Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Inda Rai 3

 *INDA RAI*.....🥰


  By


       *Maryam Abdullahi*



     (💋💋 oum shaheed💋💋)    *MIKIYA  WRITER'S ASSOCIATION*


https://chat.whatsapp.com/GGx1CkOOs2wJefdQx6ZUei



Page 03



-------- "Tafiya ta keyi tana waigo bayan ta ta na ɗaga masa hannu, idanunta  sun yi jajur, saboda kukan data ke yi ko gaban ta bata gani sosai.


"Imran kamar zai kifa dan sauri, ya na son ya'iso in da ta ke amma kamar maida shi baya akeyi, cikin azama ya ya miƙa hannu zai riƙota, sai wani abu mai hasken gaske ya rufe mai idanu, yayewar hasken sama ko ƙasa yane meta ya rasa, ta ɓace ɓat, babu alamun ta agun.


Durƙushewa ya yi agun ya na gunji me kama da kukan damisa, gashin kansa sun miƙe, fuskarsa fara tas ta koma kamar wadda aka shafawa jini,  saboda yadda ta rikiɗe ta zama jajir, take ganinsa ya fara daukewa, jinsa ya ɗauke, babu abun da ya ke buƙata irin sake ganin ta, "meyasa zakimin haka?? Ina daf da samun ki zaki ɓacemin, why??  Kukan yarinya mai firgitarwa,  shiya dawo dashi duniyar jii, da ganinsa, a take ƙwaƙwalwarsa ta fara aiki, da sauri ya waiga bayansa in da yakejin sautin kukan yaran, miƙa hannunsa ya yi zai kamo yaran, sun taho zasu faɗa jikinsa, ya ji an jashi ta baya ya fada cikin ramin,,,




     Abuja


"Alhaji ko de zaka sake kiran sa,  gudun sake ɓata lokaci??? "cewar Momy Ashashe da ke zaune a gefen Alhaji Auwal ambassador, "dogon numfashi ya yi ya ce,  Ƙyaise!, yaronnan tunda yacemin ya na  zuwa to tabbas ya na zuwa, tofa ya na zuwa ɗinne, bari muga zuwa nine, idan bezo ba  sai na kira naji, "hakane Sa'inna,  Allah yasa lafiya.



Ƙwance Barrister Sudais ya ke,  idanunsa a lumshe,  sam yau ɗin ya rasa mai ya ke damunsa,ya na son tashi ya wuce kiran da mahaifin nasa ya ke masa,  amma gangar jikinsa taki basa wannan damar why?? zuciyarsa ya ji ta buga da ƙarfi,  tunawa da ya yi Babban nasu ya na can yana jiran sa, cikin ƙarfin hali da jarunta ya tashi yaƙarisa  shiryawa,  cikin wani yadi me taushin gaske,  fari ƙal,  ɗinkin ya zauna a jikinsa sosai kasan cewar sa chocolate colour,  ya ɗauki hula kalar zaran da'akayi ɗinkin rigar dashi ya kafa a kansa, cikin sauri ya ɗaura agogonsa na zallar ɗanyan diamond, turaran oud Dubai me sanyin ƙamshi ya fesa a jikinsa, jinsa ya ke kamar fanko,  sam babu ƙarfi a tattare dashi, falon gidan nasa ya fi to,  komi fes sai tashin ƙamshi ne kwai ke tashi,  mai sanya duk wani cikekken mai lafiya zai yi burin baje kolin soyayyarsa acikin wannan gurin. 


Yana fitowa harabar gidan kai tsaye wajan a dana motoci ya nufa,  wata mota ya shiga fara tas, sai ɗauke idanu takeyi,  cikin mutuwar jiki ya ke tuƙin motar, da sauri gete Man ya wangale wasa gete tangamemen gete ɗin, cikin kwarewa ya jefa motar kan titi...



"Yanzun tsakani da Allah Malam bukar bazaka ɗaga wannan auran ba?? cewar Baban Rabi maƘocinsa,"Malam Bukar ko kallon gefen da abokin nasa yake baiyiba balle ya yi tunanin ya ji abun da ya ke faɗa masa, haka Baban Rabi ya yi ta maganarshi shi kaɗai har ya gaji ya yi shiru.


