Gidan Aunty Book 1 Page 63
BOOK 1
Page 63
Suna shiga office din principal din aka kawo mata ruwa, ita abun nasu ma mamaki ya fara bata , cikin kulawa principal din me suna rose ta fara yi mata interview da kanta, itama tahee tana bata amsa cikin baiwar da Allah yayi mata, sosai madam rose tayi mamakin kwakwalwar tahee ganin yanda take amsa questions din kamar yanxun ake koya mata babu gargada, da farko tayi tunanin za a kai tahee ss1 sai da tayi mata interview taga
kokarinta ya wuce wannan class din, harta ss 2 bazea yu Asataba , Number king madam rose ta kira har sau biyu kafun a na ukun taji an dauka , a tunaninta king ne sai da akayi magana ta gane bashi bane,” At the meeting “zaki ya bata amsa daman number sace bata king ba,ganin hakan yasa itama bata bin kiran ba ta jagoranci tahee zuwa class din da aka bata wato ss3 flora, lokacin da suka shiga gabaki d’aya hankalin yan ajin ya dawo kanta ,ganin madam rose a ajin, mikewa sukai gabaki dayansu cikin zallan turanci suka gaishe da madam rose , kafin mss Afia da take daukansu Mathematician ta gaishe da principal din itama,nuna mata tahee principal din tayi kasantuwar Itace class mistress din ajin,cikin ya ran turanci madam rose ta gabatar mata da tahee a matsayin new student kafun ta bar class din,kallanta mrs afia tayi tare da nuna mata wani kujera da ke 3rd seat alamun taje ta zauna, cikin girmamawa kuwa ta karasa ta zauna tare dayi wa wacce take wajan sallama tayi zamanta, maths din mss afia ta cigaba da yi musu, saida ta kammala kafun ta dan dawo baya sabida tahee ta fuskanta, ai kuwa gabaki d’aya ta gane maths din da a akai musu Sabida yanda take koyawa musu daki daki, saida aka kammala kafun ta kalli tahee cikin cikin yaran turanci” ko xaki gabatar mana da kanki”, a nurse tahee ta mike kafin cikin yaran turancin da maki aka sari da tayi sai da suka dauka ba bahaushiya bace sabida yanda ko wana word yake futa “My name is taheera Mohammed “, yan tanbayoyi mss afia tayi mata cikin nutsuwa ta bata amsa duk da yawan idanuwa da taji akanta,tana gamawa mss afia ta tafa mata kafun gabaki d’aya ragowar student din suma su ta fa mata, mss afia zaka fita kenan massager ya shiga da wasu books , kai tsaye desk din da tahee take mss afia ta Nuna mata, tana kai mata tayi Mata bayanin sauran subject din da zaa yi musu yau ne , ragowar books dinta yana wajan madam rose.
Tunda mss afia ta bar class din gabaki d’aya ajin yayi shiru kowa har kar gabansa yake , tagen tahee ce ta dan kalleta kafun ta miko mata hannu “ I’m husna ma’aruf me gwanjo, nice meeting you”, itama mika mata hannu tahee tayi” nice meeting you too”, murmushin jin dadi husna ta saki kafin ta cigaba da duba books dinta itama, mintuna biyar tsakani sai ga wani teacher din ya shigo shima , chemistry ya rubuta cikin bold din rubutu, book din chemistry din tahee ta dakko da wani karamin book, abun da ya koya musu jiya ya fara tanbaya wasu daga cikin class din suna amsawa, musamman ta gefen ta da mafi akasari tafi bada amsa “ Good class rep” gabaki d’aya yan class din tafa mata sukai, TAHEE kuwa na tsuwa tayi tana sauraran bayanin topic din da yake musu me suna EVOLUTION OF ARTIFICIAL ORGANS, yana gamawa ya fara tanbayoyi ko yan class din sun gane, wasu na amsawa wasu kuma nayi masa tanbayoyi, saida ya kammala kafun husna ta mike a matsayin class rep din class din ta gabatar masa da new student din da aka kawo, shima tanbaya yayi wa tahee game da topic din yau, nan ma duk bayanin da yayi saida ta basa harda karin Wanda yayi musu, tafa mata yasa yan class din sukai kafun ya kalli husna cikin yaran turanci “ ki koya mata sauran karatun baya da akai” ok sir husna ta bashi amsa, yana fita tahee ta dan kalleta “ please ko zaki iya aramun note dinki”, mika mata husna tayi tare da mathematician din da aka gamai musu “ but lokacin break yayi , ki bari inkin koma