Kurkukun Kaddara 7
*E7*
Su na Cikin Maganar nan, Su ka ji yo wani irin gurnani, A ruÉ—e su ka É—ago suna kallon su,
Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take ya zama wata halitta mai matuƙar tsoratarwa, Ya shiga girgiza jikin shi Yana wani irin gurnani,
Tashin hankalin da ba’a sama shi date, Wani irin tsoro ne ya bayyana a kan fuskokin su, Tuni zufa ta wanke su sharkaf, Don tunda Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun ya rikiÉ—a ya koma dabba ba, duk da suna Jin labarin Matsafan dake rikiÉ—a suna canza halittar su,
Ja da baya halittar nan tayi, Kafin Ya daka suka, Kaitsaye Ya faÉ—a kan Ƴa’Æ´an malamin nan, Ya shiga yagar Naman Jikin su Yana ci, malamin na kuka yana Æ™oÆ™arin ceton ran Æ´a’Æ´an shi da jini Ya wanke fuskokin su, Aikuwa nan take sauran Alhazawan guda biyar dake a kewaye da su, suka rikiÉ—a, gaba É—ayan su ka canza halittar su, Cikin lokaci Æ™anÆ™ani su ka handame malamin nan da ya’yan shi,
In taƙaice maku zance, Sai da Suka cinye namansu tass, Ko ƙashi basu bari ba, Tukunna Suka rikiɗa a lokaci ɗaya suka koma Mutane, Bakin kowannan su, Da6a da6a da jini,
A hanzarce bodyguards ɗinnan suka zura hannayen su Cikin aljihunan wandunansu kowannansu ya zaro Hanky mai girma. suka shiga goge masu jinin da ya 6ata bakunan su, Bayan sun kammala suka jefar da hanky ɗin Cikin ƙoramar dake a gabansu,
Batare da 6ata lokaci ba, suka koma Cikin motocin su, a guje suka bar cikin dajin 6aaat suka 6ace,
Jikin Taj na kerma Ya kalli Uzair wanda tuni ya jima da ƙamewa a tsaye kamar saƙago, Idanuwanshi sun firfito waje tamkar zasu faɗo ƙasa,Wani irin matsanancin tsoro ne ya ziyar shi zuciyoyin su, hankalin su ya tashi matuƙa,
A ruÉ—e Taj ya fisgi hannun Uzair suka Koma Cikin motar su, Aka rasa wanda zaiyi driving É—in su, tsakanin su biyu, jikinsu duk yayi sanyi ga wata uwar zufa dake tsatstsafo masu, tamkar waÉ—anda aka tsamo su daga cikin ruwa sun haÉ—a uban gumi, daÆ™yar Taj ya iya tada motar, ya samu ya karya kwana da wani irin speed ya fusgi motar tamkar zasu tashi sama, Duk tsoro ya kama su ga tausayin malamin nan da Æ´a’Æ´anshi, abun ya yi matuÆ™ar girgiza su,
A can gida kuwa, Sam bacci ya ƙaurace wa idanuwansu, Daga angel ɗin har aneelerh, Sun yi zugudum saman Gado, kowa da abunda yake ayyanawa a ran shi, Ganin har ƙarfe 12 ta buga amma ba su dawo ba,
“Aunty aneelerh, ni tsoro nake ji kada a ce wani abu ya faru da su daddy” Janyo ta Jikinta aneelerh ta yi Tare da shafa sumar kanta tace”in sha Allah ba a bunda zai faru da su, zasu dawo ne nan bada jimawa ba, ni inaji a raina”
“Allah bazan Æ™ara bari ya tafi ya barni ba, duk inda zai je Æ™afata Æ™afar shi, idan ba haka ba zan sa ce tayar motor shi kowa ya rasa” aÉ—an shagawa6e tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka,
Fashewa aneelerh tayi da dariya daÆ™yar ta tsagaita da yin dariyar tace”Idan ki ka sa ce tayar motar shi ae yana da Æ™afafu ko suma zaki guntule su ne? Kuma in banda abun ki, idan kika sa ce tayar motar shi, ae a kwai ta Uzair zasu fita a cikin ta shi ne,”
