Kurkukun Kaddara 9
*E9*
At first sight da Danejo ta kalli fuskar yarinyar, sai taji tsananin tausayinta, Kuma nan take taji tana son ta taimaki rayuwarta.
Tunda ta ayyana hakan azuciyarta sai taji ta daina Jin tsoron tafkeken ramin Ramin, kodan saboda Yarinyar zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta ceci rayuwarta.
Dabarace ta fado mata aranta, Da sauri ta sanya hannu É—aya, ta Kwance kallabinta data É—aura É—amara dashi, ÆŠayan hannun kuma na dafe da yarinyar,
a saman bayanta ta goyata, kafin a hankali ta cigaba da matsawa cikin ruwan harta ƙaraso jikin gwamagwaman duwatsunan dake kewaye da wurin, jikinsu akwai hudoji, tsaf mutun zai iya daddafawa ya haura sama, Sai dai yana da matuƙar hatsari idan Duwatsunan Jiki suka 6allo, mutun zai iya jin mummunan rauni ga shi ita harda goyo.
Cike da fargaba danejo ta sanya hannayenta, ta dafa jikin dutsen A haka tadin ta tafiya tana bin jikinsu, Har Allah ya taimaketa ta hauro sama, tana faman Mayar da numfashi, da sauri ta sanya hannayen ta tare da warware goyon da tayi mata, ta sauko da ita a hankali ta kwantar da ita saman ciyayin, ɗagowa tayi tare da kallon shanayenta dake ta kuka, Ta wurga masu harara don ba ƙaramin haushin su take ji, daga gani dai akwai ƙuruciya atattare da ita.
Mayar da idanuwanta ta yi akan fuskar yarinyar, ta sanya hannu tana yaye sumar kanta data rufe fuskarta.
Tayi wani irin haske, ƙananun la66anta sunyi pink sosai suka ciza, duk irin kyan danejo saida tayi mamakin Tsantsar kyawun yarinyar data tsinto acikin ruwa.
Hannayenta ta ɗaura Asaman ƙirjinta tashiga dannashi, Nan take ruwa ya sona fesowa Ta bakinta da hancinta, cigaba da dannawa tayi har saida ruwa Ya daina zubowa, natsuwa Tayi tana kallonta, ta yi tunanin zata farka amma sai taga ko motsi ba ta yi ba, Da sauri ta jogana kunnanta saitin Zuciyarta don taji, idan tana harbawa a razane ta ɗago, ranta duk ajagule fargabarta kada ace yarinyar tarasa ranta.
Tunawa tayi da saman dutsen da ta ganta akwance, hannu tasa ta juyo da bayanta, ta cusa yatsun hannunta acikin sumar kanta data cukurkuɗe, har saida ta taddo fatar kanta fara sol, Anan taga Raunin data ji, ashe kantane ya ɗan fashe daga baya, sakamakon buguwa da kanta yayi jikin dutsen, A ruɗe danejo ta miƙe tare da daukarta, ta sa6eta saman kafadarta, Sam ta manta da shanayensu, hankalinta na akan Yarinyar dake Cikin mawuyacin Hali, Watsawa Tayi da gudun gaske tamkar zata tashi sama,
Tana Cikin gudun nan, wani bafullatanin Sanye cikin kayan fulani, da ƴar hularshi, Hannunshi ruƙe da sanda zai gifta, Karaf idanuwan shi sauka sauka a kan danejo dake ta tsala gudu,
Mamaki ne ya kama shi, É—aga murya ya yi tare da kwala mata kira, har cikin kanta tajiyo kiran da ya yi mata, Batare da ta juyo ta kalleshi ba ta amsa mashi da na’am,
Cikin harshen fulatanci Yace inata baro masu shanayen su kuma menene ta dauko a hannunta, tace ma shi suna can suna kiwo, Yaje ya cigaba da kula dasu,”daga haka bata Æ™ara cewa uffan ba,
Girgiza kai Bawuro yayi a ranshi yace bazata ta6a canzawa ba, daga haka ya nufi Cikin dajin inda shanayen su suke,
Danejo kuwa bata nufi ko’ina ba, Sai wuraren wasu Bukkoki rukuni rukuni a Æ™alla sunyi Shida, A gefen É—aya daga Cikin bukkokin wani tsohone tukuf zaune cikin kayan fulani, daga gefe kuma Wasu Manyan matane, Sun kwan biyu aduniya, Sai sussukar gero sukeyi, ga wasu kuma Ƴan mata su biyu matasa Suna 6arar masara,
Tundaga nesa Tsohon Ya hangota, da ƙarfi ya ambaci sunanta DANEJO, lokaci ɗaya sauran Mutanan suka ɗago suna kallonta, Ganin yadda take ta gudu yasa duk sukayi tunanin ko wani mugun abunne yabiyo ta, aikuwa aguje Suka nufi Cikin bukkokinsu kowa ya ɗauko makaminshi, Shima tsohon ya miƙe yana ɗangyale ƙafa ya shige cikin bukkar gefen shi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da Ma shi, (to fa yaƙi ya ta shi)
Ƙarasowa tayi tana ta faman haki, lokacin da suka lura da abinda ke ruke a hannunta sai kowa ya ajiye makaman yaƙinsa, suka tattara hankulansu akan yarinyar data ɗauko, A saman Shimfiɗar kakansu ta sauke yarinyar, tare da ɗagowa ta kalli kakansu cikin harshen fulatanci tayi mashi bayanin inda ta tsinceta, koda jin hakan Jiki Na rawa Ya koma Cikin bukkarshi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da ƴar jakkar fata, a gefen shimfiɗar ya sauke jakkar, Yace ma danejo ta nuna mashi inda taji ciwon, rubda ciki ta kwantar da ita, tasa hannu ta yaye sumar kanta, nan suka ga raunin da taji, Bude jakar yayi ya curo wasu magunguna nasu na gargajiya, wanda suke Yi ma mutun treatment dasu idan yaji ciwo,
Matsowa sauran Fulanin sukayi Gaba daya sukayi masu Danejo ƙawanya, Duk sun baza idanuwansu akan yarinyar, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya kammala Yi mata treatment ɗin Raunin nata, Sannan Ya kalli Danejo yace ta dauketa takaita Cikin bukkarsu, ta kar6o bargunan da suke lullu6a dasu, A rufa mata ajikinta, sannan a hado garwashin wuta, A sanya mata a cikin ɗakin don ya ɗumama.
