Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kurkukun Kaddara 65

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

Dedicated to Aunty kubra💘🌹

*Gargarɗi!!!*


_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E65 free pages

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

 

Saboda tsabar yadda jinin ke fita hatta Mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi idon nashi ya jiƙe sharkaf da jininsa, Lamarin ya yi matuƙar gigitasu, Sautin muryarta har ya fara disashe wa saboda tsabar kukan da tasha, Gabriel da ke a zuƙunne ƙasa gabanshi sai yarfa hannayen shi ya ke yi, Yarasa uwar ubanshi zuciyarshi sai bugawa ta ke da ƙarfi da ƙarfi duk ya firgice tsoranshi kada Danish ya rasa ranshi silar naushin da yai mashi.

Jikinta ba ƙaramin zafi yai ba, har time ɗin hannayenta biyu na ƙanƙame da kanshi a ƙirjinta, Jikin shi ya saki sosai shi kaɗai yasan zogin azabar da ya ke ji a cikin idon shi. Sama sama numfashin sa ke fita, maƙoshin shi ya bushe, ta ko’ina babu sauƙi a jikin shi, addu’oi ta dinga karantowa tana tottofa mashi samar sumar kanshi,

Cikin fitar hayyaci ya ke yamutsa vest ɗin jikinta da hannayenshi masu dogayen akaifu, duk ya faffasa mata fatar bayanta, amma ko kaɗan bata ji zafi ba, batasan ma yana yi ba, damuwarta gaba ɗaya akanshi ne, Da ace tana da halin da zata iya ɗauke mashi ciwon ta maida shi akanta da tuni ta yi hakan, Zaifi mata sauƙi akan taga Danish acikin mawuyacin hali.

la66anta na rawa ta soma ambaton sunan shi tana faɗin dan Allah Danish kada ka mutu kabarni, kada ka daina motsi, ni ko idona ne ma zan iya badawa asanya ma ka, Ya Allah ka kawo mishi ɗauki, Wannan wata irin baƙar rana ce, Sosai take kuka, idanuwanta sun yi jaga jaga da hawaye ta rasa ya zata yi dashi ga jinin yaƙi daina bleeding, Gabriel da ya gama rikicewa Sai magiya ya ke yi ma Angel akan ta cire idon shi ɗaya ta sanya ma Danish tun da shi ne silar rasa idon nashi.

Duk da halin da ya ke ciki hakan bai hana shi ƙoƙarin motsa red lips ɗinsa da su ka jiƙe sharkaf da jinin da ke ta gangarowa ta cikin ƙarƙashin mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi ido da shi, magana ya ke so yai mata amma ya kasa, la66ansa sun ƙi bashi haɗin kai, Jikin shi gaba ɗaya ba sauƙi, Yanke shawarar fita tai don ta sanar ma sauran ƴan uwansu ƙwara kowa ya sani, don su nemi mafita atare, Tana kuka tana ƙoƙarin 6an6are shi daga jikinta sai dai yaƙi bari ta raba jikinta da nashi, idanuwanta cike tab da ƙwalla ta kalli Gabriel muryarta na kerma tace

“Ka… ruƙe shi, Zan je na faɗa ma su haris,” duk yadda gabriel yaso ya raba Angel da Danish abun ya faskara, mugun ruƙo yai mata bana wasa ba, Kallon Gabriel din tai”kaje ka yi musu magana kowa ya tashi su zo, ” hawaye ta ko’ina a fuskarshi yace”Angel Pls kada ki faɗa musu cewa ni ne silar rasa idon shi……” tun kan ya ƙarasa maganar ta rufe ido tana zazzaga mashi masifa

“Har kana da bakin da za ka ce kada na faɗa mu su? Dole su san cewa kaine silar komai, mugu kawai ai bansan haka ka ke ba da tun farko ban biye maka ba…..hada zagi ta haɗa mashi, Jiki duk ba ƙwari Gabriel ya miƙe har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi ga ciwon mai raɗaɗi da ya addabe shi, a haka ya fuce daga Cikin toilet din, bai shiga ɗakin ba a bakin ƙopar ya tsaya yana matse kwalla.

