,in son mijinta wani irin abune takeji Yana Mata yawo azuciya Wanda takasa Gane komiye,,,ganin tayi shiru batace komaiba yasa ummansu maheer matse hannunta dak’arfi seda tabud’e idonta da itama sukacika tab da k’walla,,Kai ta girgiza Mata alamar tayafe Masa Kuma tad’agashi sama,,goge k’wallar idonta tayi kana taduk’a ahankali tarik’o kafad’unshi,,aikamar jirayakeyi yawani zaburo tareda rungumarta da,azabar k’arfi Yana fad’ar I miss you so much my sweetheart I miss yaba sauke numfashi seda tasaki Yar k’ara sabida tamatse Mata ciki sosai,,cikin tsawa jalaludeen yace “karka jimata ciwofa alyasat bakagani ba,ita kad’ai bace,,se alokacin dayaji maganar jalaludeen yad’an sassauta rikonda yayimata.

 

Sudai su yusif gabaki d’aya sunyi mutuwar tsaye suna kallon ikon Allah 🤔 domin Koda amafarki sukaga alyasat yayiwa mace hakan sesun k’aryata mafarkin Idan suka farka balle azahiri,,gaskiya wata soyayya Kam (To bance komaiba se Allah yakyauta)

 

Sunjima ahakan rungumeda juna kamar bazasu rabuba kamun yad’an d’ago Yana dubanta Yana sakin k’ayataccen murmushi tareda d’ora hannunshi akan cikinta,,itama murmushin tayi tad’ora nata hannun akan nashi suna kallon juna suna murmushi sund’auki tsawon lokaci ahakan ga dukkan alamuma sunmatada Basu kad’ai bane awurin..lateep ne yayi gyaran murya Yana fad’ar “to Romeo and Juliet munafa awurin ayi hak’uri har mushiga cikin gida,,murmushi duk su alhassan sukayi,,,shiko alyasat yajuya Yana zabga masa harara kamun yarik’o hannun mama suk’araso gunsu abbe,,itako ammy sakin antynta zeenah tayi tajegun ummansu maheer tana Mata sannunda zuwa dudda batasan kowaceceba Amma jikinta yabata danginsu gimbiya halila ce shiyasa bataji tsoron tunkarartaba.

 

“Alyasat Ka hanamun y’ata mungaisa ko? duk kawani hanata gaida Y’an uwanta kamar kaikad’ai kesan ganinta,,abbe yafad’a cikin tsokana,,dariya sukayi duka kana sukagaisa tsakaninsu tareda yimata yajiki sunjima Sunadan raha kamun zeenah tace to Idan kungama murnar ganin kishiyar tawa kuzo mushiga ciki danko ban tambayaba nasan itace matar alyasat? Dariya alhusain yayi Yana fad’ar itace kuwa anty zeenah bakiga yadda akeshan love ba agabanmu ma ko kuny…kasa K’arasa maganar yayi sabida wata uwar hararada alyasat ya watsa Masa da wannan idanuwan nashi masu firgita Y’an maza,,ai kut yahad’iye sauran kalaman nashi Yana zare Ido.

 

Hakadai suka d’unguma zuwa cikin gidan,,mama kuwa tanad’aga k’afarta kenan ummansu maheer nafad’ar dakata zarrahh karki shiga amma Ina Sam batajiba hakan yasa akayi wani irin sama da,itaa dukkansu tashinta sama kawai sukagani tareda jefota arubda ciki,,,cikin tashin hankali kowa awurin yashiga fad’ar innalillahi wa innailaihhiraji un,, yayinda alyasat yake fad’ar zaraahhh dak’arfi Allah Yana nufar inda yaga tanufa da,aka jefata,,,itako mama kamin tak’araso k’asa ummansu maheer tayi wani irin tsalle kamarba tsohuwaba tatarota tafad’o jikinta,,,Kuma alokacinda alyasat ya,iso wuri,,cikin fishi take kallon aljaninda ya wulagarda mama,,suko way’annan yammatan dasuka bud’e Mata k’ofa tuni suka koma wasu jigajigan samudawan karti majiya k’arfi.

 

Mik’awa alyasat mama tayi cikin tsananin fishi tabud’e murya dawani irin amo tace maheerrrrr,,,tana rufe bakinta wata irin hargowa nakarad’e wurin alamar maheer d’in yazo kenan dubanshi tayi cikin bada umurni tace banaso Kowa yarayu acikin gidannan kujeda k’arfin ayar Allah zakuyi nasara akansu ko d’aya banaso nagani,,,angama ummanmu umurninki kawai nakejira zancika aiki Yana gama fad’ar hakan yajuya,,,suko gabaki d’aya kowa yashiga tashin hankali tunanin sukeyi mitake nufida Kar kowa yarayu akashesu kenan kome? Zeenah kuwa innalillahi wa innailaihhiraji un kawai take memetawa tana fad’ar Miyake Shirin faruwane daga zuwansu? Gashi har ana fad’ar akashesu.

 

Bibibo nad’agawa suka nufi cikin gidan shida zugar tawagarshi data ummansu,,,wani irin artabo akeyi acikin gidan kamar ana takin duniya Wanda da,ace su abbe naganin abunda kefaruwa ba yadda za,ayi sutsaya domin sunsan tabbas zasu iya rasa ransu,,Didi kuwa tashiga tsafinta inda take harbinsu bibibo da tsafuka kala kala tareda turo musu miyagun aljannu Amma suna tsallake tarkonta,,,sunshafe kusan awa biyu suna Abu d’aya,,suko su jalaludeen duk suna waje tsaye cirko cirko kamar andasasu,,,,seda su bibibo suka kashe kowa duk wani azaluman aljanu datake aikidasu seda sukaga bayansu,,ganin bawanda yayi saurane yasa bibibo fitowa ya kalli alyasat yace sushigo shida mama kad’ai,,,rik’o hannunta alyasat yayi suna gaba ummansu maheer nabaya ahakan suka nufi cikin gidan..!

 

 

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan nomber 👉 07937092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08207819124

 

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

 

*S F*

Post a Comment for "Soldiers Family 61-62"