Tur6une fuska tayi, ba halin tace zata sa ce tayar motar uzair,
Suna Cikin tattaunawar nan, Suka jiyo hon É—in motar su, Da gudu Angel ta zabura Zata sauko daga saman gadon, Aneelerh ta ruÆ™o hannunta”ki bari su Æ™araso Ciki mana”
Komawa tayi ta zauna jikinta har wani rawa yake yi duk ta ƙagara taga daddynta,
Baba maigadi na buɗe masu ƙopar, A tsiyace suka shigo da motar bayan sunyi parking ɗinta Taj ya kashe motar,
Uzair ya kalli shi ganin yadda zufa keta tsatstsafo mashi ya haÉ—a uban gumi”banaso su gane wani abu ya faru pls, Ka daidaita natsuwar ka”
Kallon shi taj ya yi “natsuwa fa ka ce?tayaya kenan? akan idona fa mutane suka rikiÉ—a suka canza halittarsu, kuma akan idona suka handame mutun da ya’yan shi, wlh ko a film naga hakan saina girgiza ballantana kuma a zahiri, ni wlh ka cuce ni, danasani tunfarko ban biye maka ba, da duk banga wannan tashin hankalin ba” ranshi duk ajagule ya yi maganar,
“Amma ae koba komai, mun Æ™aru ko?tun da kaga yanzu mun samu a bunda zamu taimaki al’umma,”uzair ne yayi maganar,
Wani kallo Taj ya jefa mashi”mu taimaki al’umma, ka yi hauka ne”?
Bai ba shi amsa ba, sai ma ya fito daga motar, ya nufi cikin gidan, Jiki a sanyaye taj ya fito daga motar yabi bayan Uzair suka nufi cikin palourn,
Kusan atare suka haÉ—a baki wurin yin sallama, jin muryoyin su yasa Angel da aneeleeh suka fito daga É—akin, da gudu angel taje ta faÉ—a ma daddynta,
“Nayi fushi sai yanzu zaka dawo,duk ka tayar mun da hankali, ko bacci na kasa yi”
Zuƙunnawa yayi saman gwiwowin sa, yadda tsawon shi zaizo dai dai da nata,
Sosai yayi hugginta É—inta”Am sorry angel, Nasan nayi laifi, ayi mun afwa,”aÉ—an shagwa6e tace”shikenan amma kada ka Æ™ara,” amsa mata ya yi da toh batare daya rabata da jikin shi ba, sam baiso ta gane halin da yake ciki, hawaye ne cike tab da idanuwan shi, tamkar ya rushe da kuka haka yake ji bakomai yafi tsaya ma shi a raiba fa ce yacce waÉ—annan Mutannan marasa imani suka fatattaki malamin nan da kuma Æ´a’Æ´an shi, Yanzu shikenan sun kashe su, Babu su a doran duniya, tabbas waÉ—annan mutanan sun san me suka taka,
Aneelerh da uzair tuni sun shige É—aki,
“Sannu da dawowa” batare da ya kalle ta ba, ya nufi toilet zai shiga,
“Wai meke faruwa ne? Nayi maka magana baka amsa min ba,”
Juyo wa ya É—anyi Yana kallonta a lokacin ya ruÆ™e handle É—in Æ™opar toilet zai shiga, “To matar É—an jarida, ba za ki bari na samu natsuwa ba” cikin zolaya ya yi mata maganar,
Murmu shi taÉ—an saki, shima ya mayar mata da martanin murmushin kafin ya shige cikin toilet É—in.
Tunawa da taj yasa Aneelerh miƙe wa Ta fito falon, Bata same su a nan ba hakan na nufin ya ɗauki angel sun tafi gida.
Ta so ace tayi ma shi sannu dawowa, ga shi kuma Ya tafi, Ta wani 6angaren kuma ji take kamar wani abu Ya faru ba daidai ba, Tun daga kan yanayin Uzair, da kuma shi taj É—in.