 

Fitar Gabriel ke da wuya, ta soma jin muryarshi ƙasa ƙasa yana yi mata magana, da sauri ta ɗaura kunnanta saman la66ansa don ta samu damar jin me ya ke son faɗa mata.

 

Angel ki daina zubar da hawayen ki saboda ni, lafiyata qalou, ba abunda ya sami idona…..”

Cikin muryar ku ka tace “ƙarya ka ke yi min Danish nasan ka faɗamin hakan ne don ka kwantar min da hankali na….” ku ka yaƙi bari ta ƙarasa maganar, Sassauta ruƙon da yai mata ya yi tare da ɗagowa da kanshi fuskar ta 6aci sosai da jiki, kasa tsayar da kan nashi yai, Sai dai ya kwantar da shi saman wuyanta, jikinta yai mugun sanyi, saboda ƙarfin hali irin nashi a haka ya cigaba da yi mata magana cikin raunin murya ta wanda ya gama galabaita.

_Angel, za’azo atafi dani, babu tabbacin zan dawo cikin ku, that doesn’t mean that I’ll die. Even if I’m not around, ki yi min alƙawarin ba za ki haura tagar nan ba_

cikin shessheƙar kuka tace”damuwar ka kenan Danish Ni yanzu bata wannan nake ba, lafiyarka nake so, kuma ni bazan juri rashin ka atare dani ba, wlh bazan iya zama babu batul sannan babu kai a tare dani ba…..” kwantar da kanta tai gefen wuyanshi. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka sai shesseƙar ku ke ta ke yi, muryarshi ce ta ƙara katse mata kukan nata daƙyar yake iya furta maganar

“Angel, ki tashi mu shiga ɗaki, ki ruƙe ni mu tafi, inaso inga ƴan uwana kafin atafi dani, nasan yanzu haka suna akan hanyar zuwa ɗauka na” Jin wannan maganar tashi yasa ta ɗaga murya ta ƙwala ma Gabriel kira, Jin sautin muryarta yasa shi yin saurin buɗe ƙopa ya faɗo toilet ɗin

Muryarta asanyaye tace mashi

“Ka taimaka mini mu shiga da shi ɗaki”

jiki na 6ari ya ƙarasa ciki, atare da Angel su ka ruƙo Danish, daƙyar daƙyar suke jan shi saboda jikin nashi ba ƙwari, kamar lagwanin fitila, A haka suka janyo shi har zuwa bakin ƙopar fita daga cikin sashen toilet din nasu, duk inda suka taka sai jinin shi ya ɗiɗdiga

Kamar jira ake su dira ƙafafuwansu saman floor ɗin ɗakinsu, Ba zato ba tsammani, Su ka soma Jiyo motsin buɗe ƙopa, A matuƙar gigice Gabriel da Angel suka kalli ƙofar, Wata irin zufa ce ta shiga wanke fuskokinsu, damuwa ce ƙarara akan fuskar Angel.

Wani gabjejen Giant Ne ya shigo ɗakin Yana tafiya Tsokokin Jikin shi na motsawa, zazzafan gaske Star biyu ce a gaban rigar shi, a gaggauce yake taka staircases ɗin benan tsabar sauri kamar zai tashi sama, Da zafin shi Yake taka ƙafafuwan shi.

batasan lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, don tasan zuwa akai araba ta da Danish dinta, Sautin kukan Angel ne ya farkar dasu Haris, Hakalinsu a matuƙar tashe suka soma buɗe idanuwansu kusan atare Kowannansu ya yaye bargon da ya lullu6a da shi, sai dai kafin su yi yunƙurin saukowa daga saman gadonsu, Tuni wannan giant ɗin Ya jima da ƙarasowa ciki, tsabar tsoratar da Gabriel yai ne yasa shin Yin saurin sakin Danish yabar Angel da ruƙon shi, kamar amafarki su haris suke kallon Danish da Jini ya wanke ma fuska, ruɗu ya hana su gane wanene.