Bayan danejo ta dauketa, takaita Cikin bukkar su Saman shimfidar da suke kwana ta kwantar da ita, ta fita zuwa sauran bukkokin ta kar6o bargunansu, da zannuwa duka Ta haɗosu a hannunta, ta shigo cikin bukkar ta lullu6a mata su, kamar yadda kakansu yace ta yi mata, tana Cikin nannaɗeta cikin bargunan, Adda ta shigo hannunta ruƙe da murfi na karfe, Garwashin wutane jawur a saman shi, A gefe ɗaya ta ajiye garwashin wutar,
Kafin ta samu wuri ta zauna gefen danejo, magana suka soma Yi cikin fulatancinsu,
“Tausayinta nake ji, Æ™aramar yarinya da ita, ko ya akai ta faÉ—a Cikin ruwa? Shin ina iyayenta suke ne? taya akai ta shigo Cikin kurmin dajin nan”? danejo ce ta yi maganar fuskarta da alamun tausayinta,
Adda tace”Nikaina nakamu da tausayinta, Allah kaÉ—ai yasan daga wata uwa duniyar take, har na Æ™osa tafarka, duk da nasan zaiyi wuya ace tana jin yarenmu, baiwar Allah gata kyakkyawa da ita kamar ta macen aljanna da kaka yake bamu labarinta”
Murmushi danejo ta É—anyi kafin tace”Tunkafin ma tafarka Na ji nakamu da sonta sosai, kamar ni na haifeta” wani irin kallo Adda tayi mata”Ke da ko aure baki da shi,” danejo tace”Ae ba laifi bane don na kirata da Æ´ata, balle kuma ni dana Tsinceta cikin ruwa kinga kuwa, a yanzu bata da wani makusanci daya wuce ni jinjina kai adda tayi “bazan biye maki ba, sarkin surutu” ta miÆ™e tare da fucewa daga Cikin bukkar.
_Taƙaitaccen tarihin danejo, Fulanin dajine, Masu yaɗa zango acikin daji wurin da ke da yalwataccen Abincin da dabbobin su zasu ci, kuma Su yi kiwo su yi noma, fulanine dake rayuwa acikin daji, babu wayewa attare dasu, kuma suna da ƙarancin ilmin addini, a wannan Lokacin saboda su kadai suke rayuwar su a daji,_
Family din danejo basu dayawa, Saboda yawancinsu ba’a wuri É—aya suke ba, Kowa Ya kama gabansa, KaÉ—an ne suka rage, Ita dai takasance marainiyace, Iyayenta sun rasu tun kafin ta mallaki hankalinta, kuma ita kaÉ—ai suka haifa, ta taso A hannun Æ™anwar mahaifiyarta wadda suke kira da inna wuro, Æ´a’Æ´anta huÉ—u bawuro shine babban É—anta,Yana da mata ÆŠaya Haulatu, É—ansu É—aya wanda suke kira da cubaÉ—o, bayan shi sai Adda itace ta biyu, sai gidaÉ—o sai kuma Æ™anwarsu hasiya, Kakanninsu duk sun rasu, ÆŠaya kaÉ—ai ya rage masu na 6angaren Mahaifiyarsu, sukaÉ—ai suke rayuwarsu a wuri É—aya.
Yinin ranar Danejo bata motsa ba, ta kasa ta tsare sai Yarinyar ta farka, saboda ta ƙwallafa rai akanta sosai, tunkafin ma tafarka tasan wacece ita, Allah ya jarabceta da son yarinyar,
Tun tana sa ran zata farka, har dare ya yi bata farka ba, har sun fara fidda rai, Su uku ne acikin bukkar, Danejo da kuma Hasiya, suna ta zaman jiran tafarka har bacci ya yi awon gaba da su.
