Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

My Little Sister 31-32

Page 31 & 32

 


_________”zaune anty maryam take a parlor tana yiwa y’arta kitso,,, Huzda ce tashigo parlor rik’eda plate ahannunta tayanko kayan fruit aciki tafiya takeyi medaukeda kasaita irinta manyan mata med’aukar hankali,,zama tayi tana fad’ar sannu anty… yawwa autar mom anfito? “Eh Dama anty zangaya mikine gobe zankoma kano nayi wayada ya muhfat yazo yamaidani gida..what? Mikikesan cewane Huzda? Su dady sunsanda zaki Koma goben? “Aa kawaidai zankoma kidubafa anty tinzuwana garinnan sau d’aya naje Kuma Shima ko sati d’aya banyiba abei yamaidani yanzuko gaskiya inaso naga mom d’ita Kuma inaso naga ammy da anty yuzarsiya dasu ya yusif Kai gaskiya inaso naga dika family na..kallanta kawai anty Maryam keyi Jin Bata anbaci ya Ahzad ba kodai tamantadashine? Ta tambayi kanta domin tinfarkon zuwanta data tada hankali akan tanaso Taganshi yanzu yadawo mom tace wata 2 zeyi to tunsanda dady yayi mata tass akan idan tasake zancen Ahzad zehanashi dawowa sedai yayita zama acan to wannan dalilinne yasa har ila yau Batak’ara zancenshiba shiyasa take tinanin kota mantashine..cikin dabara tace iKon allah Huzda iyasu kawai kikayi missing banji kince ya sultan ba da k’awarki Rafi,a…murmushi tak’ara saki kana tace itama nayi kewarta mana dukkansu hadda my sweet bro na duk nayi kewarsu…cikin murna anty Maryam tace to shikenan badamuwa kibari nayi maganada abei ko dady idan sunce kikoma shikenan semuje dukkanmu,,domin anty Maryam tasan cewa sultan take kira sweet bro shiyasa tak’ara tabbatar da cewa tamanta Ahzad ne (😂😂kina ruwa anty Maryam kusaga kadama kuwa❤️ first love ba,amantashi cikin sauk’i 💃 )

 

 

Tashi tayi tashiga bathroom d’inta tarufe k’ofar kana takira abei bayan sungaisa take sheda mashi yadda tayida Huzda…Dan Jim abei yayi kana yace tanemi Ahzad? “Aa dady wlh duk tsawon shekarunda tayi har ila yau batanemeshivmba ko awaya Kai ko zancenshi batayi…murmushi abei Yana fad’ar Masha allah Abu yayi dady sosai yanzu badamuwa kishirya goben insha allah muhfat zezo yad’aukeku Shima Ahzad d’in jibi Thursday zedawo Kuma Kinga Saturday ne aurenshida yuzarsiya..”eh hakane abei insha allah to zamuzo..to shikenan allah yakawoku lpy.. ameen y allah tafad’a tareda yanke wayar.

 

Murmushi abei yayi suka tab’a shida dady domin zaune suke a office d’in dady suna tattauna zancen auren nasu Ahzad,,,cikin Jin dad’i abei yace wlh wannan shawarar tayi damukayi kaga Shima Yana dawowa za,adaura aurenshi koda shi bemantataba idan yanada mata ad’aki Doline yamanta kaga munyi maganin komai cikin sauk’i…hakane gaskiya allah yak’ara rufa mana asiri cewar dady..Ameen dai,,,kana sukaci gabada firarasu.

 

 

Washe gari misalin karfe 7:00am mijin anty Maryam yakira ya muhfat yace yayi zamanshi shizekawosu insha allah…to shikenan badamuwa allah yakawoku lpy yafad’a Yana yanke wayar.

 

Gabaki d’aya wannan ahalin sunsakan kance akan cewa Huzda da Ahzad sunmantada juna domin Shima tin lokacinda yatafi beyiwa kowa zancentaba harsu muhfat kuwa Hakan yasa suka Kara sakankancewa…da yamma liss suka sauka garin kano gidan dady anan suka sauka dukkansu anyi murna sosai anyi farin cakin ganinsu musamman Huzda dagabaki d’aya tacanja mom d’inta se Yaba kyawonta takeyi itada anty asabe,,,ya sultan dayaganta kuwa har kusan fad’uwa yayi wirin kallanta cikin sauri yad’auke idonshi tareda nufar bedroom d’inshi tin ba,aganoshiba Amma sedai yanakara domin itadin taganshi Kuma tasan kallan soyayya Kuma tasan yanayinta Hakan yasa gabanta muguwar fad’uwa…yuzarsiya kuwa dasuka had’u rungume juna sukayi suna murnar Ganin juna ba Wanda yanunawa Dan uwanshi Wani abun sedai Dan bunda ba,arasaba,,, atak’aice dai awunin wannan ranar sunyishi cikin farin caki da walwala ga mom ga autarta,,seda bayan magarib kana taja mota dakanta sukanufi gidan ammy.