Yayin da wasu daga cikin su ke kallon Giant ɗin da ke tafiya yana tunkarar su Angel, Lamarin yai matuƙar ɗaure musu kai, Sun gaza yarda da abunda idanuwansu ke nuna masu, Tana ji tana gani, Giant ɗin nan ya sanya hannu biyu Duk irin tsayin Danish Kamar jinjiri Haka giant ɗin ya ɗauke shi tare da ɗaura shi saman kafadar shi, Cikin Zafin nama Ya juya dashi, Ya nufi Benan, Da gudun gaske Angel tabi bayan shi, tana kuka tamkar ranta zai fita tana ambaton sunan Danish, Adai dai bakin stair ɗin tai tuntu6e wurin taka staircases ɗin Gaba ɗaya ta kife kanta Ya daki ƙasa, ko motsi bata yi ba. Ga dukkan alamu ta sume ne, sai bayan da Giant ɗin Ya fuce daga Cikin ɗakin, Ƙopar na rufewa ta bada wanj irin sauti Garam!!

Shi ne silar dawowar su Cikin hayyacin su, Azeeza ta fashe da wani irin matsanancin kuka tun kafin ma taji meya faru, sautin rufe ƙopar ɗakin su ne yasa ta fahimci cewa Giants ne suka tafi da wani, shiyasa ta fashe da kuka, Jikin Haris har 6ari yake yi wurin saukowa daga saman gadon shi yana bin Fuskar Gabriel da kallo wanda Ya ƙame jikin bango tsabar tashin hankali ne akan fuskar shi, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya sauko daga saman gadon shi, Tun kafin ma su soma tambayar Gabriel a ruɗe yake girgiza musu kai hawaye nabin fuskarsa,

Muryar haris aruɗe ya furta”wanene aka fita dashi? Meya faru ne naga jini a jikin ka? Meyasa Angel ta ke kuka tana ambaton sunan Danish? Allah yasa mafarki nake yi ba gaske ba, zaifi min kwanciyar hankali na, akan ace wani abu ne ya faru da shi”!

tsabar ruɗanin da Gabriel ya shiga ne yasa shi Yin su6ul da baka wurin furta”Bada son raina na aikata mishi hakan ba, bansani ba, Ku ƙyale ni ku rabu dani inji da abunda ke damuna! ‘ zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa kamar ƙaramin yaro haka ya fashe da wani sabon kukan.

“Hakan na nufin wani abu ya samu Danish! Kada ka ce min Jinin shi ne wannan a jikin ka,” haris ne yai maganar tare da sanya hannu biyu ya damƙi gaban rigar Gabriel ya ɗaɗɗago dashi Ya buga shi jikin bango, Idanuwanshi tuni sun rikiɗa sunyi jawur dasu

“ka faɗa min Me ka aikatawa Danish? Jinin wanene a jikin rigarka!

Yana magana tsokokin fuskarsa na motsawa, Kasa buɗe baki Gabriel yai duk yabi ya firgice,

Hankalin su Deeja ya tashi sosai, Har sun fara sharar ƙwalla Saboda sunji a jikin su wani abu ne ya faru da Danish ɗinsu, Da gudu Su hanna su ka nufi Angel da ke baje saman matakalar bene A saman laps ɗinsu suka kwanto da ita, Sai ku ka su ke yi suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta akan ta tashi ta faɗa musu meya faru da su.

Kukan azeeza yafi na kowa sauti, Ta cika ɗakin nasu, Takaici biyu ga rashin ido, Ga takaicin halin da take tunanin waninsu ya shiga, Na tashin hankali, Abun ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, tana matuƙar jin zafin makantar daren da take fama da ita.