Tsakar dare lokacin kowa Yayi bacci Cikin ƴar bukkarsa, ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta, ƙoƙarin motsa Jikinta tayi sai dai ina sam takasa,tamkar an ɗaureta da igiyoyi haka take ji, ga wani irin zafi da take ji ajikinta, sautin muryarta sam baya fita, Can ƙasan maƙo shi take sambatu,
“Daddy mu koma gida, tsoro nake ji,”tun sautin baya fita harya fara fita da Æ™arfi, da iya Æ™arfinta na Æ™arshe Ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, buÉ—e idanuwanta tayi sosai tana kallon Bukkar, Wasu jerin kwaryoyi tagani a jere, da wani akwatin karfe da sauran tarkacensu na fulanin daji, Wurga eyes dinta tayi akan Fitilar kwan dake Ajiye a Æ™asa wadda ta haskaka Cikin bukkar, kafin takai idanuwanta kansu Danejo dake ta bacci daga zauna suna gadinta,
Wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarta, hankalinta ya tashi matuƙa, ganin baƙin fuskoki, Ga kuma wani wuri mai kama da A kurkukin kaji, rushewa tayi da matsanacin kuka, a firgice Danejo da hasiya suka farka jin sautin kukan Mutun, Tsareta da ido su ka yi suna kallonta kamar yadda take kallon su, Cikin harshen fulatanci suka soma ƙoƙarin rarrashinta, Ta wawware masu gray eyes ɗinta, jin suna yi mata gwaranci,
Cigaba da kuka tayi tana faÉ—i”Daddy! wayyo Allah na!! Ina daddyna ya ke!! Su wanene ku! A ina nake ne!!” miÆ™ewa Ta yi da Æ™yar saboda ba isasshiyar lafiya gare ta ba, Jikinta sai kerma yake yi, Ga uwar zufa data wanke mata jikin nata, ganin tana Æ™okarin neman hanyar fita daga Cikin bukkar yasa suka miÆ™e da sauri Suka nufe ta zasu ruÆ™eta, watsawa ta yi da gudu tana bin jikin bukkar a Æ™okarinta nata gano hanyar da zata fuce, su kuwa sun dage sai haÆ™uri suke bata”kiyi hakuri ki zauna baki da lafiya, muma mutane ne kamar ke kada kiji tsoron mu baza mu cutar dake ba” tunda suka soma magana take ta faman zazzare masu idanuwanta, saboda bata fahimtar yaren da su ke yi mata magana da shi, ballantana kuma harta fahimci cewa lallashin da suke Yi mata,
“Wayyo Allah daddyna, Ni ku maida ni wurin daddyna, Inaso nagan shi,” sosai take Yi masu kuka, mai tsiwar gaske, gaba daya sautin kukan nata ya karaÉ—e kunnuwan duk wani mai yin Bacci acikin bukkokin,
Kukanta Ya ishesu, É—aya bayan É—aya suka soma fitowa daga cikin bukkokinsu, kowa yana ta faman Yin hamma, A haka suka nufi bukkarsu danejo, inda suke Ji yo sautin kukan nata.
Inna wuro ce ta shigo ciki, tare da su haulatu, gaba daya suka É—aura idanuwansu Kan ANGEL, dake ta kuka, tambayar su Danejo su ka yi meke faruwa?Suma su ka ce basu sani ba, ta tashi tana ta kuka, kuma su basu san harshen da take yi masu magana da shi ba” adaren ranar babu wanda ya runtsa Cikinsu, taruwa sukayi akanta sunata aikin lallashi, ta burkuce masu sam bata fahimtarsu, kamar yadda suma basu fahimtarta, sunan Daddynta kawai take kira,
Koya rayuwar Angel zata kasance acikin fulanin daji? Yarinyar da ta taso Cikin kulawa da soyayyar mahaifinta, batasan rashi ba, batasan maraici ba, Ta saba da rayuwar gatanci sai abunda takeso daddynta yake yi mata, Yau gata a ƙurmin daji, Cikin fulanin daji mutanan da basu Jin harshen hausa Sai fulatanci, ita kuma bata Jin fulatanci daga hausa sai turanci, Sai kuma larabcin data koya a makarantar islamiyar da take zuwa, Taya zata Iya jure zama dasu? Abincinsu yanayin rayuwarsu sam ta banbanta da ta mutanan dake rayuwa Cikin gari,
Kafin safiya tayi Angel ta galabaita sosai, Idanuwanta sun kunbura saboda rashin bacci da kuma kukan data sha, sun Æ™anÆ™ance, jijiyoyin wuyanta duk sun firfito rudu ruÉ—u jikin fatarta, le6enta ya faffashe hada busasshen jini, ga wani irin zazza6i na tashin hankali daya rufarmata, a Æ™arshe yanke jiki tayi ta faÉ—i asume, Jinya ta koma sabuwa, magunguna suka shiga haÉ—a mata nagargajiya Æ´an dabarunsu da ba’a rasa ba, Hada wasu ganyayyaki suka jiÆ™a mata acikin gora, suna bata tasha, Allah ya haÉ—a jininsu da ita, musamman Danejo kullum A tare da ita take kwana, Ba Æ™aramin tausayinta suke Ji ba, Saboda ko magana bata Iya furtawa, Jikinta yayi tsauri sosai, Babu sauÆ™i tamkar zata rasa ranta, ga shi ko a bincinsu bata Iya ci, Furace kaÉ—ai itama É—in sai sun É—ura mata abaki tukunna take wucewa ta makoshinta daÆ™yar, angel ta wahala sosai, ta rame ta bushe ta Æ™anjame tayi duhu tamkar ba yarinyar nan mai Æ™iriniya ba,
Kusan Wata Uku ta yi Acikin wannan mawuyacin halin, kafin Allah ya kawo mata sauƙi, tafara buɗe baki tayi magana, Sai dai subi ta da ido don basu fahimtar me take cewa, kullum saita yi masu sambatu akan su nemo mata daddynta, daga baya da ta fahimci basu gane yaren da take yi masu, Saita Zuƙunna ta sanya yatsanta a kasar wurin da ruwa ya jiƙa,ta soma Zana fuskar mutun Asaman ƙasar, data kammala zanen ta kirasu tana nuna masu zanen, Suka zuba ido suna kallon jagwalgwalon zanan fuskar da ta zana, Kallon juna su ka yi Alamar basu fahimta ba, fashewa tayi da matsanancin ku ka, Ta watsa da gudu Tabar wurin bukkokinsu, Suma suka bi bayanta a guje, suna ƙokarin kamota gudun kada wata muguwar dabbar daji ta halakar da ita,
