Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Inda Rai 18-19

 *INDA RAI*.....🥰🥰



*MARYAM ABDULLAHI*




  💔💋Oum Shaheed  💔


   *Daga ƙungiyar, ko da kuɗinka....*


    

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*💋💋✊🏼




*Page     18 - 19*




Sosai  Alhaji Aminu ya girgiza jin abun da doctor ya ce, Allah ya yi wa ɗansa Raheem rasuwa,, innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, kullu'nafsin'za'ikatul'maut. Sosai ya shiga firgici, lalle Allah abun tsoro ne, dam yaji ƙijinsa ya buga tunawa da ya yi da matarsa Hajiya Balkisu, yanzu ta'ina zai fara faɗa mata wannan maganar.?

 

Duk da kasan cewarta mace mai tawakkali yasan dole mutuwar zata bugeta sosai, amma dole su ƙarɓi hakan, tunda suma zaman jiran ta su ke yi, haka ya mi ƙe jiki a san yaye ya fi ce daga office ɗin.


Yana barin office ɗin ya ci karo da Alhaji Auwal yana jiransa, dan tunda likita ya nuna sama shi a matsayin mahaifi ga mamacin ya ke so su haɗu ya nemi alfarmar ya ba shi zuciyar gawar ɗansa a sawa ɗansa Imran.


Da sauri ya nufesa har sai da Alhaji Aminu ya ɗan tsorata, kama hannusa ya yi ya riƙe gam, sannan cikin raunin murya da nuna buƙatuwa ya ce masa," dun Allah bawan Allah ka taimaka mini da zuciyar mamacin ɗanka, za'a sawa yarona da ke kwance rai a hannun Allah, sake danƙe masa hannu ya yi kamar zai ɓalla, kallon mauhakaci Alhaji Aminu ya hau yiwa Alhaji Auwal, lalle wannan mutumin ya samu matsala a kansa, wataƙilma mahaukaci ne, in ba wanda ya rasa hankali ba ta ya zai yadda a cire zuciyar ɗansa, kuma mamaci.?


"Fizge hannunsa ya yi ya kalli cikin idanunsa sosai, ji ya yi zuciyarsa ta buga da ƙarfi, idan dai ba idanunsa ke masa gi zo ba ai wannan shine silar duk wani hali na wahalar rafuwa da ya shiga shida ƴar uwarsa, wanda hakan ya yi silar gusar masa da hankali har tsawon lokaci, tabbas lokaci ya yi na ɗaukar fansar abun da ya musu shida ƴar uwarsa ɗaya tilo a duniya, murmushin gefen baki ya yi ya ce, "ko da ɗanka zai mutune, ko da zuciyar ɗana ne kawai ya rage a duniya, wallahi sai dai ya mutu, da matuƙar mamaki Alhaji Auwal ya ke kallon Aminu, mai ya ke nufi,? wannan ai rashin imanine, to ko tabbas zai nuna masa ƙarfi iko, "zan sa a cire mini zuciyar ɗanka koda ba ka so, nazo gare ka ne bisa umarnin likita bawai dan babu yadda zanyi ba, zaka gani, har juya zai ta fi Aminu ya ce, "kar kayi magana kamar yaro, a lokuta da dama abun da mu ke buri daban, abun kuma da ya ke kasan cewa damu daban, muzuba ni da kai, allura ta na gaf da tono garma Alhajin yara, cakkk, Alhaji Auwal ya ja ya tsaya jin sunan da wannan mutumi ya an ba ce shi dashi, Alhajin yara, hasbunallah.



Da mutuƙar mamaki Maryam ta bi bayansu da kallo, mai hakan ya ke nufi,? duk iya tunaninta ta kasa gane mai hakan ya ke nufi, haka ta ja jiki ta kuma ciki, kwanciya ta yi a gado jin wani sabi zazzaɓi na rufar mata, gefe ɗaya kuma tashin zuciya, ga shi ta gagara yin amai ko zataji sauƙi, kuka sosai ta hau yi tunawa da ta yi da Innarta abun son taa, Allah ya jiƙanki da rahma Innata, nayi kewarki sosai, haka ta kusan wuni a kwance, sallah kawai ke ta da ita.



