Kurkukun Kaddara 6
_To my biggest hero_
_There’s no better role model than you,_
_There’s no one I’d rather look up to than you._
_I’m so proud to be your daughter_
_You’re my one and only dad, and you’ll always have a special place in my heart._
_Dad, you’ve made all my favorite memories._
_Dad, you’ve always been my hero._
_I’m so lucky to have your love and guidance in my life_
ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi,
Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba,
Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel
Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta,
“Daddy sannu da dawowa Nayi missing É—inka sosai” ta ambaci hakan fuskarta É—auke da murmu shi, buÉ—e mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta Æ™arasa ta faÉ—a saman faffaÉ—an kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faÉ—in”kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin Æ™aunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maÆ™iya da mahassada, Allah ya yi maki albarka”
Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata,
ÆŠagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears É—in dake sauka akan fuskar shi”daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba”
Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waÉ—anda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai,
Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta,
Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace”daddy baka lafiya”?
Eyes É—inshi arufe yace”kinci abinci”?
“Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka” girgiza mata kai yayi”a’a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci”
Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su,
Wuraren Æ™arfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la’asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet É—in É—akin ta Ya shiga ciki,
After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci,
Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta”My angel!”shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da É—an bubbuga Æ™afarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta,
“Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci”
Muryarta a disashe tace mashi”a dawo lpy daddy,”
Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,
Jim kaÉ—an tafito É—aure da alwala, ta É—auko carpet ta shimfiÉ—a, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah,
Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur’ani mai girma daga cikin kanta,
Tana cikin yin qira’ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa Cikin É—akin, Ba Æ™aramin daÉ—i yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al’qur’ani mai girma,
Sai da takai Æ™arshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi”daddy sannu da dawowo”
“Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu’a ko”? jinjina mashi kai tayi”eh,Ae kullum sai nayi”
“Haka nakeson ji, My daughter”
Shiru ya É—anyi kafin Yace”Zamu fita tare da daddy uzair É—inki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh”?
“Daddy bazaka tafi dani ba” aÉ—an shagwa6e tayi maganar,
“Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba,”
Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaÉ—ai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma’a,
“Dan Allah daddy…….”tunkafin ta Æ™arasa yayi saurin katse mata hanzarinta”yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane,”
Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta,
Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba É—aya ya É—auketa, yana É—an bubbuga bayanta”Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne”
Cikin shessheÆ™ar tace”bazanyi ba”
“Haka nakeson ji my angel”
Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan.
Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel,
Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi,
Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh,
“Kina jin yunwa”? É—aga mata kai tayi alamar eh,
“Hawayen menene akan fuskarki”?tayi tambayar tana kallon fuskarta,
“Daddy inata roÆ™on shi ya tafi dani amma ya Æ™iya”
Murmushi aneelerh tayi”Shine kike kuka? idan ki ka yi haÆ™uri ae ba kwana zasuyi ba,” ta ambaci hakan tare da miÆ™ewa ta nufi kitchen,
KishingiÉ—awa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen É—in hannunta É—auke da plate, mai É—auke da farfesun naman Kaza, da alama ba’ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga Æ™amshi,
A saman table ta É—aura plate É—in,tare da samun wuri gefen angel ta zauna,
Jin ƙamshi Yasa angel mikewa ta gyara zamanta,
“Aunty aneelerh,duk ke kikayi wannan”?
“A’a bani nayi ba, Ana ce ta yi shi”
Yatsina fuska angel tayi”wannan matar kamar munafuka,Ni ban yadda da ita ba Allah, Kullum tana aÉ—aki kunshe, Ita bata fitowa sai zata yi girki ko gyaran gida,
Dariya sosai Aneelerh tayi”Zaki fara tsegumin naki ko”?
Ta6e baki ta É—anyi, tare da zura hannu cikin plate din tana É—an tsakurar naman, Har wani jinjina kai take yi saboda daÉ—in da ya kai mata karo, zuba mata ido aneelerh tayi tana kallonta,
“Aunty aneelerh,”
“Menene”?