Hakanan taji hankalin ta bai kwanta dasu ba, sam babu natsuwa a tattare da su, Juyawa ta yi zuwa cikin É—akin a lokacin uzair Ya fito daga toilet É—in, da alama Ruwa yaÉ—an watsa ma jikin shi, short ne kawai ya bari ajikin shi,
“Sannu da fitowa” ta faÉ—i tana kallon shi,
“Yawwa madam,”
“Bari na kawo maka dinner É—in ka, nasan ka kwaso yunwa,”
Da sauri ya dakatar da ita “No bana jin yunwa, bacci nake ji” yakai Æ™arshen maganar tare da nufar Cikin É—akin wurin Closet É—in shi, Ya buÉ—e cikin jerin jallabiyoyinshi ya É—auko É—aya Ya zurata ajikin shi,
Juyawa yai Still aneelerh tana a tsaye tana kallon shi, Ta gefenta yabi ya wuce ya kwanta,
“Nayi tunanin zaka yi missing É—ina,” tayi maganar tare da takawa Ta koma gefen gadon,
“Kodai wani abu ya faru ne? naga duk ka sauyamun, Shima taj ko sallama banyi ma shi ba, Ya É—auki angel sun tafi gida”
Ganin zata takura mashi da surutu ne yasa shi yin saurin janyota jikin shi, wata irin runguma yayi mata, sai ga shi tayi tsit bata ƙara cewa uffan ba,
Taj kuwa bayan Sun koma gidan, Upstairs Ya wuce da angel, Yakaita bedroom É—inta, Yasan aneelerh bazata barta da yunwa ba,
Dawowa down Yayi a hanzar ce ya shiga bedroom É—in shi Ya faÉ—a toilet, shaf shaf yayi wanka ya fito, wuri ya samu saman kujerar gaban mirror ya xauna, wasu zafafan hawaye ne su ka soma yin zarya akan fuskar shi, Uban tagumi ya zabga tamkar marayan da ba shi da ma fadi aduniya,
“Daddy”muryar angel ce ta katse shi, ta cikin madubin yake hangenta, tana a tsaye bakin Æ™opar,
Da sauri ya share hawayen dake a kan fuskashi cikin sanyin murya yace”Ba ki yi bacci ba?
Ƙarasa shiga cikin É—akin tayi”daddyna ba ka da lafiya ne?
“Lafiyata Æ™alou me kika gani ne”?yayi tambayar tare da É—an juyawa yana kallon ta, a lokacin ta Æ™araso in da yake zaune,
“Ni dai inaji araina, baka da lafiya,”
daÆ™yar ya Æ™aÆ™aro murmushi yace “Waya faÉ—a maki bani da lafiya?
“Naji a jikina” ta yi maganar tana Æ™are mashi kallo,
“Bana hana ki yawo da daddare ba kallabi ba”? da biyu ya yi mata maganar don ya mantar da ita wancen zancen,
“Mantawa nayi,”
Nuna mata hanyar fita yayi da hannun shi”Oya go back to ur room ki É—aure kanki da kallabi, before ki kwanta”
MaÆ™e mashi kafaÉ—a tayi”Ni dai zan kwana anan, muyi bacci a tare”
ÆŠaure mata fuska ya yi”Za ki wuce ko sai nayi ball dake” a faÉ—a ce ya yi mata maganar,nan da nan yanayin fuskarta ya canza, Æ™walla ta ciko tab a cikin idanuwanta, cikin shessheÆ™ar kuka tace
“Dan Allah daddy ka bari in kwana anan yau kawai” ta Æ™arasa maganar tana matsar Æ™walla,
GyaÉ—a kai yayi”Shikenan Ki fita waje Ki jirani zan kira ki” juyawa tayi da sauri ta koma daga waje, ta jingina bayanta jikin wall,
Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya nufi wardrobe ya ɗauko kayan baccin shi, ya soma sanya su a jikin shi,
“Daddy in shigo” jin muryarta ya sa shi yin murmushi tare da cewa”ban kammala ba”
Sai daya ƙarasa zura kayan a jikin shi, tukunna Ya kira Sunanta Angel, Shigo wa tayi cikin ɗakin A kwance ta same shi saman gado, Ƙarasawa tayi ta haye saman gadon, Can kusa da shi ta kwanta,
Addu’a ya shiga jerowa yana tofa masu, Kafin Ya janyo ta jikin shi, a daren ranar da Æ™yar ya samu bacci Ya É—auke shi,
****Boss Bature****
A washe garin Ranar, Angel ta farka bata same shi a saman gadon su ba, Tunda ya tafi sallar a suba bai dawowa ba.