Sosai Mimi ta shiga tashin hankali jin mutuwar ɗan nata, ta yi kuka ta masa addu'ar da ce wa, Amrish kan sai da Abee ya sa aka mata allurar bacci, dan gaba ɗaya ta ruɗe jin mutuwar ɗan uwanta ɗaya tilo a duniya.

Sai daga baya Abee ya ji ashe sun ce musu burkin motar akayi, saboda wani bincike da su kayi akan wani Alahji da ya kewa ƴa'ƴa mata fyɗe, haka ya bar maganar a ransa gudun sake ɗagawa iyalin nasa hankali, amma ya yi alƙwarin bin ciko ko su waye masu wannan alhakin.



Hankali a tashe ya ke sanar wa likita mahaifin yaron ya ƙi yadda ya basu zuciyar, amma yana nai man alfarmar nawa likitan zai sayar masa da zuciyar ba tare da sanin su alhlin yaron ba,? likita fa ya ci ga tashin hankali, ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ai kuwa zai karɓi wannan kasadar, "na amince Alhaji, ce war doctor, ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe kana ya saki wani munafukin murmushi,shegiya naira, ka taimaki kanka, ya fi ce zuwa ɗakin da aka kwanta da Sudais dan ganin ya nashi jikin, likitocin da ke kula dashi sun bashi tabbacin zai iya farkawa ko zuwa gobe ne, amma in bai farka ba sai dai a fita dashi waje.



Murmushi Aminu ya yi bayan gama jin bayanin da likita ya masa, kenan ta haka ya ɓullo kuma, yanzu wasan zai fara, bayan ya bar office ɗin ya ɗaga waga ya kira surukinsa, bayan ya gama shaida masa kumi, sai ya tambayesa wa ye daga cikin yaran nasa,? ina fatan dai ba Imrana ka ke ƙoƙarin hanawa zuciya don ce to nasan ran ba,? kasani idan Imran ya rasa ransa ta wannan sanadi na hana masa zuciyar ɗanka to bazan taɓa yafe maka ba, sannan kaima bazaka yafewa kankaba, kafun komi ka fara tunani tukunna, kitt ya katse kiran, tabbas ya gamsu 

 bayanan surukinnasa, to ma wa ye ba lafiya cikin yaran.?


Aunty da wannan damar ga kamata ki yi amfanin wajan cika burinki, idan kuma ki ka sa ke har kika rasa wannan damar to zakiyi dana sani, dan ban ga ya in da zamu samu nasara ba. hmmmmm Mommy ta ja ajiyar zuciya, gaba ɗaya ta rasa mai ua kamata ta yi, ua zama dole ta yi amfani da wannan damar ta kawar dashi domin cikar burinta.



Yanzu kana nufin nan da awa goma idan bamu samu zuciyar ba zan rasa ɗana? why not musamu na sayar wa mana ko a wani asibiti ne,,, "zan baka zuciyar ɗana", a tare suka juya jin magana daga bayansu, ƙarisa shiga Aminu ya yi ya samu waje ya zauna ya kalli doctorn ya ce, "na amin ce ka cire zuciyar ɗana ka sa wa ɗansa, amma da sharaɗi, "miye sharaɗin,? "zai auri ƴata bayan komi ya dai daita.



What, amma ba kada hankali, ta ya zan aurawa ɗana aure da ƴarka,? "idan baka amin ce ba a bashshi kawai, wani ɗan tunani Alhaji Auwal ya yi kafun ya sake murshin da babu wanda ya lura dashi ya ce, "na amin ce.



*KUMIN AFUWA WLH YAU BAN ZAUNA BA SAM, MU HAƊE GOBE IN SHAA ALLAH*🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼💋

Post a Comment for "Inda Rai 18-19"