gida zaki fi nutsu inyaso gobe sea na fara koya miki Wanda akayi na baya” duk da facemask din dake fuskar tahee hakan be hanata sakin murmushi ba “ thank you “, you welcome “ husna ta bata amsa ita ma, wasu daga cikin yan class din ne suka fara futa yayi saura mutane kadan, watace dake can bayan seat su uku suka taso cikin rangwada Daidai inda tahee book din tahee yake wata daka cikinsu ta saka mata kafa, book din ya fado, shewa suka saki kafun su bi tahee da husna da dirty look suna jan tsaki, “ am sorry please, haka halinsu yake basu da kunya sabida suna ganin suna da me tsaya musu”, gyada mata kai tahee tayi kafun ta dauki book dinta “ it’s ok “, messenger ne ya kara shigowa kafun ya mikawa tahee wani wasu card , yana fita husna tayi mata bayanin Wanda zata dunga karban abinci da kuma books ko wani abu da take so, ganin lokaci na tafiya ne yasa suka nufi cafeteria din kamar yanda husna ta jata , suna shiga cafterian matan dazu da wasu suka fara shewa suna nuna tahee, master card din abincinsu husna ta nuna , tanbayar abunda za a basu husna tahee, TAHEE bata karbi komai ba duk yanda husna tayi da ita, wani table aka nuna musu me zaman mutane biyar suka nufa, husna ce ta karbo musu abincin ta mikawa tahee nata, bata ci abincin ba ganin yanda mata da maza suke kwata kwata bata da sake wa, mrs afia ce ta shigo cafeterian gabaki d’aya student shiru sukai dan sun san halinta, inda tahee take ta nufa kafun ta nuna musu wani empty seat yadda tahee zatafi dadin sakewa , kamar kuwa ta sani wajan yafi Mata duk da bata ci komai na wajan ba, lokacin break na karewa suka koma class, da daddai da daddai teachers Suke shigowa class din, duk Wanda zai fita sai husna ta gabatar masa da new student din ajin har lokacin tashi yayi, gabaki d’aya tahee tayi week kamar ba ita ba har yanxu kuma bata cire face mask din fuskartaba, Ana tashi wasu dan kara dan karan motoci kuda uku ba’ka’ke suka shigo cikin harabar makarantar, Daidai inda tahee take motocin sukai parking, cikin taku Matar me suna stela ta bude mata kofa bayan books dinta da sauran abubuwa da ta dakko wa tahee, sallama sukayi da husna da itama aka zo daukarta. Tahee tana komawa gida wanka tahee da sallah kafun wani baccin wahala ya dauke ta, ba ita ta farka ba sai wajan karfe biyar, cikin sauri ta mike, Sallahr la’asar tayi kafun ta shiga kitchen har yanxu baccin fuskarta be saketa ba, cikin kankanin lokaci ta dafa musu abinci mara nauyi tare da kunun aya me shegen dadi, tana kammalawa gidan ta kara Kimtsawa kafun ta shiga wanka , har lokacin kuma baccin da take ji be sake taba, sallar magariba tayi kafun ta Jira ta isha’i shima tayi , tana Idarwa bacci ya dauketa akan daddumar.
8:50 king ya shigo part din ganin bata falon ya nufi dakinta, ganin yanda take bacci akan daddumane yasashi dan zaro ido kafun ya kara so inda take , gabaki dayanta ya dauketa ya mayar kan gadon, bude idanuwanta da suka jike da bacci tayi tana kallansa, dan hancinta yaja kadan “sleepyhead” , tashi zaune tahee tayi “ Yaushe ka dawo”, now ya bata amsa”sorry bansan bacci ya daukeni ba, sannu da zuwa, ya aiki”, ta jera masa duka tanbayoyin lokaci d’aya, “Alhamdulillah “ ya bata amsa a hade , kafun ta temaka masa yayi wanka shima ya shirya, abinci tahee ta zuba musu sukayi feeding juna kafun ya tanbayeta abunda aka koya masa, bayanin karatun ta shiga yi masa dukda shima yayi mamakin ss3 din da aka sata, question ya dunga yi mata tana bashi amsa shima, ya jinjina kwazanta sosai, book din husna ta dakko masa ya fara yi mata lession din baya da akayi cikin zallan gwarewa , be sha wahala ba wajan yi mata bayanin ganin tana saurin gane wa, hamma da yaga tanayi ne yashi ajje books din kafun ya dauketa gabaki d’aya suka koma daki, akan chest din shi tahee ta kwanta tana shakar daddadar kamshin turaren sa, a haka bacci barawo ya kwashesu gabaki d’aya .