Takaicin duniya ya ishe su, kamar su yi hauka, Gabriel ya ƙi buɗe ba ki ya basu amsar tambayoyinsu, kuma shi kaɗai ne zai iya faɗa musu abunda ya faru.

Ga Angel taƙi farkawa, Har ruwa suka yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Babu wanda ya iya runtsawa acikin su, Zuciyoyinsu sun karaya sosai musamman Haris da ya gane cewa An tafi da Danish din shi Cikin mawuyacin hali, tuni zazza6i ya kama shi mai zafin gaske, Ciwon kai mai raɗaɗi ya kama Azeeza da ke ta ku ka, Babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, Bacci ya ƙaura ce wa idanuwansu, An rasa wanda zai lallashi wani acikin su, matan gaba ɗayan su asaman benan Suka kwana kewaye da Angel har ruwa suka ƙara yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Sun yi kuka har sun gaji sun gode ma Allah, Mazan cikin su A zuƙunne suka kwana, Yadda su ka rana haka su ka dare.

Kafin safiya ta yi kowannan su ya fita hayyacin sa, babu mai iya motsa la66ansa yai magana acikinsu, zazza6i duk ya lullu6e su, Don shi Gabriel ma suman zaune yai, bawan Allah duk ya damu kan shi, ga matsanancin ciwon kai da ya ke fama dashi.

A cikin su mutun ɗayane hankalin shi ya ke akwance, majnun dake ta sharar baccinsa, ko daren jiya da Angel ta ke ta kuka za’a tafi da Danish bai farka ba, hatta jamima da ta kasance autar cikin su saida ta tashi daga bacci hada ita cikin waɗanda suka kwana zaune saman benan ɗakin su.

Tsawon lokacin babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalma, Jamima ce tai ƙoƙarin cewa”Bari naje na ɗebo ruwa a ƙara yayyafa mata asaman fuskarta” ba wanda ya kalle ta, miƙewa tai da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu, tun da ta shiga hankalinta yai matuƙar tashi ganin jinin Danish daya ɗiɗɗiga a saman floor ɗin ya bushe ƙamas, ɗago wa tai da sauri tana kallon Jikin ƙopar toilets ɗin da suke a jere guda uku, kafin ta tsayar da idonta akan ƙopar toilet ɗin da A kayi badaƙalar nan jiya, Jikin ta na kerma ta ƙarasa tare da turo ƙopar shi ta faɗa ciki, gabanta yai wani irin mugun bugu ganin uban jinin da Danish ya zubar a inda ya faɗi jiya yana birgima, a gigice Jamimah ta fasa ƙara wadda ta yi silar janyo hankalin su haris, da gudu suka shigo cikin toilet ɗin kaitsaye idanuwansu su ka sauka akan uban jinin, Lamarin yai matuƙar girgiza su, jinin duk ya daskare acikin toilet ɗin,

Zuciyarsu ta dinga azalzalarsu tana tunzura su akan cewa Gabriel ne yai mishi wani abu, shiyasa yaƙi faɗa musu, Ransu yai matuƙar 6aci don gani suke kamar ma kashe musu ɗan uwa yai, Hakan yasa suka koma ɗakin mazan dukansu, Suka tarar ma Gabriel sai da suka fara Farfaɗo dashi ya dawo cikin hayyacin shi, Su ka tasa shi gaba akan ya faɗa musu gaskiyar abunda ya faru idan har yana son zaman lafiya, a lokacin yaso ya sanar dasu sai dai yakasa motsa bakinsa, saboda halin da ya ke aciki, zuciyace ta fusge su, Su ka yi mashi jahilin bugu har sai da su ka ga ya suma, Tukunna suka ƙyale shi,

