Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kurkukun Kaddara 62

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*

*Dedicated to Aunty kubra❤*

*Gargarɗi!!!*


_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E62 free pages

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

Kwakkwance suke saman gadajensu, Sarah kaɗai ce kwance a ƙasa ta shimfiɗa bargonta kamar yarda ta saba.

Mutun ɗaya ce ta rage acikin ɗakin idonta biyu, sam ta kasa runtsawa sai juyi take yi saman gadonta, tarasa meke mata daɗi acikin duniyar nan, komai ya tsaya mata cak, babu alamun zata runtsa a daren yau, Yayin da take fuskantar ceilling, Jikin ta na asanye da tsoffin uniform ɗinta da suka maida kayan baccin su, ɗakin nasu yayi tsit sai sautin minsharin masu bacci, basu kashe hasken floor lamps ɗinsu ba, Saboda yau majnun bai yi musu haukan dare ba, tun da suka tsamo shi daga cikin trash can suka lalla6a shi ya kwanta bacci ya ɗauke shi, Har dare bai sauko daga saman gadon shi ba, Ya ji jiki da alama.

Kamar an tsunkule ta, ta zabura ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa da sauri sauri, sakamakon tunawa da ƴar uwarsu batool da ta yi, zuciyarta sam ba daɗi, sai yanzu ma take jin haushin damuwa da tayi akan ƴar gidan daddy, Sun saki jiki suna ta rayuwarsu batare da sun ta6uka komai ba, akan ƴar uwarsu.

Saukowa ta yi daga saman gadonta, ta ɗaura eyes ɗinta akan shimfiɗar Danish, Ya rungume pillow abun shi sai sharar baccin sa yake yi, Cikin sanɗa ta nufi tsakiyar ɗakin tana tunkarar sabbin gadajen da su parveen suka gaje, don har yanzu basu daina kwana saman su ba, tun ranar da aka kawo su Jamima, aka koma da mutun goma, su ka ci gaba da kwana saman su, Mutun biyar ne ba su kwana saman tsaffin gadajensu, Ita da Danish sai haris da Deeja, da kuma naufal, Amma sauran kowa ya samu sabon gado.

Agaban gadon Unaiza ta tsaya tana kallon wani sabon salon kwanciya, ta tura hannayenta cikin short ɗin jikinta, saboda jaraba Cikin bacci tayi wurga da bargonta ƙasa, Tana numfashi boobs ɗin ta na yin sama da ƙasa, Ta6e baki angel ta yi, Ji take kamar ta sanya hannu ta maida su cikin ƙirjinta su shafe, A nemesu arasa, ko sun huta da guyabarta, ” Guntun tsoki taja tunawa da abunda ya taso da ita daga saman gadonta, da sauri ta nufi ƙopar shiga sashen toilet ɗin su, bakomai take son gani ba face furen batool tana so taga awani hali yake ciki, Tana ƙoƙarin shiga toilet ɗin taji motsin shigowar mutun ta bayanta, a firgice ta juya don taga wanene, lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya ganin Danish ko me ya tada shi daga bacci, rayawa tayi aranta may be yayi tsamanin zata ƙara dura tagar ne shiyasa yabiyo bayanta.

Harara ta shiga jefa mashi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, red vest ɗin Jikin shi ta fiddo mashi da hasken fatarshi sosai, Idanuwanshi da alamun bacci acikinsu,

“Halan Ka biyo ni ne don kaga me zan yi acikin toilet? in banda sa ido, mutun na jin bacci amma ya kafe sai ya takura rayuwar wani, ni nasan saboda ni kazo nan” ta yi maganar tana murgaɗa mishi ƙaramin bakinta.

Bai tanka mata ba har sai da ya tako zuwa gabanta ya tsaya ya ɗan duƙo da kanshi saitin fuskarta, Cikin Cool voice ya furta mata”abunda kika faɗa gaskiya ne, Saboda ke nazo nan” ta6e mashi tausasa la66anta tayi tare da cewa”Kasan dai baka isa ka hana ni yin abunda na yi niya ba, zaifi ka daina wahalar da kanka akaina” ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, ganin yadda take mishi magana tana jifar shi da harara hadi da murguɗa mishi baki, a ƙarshe ma taja mishi tsoki ta juya zata shige toilet, da sauri ya damƙo damtsen hannunta ya dawo da ita jikin bango yayi mata rumfa, mamaki ne ya kama ta, Ta zuba mishi ido tana jiran ganin me zai yi mata.