 

 

Acan suka kwana hadda Huzda seda safe kana tadawo gidan mom…aduk wannan wunin datayi harta kwana bayiwa kowa zancen Ahzad ba Kuma hargidansu Rafi,a taje itama tazama cikakkiyar budurwa kamarta sunyi firar yoshe Gamo sabida sunyi kewar juna sosai bayan tadawo ma Hakan tasamu su ya muhfat da yusif da ya sultan a parlor dady har dadyn Hakan tazauna cikinsu anata fira cikin Jin dad’i da farin caki Sam batanunawa tasanda akwai Wani ya Ahzad ba sedaifa tana k’asa tana dabo domin jitakeyi kamar takama da wuta sabida rashin Ganinshi…karfe 11:00pm mom tashiga kitchen domin shirya lunch d’in tarbar Dr Ahzad,,,shigowa Huzda tayi cikin shigar kananun kaya sunkamata sosai Kuma hulace kawai akanta..Baki mom tasaki tana kallanta kamun tace Huzda wannan shigar zakiyi Kuma kinsan Maza nashigowa gidannan? Wlh Maza jekicanja kaya kokisaka hijab..d’ira kafafuwanta tafarayi ak’asa kamardai yadda tasaba tana k’arama ga dukkan alamu shagwab’arta se abunda yayi gaba,,cikin shagwab’ar tace mom acikin gidanefa Kumani allah banada wasu kaya duk irin wannan ne…”au lallai aiko sekije anjima kisiyi suturar kirki domin nankam bazaki zaunada wannan kayanba gaki allah yayi Miki ni,imar jiki mazaje kisaka hijab sa,annan kifito.

 

Komawa tayi tadauko Badan tasoba tadawo domin Huzda tatsani manyan kaya acanma Hakan anty Maryam kefamada ita Amma Bata bari…tana shigowa kitchen d’in tace mom mizaki dafane? Lunch ne za,ayi..okay jeki kihuta yaudai autarki tashiga kitchen..murmushi mom tayi tace Humm allah dai yanunamin kinshiga kece yanzu zakiyi Wani girki Huzda nafasan halin kayana Kuma nasan Hali baya canjawa…aikuwa dai nawa yacanja mom allah na,iya girki Kuma kitambayi anty Maryam kiji..shikenan naji kiyimuga ai Wanda keda girkin shine zegyara Miki zama idan kika masa kwab’a,,tana gama fad’ar Hakan tafita…shiru Huzda tayi tana tinanin towaye Wanda zegyara Mata zama? A,iya saninta mutin d’aya be mom kecewa zegyara nata zama shine ya zad d’inta tokodai shine zedawo? Tayi kanta tambayarda bame Bata amsarta,,,cikin yadda da,abunda zuciyarta taraya nata tashiga had’a lafiyayyen amunci merai da lpy da dadda d’an lemun inibi da kwakwa,,cikin k’ank’anin lokaci Tagama shirya komai kana tawuce bedroom d’inta domin tayi wanka tashirya.

 

Koda mom tafito tasamu abunci komai ajera akan dining bak’aramin mmki tayiba kallan anty asabe tayi da,alamar tambaya…murmushi asaben tayi tace allah kuwa itace tayishi mom…kamin mom tace Wani abun Sega dady yashigo waya mak’ale akunnenshi Yana fad’ar suhad’u a airport d’in dagani da abei ne yake wayar,,, k’arasawa yayi wirin mom Yana fad’ar baramu d’aukoshi saura minti 30 jirginsu yasauka..to shikenan adawo lpy tafad’a cikin farin caki..sultan ma fitowa yayi cikin shirinshi domin yusif nawaje Yana jiranshi tare zasu tafi suna kaiwa bakin k’ofar fita parlor Sega Huzda tafito itama cikin shirinta taci uban kyau cikin maroon d’in abaya meshegen kyau daga cikin abayar tasa k’ananun kaya k’aramar Riga da wando bakin gwiywarta kana tad’ora abayar Akai tad’aure bayanta domin me abun d’aurewace abaya Amma agaba lpy qalau baka sanin and’aureta se mutin yajuya Hakan yasa wannan aban hips d’in nata yak’ara bayyana kamar d’ora matasu akayi,,,tazo tayi rolling da mayafinta seta fito sak balarabiya,,, gaskiya ba k’arya Huzda kyakkyawace tagaban kwatance wadda se antona za,asamu irinta…gabaki d’aya da kallo suka bita hadda yusif dayashigo yanzu domin yagajida jiran sultan Wanda besan lokacinda yace “watafarakallah bi,ahasanil khaliqeen k’anwata kin had’u wlh wannan mak’urar kyau d’in haka se Ina?