Babu wanda yabi ta kanshi, Kwance suka barshi ƙasa, la66ansa duk sun fashe, ƴan matan sai kuka su ke yi ba ƙaƙƙautawa, An rasa me lallashin wani acikin su, Haris ne ya je wurin da su ke zazzaune bakin benan, ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki Angel ya nufi tsakiyar ɗakin su da ita, Miƙewa su kai gaba ɗayan su suka bi haris, wanda ke ƙoƙarin kwantar da Angel saman floor,

Yace da azeeza ta ƙara ɗebo mishi ruwa ya watsa mata, ta amsa mashi da toh, Da gudu azeeza ta nufi sashen shiga toilet ɗinsu, shigarta ke da wuya, su ka soma jin motsin buɗe ƙopa, Saboda halin da su ke aciki babu wanda Ya kai idonshi ga ƙopar, Giants ne da ke kawo musu abinci, A jere su ka shigo hannayen su ruƙe da kayan abincin su, Ko ajikin su jin kukan da su Hanna ke ta yi, wuce wa su ka yi zuwa saman dining carpet dinsu, bayan sun ajiye kayan abincin basu tsaya jiran su taso su ci ba, a tare suka fice daga cikin ɗakin, Babu wanda ya kalli kayan abincin, hatta parveen damuwa ta hana taje taci abinci.

Badajimawa ba Azeeza ta shigo hannunta ruƙe da bokiti, Kusan rabi ta ciko, don a watsa ma Angel ko sun samu tafarka, Hanya suka matsa mata ta sauke bucket din gefen haris.

duk da hankalin su ba a kwance ya ke ba sai da su ka dubi fuskar azeeza ganin ta kawo musu ruwa a bokiti Sai nishi ta ke yi tana haki, Hannu biyu haris ya tsoma acikin bokitin Ya ɗebo ruwan da ƙarfin gaske ya watsa Ma Angel saman fuskarta, Nan take taja dogon numfashi ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta.

Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, tunkan ta buɗe idanuwanta ta soma ƴan buge buge tana ambaton sunan Danish tana kuka tana faɗin Wlh ba za ku rabani dashi ba, Duk inda zaku kai shi saina bi ku, Wayyo Allah na Danish shikenan sun rabani da farin ciki na, Gabriel kaine silar da ya rasa idon shi ɗaya….”

Kalaman Angel sun girgiza su Har suna haɗa baki wurin furta Danish ya rasa idon shi ɗaya!?

Cikin rashin fahimtar zancenta su ke kallonta, A lokacin tafara dawowa cikin hayyacinta jin sautin muryoyinsu akanta, Wani irin matsanancin ciwon kai ta ke ji, Hannunta ɗaya dafe da goshin ta, da taimakonsu Hanna Ta miƙe zaune tana faman yin shessheƙar kuka, Idanuwanta har sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, daƙyar ta buɗe su, sunyi jawur dasu, awani irin galabaice take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya…………’

“Angel ki yi mana bayani meya faru daku ne? Meyasa aka tafi da Danish! Jinin menene Agaban rigarki? Da wuyanki’? Kamar ƴan jarida haka suka tsareta da tambayoyi.

“Dan Allah ki fidda mu daga cikin ruɗanin da mu ke, mun ga ɗazu kun fito toilet Jini duk ya wanke fuskar Danish, ba mu gasgata abunda idanuwanmu suka nuna mana ba, Kafin mu yi wani yunƙurin Giant Yazo ya tafi Dashi” Naufal ne yai magana maganar,

Cikin muryar kuka parveen ta soma magana”wlh muna acikin matsanancin tashin hankali Angel, Mun rasa gane meya faru ne! Pls ki yi mana bayani, ” Sai da ta gama sauraransu ɗaya bayan ɗaya, Muryarta a raunace ta furta sunan gabriel ba tare da ta ƙarasa maganar ba, Sai nishi take yi,

Harsuna haɗa baki wurin cewa”Me Gabriel yai masa? Shi ne Ya kashe mishi idon”? Haris yace”idan ma shine Ya ta6a shi, gashi can kwance ƙasa a sume mun yi mashi bugun tsiya”

Zafafan hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskarta, Ko ƙarnin jinin jikinta basa ji, don bashi bane agabansu, Magiya suka dinga yi mata akan ta faɗa musu abunda ya faru, Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana faman lumshe idanuwanta kafin daƙyar ta motsa la66anta.