Acikin gidan kuwa kukama ya zama rahma domin gaba ɗaya Maryama ta zama abun tausayi, bata iya komi tazama kamar sikeleto, ko sallah sai an ce ta tashi ta yi, tanajin inama ita ce ta rasu, inama ita ce tabar wannan duniyar, data huta ganin wannan ranar,tana son tayi kuka amma ta kasa, tanason tayi magana namma abun ya faskara,  Maryama!!!! Innar Rabi ta sake kiran sunan nata a karo na babu adadi,  amma shiru ta kasa amsawa, tana son ta amsa amma abun ya gagara  sai idanu da take bin Innar Rabin dashi, wai da gaske aure za'amata??? Kuma a yau ɗin da Innarta ta yi ƙwana uku da barin duniya?? Innanillahi'wa"inna'ilehirraji'un ,,,,, kimin alk'awari ko bayan raina bazaki bari mahaifinki ko dangin sa suyi nasara akan ki ba,,,, firgit ta miƙe tsaye,  cikin layi ta nufi hanyar fita daga ɗakin,  tunada  maganar da su ka yi da mahaifiyar tata, maganar ƙarshe, maganar da ba zata taɓa mantawa da'itaba"ina zakije? Inna Rabi ta tambayeta, "ko  juyawa Maryama ba tayi ba taci gaba da tafiyar ta,bokiti ta ɗauka ta nufi randa ta debo ruwa, banɗaki ta shi ga tayi wanka ta yi alwala, kowa kallonta ye keyi cike  da maɗaukacin mamaki.


Bayan tayi sallah ta daɗe ta na yi wa Innar ta addu'ar da cewa sannan ta kalli Innar Rabi tace "Inna inason magana da Bello kafun ɗaurin auremmu....


    New Delhi. 


Yau mafarkin da Imran ya yi yafi ko wanne daga masa Hankali,Sam yakasa samun sauki a ransa,"shigowar Bhu-Ali kenan yaga halin da abokin nasa yake ciki, cikin sauri ya ƙarisa kusa dashi "subahanallahi, haba Imran!! wani abu ya sake faruwane??? "da' idanu kawai Imran ya ke bin Bhu-Àli amma ya kasa cewa uffan," idanunsa sunyi jajir' da'alama yau yasha abar tafi karfin sa,

"kamasa ya yi ya na tashi ya koma ba ya zai faɗi,  "ya Allah!! "Cewar Bhu Ali.


"Wayarsa ya ɗauuka cikin hanzari ya kira doctor Anwar,  "hello!! Anwar kazo gidan Imran inaga jikin ya motsa yau,  "subahanallahi, to ganinan zuwa,"cewar doctor Anwar RANGAS TARAM...



 Cikin ƙanƙanin lokaci Barrister Sudais ya ƙarisa gidan nasu, ba suyi wani mata lokaci ba sukayiwa Ammy sallama suka ɗau hanyar Rugar.



"Washe baki Malam Bukar ya yi jin cewa Maryama ta shirya karɓar auran da zai mata, cikin farin ciki ya nufi gidan yayan nasa domin cika mata burin ta nason magana da Bello.



"Miye kikeson fadamin??? Bello ya tambayi Maryama dake tsaye a gefen sa........ Magana sukayi sosai kafun sukayi sallama ta shige cikin gidan zuciyar ta cike da fatan samun Nasara..



Gidan me gari yau sai farinciki su keyi sakamakon zuwan jikan naso, abun son kowa a Family,  wato Sudais! fadar me gari suke zaune suna tattauna yadda lamarin zai kasance bayan sayan gonakin, zasu gina makarantu da fanfunan ruwa saboda sunyi karanci acikin ƙauyen nasu,  suna cikin wannan tattaunawar megari ya dakatar da hirar har sai bayan sun dawo daga sallar juma'ah


Kofar me gari cike yake makil da mutanen wannan gari, sakamakon ɗaurin auren daza'a daura tsakanin Maryama da Bello,,, amma Sam babu alamar ango da tawagar sa,,,


Magan ganune suke tashi ƙasaƙa saboda jin shiru har kusan 3:10  amma shiruuu kakeji, isowar megari dasu Sudais shiyasa ke hautsina wajan taron,  bayan megari ya ji komi yakira mahaifin Maryama danjin lafiya har wannan lokaci babu tawagar ango??? Wata wawuyar juyace ta ɗebi Barrister Sudais jin cewa auran Maryama masoyiyar sa tun yarinta za'a ɗaura da wani......



Writing by ✍🏻✍🏻✍🏻


Oum shaheed😍😍



Comment and share 🙏🙏🥰🥰😍

Post a Comment for "Inda Rai 3"