 

Wata muguwar harara sultan ya zabga masa wadda ahi bema ganshiba hankalinshi duka nakan k’anwar tasu…murmushi tayi tace gidan ammy ya yusif kozaka kainine? Eh Amma semun fara zuwa airport tukunnah..shikenan badamuwa muje..kallan mom tayi tace mom zanje gidan ammy..to shikenan adawo lpy tafad’a tana komawa bedroom d’inta

 

Hakan yasa sukabi bayan ya sultan da dady Dan tuni sunyi waje…dady yaja motarshi yayi gaba yusif ne yaja tashi inda sultan ke mazaunin me zaman banza itako Huzda tana baya ahakan suka nufi airport d’in.

 

Koda sukaje acan suka taradda su ya muhfat da anty maryam hadda yuzarsiya gakuma abei da dady da Kuma Dr yaseer…cikin mmki tace ya yusif waye zeyi tafiya naga kowa yazo airport? Kamun ya yusif yabata amsa tuni jirgin yasauka Hakan yasa hankalinsu yakoma kan masu fitowa daga cikin jirgin hadda Huzda….Wani kyakkyawan matashun saurayine yafito mejida Isa dakuma haiba bugu dak’ari kyau gakuma nera hutuda ilimi sunzauna akanshi ba k’arya,,,kallo d’aya zakayi Miki kasan cewa shid’in kyakkyawa ne ko,acikin kyawawa,,,glass d’in idonshi yacire Yana k’arewa k’asar tashi ta haihuwa kallo wadda yabari tsawon shekaru biyar lumshe kyawawan idanuwanshi yayi Yana shafa lallausar sumarda tayiwa fuskarshi k’awanya kana yak’ara Bud’e idanun yashiga saukowa ahankali..hummm Dr Ahzad Ahmad kenan kyakkyawan matashin likita me lokaci.

 

Suko tinda yafara saukowa suka hangeshi musamman Huzda dako acikin miliyoyin mutane taganshi zata ganeshi kowacce irin sauyawa yayi kuwa,,Ido tawaro tana kallanshi ko kiftawa Babu…Shima tinda yabud’e idonshi suka hasko mishi ita dudda sauyawarda yagani atattareda ita bako kad’anba.

 

Nufarshi sukayi lokacinda yusif yace ga ya Ahzad d’in can yasauko..juyowa yayi yaga Huzda Bata biyosuba gadukkan alamu tatafi dayawa domin takafe Ahzad da Ido ko motsi batayi,,,seda ya sultan d’in yadawo baya yatab’a Yana fad’ar lpyr ki kuw…kamun yak’arasa yaga tayi wulgida jakar hannunta tareda watsawa da mugun gudu tanufi Ahzad d’in tana fad’ar ya zadnaaa tafad’a da k’arfin allah Wanda duk Wanda kewurin seda yamayarda hankalinshi akanta hadda su abei…Shima Ahzad d’in sakin jakar kayanshi yayi yawatso dagudun Danya tarbeta Yana fad’ar my little sisterrrr dak’arfi sosai,,kowannensu bud’ewa Dan uwanshi hannun yayi tinkamin sukarasa gajuna domin Gani sukeyi kamar suna gudune ana maidasu baya duk sunk’osa suhad’u,,,suna zuwa suka shige jikin juna tahanyar bawa junansu kyakkyawan hugg suna sauke Wani wahalallen numfashi mecikeda kewar juna kamar d’anda akaraba da uwarsa,,wata irin runguma ce sukeyiwa junansu suna shinshinar jikin juna kamar mayun wata kaida Gani base angayamaba kasan bak’aramin azabtuwa sukayi narashin junaba kallo d’aya zaka musu kasan cewa masoyane na hak’ik’a soyayyar da ba algussu acikin soyayya zahiran bawai mayaudariyar soyayya ba wannan soyayya ce tagaskiya da gaskiya Wanda daga can cikin raida zuciya take tasowa…gabaki d’aya airport d’in akamaidasu TV domin sun d’auki hankalin kowa,,Wanda sukuwa basumasan anayiba…daga abei har dady harsu ya muhfat dukkansu mutuwar tsaye sukayi ballema anty Maryam da yuzarsiya dasuka Koma tamkar mutun mutumi…!

 

 

 

 

Idan naga comment d’inku zakuga update anjima Amma idan banganiba sebayan kwana biyu..Kuma comment na sharhi nakeso acikin lbrn bawai thanks ko ❤️ no sharhi nakesan Gani.

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

*M S*

Post a Comment for "My Little Sister 31-32"