“Saboda na damu dake ne shiyasa na biyo bayan ki ba don wani abu ba” yatsina fuska tayi tare da cewa”Ni ban damu da kai ba don haka kaima ka daina damuwa dani, pls ka koma ka kwanta ni ka bani hanya in wuce ka na 6aramin lokaci” Hada bubbuga ƙafa irin ya takura ta ɗin nan,

Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,
“Kince ba ki damu dani ba, but why kike hana idonki bacci don ki roƙi Allah akan ya baki abunda zai faranta min raina”! Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, wani irin kallo ta soma binshi dashi, gaba ɗaya ya kashe mata ba.”

Daƙyar ta iya buɗe baki tace “Danish kana nufin duk time da nake farkawa tsakar dare ina addu’a idon ka biyu? why ka sanya min ido, ko time dana ɗaukar maka alƙawarin na faɗi ne kawai don in kawar maka da tunaninka akan wancen yarinyar, kuma ni nayi hakanne gudun kada ta 6ata maka tarbiyar ka, saboda Nifa basa burgeni, bata su nake ba” tana magana tana hura hanci, Hannu yasa yaja tsinin hancinta tare da cewa”Nafa san me nake yi angel, ki daina ƙoƙarin nuna kamar ba donni kike yi ba, kina 6oye min irin ƙaunar da ki ke yi min,” ranta a6ace tace”waya ce maka ina ƙaunarka ni? To wai ni akan me ma xan yi addu’ar Allah ya bani su….” ya bata amsa da cewa”Saboda inaso” fuskarshi a ɗaure ya bata amsa, kamar tasa hannu ta shaƙe wuyanshi haka take ji, muryarta a fusace tace”Dallah ni bani wuri na wuce, kunnuwana ba zasu juri sauraran waɗannan kalaman naka ba,”

tana ƙoƙarin janye shi don ta wuce yae saurin cewa”Its okey, kin bani damar in cigaba da kallon nata kenan”? Girgiza mishi kai ta yi alamar a’a,

“nifa bance bazanyi bane, maganarce ke bana so,” ta faɗi hakan tare da sanya hannayenta ta ture shi gefe, Ta nufi ƙopar shiga toilet, har ta kusa shiga sai kuma ta ɗan dakata da alama wani abu take tunani ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace”Ni abunda ban fahimta ba, me zakai dasu da kake son su fito min? Ka san dai bana manya bane, Na jarirai ne, don haka ka daina murna, iya kallo ne shima ba koda yaushe zan bari kana kallan min abuna ba, da zarar Mun rabu da unaiza, zan haramta maka ganinsu,” ta ƙarasa maganar tare da faɗawa cikin toilet din hada sanya jamlock ta datse ƙopa, ta kifa kanta jikin ƙopar tana

Kanga kunnuwanta ta yi ajikin ƙopar don taji idan yana nan ko ya tafi, ba zato ba tsammani taji saukar hannun shi saman bayanta, a firgice ta juyo tana kallon shi, Yayin da shima yake kallonta, Ba ta yi mamakin ganin shi acikin toilet din ba tun da ba yau bane rana tafarko da ya fara Yi mata irin hakan ba, runtse idanuwanta tayi tare da bubbuga ƙafa tace”Nashiga uku! Wai meye ruwanka dani ne eye? Ba mun shirya ba, kuma nace maka nima zanyi irin nata to me kuma kake so”? Fuskarta a hautsine tayi mishi maganar, wani irin kallo yake binta dashi idanuwanshi kamar zasu lumshe saboda baccin da yaje ji,

“Angel, kin ɗaga min hankalina why zaki ce wai na jarirai ne, menene haka ba daɗin ji, kuma kince da zarar mun rabu da unaiza shikenan ko kallon su ma bazan ƙara yi ba, Ni na yi tsammanin duka zaki mallaka min su, tun da donni zakiyi su, idan kika min hakan baki min adalci ba,” muryarshi asanyaye sautinta ke fita, Lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, har wani zazzare mashi ido take yi don ma yasan cewa ba wasa take yi ba, a cikin zuciyarta kuwa tunani take yi Anya Danish bai da ta6in hankali? Taya zai tsareta akan abunda ma basu da tabbacin zasu fito ko ba zasu fito ba.