“Mutane dayawa suna cewa Ni matar Manyace, irin matan masu kuÉ—innan, Allah idan na girma mai kuÉ—i zan aura, inda zanje in huta, Bani aikin komai sai dai Ƴan aiki suyi mun ina daga kwance,”
Tunda ta soma zuba, Aneelerh ta ƙura mata ido tana kallonta,Wato Zuzuta kyanta da mutane suke yi suna cewa ita matar manya ce, Shine ta haddace maganarsu acikin kanta, har tafara sawa ranta aure inda zata huta,
“Bakya son talaka”baneelerh ce ta jefa mata tambayar,
Yatsina fuskata tayi”ae annabima yace mu nemi tsari da talauci,”
Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba,
“kinga daddy yaÆ™i yin aure, Da a lama sai na fara haifa mashi Æ´an jikoki” takai karshen maganar tana sakin Æ´ar dariya,
Murmushi aneelerh tasa ki a ranta tana mamakin yadda take maganar aure har da haihuwa ko kunya babu halin angle sai ita kafin tace”mai zai hana kisa ma shi matar aure”
É—an zaro ido tayi bakinta cunkushe da naman data tura, ahaka tace”Tab, salon tazo ta mallake mun daddyna, Ƙwara yayi ta zaman shi a haka babu auran,”dariya sosai aneelerh tayi”Angel kenan mai abun ban mamaki” ta ambaci hakan tare da mikewa tace”zan shiga daga ciki inaso na kwanta, Idan kin kammala ci, Ki kai plate É—in a kitchen, kizo ki same ni a É—aki muyi karatun haddar da aka baki islamiyya”
Ta amsa mata da toh”sai da angel ta kammala shan farfesun tukunna ta miÆ™e ta nufi kitchen, Bayan ta ajiye plate din,ta fito ta nufi É—akin aneelerh
*** *** *** *** *** **
A 6angaransu taj kuwa, gidan wani abokinsu suka fara zuwa kai mashi ziyara, sun jima a gidan bayan sun baro gidan abokin nasu, Suka Nufi gidan Gonar uncle abdallah, da niyar suje su duba yadda komai ke tafiya, Kafin su dawo gida,
Gidan Gonar acan bayan gari yake cikin daji, lokacin da motar su ta ƙarasa Cikin dajin, Adai dai bakin Gidan gonar uzair ya yi parking ɗin motar, Wani tsohone daga waje saman benci yana sauraron radio da a lama shine ke kula da gidan Gonar,
Tunkafin Suyi parking ɗin motar, Ya miƙe yana ta faman washe baki don ya gane motar uzair ce,
At same time suka fito daga Cikin motar, A hanzar ce suka ƙarasa inda yake a tsaye, Jikin shi na sanye da riga da wando na yadi, Zariyar wandon har kasa kamar wani ta6a66e, Gashin kanshi duk hurhurace, Fari ne sol kanshi da rawani irin na buzaye,
“A’a wa nake gani kamar Tajo?’ cike da mamaki ya yi maganar yana kallon tajuddeen, miÆ™a mashi hannu taj yayi fuskar shi É—auke da fara’a yace”Nine mana, baba buzu ashe kana a raye” ya yi maganar da zolaya,
“Amana batace haka ba tajo,Yaushe rabon da in sanyaka a idanuwana tun kana É—an matashi,”
“Yau dai gani nazo, kuma bada wuri zamu tafi ba, har sai ka gaji da gani na,” yakai Æ™arshen maganar yana dariya, shima dariyar ya yi”wuni kuka zo mun kenan aikuwa har masara zan gasa mana muci muna fira,
Kafin taj ya yi magana uzair yace
“Fatan mun same ku cikin koshin lafiya, Ya komai ke tafiya”
Tsohon yace”alhamdulillah, Ku Æ™araso mu zagaya cikin gonakin mana,” Gaba ya yi su ka bi bayan shi, suna É—an tattauna fira atsakaninsu”
Sunjima suna kewaye gonakin har cikin gidan gonar suka shiga, koda aka fara kiran sallar Magrib, atare da baba buzu su ka yi sallar Acikin gidan gonar, ba su tashi tafiya ba, sai bayan da akayi sallar Isha’e, tukunna su ka yi sallama da shi,
Taj ne ya kar6i driving É—in, Uzair na gefen shi, motar su na haurawa saman titi, wasu dankara dankaran motoci masu black tinted suka shararo da gudun gaske kusan su shida, A jere suka KurÉ—aÉ—a cikin dajin,
Duk akan idonsu tajuddeen, Da mamaki akan fuskar Uzair yace”kosu wanene a cikin motocin can? Kuma ina zasu dosa ne? Ni dai a iya sanina babu wani gida dake acikin dajin nan,”
Taj yace”May be ko wani party ne za su yi, ba abun mamaki bane”
“That’s impossible, Party kuma arasa inda za’ayi shi duk faÉ—in garin mu sai cikin dajin nan, Gaskiya ni ban yadda ba Allah, tabbas inaso nasan me zasu yi a cikin dajin can, Ka juya motar mubi bayan su”acewar uzair,
Taj yace”Ni bazan bi su ba, kawai daga ganin motoci sun shiga daji sai kace mubi su, for what reason?