“Bazan iya tuna komai ba, dan Allah Na roƙe ku, Ku ƙyale ni, kaina ciwo ya ke min,” Ba don sunso ba, suka rabu da ida, babu wanda ya ƙara tambayarta, duk da sun fahimci kaɗan daga cikin abunda ya faru tsakanin Gabriel da Danish, sai dai basu san menene ya jawo da har faɗa ya kaure a tsakaninsu, kwantawa ƙasa angel tayi idanuwanta na fuskantar ceilling, Jikin ta duk ba dadi, bakomai take tariyowa ba face abubuwan da faru kafin zuwa lokacin daya rasa idonshi, Bawan Allah ya dinga bibiyarta duk don kada Gabriel ya samu damar Yin magana da ita, ashe tsautsayine ke bin shi. Sosai ta fashe da ku ka.

“Angel kina ƙara jefa mu cikin damuwa, tun da ba za ki faɗa mana abunda ya faru ba, Zamu jira har zuwa lokacin da za’a dawo mana da ɗan uwan mu wlh idan har ya tabbatar mana da abunda muke hasashe to kuwa tabbas Ba zamu ƙyale Gabriel ba, dole ya fuskanci hukunci dai dai da abunda ya akaita ma Danish ɗin mu! sai ya yi danasanin zuwan shi cikin kurkukun nan!” Naufal ne yai maganar yana fitar da huci, Haris yace”Ae basai mun tsaya jiran Danish Ya dawo cikin mu ba, Idan har Angel taƙi faɗa mana gaskiyar abunda ya faru dashi, Zamu tsare Gabriel ne ta ƙarfi sai ya faɗa mana abunda ya aikata mashi, ”

“Wannan wata irin rayuwace! Muna cikin jimamin rashin ƴar uwarmu batul, ga wata masifa ta kunno kai, Ni bansan meya haɗa Gabriel da Danish ba, Shi da babu ruwanshi da shiga sabgar da bata shi ba, bana tunanin Danish ne ya fara tsokanar shi, Gabriel shine mai laifin’!! Deeja ce tai maganar fuskarta a yamutse,

“Bawan Allah Hakanan An naƙasa mishi rayuwarshi, wlh ba zamu ƙyale Gabriel ba, dama can ni bai kwanta min araina ba, don kawai yaga yana da ƙirar ƙarfi saboda tsabar mugunta yake neman lahanta mana ɗan uwanmu” Acewar Javed, kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake yi, Sai faman tada jijiyoyin wuyansu suke yi, dole ne su damu bayin Allah, Suna matuƙar ƙaunar shi, duk da irin halin ko’in kulan da ya ke nuna musu wani lokacin, hakan bai canza ƙaunar da suke yi mashi ba, ga yunwa suna ji amma damuwa tahana su fahimci hakan, don bata cikin su suke yi ba.

Babu wanda ya lura da chinonsu da ya farka daga bacci, Idon shi bai sauka akan komai ba, Sai kan kayan abincin da aka kawo mu su, Saukowa yai daga saman gadon shi, Yaje ya samu wuri saman dining carpet ɗin su ya zauna, Ya dunga kwasar abinci yana cusawa abaki Yana ci yana satar kallon su, kamar munafuki,

Parveen ce ta lura da abunda ya ke yi, aikuwa rai amatuƙar 6ace ta nufi inda ya ke, tana ƙarasawa ta ɗauki Burger ta kifa mashi ita saman fuskarshi, ta dagargaje ta tare da cunkusa mashi har cikin hancinshi tana faɗin”munafuki Kanaganin muna kukan rashin ɗan uwanmu amma kai ta abinci ka ke yi,” Tsabar mugunta sai da ta 6ata mashi fuskarshi yai ta kuka yana buge hannunta, kamar zata kashe shi, daƙyar ya samu ta ƙyale shi ta koma wurinsu Haris ta tsaya tana hangen Majnun da ke ta yin birgima a kasa.