“Kin yi shiru baki ce komai ba”? Muryarshi ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, Ganin yana ƙoƙarin dagula mata lissafi yasa ta ruƙo hannun shi acikin nata, Tace mishi”muje mu kwanta,” bata jira amsar shi ba, ta buɗe ƙopar toilet ɗin, taja shi suka fuce har zuwa cikin dakinsu, Abakin gadon shi ta tsaya tare da kallon shi tace”nasan damuwarka, yanzu mu kwanta mu yi bacci, zamuyi magana zuwa gobe” ba don yaso ba ya ƙyale ta ya hau saman gadon shi ya kwanta itama ta wuce nata gadon ta haye, tana faman sauke ajiyar zuciya, ganin yana kallonta yasa ta janyo bargo ta rufe har kanta, lumshe idanuwanshi yae tare dajan nashi bargon ya lullube jikinshi, kowannansu da abunda yake saƙawa acikin ranshi, gani take kamar akwai shaiɗanu ajikin danish, waɗanda ke sanya shi yana yin abubuwa, Da farko yace yana son yi mata wanka yasa naci taƙi amincewa yanzu kuma so yake ƙirjinta sun fito ko uban me zaiyi dasu, Anya kuwa Danish bada biyu yake yi mata wasu abubuwan ba? Ta fara kokwanto akanshi, da wannan tunanin bacci yae awon gaba da su.

A washe garin ranar, majnun ne ya farkar dasu daga bacci, Tun da ya farka daga bacci ya sauko daga saman gadonshi yana miƙa da hamma, ya nufi gadajensu ɗaya bayan ɗaya ya dinga bubbuga ƙafafuwansu, yana faɗin su tashi ayi wasa, One by one su ka soma farkawa idanuwansu a kumbure fuskokin su duk a yamutse an sha bacci, su parveen hada miyan bacci a gefen baki, sun ji haushin tada su da ya yi, sai faɗa su ke yi mishi amma ko ajikin shi.

tsotai ne yakai Majnun gadon Unaiza ƴar gidan daddy, Ya sanya hannu yana bubbuga ƙafafuwanta don ta farka yaga ita kaɗai ce bata tashi ba, can cikin bacci ta dinga jin bugun da akeyi mata, a hautsine ta farka tare da miƙewa fuskar nan tayi jawur da ita babu annuri, suna haɗa ido da majnun Ya washe mata baki, ranta ya 6aci sosai dama ta tsani yaron, zabura tayi ta damƙo wuyan rigarshi, Haris da Danish har suna haɗa Baki wurin ƙoƙarin dakatar da ita akan karta ta6a lafiyar jikin shi, ko kallo basu isheta ba, ta daddaga ta kwakkwasa mashi zafafan maruka saman fuskarshi, azabar zafi yasa yaron ya dafe kuncinsa ya fashe da kuka, parveen hada cewa”Allah shi ƙara maka, Ae kaine da shegen jan faɗan tsiya,” duk sun yi tunanin za ta sake shi ne tun da ta mare shi, amma sai suka ga ta sanya hannu ta shaƙe wuyanshi da ƙarfi kamar zata kashe shi, idanuwanshi suka firfiro waje, A gigice Danish ya yunƙura tare da angel hada deeja suka nufi gadonta, Suna ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta amma taƙi sakin shi, rai a6ace Danish ya daddage ya watsa yatsun hannayenshi biyar saman kuncinta, ji kake tass! Abun da bata ta6a tsammani ba, Da sauri ta saki Wuyan majnun idanuwanta akan fuskar Danish, tun da take arayuwarta bata ta6a jin azabar mari irin wanda Danish yayi mata ba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta da suka cicciko tab da ƙwalla, hannayenta bibbiyu dafe kuncinta.

Su azeeza dake kallonta, dariya ce ƙumshe acikin bakunansu, Musamman da ta dinga binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, kamar tana tunzurasu ne akan su yi dariya, Angel ce ta rungume majnun ajikinta, tana lallashinshi, Sai kuka yake yi, Wuyan shi hada sahun akaifar Unaiza wurin yayi ja sosai jini ya kwanta abunka ga zabayyana dama ya lafiyar giwa.

“Wani ya samo min ruwa in bashi” angel ce tae musu maganar, da sauri parven ta sauko daga saman gadonta, ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko bottle water cikin wanda suka ajiye taje ta miƙa ma Angel tasa hannu ta kar6a tare da cire murfin ta kwafa mishi abaki, sosai yasha ruwan har yana shaƙewa, kusan rabin robar ya shanye, kafin ya janye bakin shi, Yana faman tatta6e fuska ya kalli unaiza a lokacin ta dawo da kallonta kan Danish, da alama bakinta ya gama mutuwa saboda marin da yayi mata ba.

