Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Aunty Book 1 Page 68

Book 1

PAGE 68


Direct yana shiga cikin asibitin ta baya yayi parking, da Sauri ya daukota ganin yanda jinin da yake zuba a jikinta har yanxu be tsaya ba, office dinsa na sama ya hau kai tsaye bayan ya bada umarnin a kira masa Dr Maryam, tunda kafun ta karaso ya tsayar da jinin, tana zuwa be jira ta cewar ta ba suka fara aikin duba Tahee , gabaki d’aya fuskarsa tayi jawur jijiyoyin kansa sun tashi, cikin

ikon Allah suka gano matsalar, tare da d’aure mata mahaifa sabida yanda wajan yayi rauni, saida ya tabbatar komai yayi settling kafun ya sauke a jiyar zuciya , test d’in da ya umarci Dr maryam tayi masa ne ta kawo masa , akan gadon sa dake cikin dakin office d’in take , a hankali ya kara murza hannunta cikin nashi kafun ya sauke idanuwansa kan kyakkyawar fuskarta da yi fayau da ita, hannunsa d’aya ya d’ora kan cikin ta yana shafawa a hankali , cikin ranshi kuma wani irin tafasa ransa yake, gabaki d’aya jijiyoyin kansa sun mike tsaye , launin idanuwansa sun sauya daga ainahin kalar su zuwa wani kalar launin ja daban, be san wanene yake gangancin ta’ba masa ciki ba , shikansa be san Wana irin hukunci zai yiwa Wanda yake ‘ko’karin salwantar masa da ciki,sunan Allah ya fara nanatawa aransa ganin yanda ransa yake ‘kara baci , yana dad’e a zaunan da yake yana karanto duk adduar da tazo masa rai kafun ya fara yiwa Tahee addua itama .

Agogon hannunsa ya duba almost past 10, allurar baccin da yayi mata har yanxu be sake taba , Sabida ba ‘karamin jigata tayi ba , Sabida maganin da akai anfani dashi ba’karamun illane dashi ba da kai tsaye yake kisa, forehead d’inta ya sun bata “ am really sorry Angel “, kafun ya dakko phone d’inshi,a haroon ya kira a waya, cikin wata irin zabura haroon ta sakko daga kan gado ganin kiran King abunda bai ta’ba faruwa ba , safa da marwa ya fara gumi har ya fara tsatstsafo masa , yana d’aga kiran tunkan ya fara bawa king hakuri ya ji saukar muryarsa, “Number ihsan”, kittt ya kashe wayar tasa, tazo idanuwa haroon yayi, Allah yasa yarannan ba lefi sukai ba, gudun karya yi wani kuskuren yasa yayi saurin tura masa number ihsan ba ‘bata lokaci.

Daidai lokacin da king ya kira number ihsan , a Daidai lokacin ne ta fito daga part d’in ammeey zata koma part d’insu, sabuwar number da ta ganine yasa ta share kiran kamar katta d’aga , sai wani zuciyar ya ce mata ta d’aga , tun kafin ayi magana zuciyarta ta soma dukan uku uku, “ where are you “, taji saukar muryar king, da mugun sauri ta cire wayar a kunnanta kafun ta mayar murya na rawa ta furta “ na fito ne zan koma part d’in mu “,shiru yayi kamar baze ce komai ba sai kuma taji saukar muryarsa “ wanene ya kawo mata abinci”, ta gane Tahee yake b
Nufi shiyasa tayi saurin bashi amsa “ Ummey ce tace na kawo mata”, wani irin harbawa zuciyarsa yayi , besan lokacin da ya furta “ wacce ummeyn”itama amsa ta bashi da “ummeynka “ yanxu kam runtse idanuwansa yayi, me Hakan ke nufin ,”ummey, no”, kusan 2 minutes be ce komai ba ta d’auka ya kashe , itama har zata kashe cikin wata iriyar murya ya furta ,” kije ki bawa zaki kwanukan abincin, and ki gyara wajan, don’t said anything to anyone ko wanene , okay “, da Sauri ta furta “ insha Allahu yaya”,. Cikin sauri sauri ta nufi part d’insa zuciyar ta har ta fara bugawa itama , tana shiga ta tarar da uban Jinin da Tahee ta zubar, a mugun rud’e take bin wajan da kallo ga abincin da ummey ta bata . Da Sauri ta d’akko jakar zuba abinci ta had’a kayan abincin , Kafun ta kaiwa zaki dake waje , tana dawowa Jinin ta fara gyarawa kafun ta gyara falon, har yanxu zuciyarta be dena bugawa ba , fatan ta Allah yasa Tahee lapiya take. Saida ta tabbatar komai ya gyaru kafun ta kulle musu part d’in ta nufi nasu duk jikinta yayi sanyi.

