Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

My Little Sister 35-36

 

Page 35 & 36

 


__________”Sega anty Maryam tayi sallama a part itada sultan…juyawa mom tayi tana kallan anty Maryam d’in Dake tinkarota domin sultan tuni yashige bedroom d’inshi…suko Jin k’ofar tabud’e ne yasa Huzda haurawa kan bed cikin sauri tarufe jikinta da blanket..shiko yayi sauri d’aura towel d’inshi Yana mayarda numfashi tareda zama Bakin bed d’in kallo d’aya zaka masa kagano wani abun atattaredashi….anty Maryam nakarasowa tace mom Dama su abei ne sukace nakiraki shiyasa nabiyoki..to shikenan kice inazufad’a tareda kunna Kai cikin bedroom d’in,,,da kallo tabu d’akin tareda Ahzad Dake zaune Yana danna wayarshi.. d’agowa yayi yaga yadda takeyiwa d’akin kallon tuhuma yace “mom lpy kuwa?

 

Kallanshi kawai tayi batareda tace komaiba tajuya zata fita Idonta yasauka akan rigar Huzda Dake yashe ak’asa..gabantane yak’ara yankewa goma yafad’i tabbas taji sautin muryar Ahzad Yana sambatu kamar Wanda ketareda mace Kuma shakka Babu kokwanto acikin wannan abun,,Amma yanzu Kuma bataga kowaba ataredashi sedai Kuma garigar Huzda ak’asa mihakan kenufi kenan? Badai yarannan Neman junansu sukeyiba? Dumm Daram damm Haka k’irjinta yarik’a bugawa cikin sauri tace Kai Ina Hakan Sam bazeyuba,,,wata zuciyar Kuma tace to idan bahakabane mikayan Huzda keyi anan Kuma ak’asa Kuma mi Ahzad d’in keyiwa ihu? Gabaki d’aya mom tashiga rud’ani zuciyarta takasa gasgata mata abunda take zargi Kuma takasa yadda da abun bahaka bane tabbas akwai Wani abu dayarannan ke aikatawa allah Gani kareka ni halima..janyo k’ofar tayi tarufe tayi tsaye tana tunanin abunda yadace tayi kamar daga sama taji ana fad’a ya zadna mom tatafine? Mitazoyi?

 

Wani irin waro Ido mom tayi tabbas dai kenan hakane Neman juna sukeyi innalillahi wa innalahi Raji un,,,tafad’a cikin kukanda ke k’ok’arin zomata Amma Kuma yak’i fita sabida tashin hankali…cikin sauri tanufi parlor inda tasamu  dady da abei sekuma ammy suna zaune da ya muhfat ana jiranta tana zuwa tazube gaban dady tinkamun suyi maga tarik’o hannunshi duka biyu tace Dan girman allah Alhaji adaura aurennan yau base gobenba Kuma Maryam takomada Huzda har allah yabata Muji Dan Allah Tana fad’a kukana zomata….cikin tashin hankali suke tambayarta mike faruwane..akuma Dede lokacin Huzda tafito daga part d’insu Amma Bata k’arasa shigowa parlor ba sabida bedroom d’inta tanufa taji ana wannan zancen tatsaya saurara…cikin kuka mom tashiga Basu lbrn abunda taji da Wanda tagani tak’ara dafad’in yanzu har abun yanuna musu sunemi junansu karfa mutsaya kallon ruwa k’wado yamuna k’afa abunnan yafara fin k’arfina fad’a cikin tashin hankali….inbanda salati ba,abunda su dady keyi ammy kuwa kuka takeyi itama tamkar ranta zefita…da k’yar dady ya,iya cewa bazasu nemi junaba sedai abunda ba,arasaba Amma yanada wuya jininmu suyi Zina Badan sunfi k’arfin jarabawar uban gijiba sedai kab d’inmu Babu mazinaci Kuma munatsaye gun rokon allah yakare zuri,armu sabida Hakan bana wannan tinanin agaresu,,,sedai kamar yadda anty halima tafad’a rabasun shine yafi dacewa ayanzu Kuma Doline ad’aura aurennan gobe idan allah yakaimu…kallan muhfat yayi yace muhfat ashirya duk abunda yace gobe karfe 7 nasafe za,ad’aura  auren yuzarsiya da Ahzad insha allah.

 

Wani irin zaro Ido Huzda tayi numfashinta naneman d’aukewa juyawa tayi danufin komawa bedroom d’in Ahzad sekawai taganshi abaya..hannu yasa yarufe mata Baki tareda girgiza kanshi Yana matanunida yaji komai kana yaja hannunta suka Koma bedroom d’inshi

 

Jallabiyarshi kawai yad’auko yabata kana yad’auki car key d’inshi yarik’a hannunta sukafita ta hanyar kitchen tinda badamar bita general parlor,,,suna fita yashiga motarshi itama yasaka kana yatada motar damugun gudu yabar gidan Dede lokacinda Dr yaseer shiko yasamo motarshi gidan sabida yamanda computer d’inshi a parlor mom…ganin yadda Ahzad d’in Yaja motar Hakan yasa yabibayanshi domin Yana tinanin ba lpy ba..suko sunacan basumasan abunda kefaruwaba.