“Azeeza ɗauki ruwan nan ki watsa ma wancan ƙaton a saman fuskarshi,” Haris ne yai maganar, Dama kamar jira take yi don ba ƙaramin damuwa tayi da Gabriel ba, Allah yayita da tausayi, Hannu biyu tasa ta kimkimi bokitin zuwa gaban gabriel, A saman fuskarshi ta yayyafe mashi ruwan, nan take yaja dogon numfashi tare da saukr ajiyar zuciya,

“Sannu Gabriel,” muryar azeeza ce tasa shi yunƙurin buɗe idanuwanshi, zuƙunnawa ta yi saman gwiwowinta agaban shi, tare da kai hannayenta saman kanshi ta ɗago da shi ta kwantar saman cinyoyinta, Ganin ya farka yasa su haris Tunkarar shi Da niyar su takurasa akan ya faɗi masu me ya yi ma Danish, Idan yaƙi faɗa musu zasu ninka mashi bugun da su ka yi mashi ne, sai dai kafin su kaiga ƙarasawa inda ya ke muryar Angel ta katse masu hanzarin su.

“Haris kada ku ce zaku buge shi, saboda ba laifin shi bane abunda ya faru, shima bada son ranshi ya akaita mashi hakan ba……..” daƙyar take magana duk don kada su bugi gabriel yasa take Ƙoƙarin faɗa masu abunda ya faru, duk da ta 6oye musu Ainihin dalilin faruwar hakan, ta dai ce musu tsautsayi ne da ƙaddara suka ja har Gabriel ya naushi idon shi, ba tare daya sani ba, sun ɗan samu sa6ani ne akanta, haris yace taya zasu yarda da maganarta? Wani irin tsautsayine wannan da har danish zai rasa idonshi ɗaya? Kawai saboda da ita zasu kama yin faɗa? Shifa bai fahinci zancen ba! Anya kuwa taga uban jinin da ya wanke toilet ɗinsu, Ga shi nan har a jikinta, Ya ƙara da cewa bazasu yarda ba, dole shima Gabriel su cire mashi idon shi ɗaya, in yaso Giant sunzo su ɗauke shi shima akaishi treatment room ɗin don ayi jinyarsu atare!! ganin dagaske haris ya ke yi Ne yasa tai saurin cewa”Danish bai rasa idonshi ba, da kanshi ya faɗa min cewa lafiyar shi ƙalau, babu abunda ya sami idon shi, kada ku yi gaggawar yanke hukunci, ku jira har zuwa time da za’a dawo da shi.

Angel taci wahala kafin ta samu ta shawo kansu, ba don sun haƙura ba, sun dai jira ne zuwa lokacin da za’a dawo musu dashi don suga idan idon nashi yana nan ko ya naƙasa. Yinin ranar babu daɗi su ka yi shi, sai wuraren marece Ne suka ɗan motsa, Da taimakon mazan suka gyara toilet ɗin daya 6aci da jini tass suka wanke shi, kamar wani abu bai ta6a faruwa ba acikinsa, Har wajen shi zuwa bakin ƙopar shiga sashen duk suka wanke, Bayan sun gama suka gyara cikin ɗakin nasu, Ko’ina ya dawo fes sai dai zuciyoyinsu a ƙuntace su ke, ƙarfin hali kawai suke yi babu wani mai lafiya a Cikinsu, sai da marece ya nutsa tukunna su ka ci abincin su, banda Angel da mazan cikin su, ko kallo abincin bai ishe su ba.