Cikin ƙurmin dajin ta nutsa, har tazo inda wannan ruwan Yake inda Taj ya jefa ta ciki, Juyo wa Tayi tare da kallonsu, sai faman haki suke yi sun sha uban gudu, da hannu ta dinga nuna masu cikin ruwan Saboda ta gane cewa a nan ne inda daddyn ta Yazo da ita Ya wurgata ciki,
Duk yadda taso ta fahimtar dasu, Sam sun gaza fahimta, dunƙule hannayenta tayi tare da murzasu, tana kwatanta masu a cikin mota suka zo dajin, Nan ma still basu gane me take nufi ba, Zuƙunnawa tayi agaban ruwan, ta rushe da matsanancin kuka, duk jikinsu yayi sanyi,
Babu yadda angel ta iya adole ta haƙura taci gaba da rayuwa acikin fulanin daji, tun bata saba ba da su ba, har ta fara sakin jiki da su, Bata da abincin daya wuce fura da nono, da kuma Gasassar masara, Sai kuma nama idan sunyi farauta, shigarta ta koma ta fulanin daji, Danejo ce tayi mata kyautar kayanta, Wanda tun tana yarinya kayan suke ajiye cikin akwatin ƙarfenta, Zuwan Angel Cikin rayuwarsu Ta fiddo da kayan, Ta bata su ta sanya,
Duk rana ta Allah sai angel da danejo sunje Bakin ruwan nan, Kullum ne wani lokacin har dare suke kaiwa abakin ruwan, atare suke fita kiwon shanu, hatta tatsar nono sai da danejo ta koya mata, da wasu abubuwan nasu na fulanin dajin, baiwar Allah ba yadda za ta yi don dole take rayuwa a cikinsu, Allah ne kaɗai yasan halin da Zuciyarta take aciki, a kullum idan suka kwanta suna Bacci, tare da su danejo da hasiya, bata iya runtsawa, Zama take yi tsakar dare, tadinga kukan zuci tana roƙon Allah yasa daddynta yana A raye, ta karaya sosai, wani sashe na zuciyarta yana raya mata cewar Waɗannan mutanan da suka Biyo su suna harbin motarsu sun kashe mata daddynta, amma kuma har cikin ranta tana jin cewa Yana A raye, taya zata tabbar da hakan? Ita dai bata ga gawar mahaifinta ba, balle tashai da yabar duniya, A ƙalla Angel tayi shekara Biyu A hannun fulanin dajin nan, A lokacin Tafara Jin fulatanci sama sama saboda xama da tayi da su,
duk da sabon da tayi da su hakan bai sa ta fasa ƙudirinta na guduwa daga Cikin dajin ba, duk don saboda taje neman Mahaifinta, abunka ga Yaro ga kuruciya, zuciyarta saita dinga raya mata cewa ta gudu taje gidan su, zata samu mahaifinta agida.
A ranar data shirya guduwa daga Cikin dajin, Sai da tabari kowa Ya yi bacci, batare da jin tsoro ba ta fito daga Cikin bukkar, Ko’ina duhu kasancewar darene sosai, Cikin sanÉ—a take tafiya Tana nufar cikin dajin, duk in taji kukan shanayensu saita firgita, gani take kamar zasu farka daga bacci ne su hana ta guduwa
Ganin tayi nisa daga inda bukkokinsu suke, ta soma tunanin wace hanya zata bi don ta fita daga cikin dajin, ga duhu ko’ina, sai É—an hasken farin watan da ba’a rasa ba, tana cikin wannan tunanin ta jiyo muryar mutun a bayanta, A firgice ta juya don taga wanene, Hasken fitila tagani amma ba ta iya tantance wanda ya biyota ba, duk da taso ta É—auki murya,
Tattare zanin jikinta tayi na kayan fulanin da suka bata sune sanye ajikinta, ta watsa aguje cikin dajin tamkar zata tashi sama, tana gudu tana tuntu6e wani lokacin har faɗuwa kasa take yi a haka za ta daure ta miƙe taciga ba da gudu tana waiwayan mutumin daya biyo ta, ganin shi ma yana gudu, nan fa ta ƙara gudun nata, tsawon lokaci suna wannan ƴar guje-gujen cikin dajin ita da mutumin daya biyo ta har Allah Ya kawo ta bakin titi a galabaice ta haye saman titin, wani irin jirine ya soma ɗibar ta. Ta fara tangal tangal za ta faɗi ƙasa, a haka ta jure taciga ba da gudu, ba zato ba tsammani sai ga wata zungureriyar mota baka ta yi parking a inda take a tsaye, A slow murfin motar ya zuge,
Zuro Hannu aka yi daga cikin motar aka ɗauke ta, murfin motar ya koma ya zuge da kanshi, da gudu motar ta miƙi titin.
A daidai wannan lokacin Danejo ta faɗo saman titin a galabaice hannunta riƙe da ƴar filita. Ashe ita ce ta biyo Angel, don ta ga lokacin da za ta gudu daga Cikin bukkarsu.
Waro ido waje ta yi ganin dankareriyar motar da ta ɗauki Angel, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta fara yin tozali Mota, Tsoro duk ya cika ta, hankalinta ya yi matuƙar tashi, ganin an raba ta da Angel. A gefen titin ta tsugunna tana kuka tamkar ranta zai fita. Wannan shi ne silar rabuwar Angel da Fulanin Daji.
A nan gefen titin Danejo ta yanke jiki ta faɗi a sume, a washe garin ranar ƴan uwanta suka farka daga barci, ba su ga Angel da Danejo ba, hankalinsu ya tashi gabaɗaya suka bazama cikin dajin neman su. Har Allah Ya sa Su Bawuro suka tarar da ita a gefen titi ita kadai a kwance ba numfashi, lamarin ya yi matuƙar girgiza su, tunda suke da Danejo ba ta ta6a yin nisan kiwo irin na yau ba, sun yi mamakin ganin ta ita kaɗai ba tare da Angel ba.
Bayan komawarsu cikin rigarsu, Suka yayyafa ma danejo ruwa ta farfaɗo, fashewa ta yi da matsanancin kuka tana faɗa masu yadda suka rabu da Angel. Duk jikinsu ya yi mugun sanyi, kowa bai ji daɗin lamarin ba, sai dai ba su da yadda za su yi. Da ma tsintacciya ce duk da sun yi sabo da ita, zuwan Angel cikinsu ba ƙaramin farinciki ta samar masu ba. Sun ji takaici da baƙin cikin ɗauke tan da aka yi, to ya za su yi? Allah Ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan.