Duk wannan abun da yake faruwa babu Wanda ya sani a cikin gidan, zaki na kawo masa kayan abincin yasa akan bin cika masa su, tabbas kuwa a cikin su maganin yake , wani irin zazzafan zazza’bine ya fara kamata , gabaki d’aya ya rasa Wana irin tunanin zaiyi , yana ganin kiran Ukti amma ya kasa d’aukan kiran nata, sai bin Tahee yake da kallo ,har yanxu ya kasa gasgatawa, yana cikin tunanin da ya fad’a Tahee ta soma mutsu mutsu da ido, har ta ware kumburarrun idanuwanta kan kyakkyawar fuskarsa da ya du’kar ‘kasa “ sweetheart “ ta furta a hankali kamar me rad’a , da Sauri ya d’ago rinannun idanuwansa da suka canza kala, cikin sauri ya ‘karaso inda take “ are you okay “, shima ya furta mata kamar me rad’a , kanta kawai ta girgiza masa alamar eh, ahankali ya furta “ Am sorry “, rufe masa baki tayi da tafin hannunta “ Ni bakayi mun lefun komai ba , Babyn mu?” Ta tanbayeshi duk da shakkar tanbayar da tayi masa , kallanta yayi for second kafun ya furta “ he’s safe too” ajiyar zuciya ta sauke da har shi da yake kusa da ita sai da yaji,duk da bata da wani ‘karfi sosai a jikinta akan me hana ta kamo hannunsa ba tana shafa gefen fuskarsa “ wannan face d’in fa ta canza ba haka na santa ba “, rungumeta kawai king yayi a jikinsa ya kasa magana jiya ke kansa kamar zai tar watse, har sai da ya samu nutsuwar da yake bu’kata kafun ya raba jikinsu “ Sleep !! Okay “, da d’an mamaki Tahee ta kallesa tasan dai nan ba gidan su bane duk da ‘kamshin da ya karad’e ko ina na d’akin hakan be hana ta jin wari asibiti ba, “ bazan iya bacci ba , bana san warin asibitin nan kamar zan yi amai”, but har yanxu jikinki ba’kwari , “ Dagaske nake yanxu bana jin ciwon komai , inna cigaba da shakar warin asibitin zan iya amai fa “ ta fad’a tana ‘karasa turo masa ‘karamin bakinta , kansa kawai ya jinjina mata kafun ya temaka mata har zuwa cikin motar yana ri’ke da hannunta, saida ya tsaya a ocean basket yayi mata order d’in abunda zataci kafun su koma gida . Bai zaunar da ita a kasa ba da kansa ya d’auketa ta cikin lifter ya kai ta master bedroom dinsa , sai da ya tabbatar tayi wanka kafun ya fara bata abuncin da suka taho dashi, duk yanda take ce masa ta ‘koshi saida ya sata ci kafun ya bata wani magani ta sha , ba jimawa bacci ya d’auketa. Tunanin abunda ya faru yake har yanxu ya kafada fita daga cikin kansa , ga wani irin lafiyayyan ciwan kai da ya haifar masa , duk yanda ya so runtsawa abun gagara yayi sai wajan 2:40 kafun bacci ‘barawo ya sace shi.