Cikin shessheƙar kuka Chinonso Ya nuna ta da yatsa yana faɗin”I hate u, mai idon dodo, bana son ki,” Dama ranta a6ace yake, azabure ta yunƙura ta sauko daga saman gadon da niyar ta sake bugun chinonso, a tsorace yaron Ya yi saurin faɗawa jikin angel ya ƙanƙameta, Wata irin gigitacciyar tsawa Danish Ya daka mata, wadda tayi silar dakatar da ita, Da kakkausar murya yace mata”kada ki kuskura kice zaki ƙara ta6a shi, ke baki da hankali ne baki ga yaro bane? Ko so kike ki kashe shi ne shiyasa kika shaƙe mishi wuya” yae maganar idonshi akan fuskarta, wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, la66anta har kerme suke yi wurin faɗin”Ni ka mara? Sannan ka rufe ni da faɗa sai kace wata ƴar cikin ka, To ni ko ubana bai ta6a ɗaga min murya ba, balle har yayi gigin ta6a lafiyar jikina, rana ta farko da mahaifiyata ta fara yi min tsawa akan idona daddyna ya kwashe ta da mari, Amma zuwana Cikin ku, kun maidani kamar wata jaka, Wai me kuke nufi dani ne? Na kasa ganewa……..” daƙyar ta ƙarasa maganar, hawaye ta ko’ina saman fuskarta, Still idonta akan fuskar Danish, su Deeja sun kasa kunne suna sauraronta babu wanda ya tanka mata, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yai ba.

tana magana jijiyoyin wuyanta duk sun firfito ruɗu ruɗu saman fatarta, Sautin muryar ma daƙyar yake fita

“Ni bazan cigaba da zama acikin wannan Munafukin Ginin ba, nafara kokwanto akan ku, Kun ƙi ku sanar dani ina ne nan, wai me ake nufi dani ne? So ake dole sai nayi rayuwa kamar dabba! to nagaji! nagaji!! bazan Iya cigaba da zama acikin Ƙuntataccen dakin nan ba, wlh ban yarda da kowa ba, so ake akashe ni, Ni ku faɗa min me ake aikatawa acikin ginin nan? Kowa ya maidani jaka, Ni da nazo ɗaukar karatu? Ance min school ce but why har yau ba’a kai mu class room ba? Na yi shiru ne don inga ko akwai wani shiri da ake yi mana amma naji shiru har yau, babu zancen zuwa aji mu ɗauki karatu, nayi expecting ɗin zan samu abunda nake so shima kun hanani saima neman kassara rayuwata da ku ke yi, ta ko’ina kun ƙuntata min, Nifa ban saba da irin wannan rayuwar kullen ba, Ni school din ma na fasa amaidani gidan daddy na, wlh bazan zauna ba!!! ” tana magana tana matsar hancinta, fuskar tayi jaga jaga da hawaye,.

Da alama marin Danish ba ƙaramin zaburar da ita yayi ba, sai sambatu take yi tana zazzaga masu masifa ta inda ta shiga bata nan take fita ba.

“magana fa nake yi maku, duk kunyi min shiru sai kace kurame, Ku faɗa min ina ne nan? Kuna ƙara jefa ni cikin ruɗani! Abubuwa dayawa suna neman rikita min lissafin ƙwaƙwalwata! meyasa tun da nazo babu wani sauyi, ni fa ba haka daddyna ya faɗamin ba, yace min school ɗin akwai wuraren shaƙatawa acikinta, amma ni bangani ba, shi fa ya faɗamin hada lunch room da garden da swimming pools ga zoo irin na gidan mu, hada cinema but why are we always locked in the same room like an animal? Nifa na saba agidan mu, Ina yin duk abunda nakeso, ban saba da wahala ba, duk rana saina fita yawon buɗe ido, Har night club ina zuwa sometimes a hotel nake kwana tare da friends ɗina, Taya rana ɗaya za’a kawo ni wannan gurin me kama da Gidan Yari!”

a hargitse ta ƙarasa maganar, Cikin raunin murya da sagewar gwiwa ta zube saman ƙasa tana ci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita, basu ta6a jin tausayinta ba irin na yau, ganin yadda duk tabi ta burkice, tsawon lokaci babu wanda Ya tanka mata, da zarar angel ta yi yuƙurin buɗe baki ta yi mata magana, da sauri Danish ke dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kan shi alamar karta fada mata, tuntuni take son faɗa mata gaskiyar zance akan daddynta mugune sadaukar da ita yayi kuma nan ɗin kurkukun ƙaddara ne, da komai da suka sani dangane dashi wata’ƙil ta dawo hayyacinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne! Sai dai Danish yaƙi bari a sanar da ita.

Sosai take yin kuka babu mai lallashinta, Gefen fuskarta inda Danish ya mara hada sahun yatsun hannun shi ruɗu ruɗu, Tamkar da bulala aka shafi wurin, shi kanshi sai daga baya ya yi danasanin marinta da yayi duk da laifinta ne itace taja ma kanta,.