Hannah ta yi fama da Angel akan taje ta yi wanka ta wanke uniform ɗinta idan ma bazata iya ba, ita zata wanke mata uniform ɗin da kanta, Amma ta maƙe kafaɗa, gani take kamar inta wanke jinin Danish dake ajikin Uniform ɗinta shikenan bazata ƙara ganin shi, shiyasa taƙi zuwa tai wanka.

idan mu ka koma 6angaren Gabriel, Bawan Allah azeeza ce kaɗai ta damu dashi, ganinta ya ke kamar ƴar uwarsa daya rasa, saboda mutuncin da ta yi mashi, Ita ta wanke mashi tsoffin uniform ɗinshi da suka 6aci da jinin Danish, tun bayan da yayi wanka, Ya cire su ya bata, Ya maida tsoffin a jikinsa.

Saman Gado ya koma ya kwanta yanata juyi kanshi na sara mashi, Har sai da ya samu bacci ya ɗauke shi tukunna ya ji sauƙin ciwon nashi, A taƙaice Cikin kwanakin Nan Jin daɗin su Ya zama ragagge, me faranta musu rai Angel babu lafiya, Gashi taƙi zuwa ta yi wanka ta cire kayan Jikinta, Ta zama ƙazamar ƙarfi da yaji, duk akan Danish, kwana ɗaya da faruwar abun ko ruwa bai gifta ta maƙoshinta ba, ta haranta ma kanta duk wani jin daɗi ta ƙuntata sosai, A daren ranar da aka tafi dashi, gefen gadon shi ta kwana a zaune kamar gunki,

A cikin kwana na biyu ne su Deeja suka tasa ƙeyarta gaba akan taje tayi wanka idan ba haka zasu yi mata, Su kan su tsananin tausayinta su ke ji, Ba irin lallashin da basu yi mata ba, amma taki sakewa, hatta Haris daya fi kowa Kusanci da Danish Ya haƙura yabarwa Allah tun da ba yadda za su yi, babban abunda yafi damunsu shine awani hali ya ke aciki? Ya idon shi ya ke? jikin shi da sauƙi ko akasin hakan?

Daƙyar suka samu Angel ta je ta yi wanka, A cikon kwana na uku da aka tafi dashi, Hanna ce ta wanke mata uniform ɗinta, Dogon wandonta sabo da vest ɗinta, dama su ne ajikinta aranar da abun ya afku, Tsaffin kayanta ta maida ajikinta, yanzu ta daina kwana gefen gadonshi, Asaman gadon take kwanciya tasha kukanta, duk Idan dare ya nutsa tashi take ta zauna, tana yi masu addu’a shida batul, Da daddynta, Kwana ta ke yi a zaune tana kai kukanta wurin Allah, Da ga ita har Gabriel babu wanda ya ƙara tada zancen haura tagar nan saboda babu lafiya atattare dasu, baiwar Allah azeeza ita keta yin jinyar Gabriel, Yaji jiki sosai, Gashi ƴan uwa nasu haushinsa suke ji, gani suke kamar baya ƙaunar Danish ne shiyasa ya ke neman naƙasa musu ɗan uwansu, A kwana atashi ba wuya wurin Allah yau tsawon 2 weeks kenan Ba’a dawo da Danish ba, A lissafi na Batul ta shiga Cikin wata na biyu kenan ba’a dawo musu da ita ba, Haka zalika Unaiza ƴar gidan daddy, Yau ta cika sati Sati biyu da kwanaki ba’a dawo da ita ba……….

 

(Iya abunda ku ka samu yau kenan, Da babu ƙwara ba daɗi, Mu haɗu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya)

*Idan Allah yakaimu next week zan Kammala Free pages of Takun farko, zan ɗauki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ƴar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 65"