Da daÉ—i da ba daÉ—i haka Danejo ta ci gaba da rayuwa cikin Æ™unci da takaicin rashin Angel, ta rame ta Æ™anjame tamkar ba Bafullatanar nan ba mai yawan fara’a mai son yin rawa, yanzu ta koma salihar Æ™arfi da yaji. Kullum cikin yin zazza6i take, kuma kullum tana akan hanyar zuwa bakin ruwan nan inda suke yawan zuwa ita da Angel su zauna. Kafin tafiyar Angel ta ba su labarin mahaifinta daya gudo da ita cikin daji, a lokacin ta fara jin Harshensu na Fulatanci, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da su.
*ANEELERH*
Kwance take saman haɗaɗɗen gadonta na gidan su, A gefenta ƙaramin yaronta ne wanda bai wuci shekara ɗaya da ƴan watanni, Jikin shi na a sanye da overall pink colour, Kyakkyawan yaro rainon madara, fari tass kamannin shi sak na mahaifiyar shi, tamkar ta yi kakin shi, kan shi a cike yake da kwantacciyar suma mai laushin gaske, mommyn ta shi dake kwance gefen shi tana ta sharar bacci Rigar bacci ce a jikinta launin sky blue,
Wata irin zufa ce ta soma wanke mata fuskarta, ta ko’ina zufar take tsastsafo mata, rurruÆ™e bedsheet É—in tayi da hannayenta da ke ta kerma, sambatu ta soma yi tana ambaton sunan ANGEL, still idanuwanta suna a rufe da alama mafarki take yi, Cikin shesshekar kuka take faÉ—in”Angel meyasa nake ganin cikin mawuyacin hali? Waya ta6amun ke? Angel kiyi magana meyasa ki ke kuka? Dan Allah ki faÉ—amun angel,” Ciccije lips É—inta take yi sosai take Æ™ara sautin kukan nata,
A dai dai lokacin mami ta fito daga É—akinsu, itama kayan baccin ne a jikinta doguwar riga, sai hamma take yi da alama daga bacci ta farka, É—akin Aneelerh ta nufa tunkafin ta shiga ta soma jiyo sautin muryarta, ta cikin É—akin tana kuka,
Da sauri mami ta faÉ—a cikin É—akin babu wadataccen haske sun kashe Kwan É—akin kafin su kwanta, bedside lamp ce kaÉ—ai take a kunne ta É—an haskaka É—akin,
Ƙarasawa tayi daga gefen gadonta, takai hannu tana É—an bubbuga shoulder É—inta”Aneelerh! Aneelerh! Lafiyar ki kuwa? Kike ta ku ka”? Muryar mami ce ta farkar da ita, lokaci É—aya ta zabura zata sauko daga saman gadon, damÆ™o damtsen hannunta mami tayi’ke lafiya? Bakya ji ina magana”?
“Mami ki barni in tafi, tana buÆ™atar taimako na,” la66anta na kerma tayi maganar,
Fuskar mami da alamun ruÉ—i tace”wai wacece kike magana akai”? Juyowa tayi suna kallon juna, idanuwanta sunyi jawur tace”ANGEL ”
Sakin hannunta mami ta yi ta dafa kafaÉ—unta, cikin natsuwa ta soma magana” ki kwantar da hankalin ki, ki faÉ—amun meya faru da angel, kinyi mafarki ne akanta”?
Jinjina kai tayi cikin shessheÆ™ar kuka tace”Mommy, I had a really scary nightmare about angel, tana a cikin mawuyacin hali, yanayin da nake ganin angel abun ya ta6a zuciyata……” takai Æ™arshen maganar hawaye na bin fuskarta
Shiru mami ta yi idonta akan fuskar aneelerh, Kafin tace”addu’a yakamata ki yi,”
Cikin disasshiyar miryarta, ta ambaci “Ø£َعُوذُ بِاللَّÙ‡ِ Ù…ِÙ†َ الشَّÙŠْØ·َانِ الرَّجِيمِ ÙˆَÙ…ِÙ†ْ Ø´َرِّ Ù‡َØ°ِÙ‡ِ الرُّؤْÙŠَا”
Kusa sau uku tana ambaton addu’ar,
“Aneelerh mafarki ba gaskiya bane, ShaiÉ—an ne kawai yake son rikitar dake” girgixa kai aneelerh tayi”mami wannan mafarkin ya wuce a ce shaiÉ—an ne, ba yau ne rana ta farko da nafara yin shi ba mami, kuma a duk lokacin da zanyi shi, angel nake gani ita kaÉ—ai tana kuka jikinta sanye da yagaggun kaya kamar Almajira,”
“A kowani lokaci, ki ka yi mummunan mafarki akan angel, you should pray for her, alama ce da ke nuna cewa tana buÆ™atar addu’ar ki, duk da ki nayi saiki ninka akan wadda kike yi masu, muma kuma in sha Allah zamu dage” miryar abie ce, sam basu ji alamar shigowar shi ba, a tare suka Kai idanuwansu kan shi,
A tsaye yake bakin ƙopar ɗakin jallabiya ce a jikin shi, yayi shirin zuwa masallacin domin yin sallar asubahi da ake ta kira,
Tafiya yaci gaba da yi cikin É—akin yana nufar su,
“Wipe ur tears aneelerh, bana so na sake ganin hawayen ki, ” cikin sanyin murya ta amsa mashi da “toh”
“That’s good, Jiya munyi waya da uncle abdallah” ya dakata da maganar, a Æ™agare suke kallon shi, sun Æ™osa su ji mai zaice,
“Yayi mun magana akan BABY JUNAID, nasan aneelerh bazata ji daÉ—in maganar ba, shiyasa tun jiya ban sanar maki ba,” tunkafin ma yakai Æ™arshen maganar aneelerh ta É—aure fuskarta walwalarta gaba É—aya ta É—auke,