Ita kaɗai acikin gidan, Ga yunwa tana ji, fito wa ta yi daga bedroom ta sauko down kaitsaye ta nufi cikin falo, Fridge ta buɗe ta ɗauko Fura a cikin roba, Ta koma saman sofa Tana sha, duk in taji kamar motsin mutun saita kalli ƙopar taga idan shi ne Ya shigo,
Wuraren ƙarfe tara na safe Ya shigo Cikin falon, A kwance ya sameta, Tana ta bacci, ga robar furar data sha a jiye saman table,
Ƙarasawa yayi a gabanta ya zuƙunna tare dakai hannu yana shafa gefen fuskarta, Yasan tayi neman shi har ta gaji, Shi kan shi baisan ya akai bacci ya ɗauke shi a masallaci ba, Kodan jiya bai samu isasshen bacci ba ne,
Kasa janye eye ɗinshi ya yi daga kan fuskarta, hakanan ya dinga jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sallamar uzair ce ta katse mashi kallon nata da ya ke yi, Miƙewa taj ya yi tare da juyawa Yana kallon shi,
Gaisawa suka fara yi, kafin suka rungume juna kamar yadda suka saba,
“Inason magana dakai” acewar uzair,”
Nuna mashi wuri yayi saman sofa”bismillah”
Zama Yayi saman 2 seater, taj kuma ya zauna a saman 1 seater, kallon kallo su kayi ma junansu na tsawon mintuna biyar batare da wani daga cikin su yace ƙala ba, Sai da taj ya gaji da zaman tukunna yace
“Ina sauraronka”?
A tsanake uzair ya soma magana”game da waÉ—annan mutanan da muka gani jiya”
“Suwa kenan”? yadda yayi tambayar tamkar baisan komai ba,
“Ina nufin waÉ—annan Miyagun da suka Kashe malamin nan da Æ´a’Æ´an shi,
Wani irin kallo Taj ya yi ma shi”Wai dama ba mafarki bane”?
Harara uzair ya É—an jefa ma shi”take it serious pls, Banason wasa so nake muyi magana a kansu,’
Girgiza kai taj yayi”badani ba wlh, Na riga da nabar komai a matsayin mafarki, Bana so kasa ke tunamun a bunda ya faru jiya,”
“Kana nufin xamu Æ™yalesu ne suna aikata 6arna acikin Æ™asarmu”?acewar uzair ,A harzuÆ™e taj yace”Æ™warai kuwa, tunda bamu da yadda zamu yi da su, sunfi Æ™arfin mu, mubar su da Allah shi kaÉ—ai ne zai yi mana maganin su,
Uzair yace”Ba haka na sanka ba taj, Nayi tunanin zamu haÉ—a hannu a matsayin mu na Æ´an jarida wurin ganin mun fallasa su, don a É—auki mataki a kansu,”
Taj yace”Allah ya taimaka, Amma ni dai babu hannuna a ciki, kaima kuma ina gargaÉ—in ka akan ka manta da su, tamkar baka ta6a sanin su ba, In ba haka ba zaka jefa kanka cikin matsala ne , domin kuwa waÉ—annan mutanan da kake gani ShaiÉ—anu ne, sunfi Æ™arfin hukuma ita kanta ballantana kuma mu da muke Æ´an jarida”
Abu kamar wasa, suka soma gaya ma juna magana, Shi uzair yasa kafiya a kan saiya bi Æ™waƙƙwafinsu don ya tona masu asiri, Shi kuma taj yana Æ™oÆ™arin fahimtar da shi irin haÉ—arin da zasu jefa kan su, a Æ™arshe dai Uzair Ya miÆ™e rai a6ace yace”idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na É—an jarida ne, domin ban cancance shi ba” yana kai Æ™arshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaÆ™e yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi,
Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun É—azu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba,
“Daddy faÉ—a kuke da Daddy uzair?” a É—an ruÉ—e Ya kalleta, da sauri yace”a’a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faÉ—a mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare”
Murmushi tasa ki”Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama”
“Me zaki Ci in kawo maki”?
“Komai zaka ci nima zanci” miÆ™ewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita.
Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din
tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waÉ—annan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaÉ—ai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya
Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, “Daddy!”
Firgigit ya yi tare da kallon ta, “Na’am!”
Fuskarta da alamun damuwa ta ce, “Tun É—azu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa.”
Girgiza mata kai ya yi, “Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al’ajabi, rashin tsoron Allah ya yi Æ™aranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi.”
Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa.
HaÉ—a ido sukayi da ita, lokaci É—aya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace”Daddy, Meya faru”?