Ana kiran sallahr asuba ya farka , sabida tsananin yanda kansa yake ciwo bai je masallaci ba yau a gida yayi sallahn shi ganin Tahee na kokarin saka damuwa a ranta ne yasa shi cire komai ya mayar dashi gefe dan kansa ya fara kula da ita , tun daga kan abincin da zataci , da kanshi yake fita ya kar’bo mata order d’in duk abunda take so ko ya kira ihsan ta girka mata. Kwana biyu da rashin lapiyar ta jikinta har ya murmure ta dawo normal sai wani ci kowa da ta karayi na musamman , Tunda abunnan ya faru Tahee bata ta’ba kawo wa ranta cewa ummey ta mata abu ba , duk da tasan tana gama cin abinci cikinta ya fara mata ciwo , ga Tamar dar king your husband da take samu har yanxu, ta ‘bangaran king shima har yanxu be ce komai ba akai ba , amma ga baki d’aya mood d’insa ya sauya , wani irin miskilanci ne ya ‘kara shigarsa , Tahee ce kadai ke iya controlling kayanta .

Karfe 3:02 biyu Tahee ta nufi part d’in dada ganin kwana biyu bata le’kasu ba kuma har yanxu basu san abunda ya faru ba, Tana shiga kuwa dada na damun fura, cikin washe baki ta karaso wajan dadan, “ Nazo a Daidai kenan , yau zansha furan dada “, murmushi dada ta sakar mata “ kamar kinsan kuwa ke nake damawa , wancan tanbad’ad’d’an mujin naki da ke kadai zaki iya naga sai faman shan kamshi yake kwana biyu, ko taya kuke rayuwa oho”, tana karasa zancanta ta mi’ka wa Tahee furar, in banda murmushi da Godiya ba abunda Tahee take wa dadar, sosai ta sha furarta har su ihsan suka shigo cikin falour suka cigaba da hira, kamar daga sama amrah ta shigo falon dadar, wayar hannunta da take dannawa ce ta su’buce mata bata san lokacin da bakinta ya furta “ Kutmar uba” da wani irin kallo dada ta kalleta ,” Wana irin shashan cine wannan sai kace nasara zaki magana ashariya “,gabaki d’aya amrah bata jin ta ban da kallan Tahee da take jikinta na tsanan ta rawar da yake , ko ta bun wayar ta batai ba ta ruga a guje tana d’ora hannu aka. Babu Wanda ya damu da halinta , inda samo kuma yaci ace sun saba, share zancanta sukai sukaci gaba da hira , a part d’in dada Tahee tayi sallar la’asar d’inta kafun ta wuce part d’in ummey. Kamar yadda ummey ta saba kar’barta yanxun ma hakance ta faru, gabaki d’aya saida ummey ta cika gaban Tahee da abubuwan ciye ciye, dukda tsananin kunyar da ummey ta sakata sai da ummey tasa ta saki jikinta sukai hirar su babu wani surukanci a ciki, kasan tuwan ummey balarabiyya shiyasa ta fuskanci Tahee sosai ta nuna mata dabarun zaman aure da yanda zata kula da cikinta , duk da kunyar ummey da taji hakan be hana ta share shawarwarin ummey da zasuyi mata anfani ba , da zata tafi sai da ummey ta hada mata kayan kwad’ayin datasa a kawo mata, tun kafin a kai mata part d’inta ta soma shan magarya tsabar kwad’ayi irin nata. Apart d’in ummey ma ta d’an jima , har ta yi hanyar part d’in ammey ganin ana kiran sallah yasa bata tsaya ba ta nufi part d’inta , sosai tayi missing ammeey kwana biyu kwata kwata bata ganin ta a part d’in dada , tana idar da sallahr ta shaf shaf ta dafa musu abinci mara nauyi, kafun ta ‘kara gyara jikinta , tana so ta shiga part d’in ammeey ganin lokaci ya ‘kurene yasa ta hakura da niyar gobe taje.