Saukowa gabriel yae daga saman gadon shi, gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan shi, Bai nufi ko’ina ba sai wurin da Unaiza take zuƙunne tana kuka, Zuƙunnawa yayi tare da sanya hayyanshi biyu ya rungumota jikin shi yana lallashinta, sai ya dinga ganin kamar twin sister ɗin shi ce take kuka, muryar shi ƙasa ƙasa yake faɗin”its okey unaiza, Stop shedding ur tears, ina atare da ke” kallon kallon sauran ƴan uwan nasu suka somayi atsakaninsu, sun yi mamaki ganin yana lallashinta, bayan shima yasan halinta na dabbanci da rashin kamun kai, dakatawa tayi da yin kukan tayi lamo ajikin shi, dama Gabriel akwai ƙira, Ta samu wurin zama, kamar zata shige cikin shi, jin tayi shiru yasa shi ɗagowa ya kalli su Danish dake atsaye suna kallon su, Magana ya soma yi musu

“Nima na jima ina so in tambaye ku game da kurkukun nan amma nakasa, Mu tamkar baƙi ne acikinsa, ina so insan komai agame da shi, Tsawon kwanaki, Banga an dawo min da ƴar uwata ba, kuma ni banga ana fidda mu waje ba, kullum muna kulle a room ɗaya, sannan waɗannan mutanan dake zuwa wanda ku ke kira da giants sam basu kwanta min araina ba, meyasa koda yaushe suke zuwa cikin shiga ta baƙaƙen kaya? Suna 6oye kan su don kada mu gansu, na fara zargin wani abu, it seems like something strange is going on in this prison. I wonder what they’re hiding from us.”

Shiru suka yi babu wanda ya tanka mashi, A ƙagare yace

“Na yi magana anyi shiru ba’a tanka mini ba, hakan na nufin hasashe na ya zama gaskiya kenan? Akwai wani abu dake faruwa wanda ba’a so mu sani, pls ku faɗa mana abunda ku ka sani tattare da gidan kurkukun ƙaddara, ku wayar mana da kanmu Ni da Unaiza! ni ƴar uwata ma itace damuwata, bansan Ina aka kaimin ita ba, awani hali take! Idan naci gaba da 6ata lokaci za’a iya cutar min da ita batare da sanina ba,”

Wani irin mugun bugu zuciyoyinsu su ka yi bakomai ne ya faɗo musu aransu ba, fa ce Ƴar uwarsu batool, haƙiƙa Gabriel Yayi wata magana da su ba suyi tinaninta ba, lokacin da suke 6atawa na rashin ta6uka komai akan adawo musu da ƴar uwa, kamar suna ƙara jefa ta cikin matsala ne, idan ma mutuwa ce ae yanzu ya isa ace batul ta mutu saboda azabtarwar da su ke yi musu idan su ka ɗauke su.

Shessheƙar kukan su Azeeza ne ya karaɗe cikin ɗakin, Jikin su yae mugun sanyi, ita kanta angel hawaye ne suka cicciko mata acikin idanuwanta, a marairaice take kallon Danish.

kukan su parveen ya ƙara dasa tsoro da firgici acikin zuciyar Gabriel, Yana ƙoƙarin Tambayarsu meyasa su ke ku ka, Danish yae saurin dakatar dashi ta hanyar yi mishi magana

“Gabriel, is enough! Maganarka bata da amsa, kamar yarda ka tsinci kanka acikin kurkukun nan ba tare da kasan komai dangane dashi ba, mu ma haka muka tsainci kan mu, Ƴar uwarka da aka ɗauka ba’a ita kaɗai ba ce, ka tuna su goma ne aka juya dasu, so ka kwantar da hankalin ka, Su ma suna acikin kurkukun nan kuma suna rayuwa kamar yarda muke yi”. Cikin karyayyiyar murya gabriel yace”Bana tunanin haka, Saboda ina ji acikin zuciyata wani abu yana faruwa da ita, ya za’ae na tabbatar da cewa tana Lafi…….” bai ƙarasa maganar ba, sakamakon ganin angel da ya yi ta miƙe da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu tana kuka,