ƘaÆ™aro murmu shi ya yi”halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi”
Murmushi tasa ki”Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best’ ya amsa mata da ameen,
*ANEELER*
A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi.
Gyaran murya ta É—anyi ma shi, Ya É—ago suka haÉ—a ido tace”My man, kaÆ™i faÉ—amun abunda ke damunka, tun É—azu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls”?
DaÆ™yar ya iya bude baki yace”don’t worry ur self am ok, just bana jin daÉ—in zuciyata ne,”
“daka daure ka faÉ—amun may be in sama mana solution”
Murmu shi ya É—ansaki cikin zolaya yace”Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauÆ™i”
Ta6e baki ta É—anyi tare da mayar mashi da martanin murmushin “kana nufin matsalar data shafi asibiti kaÉ—ai zan iya magani”?
Girgiza kai yayi”karfa ki dauka da zafi, It was a joke”
Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes É—inta akan abincin dake gabanta,
Wuraren ƙarfe shida na marece, taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta,
ƘwanÆ™wasa Æ™opar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya É—an buÉ—e i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar É—akin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miÆ™ewa zaune taj yayi yana kallonshi yace”Shigo ciki mana”
Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba,
“Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka”
harara ya dan jefa mashi tare da cewa”Kaine damuwata Taj, saboda kaÆ™i bani haÉ—in kai akan abunda nakeson Cimmawa”
Murmushin takaici taj yayi”cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naÆ™i goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leÆ™en asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them,”
Jinjina kai Uzair yayi”Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba”?
“Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu’ar Allah ya kawo mana Æ™arshen su, that’s the only solution”
Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata
“Ka manta alÆ™awarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki’? shiru taj ya yi yana kallon bayansa,
Cigaba da magana uzair yayi” duk runtsi duk wuya zamu Æ™arfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki Æ™asar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina,”
MiÆ™ewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana”Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da Æ´a’Æ´ansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada Æ´a, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai Æ™arshen maganar shi uzair yace”In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haÉ—in kai kawai”
Duk yadda Taj yaso ya fahimtar dashi amma YaÆ™i ya gane, ba don yaso ba, Ya amince mashi akan suyi Bincike akansu, don su samu hujjojin da zasu fallasa su, har hukuma ta É—auki mataki a kansu, Tun daga wannan Lokacin Suka soma tunanin ta ina zasu fara neman su, A Æ™arshe Uzair ne ya ba shi shawarar su koma inda suka fara ganinsu acikin dajin nan, Cikin sa’a ranar da suka je again suka sake ganin miyagun mutanan nan sun kamo wani mutumin, kamar yadda suka kamo malamin nan, da alama LeÆ™en asiri shima Yayi masu, Akan idonsu suka koneshi, ranar Taj hankalin shi ya tashi matuÆ™a har yace ma Uzair shidai zai Cire hannun shi, kusan faÉ—a sukayi da uzair akan hakan, daÆ™yar suka sasanta kansu, kuma suka Cigaba da bibiyan Alhazawan nan, Sai dai duk wannan tsawon lokacin da suka É—auka suna Bibiyarsu Allah bai basu damar sanin kosu wanene su ba, daidai da fuskokin su ba su sani ba, Abu É—aya kawai suka sani inda suke yankewa mutum hukunci wato Cikin dajin nan a bakin Æ™orama, Abunda su taj basu sani ba, duk wani motsinsu akan idanuwansu suke yin shi, Sunsan komai game da bibiyar su da su ke yi zuba masu ido kawai su kayi, yayin da su basu san da hakan ba, Lalube kawai su ke yi acikin duhu…………
Ganin babu Riba a bindiddingin su da sukeyi ne yasa Taj ya cire hannun shi, uzair kuma yasa naci Akan binciken shi, duk yadda taj ya gargaÉ—eshi amma Ya sanya kafiya, ashe ajaline ke kiran shi.