Ita kanta mami yanayinta ya canza, don tunkafin ma ya ƙarasa sunsan inda zancen nashi ya dosa,
“Suna so A basu shi, ya koma hannun su da zama, da zarar kin yaye shi,…..’ girgiza kai aneelerh ta shiga yi tana faÉ—in”Haba abie, idan aka raba ni da shi ya ake so inyi da raina? Yaron nan fa shi nake gani inji daÉ—i araina, ina kallon shi amatsayin kyautar Allah, inaji araina Allah yabani shi ne saboda rashin da na…..” Æ™asa Æ™arasa maganar tayi saboda kukan da ya ciyota, da sauri ta kifa kanta saman pillow,
Dariya sosai abie ya yi, ganin yadda ta harzuÆ™a jin za’a rabata da gudan jininta,
Kallon juna su kayi shi da mami, “meyasa? Kana ganin halin da take ciki, kuma ka ke son Æ™ara tayar mata da hankali, dagaske ka ke ko wasa? Nasan ka da son zolaya”
Bai bata amsa ba, Ya juya ya nufi Æ™opar fita yana faÉ—in”Idan na dawo daga masallaci zamu yi magana” daga haka ya fuce daga cikin É—akin,
Shafa bayan aneeleeh mami tayi”ke ki kwantar da hankalin ki, ae wlh ba wanda ya isa ya raba ki da É—anki, Sai Allah nasan aikin hajiya adama ne, ita zata tunzura shi akan su É—auko yaro, in banda ma abunsu ae yaron bai kai shekarun da zasu É—auke shi ba, koda kuwa an yaye shi, nifa ko ya cika shekarun da zasu É—auke shi bazan bari su rabaki da shi ba, idan suna son É—a su haifi wani mana, wannan dai naki ne ke kaÉ—ai……..”
Jin kalaman mami yasa aneelerh ta tsagaita da yin kukan, ba ƙaramin daɗi taji ba, ɗagowa tayi daga kan pillow ta kwantar da kanta saman kafaɗar mami,
“Mami karki bari araba ni da baby junaid É—ina, wlh zuciyata zata iya bugawa” shafa sumar kanta mami tayi”ae me raba ki da shi sai ya shirya, Idan ma suka matsa number zanyi wa lawyer na magana,” murmushi aneelerh ta saki saboda jin daÉ—in maganar, tasan mami tana son farin cikin ta, bazata so a bunda zai6a ta mata ranta ba
“Kada mu makara, ta shi kije kiyi sallah, shime babyn naki ki tada shi yaje ya yi sallah,” dariya aneelerh tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet, mami nata kallonta har ta shige ta rufe Æ™ofar, ajiyar zuciya taÉ—an sauke dama ta faÉ—i hakan ne donta kwantar mata da hankalinta,
Juyawa ta yi tana kallon Junaid dake kwance sai sharar baccinsa yake yi, hannu takai ta shafa sumar kanshi” Grandson, Allah yabar mana kai,” bargo taja ta lullu6e mashi jikin shi, yaron ba ruwanshi sam baida damuwa, ga nauyin bacci da Allah ya yi mashi, shifa ba Æ™aramin abu ke tada shi daga bacci ba,
Saukowa mami ta yi daga saman gadon ta fuce daga É—akin zuwa nata É—akin domin tayi sallah,
Fitarta keda wuya aneelerh ta fito daga toilet, shaf shaf ta canza rigar baccin jikinta zuwa Jallabiya, ta É—auko hijabi ta zura a jikinta, ta koma saman darduma ta kabbara sallah a tsanake ta shiga yin ibadarta,
Bayan ta kammala yin sallar saman darduma ta zauna tana yin tasbihi, hannunta É—aya ruÆ™e da cazbaha, bayan ta kammala tayi azkhar, kafin ta É—aga hannayenta sama ta soma yi masu Angel addu’a, Yayin da hawaye ke bin fuskarta,
“Ya Allah kafi kowa sanin a wani hali waÉ—annan bayin naka suke ciki, ya Allah ka tsare su da tsarewarka, Ya Allah ka kare su daga sharrin mutun sharrin aljan da sharrin duk wani abin cutarwa, Ya Allah idan har suna araye ya Allah ka bayyanar mana da su, idan kuma……kasa Æ™arasa addu’ar ta yi, sam bata so ta ambaci mutuwa, tuni idanuwanta sun cicciko tab da kwalla, lumshe idanuwa ta É—anyi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata fuskokinsu, Uzair taj da kuma Angel,
Ta yi nisa acikin tunaninta, Sautin kukan Junaid ya farkar da ita, ajiye cazbahar tayi saman dardumar ta miƙe da sauri ta nufi saman gadon, yana ganinta ya dakata da yin kukan ya tsareta da manyan idanuwanshi, murmushi tasakar mashi sai gashi shima ya sakar mata murmushi,
Cire hijabin jikinta tayi tare da ninketa ta É—aura saman mattress É—in, hawa saman gadon tayi tare da kai hannu ta É—auke shi jan hancin shi tayi”i know u are not hungry rigima ce kawai ko”? ta6e tausasa la66ansa yayi alamar zaiyi kuka, dariya tasaki tare da cewa”stop crying my baby boy, shagwa6a66an yaro na” a gefen gado ta zauna tana shayar da shi, bayan ta kammala ta zaunar da shi, takai hannu ta É—auko hoton su angel dake ajiye saman drawer,