Da sauri gabriel Ya janye unaiza daga jikin shi ya miƙe Ya nufi hanyar shiga sashen toilet ɗin da niyar yabi bayan angel, sai dai kafin yakai ga ƙarasawa Danish yasha gabanshi, damƙar damtsen hannun shi yae tare da cewa”Kada ka yi gigin cewa zaka bi bayanta, Ka koma ka lallashi waɗanda ka fama ma ciwon dake acikin zuciyarsu, har sai sun yi shiru,” Kamar wani ubanshi haka ya bashi umarni, ku ma abin mamaki gabriel bai musa mishi ba, Ya amsa mishi da toh, kafin ya juya ya nufi su azeeza, ɗaya bayan ɗaya ya dinga zuwa bakin gadonsu yana lallashin su, Har sai da ya samu su ka yi tsit Sannan Ya koma bakin nashi gadon ya zauna, Jikin shi duk ba daɗi kewar ƴar uwarshi ta addabe shi, tuni unaiza ta koma saman gadonta, chinonsa ma ya hau nashi gadon.

Sam bata ji alamar shigowar shi cikin toilet ɗin ba, tana zuƙunne gaban tukunyar furennin nan, Sai kuka take yi kamar marainiyar da ta rasa gata a duniya, Furen batool ya ƙara tayar mata da hankalin ta, ganin yadda Jikin shi ya bushe Ƙamas, Ganyayyakin jikinsa duk sun tsamure, Alamar babu lafiya atattare da mamallakin furen, A gefen ta Danish ya zuƙunna Tare da ambaton sunanta, Angel kusan sau uku Yana kiranta bata ɗago ba, sai da ya ɗaura hannun shi ɗaya asaman kafaɗarta tukunna ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu, fuskar tai jaga jaga da hawaye wasu nabin wasu

Cikin shessheƙar kuka tace”Me zaka faɗa mini? Kai idan ma lallashina zaka yi to banso! Ko ka yi abanza tun da ba iya dawo min da batool za ka yi ba, Ku ma wlh rantsuwar ɗan musulmi, zanje na dawo da ƴar uwata ne, ko da zan rasa raina ne akan hanyar zuwa wurin ta….” bata ƙarasa maganar ba, Ta daura kanta saman gwiwowinta, gaba ɗaya ta kashe mishi baki, Ya rasa me zaice mata, don ya lura babu sassauci akan fuskarta, shiyasa tun farko bai so Gabriel Ya fara maganar ƴar uwarshi ba. Ga shi yanzu yaja mishi masifa,

Jim ya ɗan yi kafin cikin cool voice ya furta”Angel, nasan bazan iya dawo maki da ita ba, kamar yarda kika faɗa, ku ma kema haka koda ace kin ƙara dura tagar nan da niyar kije neman ta, ba lallai bane Ki iya tsira, ko kin manta abunda Ya faru dake ne a rana ta farko da kika haura…..”? Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda yadda ta ɗago tana wurga mishi harara gwanin ban tsoro launin idanuwanta kamar na zombie, masifa ta soma zazzaga mishi

“Bana son ganinka, sai iya daɗin baki, Danish idan har ni bazan iya shiga prison ba, kai zaka Iya, tun da har ka iya zuwa ka ɗauko ni, dan haka inaso kaje ka dawo mana da batul ɗin mu, Danish ka taimaki rayuwar batul, tsawon wata ɗaya da weeks babu ita, ka duba ka gani fa, ko su deeja 2 weeks ne aka dawo mana su, amma Jibi kaga yarda aka canza musu halittarsu to inaga ita da ta jima a hannunsu”

Baisan ya zaiyi ya fahimtar da angel ba, ya san koya lallashe ta abanza don ba jin shi zatayi ba, hakan ya sa shi miƙewa Ya fuce daga Cikin toilet din tabi bayan shi da kallo, Zuciyarta akarye ta miƙe, Tana sharar kwalla, Bata fito daga Cikin toilet din ba, Sai da ta goge bankinta, Tayi wanka,

Lokacin da ta fito, su hanna ta taras A cikin sashen toilet ɗin nasu, suna jiran wanda ke aciki su fito suma su shiga, kallon su kawai tai batare da tayi musu magana ba tasa kai ta fuce daga wurin, shigarta ɗaki keda Wuya, Sai ga Giants sunzo kawo musu abinci, nan take ta ɗaure fuskarta, su uku hannayensu ɗauke ta farantan kayan abincin su, ciki suka shiga tare da sauke trays ɗin saman dining carpet ɗin su, Atare suka ja baya kamar yadda suka sa6a ƙame wa,

Kaitsaye angel ta nufi inda suke, Danish na jin takun tafiyarta ya ɗan ɗago daga kishingiɗan da yake saman gadon shi, Hatta haris da Gabriel da suke acikin ɗakin hankalinsu na akanta