*************************
A daren Ranar Alhamis ne Wannan mummunan ƙaddarar ta riskesu wadda tayi silar rasa rayukan su,
Wuraren ƙarfe 9 na dare, Taj na zaune tsakiyar gadon shi, ya tasa laptop ɗinshi agaba yana ta ƴan danne danne acikin, har ma ya yi shirin kwanciya singlet ce ajikin shi tare da short, wani aiki ne ya tsayar da shi, Allah Allah ya ke yi ya gama aikin ya je ya kwanta, sai hamma yake yi, ba zato ba tsammani yajiyo bugun ƙopar falo,
Agogo ya kalle, Cike da mamaki Ya sauko daga saman Gadon ya fito É—akin ya nufi cikin falon, a baÆ™in Æ™opar É—akin ya tsaya tare da tambayar wanene? Daga waje yajiyo muryar aneeleerh,ka bude mun kopa nice” muryarta Cikin shessheÆ™ar yaji sautinta, jiki na rawa ya buÉ—e mata Æ™opar har saida gaban shi ya faÉ—i ganin Yadda fuskar ta tayi jawur saboda kukan da ta sha, kayan Bacci ne ajikinta riga da wando sai mayafin data yafa akanta, gefen goshinta kwantaccen gashin kanta,
AruÉ—e yace”Aneelerh? Lafiya? me meya faru ne? Ya akai naganki acikin daren nan’?
Daƙyar take iya kallonshi, da runannun idanuwanta wadanda suka yi jawur da su,
“Uzair ya fita bansan inda yaje ba Cikin daren nan, na farka bangan shi ba, hankalina bai kwanta ba, na je wurin baba mai gadi don in tambaye shi ko sun yi magana da uzair kafin fitar shi, yace mun eh sunyi magana da shi kafin ya fita amma bai faÉ—a ma shi inda zaije ba,……” tunda ta soma magana hankalin taj ya É—ungunzuma, jikin shi ya soma kakarwa, fargabar shi kada ace uzair ya tafi Wurin mutanan nan, dama yace mashi bazai fasa bindiddiginsu ba, idan kuwa hakane to kuwa tabbas yaje yi masu leÆ™en asiri ne,
Jin yayi shiru bai ce mata komai ba yasa tace”ko kasan inda ya tafi ne”? girgiza mata kai yayi alamar a’a, saboda bai son ya tayar mata da hankalinta,
“Kin kira layin shi”? ya yi tambayar yana kallonta,
“Na kira shi har bansan adadi ba, Amma bai É—aga ba, kuma kiran yana shiga”jinjina kai yayi” Bari na jaraba kiranshi, ki shigo Ciki ki zauna” yakai Æ™arshen maganar yana nuna mata sofa,
Cikin sanyin murya tace”bazan Iya zama ba,” tausayinta duk ya kamashi, bedroom dinshi ya koma a hanzarce Ya kai hannu ya É—auki wayar shi dake a jiye gefen laptop É—in shi, Ya shiga call logs, ya danna ma uzair kira, tana fara ringing, uzair yayi picking call É—in,
Rufe shi da faÉ—a yayi ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba,
“Duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu, kasa baiwar Allah sai kuka take yi, Saboda rashin hankali, Ka kama hanya Æ™arfe tara na dare ka tafi ka barta batare da ka sanar da ita inda kaje ba, Anya kuwa kasan me ka ke yi? wai shin ina kaje ne ma…….? duk wannan suratan da taj ke yi uzair baice mashi uffan ba, A Æ™arshe ma saiya yan ke kiran gaba É—aya, jikin taj ba Æ™aramin sanyi ba, tunani ya shiga yi wai shin dawa ma yake waya? idan uzair ne meyasa bai yi ma shi magana ba? kuma ya É—aga kiran Anya kuwa ba’a samu matsala ba, sake kiran Layin ya yi a switched off ya samu wayar, Nan fa jikin shi ya mutu, hankalinshi Ya tashi
Saman bedside drawer Ya É—aura wayar, ya fito daga É—akin ya koma falon, Cike da zullumin amsar da zai ba aneelerh,
Lokacin da ya shigo falon ya ƙaraso inda take tsaye, sai ya shiga Yin ƴan kame kame,
“Bai É—aga kiran ba ko” ta yi tambayar a Æ™agare,
Muryarshi na inda inda yace”Am..um..kingane..eh..muyi waya dashi, ki kwantar da hankalin ki, Yana kan hanyar dawowa gida, yanzu ki koma ki kwanta, kada ki takura kan ki,”
Wani irin kallo yaga tana yi ma shi kallon ban yadda dakai ba, da sauri yace”kiyi hakuri ki koma gida, nan badajimawa ba zai dawo”
