Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Inda Rai 16-17

 *INDA RAI*....🥰🥰



**MARYAM ABDULLAHI*


 💔  Oum Shaheed 💔



   *Daga ƙungiyar, ko da kuɗinka sai da rabonka*✊🏼✊🏼


   *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*💋💋



*Page    16 - 17*



Sannu a hankali ta ke sauƙowa daga cikin jjrgin  cikin izza da sanin ƴan cin kai, matashiya ce mai kimanin shekaru ashirin a duniya, kyaykyawace ajin ƙarshe, tana sanye da      riga da wando ta ɗaura top akan ƙaramar rigar dake jikinta ruwan milk, ta yane kanta da wani ƙaramin  gyale kalar wandonta brown, sai wani ɗan iskan glass daya kusa rufe mata rabin fuska, daga gani bazata ɗau raini ba.


"Da gudu Amrish ta nufo iyayen nata, kai tsaye ga mahaifinfa sai washe baki ta ke yi kamar ba ita ce yanzu fuska a ɗaure ba.


Oyoyo my life, ta manna masa kiss a kumatu, sannan ta sake sa ta nufi Miminta amma sai ta juya mata baya, "oh sorry dear, ita ma ta manna mata kiss ta sake juyawa ta kalli Alhaji Aminu ta ce, "Abee me kake bawa Mimi naga ta yi wani fresh kamar sabowar amarya, ta ƙarisa maganar da juya fararan idanunta, dariya Abee ya yi ya ce, "tambayeta zata miki bayani ƴar Abee, hararar wasa Mimi ta masa sannan ta kama kunnen Amrish, ta murɗa ta ce, "to rasai  kin dawo ai, wu ce muje gida da'alama yau baki gaji ba tafiya tayi daɗi.


A cikin motar ma labari ta ke basu na wani guy daya ce yana sonta acikin jirgi, faɗi ta ke Abee guy ɗin ya haɗu sai dai ya cika kallo, ta juya idanu ta yarfe hannu kamar har lokacin yana gabanta, surutu sosai ta kewa iyayennata har suka ƙarisa gida bata yi shiru ba.


Ma'ai kata sai kawo gaisuwa suke amma Amrish ko kallo basu isheta ba balle suyi tsammanin zata amsa musu, Mimi ta ce wai bakiji ana magana bane kan Amrish,? kaɗa idanu ta yi wanda hakan al'adar ta ce, "wlh shiyasa bana son zaman Nogeria, sam babu ƴanci, to yanzu dole ne saina kulasu? idan takura mini za'ayi to fa zuwa gobe zan juya Jamus, "ki sani haramunne wala ƙanta ɗan adam, ina lafin a kulaka, "Mimi bazaki gane waye mutum ba, suma badan Allah sukeyi ba aikinsunne, da yanzu niɗin ba kowa ba ce babu mai kulani a cikinsu balle gaisuwa da girmamawa, fuuuuu ta wu ce ɗakinta ta faɗa toilet, a al'adar Amrish idan zatayi wanka sai ta cire kaya tun a bedroom, sannan ta wu ce toilet, kuma haka zata fi fo a cewarta bazata iya saka abu a jikinta ba bayan ta gama wanka, bayan ta fi to mai kawai ta shafa sama sama kasan cewar bata shirinda zafi ko kaɗan, shiryawa ta yi cikin riga da wanda kaf kayan Amrshi babu atamfa ko ɗaya, har gara dogin riguna tana sawa sa'i da lokaci.


"Cin abin cin ta ke yi kamar bata so a yangace kaɗan ta ci ta kalli Mimi ta ce Mimi ina yaronki ne,? naga ban jishi ba har yanzu. Abee dake kai lomar abinci ya ce ai ya kuma bakin aiki jiya, kiran gaggawa ya samu daga can zai wu ce JUMETA.



Likitoci biyar ne a kansa suna ƙoƙarin dai dai ta bugun zuciyarsa, sunfi awa biyu akansa kafun suyi nasara komi ya zama dai dai, fi to wa babban likitan ya yi yana sharce gumi, da sauri suka ƙarisa garesa suna tambayar ya Imran ɗin,? "ku biyoni office. Acan yake shaida musu sunyi nasarar saita bugun da zuciyar ta keyi, amma akwai matsala, Mommy dake kuka tun badinsu gidan ta cewa doctor pls kar kabari na rasa yarona, shine farincikina, kuka take sosai, "likitan ya kalleta cike da tausayawa halinda take ciki, "ki kwantar da hankalinki Madam, a yanzu mungama iya namu aikin, sauran kuma yana gareku, da sauri Sudais da Mommy suka haɗa baki wajan cewa, "ka faɗa mana mai ya kamata muyi, a yanzu ba sai anjima ba,amuyi domin ceto rayuwarsa, Sudais ya ɗaura da faɗin, "koda kuwa zan rasa raina wajan ganin na ceci tasa rayuwar ne, doctkr taimaka ka faɗamin, ya ƙarisa maganar zuciyarsa na ɗagawa da sauri sauri, ganin yadda hankalinsu n ya tashi sai doctor ya ce su bari zuwa anjima zai musu bayani yanzu akwai rusults ɗin dasu fito ba. 

Badan sun gansu da bayaninsa ba suka fi ce zuciyar ko wanne fal da tunanin mafita. 



A can gida kuwa tun bayan ihun da Maryama taji ta farka daga bacci jin har cikin kanta ihun ya shiga, samun kanta ta yi da kasa motsi har sai da taga, Sudais ya fi ce hankali a tashe sannan tasamu zarafin miƙewa, shin waye wannan da aka fita dashi yana aman jini,? tabbas koma waye yana jin jiki, jiki a mace ta nemi kujera a falon ta zauna, sai tunani ta ke yi waye wannan,? jitayi zuciyarta ta yi wani wawan bugawa tunawa da da tayi da yayan Sudais da Samha ta bata labari, subhanallahi, Allah yasa ba shi bane, ta ke taji hankalinta ya tashi, addu'ar samun lafiya ta tsinci kanta da masa.




"Innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un, shine kalmar da Abee ya ke ta maimatawa ya kasa ce wa komi, daga ɗaya bangaran har ya gajinda magana ya kashe wayar, "Mimi da fitowarta daga kitchine kenan taji yana rafka salati, ƙarisawa ta yi da sauri tana tambayarsa lafiya,? Amrish ta ƙariso suka haɗu suna tambayarsa, da kyar ya samu kalmar suka fito daga bakinsa.


"Waya akamin yanzu Raheem ya samu accident a hanyarsa ta zuwa jumeta, salati suka ɗauka a tare suka sauƙe suka sake ɗaukar wani, gaba ɗaya sun kiɗime sun ruɗe, Amrish ce ta yi ƙarfin halin cewa Abee yana ina yanzu, a wanne gari ya ke yanzu,? "yana asibitin murtala da ke kanon dabo take suka hau shiri a gaggauce, Abee ya kira danjin ko za'a samu jirgin da zai tashi zuwa Kano, sunyi sa'a akwai mai tashi nan da minti arba'in.



Zuciyar Daddy ta buga da ƙarfin jin cewar zuciyar Imran ta kumbura sai ammasa dashen zuciya, gumi sosai jikinsa ki fiddawa ta kowacce kusurwa, tashin hankali wanda ba'asaka masa rana, taya zai fara sanar da Mommy wannan labarin,? sunan Allah ya ke ambata har yafara samun sauƙi a ransa.


"Yanzu ya ka ke ganin za'ayi doctor,? a'ina zamu samu zuciyar mamacin da bai haura awa uku da mutuwa ba,? taya idan aka samu ahlin mamacin zasu amince subamu.?


"Wannan kuma ya rage naku Alhaji, mudai mun gama namu.


Hankali a matuƙar tashe Daddy ya ke sanar dasu halin da'ake ciki, Mommy najin wannan lamari ta yanke jiki ta faɗi a sume, Sudais kuwa mutuwar tsaye ya yi kamar an dasashi, cewa ya ke "Daddy a cire tawa a saka masa, karku bari na rasa ɗan uwana ɗaya tilo a duniya, nasan miye matsalarsa, nasan abun da ya ke so, zan bashi, zan sadaukar masa da ita, Daddyyyy!!! shima ya faɗi yirif kamar gawa,,, gaba ɗaya Daddy ya kiɗime ya rasa ta'ina zai fara, zuwa akayi a ɗaukesu zuwa E/C don basu taimakon gaggawa, wannan tashin hankali da me ya yi kama.? 


Dai dai wannan lokaci da Daddy ya ke neman zuciyar matacce aka zo aka wuce da wasu bayin Allah sun samu hatsari a hanyarsu ta zuwa JIMETA, kuma ga dukkan alamu akwai gawarwaki a ciki, hamdala ya yi a ransa ganin komi zai zo masa da sauƙi in har kuɗi sunada rana to yau zasu masa gurin ceto rayuwar ɗansa guda daya tilo.


An samu nasarar ceto Mommy daga suman da ta yi amma ammata allurar bacci saboda ta samu hutu, amma har yanzu Sudais bai farka ba, ƙarin tashin hankalin shima ana ganin ya samu matsala a tasa zuciyar, kalu innalillahi, Daddy ya haɗu da tashin hankalin da rabon sa dashi tun mutuwar matarsa ta farko, zama ya yi yana so ya yi kuka ko zai sassauci a zuciyarsa amma sam ya ƙi zuwa saima ji da ya yi numfashi na ƙoƙarin masa wahalar shaƙa.


Maryama ce a toilet sai ƙaƙarin amai ta keyi amma babu abun da ya fito, kasan cewar babu komi a cikinta, rabonta da acinci tun wanda Sudais ya bata jiya, sosai tasha wahala kafun ta samu da kyar ta fito zuwa falo, zata wu ce kitchine ta ji muryar Sahla tana magana cikin kuka, har zata wu ce sai ta samu kanta da tsayawa ta ji abun da ke faruwa, jin Sahla ta yi tana shaidawa Ammi rashin lafiyar Imran da kuma halin da Sudais da Mommy suke ciki, kaɗan ya hana ta kai ƙasa jin wani jiri na kwasarta ta yi saurin jan jiki ta bar wajan jin Sahla na ƙoƙarin fitowa, ɗaki ta kuma ta ma manta abun da ya fito da ita, kuka Maryama takeyi sosai jin halinda mijinta ya ke ciki, ta ɗauki dogon lokaci tana addu'ar samun lafiya ga wannan ahli ta ji motsin Samha ta zo ɗaukar abinci da sauran abubuwan buƙata, da sauri ta shirya don gara ta je taga halin da mijinta ya ke ciki, tana fitowa ta nufi Samha da Sahla da ke ƙoƙarin fita ta bisu a baya tana cewa Samha ta jirata su wu ce tare, cak Samha ta tsaya dama kuma abun da ta ke gudu kenan, "kiyi haƙuri Aunty Maryam Mommy ta ce kada ki yadda kije asibiti ko ta halin ƙaƙa har sai ta baki umarnin hakan, Sahla taja  tsaki suka sa kai suka  barta baki sake kamar doluwa.


"Bangane mai kake nufi doctor, kana nufi  ɗana ya shiga COMA.



*WRITEEN BY OUM SHAHEED*🥰🥰🥰🥰

Post a Comment for "Inda Rai 16-17"