“Har yaushe ne zaku kammala amfani da ita ku dawo mata da ita? Nasan kun gane akan wa nake magana, Ƴar uwar mu batul tana ina”? Ranta a6ace take yi musu magana, babu wanda ya motsa, tsawa ta daka musu tare da cewa”Da ku fa nake magana? Nasan kuna ji na, mugaye kawai……” jiki na 6ari danish Ya sauko daga saman gadon shi ya nufi angel ya ruƙo hannunta yana ƙoƙarin janyeta baya, gudun kada su cutar da ita, fashewa tayi da matsancin kuka, Tana bugun Danish akan ya saketa, wlh sai sun fito musu da ƴar uwarsu, Wannan maganar tayi matuƙar ɗaure ma Gabriel, da Unaiza kai, don tuni ta miƙe zaune saman gadonta, idanuwanta luhu luhu take kallonsu, Saboda sautin kukan Angel har na cikin sashen toilet dinsu saida suka fito, hankalinsu yayi matuƙar tashi ganin yadda take kuka tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannun danish donta kaima Giants hari, A ƙarshe da ta ga dagaske Danish bazai Ƙyale ba, ta daddage ta gartsa mishi ciwo a damtsen hannun shi tare da sanya hannayenta biyu ta ingije shi gefe ɗaya, taku ɗaya zuwa biyu takai ga farantan kayan abincin da aka kawo musu, Robar ruwa ta ɗauko ta buɗe murfin, Cikin zafin nama ta watsa ma giants ruwan ajikinsu kaf ta zazzage musu shi.

waro ido waje su Parveen su ka yi ganin irin bala’en da take so taja musu, kowa yasha jinin jikin shi, Tana haki tace”Dama nasan bazaku motsa ba, saboda ku ɗin dabbo bi ne, Marasa imani, Allah dai yana ganin ku mugaye, Wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har wani abu ya sami batul sai kun gane ba ku da wayau, domin kuwa saina addabi rayuwarku, inyaso ku kashe ni, kai bazan ma mutu ba bi’iznillahi har sai na ga bayan ku…” Bata kai ƙarshen maganar ba, Danish Ya sake damƙota, kamar ƴar dambe sai harba ƙafarta take yi, ahaka yaja ta har zuwa saman gadonta, Ya jefar da ita, Kafin ya juya ya kalli Sauran yace dasu su je su ci abinci,” da sauri suka nufi kayan abincin nasu kowa ya zauna banda Gabriel da Unaiza, kalaman angel sun yi matuƙar ɗaga musu hankali, tunani suke yi wacece batul? Meyasa aka ɗauke ta?

A gefen gadon Angel Danish ya zauna yana gadinta, gudun kada ta ƙara zuwa ta 6allo musu aiki, Shi kaɗai yasan me yae mata, da har tagaza ɗagowa, hawaye sai bin fuskarta suke yi, ta ɗaura kanta saman pillow,

Bayan sun kammala cin abinci sauran da suka rage ma waɗanda basu samun damar xuwa suci ba, acikin kwando suka adana mu su nasu, Giants na fita daga Cikin dakin, Gabriel ya soma tambayarsu wacece batul? su azeeza suka bashi amsa da cewa ƴar uwarsu da aka ɗauka, yaso ya ƙara tambayarsu dalilin dayasa aka ɗauke ta amma Danish Ya hana shi, ta hanyar
Ƙura mishi ido yana kallon shi, nan take yaji maganar ta fita aranshi, bai ƙara tada ta ba.

Yinin ranar babu daɗi suka yi shi, Saboda halin da suka shiga na tunawa da ƴar uwarsu, Kowa jikin shi yae sanyi, Har marece ya yi babu wanda ya motsa acikin su, majnun ne kaɗai yake ta tsalle tsalle shi kaɗai atsakiyar ɗakin su.

Lokacin da marece ya nutsa, Gabriel ya bukaci yin wanka, Saukowa Yae daga saman gadon shi, Ya nufi toilet ɗinsu Ya shiga, bayan yasanya jamlock ya datse ƙopar Ya dan jingina bayanshi Jikin ƙopar, yayin da zuciyarshi ke acunkushe da tunanin abubuwan da suka faru ayau, Tabbas ya razana sosai da gidan kurkukun nan, duk da baisan komai adangane dashi ba amma yana ji aranshi cewa wani abu yana faruwa badai badai ba, Shi bakomai yafi jimawa ba face ƴar uwar shi Gabriella, maganganun da angel tayi ɗazu akan tasu ƴar uwar sun tsara mishi aranshi.