Jiki asanyaye Ta juya ta fuce daga falon, Ko bayan tafiyarta saida ya kuma kiranta awaya, Ya ƙara kwantar mata da hankalinta,
Kasa zama ya yi, zarya ya shiga yi tsakanin É—akin shi zuwa palour, ya rasa meke yi ma shi daÉ—i duniyar nan, duk bayan Æ´an mintuna sai ya jaraba kiran Layin Uzair don yaji in ya bude wayar amma a kashe yake samun ta,
Bawan Allah ya rasa ta zama, duk ya shiga damuwar rashin amininsa, juyawa ya yi da sauri Ya haye upstairs É—akin angel, ya tura Æ™opar É—akin a hankali, ko’ina duhu, ya lalauba jikin bangon ya kunna switch, tare dakai idanuwanshi kanta, Sai bacci take yi, ta Æ™udundune Cikin bargo, murmushi ya É—an saki kafin ya É—auke i danuwan shi daga kanta, ya mayar dasu kan wall É—in dakinta, Zanunnukan da tayi ne tare da kalaman da ta rubuta ma shi, a kullum ya kallesu sai yaji farin Ciki acikin zuciyar shi, duk mun baÆ™in Cikin da yake ciki,
A hankali Yake tafiya cikin É—akin nata, ta 6angaren hagu ya zagaya saitin inda take kwance saman gadon, Kneel down Yayi tare dakai hannu Ya yaye blanket É—in data rufa da shi, rigar bacci ce ajikinta,
Kyakkyawar fuskarta Ya Æ™urawa ido yana kallonta, Hakanan ya dinga jin bugun zuciyar shi na Æ™aruwa, wani irin matsanancin faduwar gaba, a cikin zuciyarshi ya shiga ambaton Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” ya ambaci hakan ba iyaka,
“Daddy” muryar ta ce ta katse shi, kallonta yayi ganin ta buÉ—e manyan idanuwanta a kan fuskar shi,
“Dama bakiyi bacci ba”? murmushi ta sakar mashi tare cewa”Nayi mana, yanzu na farka” hands É—inshi ya sanya ya tallabo fuskarta”Æ´ar kyakkyawata, Allah yabar mun ke,”
“Ameen daddy, gobe uncle da aunty zasu dawo ko sai mu tafi buzaye ? tayi tambayar tana Æ™oÆ™arin mikewa zaune,
Girgiza mata kai yayi”Till next week nake tsammani”
Ta6e baki ta É—anyi”daddy ka kwana É—akina yau”yatsina fuska yayi”Gadonki yayi mun Æ™anÆ™anta” cikin zolaya ya yi mata maganar,
Turo mashi baki tayi”To muje É—akin ka mu kwana” maÆ™e mata kafaÉ—a yayi”A’a, kowa ya kwana a É—akinsa,” shagwa6a ta soma yi mashi, sosai ta ba shi dariya, suna Cikin Yin fira, Ya tuna da uzair, Rass yaji gaban shi Ya faÉ—i, Da sauri ya kali agogo, Ƙarge goma da rabi mayar da idanuwanshi kan angel yayi” ki koma ki kwanta, Sai da safe” yana Æ™oÆ™arin mikewa tayi saurin ruÆ™o hannunshi da sauri kallonta ya yi idanuwanshi sun taunta sosai, Æ™aÆ™aro murmushi ya yi don ya gane me take nufi, Kiss ya mannata mata a saman forehead É—inta, Yasa hannu ya kwantar da ita tare da lullu6e mata jikinta da bargo, addu’a ya yi mata, kafin ya kashe hasken É—akin,
Lokacin daya fuce daga É—akin yana jiyo sautin muryata tana faÉ—in”I love u so much daddy, Allah yabar mun kai, ina matuÆ™ar Æ™aunar ka habibi” murmushi yasaki A hanzarce Ya sauko down stairs, ya faÉ—a É—akin shi, daga gefen gadon shi Ya zauna tare da É—aukar wayar shi, ya ci gaba da jaraba layin Uzair, still a kashe yake samun ta, Zuciyar shi tajima da karaya, A sukwane ya É—aura wayar saman bedside drawer, a wannan yanayin ne Bacci ya yi awon gaba da shi, sama sama yake yin baccin na shi, 🥺🥺🥺
Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah,
Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer É—in ya É—auki wayar,
Lokacin daya kalli screen É—in wayar Sunan Aminina ne Ya bayyana, ajiyar zuciya ya É—an sauke dama jiran kiran shi ya ke yi, A tunanin shi ya dawo gida ne, Shiyasa ya kira shi dan ya sanar ma shi game da dawowar shi, picking call É—in yayi tare da manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, “Aminina!” Kafin Ya Æ™arasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruÉ—e yake faÉ—in,”Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta Æ™are.”