“Nidai kawai kayi a bunda nace maka, Kada ka manta mu fa Æ´an jarida ne,
rai a É—an 6ace taj yace”Mu Æ´an jarida ne, Ba jami’an sirri ba, Don haka ni bazan bisu ba, Gida zamu koma”
Yana ƙoƙarin juya sitiyarin Uzair ya damƙi hannun shi, juyowa yayi suka haɗa ido,
“Ka yi abunda nace maka, In ba so ka ke in sauka daga Cikin motar nan ba, in bayansu da Æ™afafuna”
Sanin kafiyar Uzair ne, Yasa Taj Juya motar Ya nufi Cikin dajin, Zuciyar shi duk a jagule don ba ƙaramin takura shi uzair yayi ba,
“Ka rage gudun motar” acewar uzair, a takure taj ya rage gudun motar, yayin da yake kurÉ—aÉ—awa cikin dajin har Allah ya kawo shi wurin da waÉ—annan danÆ™ara danÆ™aran motocin su ka yi parking, A jere su shida a bakin wata Æ™orama,
Daga nesa dasu taj yayi parking É—in motarsu, tare da kashe hasken motar su, don kada su gansu, Amma su suna iya hangensu saboda sunbar nasu hasken motocin su a kunne,
Natsuwa su ka yi suna jiran ganin Su wanene zasu fito daga Cikin motocin,
Kusan Æ´an mintuna, kafin a buÉ—e motocin, kamar a shirin film suka fito a tare, Kowannansu Na sanye da suits ajikin shi black colour, fuskokinsu na sanye da mask, daga ganin bodyguards ne, At same suka buÉ—e murfin Back seat na motocin,
Wasu Manyan mutanene suka soma saukowa daga Cikin motocin, kowannan su na sanye Cikin shigar hausawa, Daga ganinsu dattawane sun kwan biyu aduniya,
Kallon juna taj da uzair sukayi a lokaci É—aya kafin suka mayar da hankalinsu kan abunda suke kallo,
Bayan Alhazawan sun kammala fitowa daga Cikin motar, ÆŠaya daga Cikin bodyguards É—in Ya zagaya bayan motar Æ™arshe, Ya buÉ—e boot É—inta, Hannu ya sanya ciki tare da danÆ™o rigar Wani bawan Allah dake naÉ—e cikin boot É—in, Ya wurgo shi waje, Gaba É—aya mutumin ya kife Æ™asa, Rawanin dake naÉ—e a kan shi Ya warware, Jikin shi sai kerma yake yi, kamar wanda sanyi ya kama, daga ganin shi dai Malami ne, duba da irin shigar shi,Jallabiyace ga kuma rawanin shi, hada cazbaha a hannun shi lokacin daya É—ago, La66an shi nata kerma Yana ambaton”Innallahi wa’inna ilaihirraji’in, La’ila ha’illah anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin,’duk yabi ya susuce,
Cike da taku irin na majiya karfi, Bodyguard ɗin ya kuma takawa Zuwa mota ta biyun ƙarshe Ya buɗeta,
Wasu ƙananun Yara ne guda biyu, Gwanin ban tausa yi sun ƙankame junansu mace da namiji, Sun cunkushe acikin boot ɗin,Yadda kasan irin kifin gwangwanin nan,
Damƙo wuyan rigunan jikinsu yayi tare da ɗago dasu Ya wurgo dasu ƙasa, Gaba ɗaya suka kife saman Ciyayin dake a wurin,Sautin kukansu ya ƙarade wurin, Miƙewa Yaran su ka yi da gudun gaske suka nufi wannan malamin daga gani ubansu ne, Rungumesu ya yi a jikinshi sunata kuka, A ƙalla macen bazata wuce shekara Takwas ba, Namijin kuma goma,