A gajiye ya shigo gidan , Kai tsaye wanka ta tameka masa yayi kafun tayi serving Dinsu , abincin ma yau Asama suka ci kafun ta d’ebo magaryar ta cikin yar karamar roba tana sha , kallan ta ya tsayayi ta kashe masa ido d’aya “ magaryace fa , zakasha ?” Tayi tanbayar tana kallansa , gyad’a mata kai king yayi alamar eh, guda d’aya ta dakko masa zata saka masa abaki ya kawar da kansa gefe, hannunta biyu tasa ta kama fuskarsa zata saka masa magaryar ya kara dauke fuskarsa “ kace zaka shafa “ ta fad’a a shagwa’be , shima kansa ya d’aga mata alamar eh kafun ya nuna breast d’inta da ya fi komai tsone masa ido , “ wannan nake so” bata bari ya kara zancansa ba ta mi’ke zata gudu yayi saurin ri’kota , “ please baby “, marairaice masa tayi kamar zatayi kuka “ ban warke bafa kamanta “,d’an ‘karamin ya’ke kawai ya saki ba tare da yace mata komai ba , a kwana biyun nan Sam ta kasa gane kansa “ meke damunka “ girgiza mata kai yayi alamar bakomai , “ kamanta al’kawarin da Kayi mun, duk abunda yake damunka zaka fad’a mun, it’s a promise, kamanta ?”girgiza mata kai yayi alamar a’ah, gefen fuskarsa ta shafa cikin kwantar da hankali ta furta “ To fad’amun , Sabida ni nafisan my old king ba wannan da baya mun fara’a sosai ba “, ita kadai ta ke shawo kansa , kallanta yayi for second , besan ta yarda zai fad’a mata ba , “ please “ ta kara maimaita masa , a hankali ya furta “ Abincin da kika ci last was from ummey, and …” bata bari ya ‘karasa zancan saba sabida ta gano me yake ‘ko’karin cewa da mamaki ta kallesa “ I thought wannan magana ta wuce , me ya kawo zancan ummey a ciki , don’t even start it , I’m fine , our baby is fine , all this days damuwar da ka sawa kanka kenan? Why?”kallanta yayi ganin ranta na ‘ko’karin ‘baci “ it’s like that baby, karki fara wannan fushin please “, gefen fuskarsa ta shafa “ it’s okay , but ka cire wannan damuwar aranka , okay?”, kanshi ya d’aga mata alamar toh kafun ta furta haaa, hakan kuwa yayi kamar yanda tace, magaryar ta saka masa a baki tana sakin dariya , d’an kad’an ya tsotsi magar yar kafun ya cire ta cikin bakinsa “ wannan baby ya koya miki kwadayi da yawa , komai ke kina ci “, gwalo kamar tahee tayi masa , tana jingine a jikinsa shi kuma yana aiki a system, tunanin maganar sa ta d’azu ne ya fa d’o mata arai, da sauri ta kawar da zancan tana anbatan sunan Allah. Ganin ta soma gyangyad’ine yasashi ajje system d’insa , adduar da ya saba yi mata duk dare ta tsari yayi mata kafun bacci ya d’aukesu manne da juna .