A firgice ya dakatar da shi, “Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?”
“Sun kama ni ina yi musu leÆ™en asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su Æ™yale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na É—auka a wurinsu, yana a cikin memory É—ina, ita kaÉ—ai ce hujjar da asirinsu zai tonu…” Bai kai Æ™arshen maganar ba, É—if ya ji kiran ya katse.
A gigice yake kwaÉ—a masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa’a aka É—aga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuÆ™ar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, “Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka.” Jiki na rawa ya É—ago da wayar yana kallon screen É—in yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.
Saboda tsabar firgita, a ruÉ—e ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar Æ™wayar idon za ta faÉ—o kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiÉ—ime ya shiga furta, “No, no!” Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.
Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon a zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan.
Yana cikin wannan halin ha’ula’in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, “Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku.” Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face Æ´arsa É—aya tilo da ya mallaka wato Angel.
A matuÆ™ar ruÉ—e ya miÆ™e, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key É—in motarsa ya É—auko saboda tsabar ruÉ—u wardrobe ya dosa zai buÉ—e a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin Æ™ofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom É—insa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiÉ—ime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko’ina ba sai É—akin Angel, bugu É—aya ya yi ma Æ™ofar ta buÉ—e, ko’ina duhu, kunna hasken É—akin ya yi, nan take haske ya gauraye ko’ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke Æ™unshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya Æ™arasa shiga É—akin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, “Angel, Angle my daughter!Azeezaty!” Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaÉ—arsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, Sam baya a cikin hayyacin shi, balle ya iya tunawa da aneelerh dake a cikin mawuyacin halin na rashin dawowar mijin ta gida,
kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, É—aya daga cikinsu ya buÉ—e Æ™irar Range Rover, back seat ya buÉ—e ya kwantar da Angel tukunna ya buÉ—e diver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buÉ—e gate É—in, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danÆ™ara-danÆ™aran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka daga gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba Æ™aramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror É—in motar, hakan yasa shi Æ™ara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La’ila’ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheÆ™ar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.
A ruÉ—e take furta,”Daddy…What’s happening, where are u going in this darkness night?”
Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.
“Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba.” Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheÆ™ar kuka ta kuma cewa, “Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaÉ—aya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daÉ—i. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.
Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faÉ—a wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruÉ—e ya yi parking É—in motar ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya É—auko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yavyi cikin dajin da ita yayin da take sa6e avsaman kafaÉ—arshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare davya ankara ba, ya É—aura kafarsa saman wani Æ™arfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin Æ™asa, kaifinsa tamkar na wuÆ™a, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin Æ™afar ya 6ulo ta sama, wani irin raÉ—aÉ—in azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke Æ™afarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, “Innalallahi wa’inna ilaihir raji’un.” Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, “Dad let’s go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?” Ta yi tambayar still tana shassheÆ™ar kuka.
Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, “Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne.” Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, “Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji.” Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,
A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.
Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.
Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faÉ—i a mace.
A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.
Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.
Guntun tsaki É—aya daga cikinsu ya ja, “Mala’ika ya riga mu É—aukar ransa, ba haka na so ba.”
Na gefensa ya ce, “Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir.”
Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka É—aure fuskokinsu. ÆŠaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan É—aya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, “MiÆ™o mini galon É—in fetur tare da lighter.” A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.
“Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abuvne mai sauÆ™i.” Bai kai Æ™arshen maganar ba, aka miÆ™o masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur É—in a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.
Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus.
*To Jama’a Zaku ga nasanya Farkon labarin nayi hakan ne don in tariyo maku daga inda zamu tashi fatan an waye ni*
*waɗan da su ka shirya yin payment zasu iya farawa, 08103884440 cikin wata mai zuwa free pages book one zai ƙare, Ina yi ma kowa fatan alkhairi, sai mun haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya*
*💋Boss Bature✍️💋**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
_daga alÆ™alamin Boss Bature✍️_
*Dedicated To Aunty Kubra❤*
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 7"