 

Gudu yakeyi sosai yad’auki hanyar fita garin kano,,Abu d’aya yacewa Huzda karki kuskura kisaka wannan abun aranki balle yazama matsala bazan tab’a zamada kowacce maceba aduniya seke zamuje inda zamuyi rayuwarmu hankali kwance batareda sunsaniba..tofa wannan zantukan nashi sune suka kwantarwada Huzda hankali…..shiko Dr yaseer cikin mmki yake bin bayanshi kamun yad’auki waya yakirashi Amma Bata shiga,, muhfat yazomishi arai ahakan yasa yakirashi”yana d’agawa yace muhfat lpy kuwa mike faruwane agidannan?

 

Mik’ewa muhfat yayi Yana fad’ar banganeba mikaganine Dr? “Wlh zanshigo naga fitar motar Dr kamarba lpy ba Kuma nabi bayanshi Amma naga yanufi barin gari yanzu Hakan munakan hanyar shiga KD….what? Muhfat yafad’a dak’arfi kana yace shikenan Dr yaseer ngd sosai dan allah kacigabada binshi zamuzo yanzu duk inda kaga yayi Sega gayamin Amma karka bari yaganka….shikenan badamuwa yafad’a tareda yanke wayar.

 

Komawa cikin parlor yayi yagama su dady abunda kefaruwa…cikin sauri mom tace aduba Huzda tana,Nan kosuna tare…aiko kuda akaduba Bata gidan..kamun suyi Wani yunk’urin Sega Kiran Dr yaseer yashigo… muhfat nad’agawa yace gashi yatsaya Wani gida Kuma ga dukkan alamu gidan bakowa Kuma abun mmki shida Huzda suke bashi kad’ai ba… innalillahi wa innalahi Raji un “shikenan Dr ngd katsaya please gamunan zuwa yanzu insha allah komikenan idan munzo zakaji…okay allah yakawoku lpy.

 

Juyawa yayi Yana gayamusu abunda Dr yaseer yace…ai ko Baku berufeba ammy tace kutashi mujecan din Muga halinda suke ciki Dan Allah karsu jefa kansu ahallaka…bamusu kuwa duk suka mike suka bar gidan.

 

Kaitsaye inda Dr yaseer yayi musu kwatance suka nufa cikin sauri da b’acin rai…suko su Dr Ahzad suna shiga gidan a parlor suka zauna Huzda tafad’a jikinshi tana rusheda matsanancin kuka tana fad’ar miyasa iyayenmu suka kasa fahimtarmu ya zad miyasa sukesan rabamu kota k’arfin tsiya? Miyasa bazasu barmu musamu abunda mukesoba? Nagaji nagaji ya zad garana mutu dadai naga ranar aurenka da wata…ya,Isa Hakan Huzda nikaina nasan bazasu tab’a fahimtamu ba domin addininmu beyadda da wannan tsarinba Muna musulmai uwa d’aya Uba d’aya Kuma munasan mu auri juna Sam Hakan bazeyuba Huzda Amma sanzuciya da soyayya sunrufe mana Ido mukasa fahimtar Hakan tabbas bazeyu mu auri junaba Amma inaji ajikina komai rintsi ked’in mallakinace Kuma uwar yayana Amma bansan tayaya Hakan zata faruba Huzda kigayamin yazamuyi da wannan k’addarar tamu,,,yafad’a cikin k’unar Rai…cikin kukan itama take fad’ar wlh wlh duk ranarda aka d’aurama aurada wata Sena kashe kaina Kona kasheta iyaso Nima akasheni..

 

 

Sedai ki kashe kanki wlh Kuma kimutu kafira tinda bakwa kallan tashin hankalinda zakujefamu Huzda…suka tsinkayo muryar mom,,,cikin tashin hankali duk suka mik’e tsaye suna kallan way’anda keshigowa parlor…dady ne yazo wurinsu tareda d’aga Hannu ya shararawa Ahzad maruka har biyu cikin dacin Rai yace Ahzad da hankalinka zaka daukemin yarinya kagudu da,ita kamarda ita dadironka kamar yadda kayi agida kome? Dafe kumashin duka biyu Huzda tayi shi akamara Amma kere fuskarshi Kuma itake Kuma…Shima cikin bushiwar zuciya yafara magana kamar Hakan “dady nibazan mayarda little sister dafironaba Amma zan mayarda ita matata tinda kunk’i fahimtat…Kau yasakejin saukar Wani Marin abei yad’aukeshi dashi Yana huci yace bakada hankaline har munyi lalacewarda zamu fad’a y’ay’anmu sufad’a wlh Baku isaba…innalillahi sukaji ya muhfat yafad’a dak’arfin gaske tareda buga Wani tsulli se wurinda Huzda take k’ok’arin sokawa kanta wata fasashiyar kwalba data Gani awurin,,,aiko suka shiga kokawa da,ita kowa awurin yasandare Yana kallansu domin bil hak’k’i nema takeyi takashe kanta,,iyayi muhfat yakasa karb’ar kwalbar ahannunta Sema yanyankasu datayi duka dagashi har ita…Ahzad yanufesu tareda Saka hannu biyu yarik’e nata hannayen kawai yatsareda Ido..aiko setasaki kwalbar tana fad’awa jikinshi,,,Shima rungumeta yayi sosai kana yace kikashe kanki my little sister duk sabida ni? To Niko narayu dawa kenan? Komai rintsi komai wuya karki kuskura hukuntamin kanki tahanyar d’aukar rayuwarki dakanki kinji my little sister idan basokikeyi allah yak’onamu dukkanmu….cikin kuka take d’aga mishi kanta tana fad’ar bazan k’araba ya zadna bazan k’araba Kuma wlh bazan tab’a rabuwa dakaiba koda za,akasheni Dan Allah karka barni yayana… lumshe kyawawan idanuwanshi yayi hawaye mazubomashi yace har abada abadan gaban abadan bazan tab’a rabuwa dakeba koda kuwa Hakan nanufin barin numfashi na daga kangar jikina..

