Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Aunty Book 1 Page 69

BOOK 1

Page 69

A rude Tahee ta dafe cikin ta , da wani irin shock take kallan Ammeey, kallo na tsantsan tsana , idan kowa yace zai ce Ammeey zata yi wannan abun bazata taba yadda ba sabida


yadda ta nuna musu ‘kauna tun suna ‘kanana , bata gama shiga Rudu ba sai da taji muryar Ammeey ,” zaki yi tunanin ina sanku ko, toh babu Wanda na tsana a duniya kamar ku, sau dadama da na fara gina masarauta ta kune kuke ruguzamun, shiyasa nayi al’kawarin ruguza duk Wanda yayi ‘kokarin ta’bamun masarauta, bama ke ba koma wanene yayi gigin shiga gonata sai na kawar dashi. Ada nayi tunanin ‘kyaleki amma sam sai naga kin fu kowa za’kewa a cikin su wanda shine babban kuskuren da nayi na shigo dake cikin a halin nan,azato na baki da wayo,Aushe sam ba hakan bane , bana kawo ki gidan nan dan ki zauna cikinsu bane , na kawo kine dan ki ‘karasa aikin da na fara , na kawo kine ki kashe mun tahnoon , Wanda kike i’kirarun mijin ki a yanxu “. Cikin rud’ewa Tahee ta soma binta da idanuwa, gabaki d’aya jikinta rawa yake , jin maganganun ammeey take kamar a mafarki ko a cikin wani film da ba gaskiya ba ,”Ni na kashe mijina , bazai yuwa ba , mijina fa , kisa “, abunda Tahee take faman nanawa a cikin ranta . Ta sowa Ammey tayi daga kan kujerarta fuskarta babu ko alamun fara’a, Daidai inda Tahee take a zaune ta tsugunna itama tana bin fuskar Tahee da wani shu’umin murmushi,hannunta d’aya ta d’aga zata ta’bata Tahee tayi saurin bige mata hannu hawaye na sakkowa daga cikin idanuwanta, a zuciye Ammeey ta janyo kanta ba imani ta tsinkawa Tahee mari , cikin ‘kunar rai ta cigaba da magana “ idan kikai kuskuran musa mun abunda zansaki to ki tabbata yanda na kashe mahaifinki haka zan kashe mahaifiyarki da d’an uwanki, sannan na dawo kanki Keda abunda ke cikin ki da dole sai ya fita ko kina so ko ba’kyaso dan King nawane ni kadai, bazan ta’ba yadda wata taso abunda na dad’e inaso ba “. A zuciye Tahee take kallanta zuciyarta harwani tafarfasan ba’kin ciki take , cikin kunar rai ta d’aga hannunta da suke faman yi rawa tana nuna Ammeey, murya a sha’ke Tahee ta soma magana “ kece kika kashe mana Abbu dama, kece kika sa ayiwa Abbu yankan rago, duk tsawan wannan lokacin da sa hannunki a ‘batan Oumma da Taheer ?me mukai miki ?lefin me iyayena sukai miki da zaki sakamusu ta wannan hanyar?”mi’kewa tsaye Ammey tayi batare da ta damu da amsawa Tahee amso shin taba ,Wani ruwa da ta gani akan center din kujeran ta d’auta,cikin sakin murmushi ta soma magana “bani da lokacin amsa miki wannan tanbayoyin naki,amma kamar yadda nasha Alwashi , duk wanda yayi gigin tarwatsamun burukana toh kamar ya tarwatsa rayuwarsane, kamar yadda na salwartar da ran ubanki, na tarwatsa ahalinki, sannan na kashe miki d’an uwan mijin ki, na raba tsakanin uwa da d’a , bani da wani sai na cikar burukana da yayi saura yanxu kuma kece mukullun Karshen cikar burina , zan baki d’an kwanaki biyu , ki salwartar da abunda yace cikin ki sannan da ki kashe mijinki, idan ba haka ba ki fidda rai da kara ganin ahalinki har Abadah,”Tana kai karshen zancanta Ammey ta bar d’akin tana sakin wani shu’umin murmushi . “Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni karyan minha, Ya Allah kaga baiwarnan taka, Allah kai ne Wanda kace mu rokeka, Allah kaga wannan baiwa taka , Allah ka nuna ikonka akan bauwarka,” ta karasa zancanta tana sakin wani kukan bakin ciki, kukan da ta dad’e batayi irinsa ba , ace maka shin ka yana kusa da kai Wanda ka Amin ta dashi ka basa yadda yazamo shine makashinka, “Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un “,gabaki d’aya Tahee ta rasa Wana irin tunani zatayi sabida yanda komai na tunaninta ya tsaya mata , ji take komai da yake faruwa kamar a mafarki ne ba a zahiri ba , Wacce ta nuna masu so Itace maka shin mahaifinta , wani irin tsantsan tsanace taji tana yiwa Ammey da ya kore duk san da take mata , ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta lokaci guda , da kyar idanuwanta suke buduwata , a hankali ta lallaba ta nufi dakinta ko kallan gabanta batayi sosai , bata tsaya a ko ina ba sai kan gadonta, lokaci d’aya zazzabi da ciwon kai ya rufar mata daya sa wani irin bacci mara dadi ya d’auketa me cike da mafarkai.