A ƙalla ya ɗauki kusan minti talatin Yana tunani acikin toilet ɗin ba tare daya ta 6uka komai ba, Sai daga bisani ne ya soma ƙoƙarin cire rigarshi, Kwatsam idanuwanshi suka sauka akan Glass window ɗin nan, A wani slow yake kallonta sai yake ganin kamar glass ɗin jikinta bai zauna dakyau ba, nan take ranshi ya bashi cewar Yaje ya duba ya gani, wata’kil ma ya samu hanyar shiga Cikin kurkukun ko dan yaje ya ɗauko ƴar uwarshi, ba tare da yayi shawara da zuciyarshi ba, Ya fasa cire rigar ya nufi tagar, Yakai hannu ya tatta6a jikin glass ɗin Yaji yana girgiɗi, ya daddage ya zame shi daga jikin tagar ya sauke shi ƙasa, wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyarci, bakomai yake hange ba face fuskar sister ɗinshi.

Rashin sani yafi dare duhu, cike da ƙwarin gwiwa Gabriel ya dura tagar ya faɗo ta cikin wannan hanyar da angel ta tsinci kanta lokacin da ta ta6a durawa, hada saurin shi wurin miƙar hanyar, babu wadataccen haske, amma yana iya gani dakyau, yana kaiwa ƙarshenta, Ya faɗo cikin wannan babban filin mai ɗauke da dogayen benayen nan, A hankali yake ƙarewa ginin kallo, bai ta6a ganin wuri mai matuƙar ruɗarwa ba irin wannan wurin, hakanan ya dinga jin faɗuwar gaba, tun daga kan hauwa na farko har zuwa na biyu, a ƙarshe ya tsayar da idanuwanshi kan hawa na uku, ba zato ba tsammani idanuwanshi suka hango mashi kyakkyawar matashiyar budurwa tana gudun ceton rai saman hawa na uku, fara fat kamar fatalwa, Jikinta sanye da riga ja, wadda bata kai gwiwarta ba, fararen cinyoyinta santala santala, daga gani babu hankali atattare da ita, tana gudu tana waiwayon bayanta, ga uban gashin kanta dake yarfowa harta saman idanuwanta, hakan yasa ta dinga faɗuwa ƙasa tana miƙewa saboda bata ganin gabanta dakyau, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyar Gabriel, Ganin tana saukowa daga saman benan mai hawa talatin, Girgiza kanshi ya dinga yi, zufa tako ina saman fuskarshi, Ya rasa gane shin mutunce ita ko aljan, ko kuma fatalwa ce, Idanuwanshi ne suka dinga nuna mashi kamar sister ɗinshi ce, sai dai akwai banbanci sosai, Ƴar uwarshi ba fara bace, kuma bata da tsayin sumar kai da yawa irin na wannan yarinyar, ‘ A tsorace ya juya zai koma hanyar daya fito, A lokacin harta ƙarasa saukowa saman benan, sai miƙa mishi hannu ta ke Yi, tana magana sautin muryarta sam baya fita, ranshi ne ya bashi cewar Ya juya ya kalle ta, ya ɗan dakata ya waiwayo baya yana kallonta, sai jan ƙafarta take yi, saboda nauyin da tayi mata, Taya zai iya yarda cewa mutunce ita? Bai gama yanke shawara da zuciyarshi ba, yaga ta faɗi ƙasa kanta ya bugu, ‘ Gaba ɗaya sumar kanta ta rufe mata fuskarta, Tsananin tausayinta ne ya kama gabriel, koma dai aljana ce wannan ba ƙaramin jiki taji ba, sai motsi take yi alamar tana son ɗagowa da kanta amma ta kasa, kuma duk da tana kwance ƙasa hakan baisa ta fasa miƙa mishi hannunta ba, yayi niyar yaje wurinta amma sai yaga Benayen dake awurin sun soma motsi suna yin sama da ƙasa, Ya zazaro ido ganin suna tunkaro shi, aiko da gudu ya juya ya bi ta hanyar daya fito Ko waiwaye babu ya koma bakin tagar nan, Allah ne ya taimake shi bai 6ace hanyar ba, Jiki na kerma ya haura tagar Ya dura Cikin toilet ɗinsu Yana ta haki, Sai da ya samu natsuwa tukunna yakai hannu ya ɗauki glass ɗin daya jingine jikin bango ya maida shi jikin tagar kamar yadda ya ganshi,

Kamar amafarki yake tariyo abubuwan da suka faru Cikin ƙanƙanin lokaci, zuciyarshi cike fal da tunanin matashiyar yarinyar nan daya gani …………..”!

 

*Idan Allah yakaimu next week zan Kammala Free pages of Takun farko, zan ɗauki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ƴar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 62"