 

Gabaki d’aya wurin anyi tsit ana sauraronsu inbanda bugawa Babu abunda zuciyoyin iyayen keyi na tashin hankali bakajin komai awurin se sautin kukan mom da ammy….cikin kukan nadama da takaici ammy tace hak’ik’a yau yazama Doli kowa yasan abunda besaniba yazama Doli nabud’e wannan b’oyayyen sirri kodan kawo mafita acikin rayuwar yaranmu hak’ik’a akwai abunda Baku saniba acikin wannan Al,amarin wannan wahala darannan keyi ta,Isa haka ta,Isa,, tak’arasa zancen cikin kuka metsima zuciya….kowa kallanshi yamaida kanta kamun abei yace mikikesan cewane hajara? Wanne sirrine bamusaniba? Yatambaya cikin tuhuma.

 

 

“Tabbas akwai abunda Baku saniba…ashekarun baya..lokacinda kuka auremu nida halima inbaku mantaba halima nada burin samun y’amace ta k’wallafa rayuwarta sosai akan mace sedai haihuwarmu ta fari muka samu duka Yara Maza wato muhfat da Ahzad da,akazo tabiyu na haifi Maryam itakuma tahaifi sultan Kuma dukan haihuwarmu waya kwana 3 ne tsakani wata wuni d’aya kamar muhfat da,akahaifa da safe aka haifi Ahzad da yamma.

 

To dazoyin ta ukku itako alokacin batada ciki Sena haifi twins su yusif kenan…bayan shekara 5 da haihuwarsu muka K’ara samun ciki atare nida halima,,awannan cikina halima ta Saka ranta sosai akan tasamu y’a mace kullun mukayi magana akan y’ay’a setace natayada addu,a allah yabata mace haka mukayita fama nida ita munarenon cikinmu…wata Rana inazaune alh. Kace nazo muje asibiti halima batada lpy haka nashirya mukaje dudda cewa Nima alokacin ba loyr cedaniba kawaide banfad’a bane,,bamu jima dazuwaba Nima nak’uda tazomun sosai Ba,ad’auki Wani dogon lokaciba na haihu nasamu y’a mace,,,,wadda tak’arb’i haihuwar zata fita tagaya muku nahanata nace Dan Allah tabari idan Yar uwata tahaihu tafad’a muku atare tinda tariga jimawa tana nak’udar…hakanko akayi Bata gaya mukuba seda halima tahaihu tasamu yaro namuji Kuma bezoda raiba bayan haihuwarshi Kuma tasuma sabida ta wahala sosai…naji tausayin halima sosai akan rashin samun mace dabatayiba Amma ba yadda na,iya tinda Wanda kebadawa Hakan yatsara alokacinda za,agaya muku haihuwar nida nurse d’inda tak’arb’i haihuwar muka had’a Baki bayan narok’eta Kuma nabiyata makodan kud’ad’e akan tace muku halima tahaifi mace nikuwa namujinda bezoda raiba tinda halima bataga abunda tahaifaba….wannan dalilinne yasa akacemuku Huzda Yar halima ce Amma zance na gaskiya Huzda y’atace nice nahaifeta ba halima ba nayihakanne domin nafarantawa Yar uwata Ashe abun zezame muna matsala koyanzu dabadan da wannan abunba bazaku tab’a sanin cewa nice nahaifi Huzda ba halima Kuma cikin iyawar uban giji Ahzad da Huzda basusha nono d’aya ba domin tinda aka haifi Huzda nonon halima bezoba Kuma anyi yawon asibiti har angaji babu ruwan nono Hakan yasa akebata Madara..Gani tana tsamurewa sabida Madarar Bata karb’eta ba yasa nacigabada wanka inasan abunda zezoda nono shiyasa namayarda Huzda wuni gidana tana Shan nono Wani lokacin har bacci takeyi acan harna yayeta bawanda yasanda wannan zancen daga allah seni sekuma nurse binta…!

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

 

*M S*

Post a Comment for "My Little Sister 35-36"