***** 2:30pm ta farka daga baccin daya kwasheta tana karanto adduar da tazo bakinta , lokaci d’aya abunda ya faru d’azu ya shiga dawo mata cikin kwakwalwarta, tabbas d’an Adam butulune, sallahr azahar ta gabatar tana mika ka Allah kukan ta tare da adduar neman tsari daga Sharrin Ammeey da masu hali irin nata , a hankali kuma wasu zafafan hawaye suka shiga sakko mata cikin kwayar idanuwanta tuno irin yankan ragon da akai wa abbunsu, gashi bata san Wana hali oummanta suke ciki ba , a d’aya ‘bangaran kuma tana tsoran halin da mijinta zai shiga idan yasan wacece ta kashe masa d’an uwa , macen da ya d’auketa kamar mahaifiyarsa, macen da tafi mahaifiyarsa kusanci dashi , rana d’aya ya fuskanci Itace makiyarsa , “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un “,Na barki da Allah shi kadai yasan yanda zaiyi dake cewar Tahee tana goge hawayen fuskarta , a d’ayan ‘bangare na zuciyarta kuma ta sha alwashin sai ta tonawa Ammey a siri ko ta halin ‘ka’ka . Bata jin yunwa shiga bata yi abinci ba , sai ma addu’oi da ta du’kufa yi na Kariya a gareta da abunda yake cikinta . Yinin ranar gaba’ki d’aya cikin ‘kunar rai tayi shi , sai ma kokarin sassaita fuskarta da tayi gudun kar ya dawo yaga mood d’inta ya canza.

✨✨✨✨

Karfe 8:40pm king ya shigo part d’insa lokacin har Tahee ta kammala komai na ta ,ta saka wasu kayan bacci masu matu’kar d’aukar hankalin, gabaki d’aya kayan jikinta ana ganin surar jikinta,cikin wani irin salo ta karasa Wajansa tare da hugging d’insa , shi kansa king saida yayi ajiyar zuciya ga idanuwansa da ya fara canza kala zuwa kalar ja musamman yanda cikakkun breast d’inta suka ta’ba masa kirji, medium size jug d’in hannunsa yayi saurin dam’kewa , d’an d’age Tahee tayi kafun ta sakar masa peck a kumatunsa , cikin disashewar murya ya furta “ welcome back baby “, be amsa mata ba sai ma face d’inta da ya bi da kallo,” me yasa face d’inki tayi Jaa, are you okay ?” Saurin kawar da kanta gefe tayi tana kara saisaita face dinta , cikin yar shagwaba ta furta “ bakaine ka’ki dawowa ba , kuma babynka suna so su ganta , yaufa kamanta da mu gabaki d’aya ta ‘karasa kamar zata saka masa kukan shagwa’ba,”oh my god, zaki kasheni da wnnan salad naki ,okay dadyn baby yayi lefi ayi masa hakuri and anjima zamu gaisa da baby ai ko ?” Ya karasa yana kashe mata ido d’aya , kawar da zancan tayi ta hanyar karban karamin jug din hannunsa “ Menene wannan ?”, kallan jug d’in yayi kafun ya furta “ kunun aya Ammey tayi mun”, yana kai karshen maganarsa jug d’in na subucewa ya fad’i tass, gabaki d’aya ya tarwatse sai yar kwalbar da ta saukar wa Tahee a ‘kafa, kuka ta fashe masa dashi, cikin rud’ewa ya d’auketa yayi bedroom dinsa da ita , atunaninsa kwalbar data caketane amma ita sam ba haka bane , kukan bakin ciki ne yazo mata ganin saban Salan iskanci Ammey wato ta basu kunun aya su mutu.

 

#MANAGE PLEASE 🙏
GIDAN AUNTY

07041879581
MSS LEE 💖

Post a Comment for "Gidan Aunty Book 1 Page 69"