Su haɗu ne a haton ranar birthday ɗin Angel a kayi masu hoton, sunyi matuƙar yin kukan, kowannansu fuskar shi ɗauke da dariya ga cake duk ya 6ata fuskarsu, yatsun hannunta ta ɗaura saman hoton tana shafa fuskokin su, tun daga face ɗin Uzair zuwa ta taj, kafin ta tsayar da hannunta a kan hoton Angel, murmushin takaici ta ɗan saki, ta ɗago ta kalli junaid, ya tsareta da ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, gefen shi ta matsa ta zauna, ta saita hoton saitin fuskarshi, magana ta soma yi mashi saitin kunnanshi,
“Ka ga wannan shi ne daddyn ka, sunanshi Uzair, wannan kuma Taj, shi aminine kuma É—an uwa ga mahaifinka, ita kuma wannan she’s ur elder sister Sunanta ANGEL” tana rufe baki taji ya maimaita sunan Angel, murmushi tasaki dama wani lokacin duk in tayi magana saiya maimaita,
“Da ace tana nan, da yanzu ita zata dinga goya mun kai abayanta, Allah sarki Angel tayi jiran zuwanka na tsawon lokaci kullum tana tambaya aunty aneelerh wai ke bazaki haifa mun Æ™ani ba, ni na Æ™osa naga É—an yaron ki, sai ga shi na same ka a lokacin da angel bata nan, tana a raye kota mutu bani da masaniya akan hakan,” duk wannan surutun da Aneelerh ke yi, Ya natsu yana sauraronta kamar yana fahimtar me take cewa”
“KANA NAKA ALLAH NA NA SHI wa ya yi tunanin ma za’a wayi gari babu su a lokaci É—aya? Ban ta6a kawo hakan araina ba, kaima kuma ban sanya ran zan same ka ba, sai gashi Allah ya bani kai, ina matuÆ™ar sonka my baby boy,” takai Æ™arshen maganar tare da manna mashi kiss saman forehead É—insa, kafin ta É—aura hoton saman side drawer,
Rungumoshi ta yi a jikinta, wani baccin ne ya kuma É—aukarsu,
Wuraren ƙarfe tara na safe, Mami ta shigo ɗakin nata, har ta kimtsa kanta Cikin Atampa,
Ganinsu rungume da juna ita da junaid, yasa ta saki murmushi, baƙaramin ƙaunar yaron take ji ba, ita kanta mamin saboda sunan yaron yaci Sunan marigayi mahaifinta Alhaji Junaid Shuwa, tun lokacin da mami ta auri Mahaifin Aneelerh Alhaji Muhammad falgore ta ƙwallafa rai akan ta samu ɗa namiji don ta sanya ma shi sunan mahaifinta, Allah bai nufa ba, ƴa ta samu mace kuma daga ita bata ƙara haihuwa ba, Aneelerh tasan da wannan burin na mahaifiyarta, shiyasa ta sanyawa yaron Suna Junaid, kuma aka amince mata da sunan, ko lokacin da su Uncle abdallah suka zo Nigeria don su ga jikan su, basu yi gaddama ba da aka faɗa masu sunan yaron, saima farin Ciki da su kayi An haifa masu ɗan kyakkyawan Saurayi.
Ƙarasawa gaban gadon tayi ta kira sunanta”Aneelerh wake up, lokacin yin breakfast ya yi, abie na son magana dake,”
BuÉ—e ido aneelerh tayi akan mami, biji biji take ganinta kafin idon ya washe,
“Mami,” ta ambaci sunanta muryarta da alamun bacci,
“Muna jiran ki a dining area,” mami ce ta yi maganar, tare da juyawa ta fuce daga É—akin,
A lalace Aneelerh ta miƙe ta sauko daga saman gadon, toilet ta nufe ta shige, bayan ta fito daga wankan, bata canza jallabiyar jikinta ba, mayafi kaɗai ta dauko cikin closet, tayi rolling ɗin shi a saman kanta,
Fitowa daga É—akin tayi ta nufi dining area, A saman dining chairs ta iske su zaune su biyu, sai Ana mai aikin gidan Aneelerh dake tsaye tana yin serving É—insu,
Tana Æ™arasowa Ana ta soma gaishe da ita cikin girmamawa”good morning madam, how was ur night” murmushi Aneelerh ta sakar mata”Alhamdulillah, ina fata kema haka,” jinjina mata kai ta yi alamar eh,
Mayar da idanuwanta tayi kan iyayen nata, gaba É—aya ita suke kallo, da sauri ta gaishe da su, su ka amsa mata fuskokin su a sake,
Kujera taja ta zauna, Ana tace” me zan zuba maki”?
“Cup of tea, ki haÉ—a mun da noodles,” amsa mata tayi da toh, ta É—auki serving spoon da plate ta soma zuba mata noodles É—in, bayan ta gama haÉ—a mata ta tura mata gabanta, tare da kofin tea,
Har ta É—auki fork zata fara cin abincin ta É—ago ta saci kallon iyayen nata, da yake suna fuskantar juna,
Ganin suna kallonta yasa ta sunnar dakai Æ™asa, murmushi su ka sakar mata, mami tace” Ina kika baro mana baby junaid É—in mu”?
“Bacci yake yi,”
“Ya cika bacci anya kuwa lafiya”?