Tsananin tsoro ne Bayyane akan fuskokin su, Hankalinsu amatuƙar tashe yake, Daga gani bada shiri aka ɗaukosu ba, Saboda kayan dake a jikin yaran duk na bacci ne, Ita macen ko kalli babu a kanta, ɗan kitson Shukkun da akayi matane, ƙafafuwansu ko takalma babu,
Ƙawanya waɗannan Alhazawan Sukayi masu, Suka sanya su a tsakiya, Yayin da bodyguard ɗin ke a bayansu,
Wani irin kallo suke binsu dashi, kafin daga bisani wani dattijo daga cikin alhazawan Ya soma magana”Malam wa kake da suna”?muryar na kerma Malamin yace”Jazuli”
Jinjina kai dattijon yayi”sau nawa ina jan kunnanka”?
“Sau biyu” cikin shessheÆ™ar kuka ya yi maganar,
“Okey,Saboda kafiya da taurin kai irin naka Baka daddaraba ka sake shiga hurumina ko? Meyasa ka tsananta bincike akaina? Ka sanni ne? ko ina da wata alaÆ™a dakai ne?ya yi tambayar idonshi akan malamin
Shiru Malam Jazuli yayi, yana ta faman mazurai, Hannunshi bibbiyu ya tallabe Æ´a’Æ´an shi,
“Koda zaku cutar dani, Ina roÆ™an alfarma É—aya a wurinku, dan Allah kada ku ta6a Æ´a’Æ´ana,”
Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba É—ayan su, mai sautin gaske,
Taj da uzair dake la6e acikin mota suna kallonsu, Tuni sunsha jinin jikinsu, buÉ—e murfin motar su uzair ya yi da niyar ya fita, da sauri taj ya ruÆ™o Hannnunshi murya Æ™asa Æ™asa yace”baka da hankali ne, Idan suka kama mu fa”
Uzair yace”bana jin abunda suke cewa, dole na fita” ya zame hannunshi daga ruÆ™on da taj yayi mashi, yasa kai ya fuce daga Cikin motar, kasa zama Cikin motar ya yi ya Æ™wammace yabi bayan uzair komai zai faru ya faru, BuÉ—e motar ya yi tare da fitowa Yabi bayan Uzair Cikin sanÉ—a suke tafiya har suka Æ™araso gab da su, a bayan wata gabjejiyar bishiya, suka la6e suna kallon su,É—an Jarida da kasada,
“Nifa inaga,Yakamata mu tafi uzair”acewar Taj,
Girgiza kai uzair yayi”KaÉ—an jira muga Mai zasuyi ma shi, bari ma na É—auki video,”yana Æ™okarin zaro waya, Taj ya buge hannunshi”ashe baka da hankali, So kake hasken camera ya tona mana asiri, ba don yaso ba Ya haÆ™ura da É—aukar video É—in,
Suna Cikin yin Maganar nan, Su ka ji wani irin gurnani mai matuƙar tsoratarwa, A ruɗe suka ɗago suna kallon su,
Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take yazama wata irin halitta mai matuƙar tsoratarwa,Ya shiga girgiza jikinshi Yana wani irin gurnani,
*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*_daga alÆ™alamin Boss Bature ✍️*_
dedicated to Aunty kubra❤
قصة Øزينة جدا عن السجناء🥺💔
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 6"