♾️♾️♾️♾️♾️
♾️♾️♾️♾️♾️♾️
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

BUNKURE

A cikin ‘yan kwana kin nan abubuwa da dama sun faru, a wannan lokacin sosai kaka ta bawa ta fara danasanin musgunawa su oumma da tayi arayuwa, kullum cikin ro’kar Allah take akan Allah yasake had’a ta dasu ko zasu yafe mata. Yanxu komai ya sauya agidan ganin irin rayuwar rashi da suka fara tsintar kansu a ciki. A ‘bangaran Dije kuwa kud’i takesamu, Sabida yara ‘yan matan da suke kaiwa karuwanci , sosai liyafa ta cigaba , har tsawan wannan lokaci bintalo bata ‘kara waiwayar gida ba , itama dijen yanxu kwata kwata bata damu da dawowarta ba . Kullum ‘yan gidan sai dai su zuba mata ido dan babu Wanda ya isa ya tanka mata .Gabaki d’ayansu sunyi nadamar abubuwan da sukayi wa oumma da su tahee , ganin yanda rayuwa take garasu, Dije kuwa sai saban wulakanci da ta ‘karo, ganin yanxu ita ke temaka musu, sai ta gama yi musu wulakanci san ranta kafun ta san musu abunda za su d’anci a bakinsu.

➰➰➰➰➰➰➰
Yau ta kama Thursday, har wajan karfe 9am na safe king na tare da babynsa sai faman shagwa’ba take sakar masa , yana fita d’an malele Tahee tayi , ta zauna ta shanye kayanta tass, kamar yan da tayi niya jiya , shiryawa taya cikin doguwar pink din Riga da bata kamata sosai ba , Hakanan yau ta d’auke dogon hijab abunda ta nufi part d’in ammeey, tana shiga taji wata iriyar hajijiya na kamata , cikin Sauri ta samu waje ta zauna , babu kowa a cikin falon har tsawan mintuna 10, ganin har yanxu ammeeyn bata fito bane yasa Tahee nufar ‘kofar d’akin ammey da niyar ‘kwan’kwasawa, kalaman da tajine ya matukar hautsina mata ‘ya ‘yan cikinta, gabaki d’aya ta rasa Wana irin tunanin zatayi, wata iriyar hajijiyace take kokarin kayar da ita tayi saurin dafe bango, wasu irin azababben hawaye ne suka fara sakkowa daga saman kuncinta , babu abunda ta ke nanatawa sai kalmar “Innalillahi wa ‘ inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musi bati, wa akhlif li khairan minha “bakinta rawa ya fara , so take tace wani abu amma ta kasa ga wani irin masifaffen ciwan kai da ya sakko mata lokaci d’aya , cikin fitar hayyaci Tahee ta bar part d’in , Allah ya temaketa bata had’u da kowa ba , Tana shiga cikin part d’inta ta ‘kara tarar da abunda ya hautsina mata ciki, kallan kallo suka tsaya yiwa junansu, kafun a hankali cikin wani irin shu’umin murmushi Ammey ta kalli Tahee da tayi mutuwar tsaye , “ yarinya kenan, kinji abunda kunnuwanki be kamata suji ba yanxu ,amma duk da hakan kin rage mun aiki”cikin wata gigitacciyar tsawa Ammeey tace wa Tahee ta zauna, ita kanta Tahee bata san lokacin data zube ‘kasa ba tana bin Ammeey data had’e rai da kallo. Cikin wata iriyar murya me firgitarwa ammeey ta soma magana “ bazan tsaya kwana kwana ba , bari na fito miki a mutum yanda zaki fi saurin fahimta, abunda kunnuwanki suka ji miki hakane, nice na suba maganin zubar da ciki a cikin abincin da waccan munafukar ta kawo miki” da mugun zabure Tahee ta kalleta, bakinta har rawa yake wajan furta “ AUNTY”, akaro na biyu da ammey ta kara dakawa Tahee tsawa ,karki kuskura ki kara kirana da wannan sunan,har yanxu ke yarinyace , tsawan shekaru na dauka ina Gina masarauta ta , rana d’aya kice zaki rusamun ginin da na dade inayi, tabbas shi zai janyo a jalinki, kamar yanda ya janyo ajalin sauran.GIDAN AUNTY
07041879581
Mss Lee 💖

Post a Comment for "Gidan Aunty Book 1 Page 68"