Abie yace”lafiyar ce ta kawo haka ae, yaron fa É—an hutu ne, ” da zolaya ya yi maganar, murmushin gefen fuska aneelerh tasaki”mami ae ya farka É—azu, daga baya ne ya koma bacci” mami tace”Okey, ki ci abincin ki, yana huce wa” kallon abie ta yi tare da cewa”abie da gaske ne uncel abdallah ya kira akan zasu kar6i baby junaid”? yanayin yadda tayi maganar a É—an tsorace take da jin amsar da zai bata,
“Dagaske na, Amma ki kwantar da
hankalin ki, bawan da zai raba ki da babynki, mutu ka raba takalmin kaza” dariyar farin ciki ta saki, hatta Ana dake a tsaye saida ta murmusa,
“Ci ki Æ™oshi daughter, farin cikinki ae shi ne namu,” yakai karshen maganar tare da kallon Ana dake a tsaye”Nayi magana da drivern da zai kai ki garin ku, ki kasance a cikin shiri a kowani lokaci zai iya zuwa ku tafi” jin wannan maganar yasa yanayin fuskarta ya canza ta shiga yarfa hannu, cike da mamaki suke kallonta, tattara skirt É—in jikinta tayi tare da zuÆ™unnawa saman guiwowinta, tana faÉ—in
“Allaji ayi haÆ™uri abarni anan tunda har nakai wannan lokacin, wlh kona koma Æ™auyanmu wahala zanci, Noman doya za’a sanya ni, dan Allah Alaji a taimaka, Æ´an uwana duk suna a cikin garin nan suna aiki, dama mu uku ne marayu iyayen mu sun rasu,” tuni hawaye sun wanke fuskarta, kallon aneelerh tayi a marairaice tace”madan ki taimaka, abarni anan wlh noman doya da wahala”, duk wannan Æ™ibar da nayi idan har na kuskura na koma Æ™auyan mu, Cikin kwana uku zan sace,” mami dai dariya ce ke son kufce mata, amma ta gumtse ta cikin baki, shi kanshi abie taso ta ba shi dariya, musamman hausarta da bata fita sosai,
“Abie, tunda tana taimaka ma Inna hauwa wurin yin girki, da aikace aikacen gida ni ina ganin barta kawai,”
Mami ma tace”Nima na goyi bayan haka, saboda ta nuna bata son noman doya…..”takai Æ™arshen maganar tana Æ´ar dariya,
“Yanzu ina Æ´an uwan naki”? Abie ne yae mata tambatar,
Hannu tasa tana matse ƙwallar dake akan fuskarta,
“Esther tana aiki a restaurant itace take aiki gidan Iyayen Sir uzair, Tun bayan barin su Æ™asar ta koma restaurant da aiki, ita kuma janet, tun lokacin da madam Benazir ta koreta, ta samu aiki a hotel,”
Ajiyar zuciya abie ya sauke, kafin yace”Shikenan zaki zauna anan, amma fa zan sa maki ido, duk ranar da kika aikata badaidai ba, zan turo ki Æ™auyan ku, aje can ayi noman doya,”
Gaba É—aya suka saki dariya, miÆ™ewa tayi muryar na rawa ta shiga faÉ—in”thank u sir, thank u madam ngde ngde,” tsantsar farin ciki ne akan fuskarta,
“Ki koma wurin Inna hauwa, ku yi breakfast É—in ku,” mami ce ta yi mata maganar, da sauri ta juya ta nufi part É—insu,
A tsanake suka cigaba da yin breakfast É—insu, sai da suka kusa kammalawa, aneelerh ta mike mami tace ina zuwa,
“Inaji araina kamar Junaid ya farka, bari naje na duba shi,” da sauri ta wuce É—akinta,
Kallon Juna abie da mami su kayi,
“Namanta ban faÉ—a maki ba, Munyi waya da É—an Iya, wai yana so Aneelerh ta koma hannun shi da zama, Zai sama mata aiki a Asibitin *CHIEF OBINNA* ” rass Mami taji gabanta ya faÉ—i, can kuma ta É—an saki murmushi,
“Ka daina yarda da maganar É—an Iya, kasan halin shi, Ya iya shirga Æ™arya in banda abunka taya za’ae ya iya sama mata aiki A wannan katafaren asibitin wanda ma’aikatan cikinsa ma fa, É—ai É—ai ku ne Æ´an Æ™asar nan, amma fa in ta samu aiki acan zan fi kowa mafarin ciki, don naji ance Æ™aramin ma’aikaci na asibitin just cleaner kawai albashin shi yakai Dubu É—ari da hamsin,
Abie yace”nima nayi mamaki da yace haka amma kuma kinsan shi, mutunne na jama’a, duk wani politician daya shahara yasan shi, to ba abun mamaki bane don yace zai iya sama mata aiki acan, Ni abunda yasa ma na yi mata sha’awarar zama can abujan, zata fi samun kwanciya hankali akan nan, yau fa tsawon shekara biyu da watanni, rabon aneelerh da taje aiki, badan Dr Aisha ta kar6i ragamar kula da asibitin ba, da yanzu komai ya durÆ™ushe”
Shiru mami tayi na wani lokaci, aranta ta ayyana cewa in kuwa har Aneelerh ta samu aiki a asibitin *CHIEF OBINNA* tabbas cikin Æ™ankanin Lokaci zata zama hamshaÆ™iyar mai kuÉ—i, kuma zata ji daÉ—in rayuwa agidan É—an Iya, saboda barkwancin shi dana matar shi, Æ´an sharholiya ne ana shan drama a gidansu, sai dai kafin Ashawo kan Aneeelerh ta zauna acan É—in shine abu mai wuya, kuma suma kansu baza su so tayi nesa da su ba, duk da shima abie Suna hasashen zai samu Æ™arin matsayi a wurin aikin shi, nan badajimawa ba za’ayi mashi transfer zuwa Ministry of finance dake abuja,
Sun jima suna tattaunawa da abie kafin Yayi mata sallama, Ya tafi zuwa wurin aikin shi, ita kuma Mami ta koma falo, a lokacin aneelerh ta dawo falon hannunta É—auke da juanid, fira suka zauna sunayi yayin da plasma tv ke a kunne suna kallon tashar arewa 24,
*To fa😳Su Angel An yi gudun gara An faɗo gidan zago, ko ina ne Wurin nan? Lamarin ya ɗaure mun kaina, To dai mu haɗu a next page gobe in Allah yakainu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya, kada ku manta friday da weekend ba posting, Amma zanyi ƙoƙari in dinga yi maku Long pages, Ga waɗan da suka shirya yin payment ƙopa a buɗe take su yi mun magana (08103884440)**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*Boss Bature ✍️*
dedicated to Aunty kubra❤
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 9"