***** Washe gari tueday da wuri tahee ta shirya ta nufi school bayan king yasata cin abincin dole, suna zuwa ba assembly shiyasa ajikin su ta nufa , lokacin itama husna tazo, ganin da sauran mintuna kafun a fara classes din husna ta fara koya mata previous karatun da aka yi na baya, suna cikin yi yan class din suka fara shigowa da d’ad’d’e da d’ad’d’e, wayan nan yan matan ne suka kara shigowa ynxu ma cikin isgili suka zo zasu yardar wa tahee book , husna ta tsawatar musu daman itama ba sa ga miciji da zuna, tsaki ta tsayen tayi kafin ta kalli ta gefen ta me suna kubra , “kubry let’s go”, tana fadar hakan tayi wucewarta , itama dayar suna salma ana kiranta salmyyy baby wucewa tayi tana Jan kwafa, guntun tsaki husna ta saki Daidai lokacin da teachers suka fara shigowa, yau ma lokacin break nayi husna ta kara koya mata wasu abubuwan kafin su nufi cafteria , a wnnan karan ba leafi ta dan taba abincin dukda yanda husna ta rikice da kyawun tahee duk da itama ba baya ba wajan kyau, da ta kalleta sai tace “ gaskiya friend ke kyakkyawa ce “ ba abunda tahee take ce mata saidai tayi dariya , suna kammalawa classes Dinsu suka nufa ganin lokaci yayi, suna shiga teacher din biology ta shigo class din, tana kammalawa wan teacher din ya shigo, haka teachers suka cigaba da shigowa har lokacin tashi.
Yau ma da gajiya tahee ta koma gida , tanayin sallah cornflakes ta dama da yasha marada sosai , tana gama cinsa ta dakko ice cream ta sha har roba biyu kafin ta dakko wasu chocolate din suma masu shegen dadi, ko ina a gyare ya’ke sai faman tashin kamshi yake shiyasa 3rd floor din king kawai ta gyara kafun ta shiga wanka, sai yau ta tuna da wayarta, ganin ba charge ne ysa ta saka wayar a chargy, bayan sallah la’asar kitchen ta shiga ta girka musu abinci kafun ta shiga wanka , ana kiran magariba sallah tayi kafun tayi isha’i shima , tana idarwa kara shirya jikinta tayi duk da bata saka turare ba sai wani mara karfi da bazata jishi sosai ba da ta saka.
Yana dawowa ta rungumeshi kamar ba ita ba , ganin yanda ya gaji ne yasa ta hada masa ruwan wanka, “ I can’t do it my self , I need my wife’s help”, duk da bashi da tabbacin zatayi abunda yace din, amma ga mamakinsa batayi masa musu ko kadan ba ta temaka masa yayi wankan sai wani kakkare fuskatake wai karya kalli fuskarta, sosai king yaji dadin hakan da tayi, suna kammala cin abincin karatunta da akayi mata ya kara koyamata. Suna shiga daki king ya kashe hasken dakin ya bar ita dum light , janyo tahee yayi jikinsa kafun ya hade bakinsu waje d’aya, bata hanashi ba itama ta fara maida masa da martani, wani irin susucewa king yayi sai faman gurnanin dadin yake saki, gabaki d’aya tahee ta zautar dashi da salon kiss dinta, cikin sauri ya fincike mata rigar jikinta kafin ya fara ya mutsata yanda ya keso, yanxun ma tahee bata hanasaba musamman wani dadi da ya fara ratsa mata kwakwalwa sai faman tura masa breast din ta take yana kara zaucewa, daga nan salo ya canza,wannan karan batayi wani rakiba duk da ta danji zafi amma dadin da takeji ya nunka zafin, king sai faman surutai yake mata yana shi mata albarka , wani abun duk bata gane me yake cewa, yana kara kusantar ta ta ya tanbayeta ko da dadi, cikin sauri tahee ta daga masa kai tana kara rungumosa jikinta.
Bayan komai ya lafa king ya soma tsokanar ta , itama
Kam ba bakin magana sai boye fuskarta da take a cikin kirjinsa.
Washe gari me haka tahee ta cigaba da suka makarantarta kome aka koya mata in ta dawo king zai kara koya mata, yanxu har karatun alkurnani take basa musamman yanda suke tashi sallar tsakar dare, a kwanakin nan gabaki d’aya tahee bata samu damar shiga cikin gida ba sabida makaranta da take zuwa.
Haka ranaku suka ci gaba da tafiya yau ya kasan ce satin tahee biyu da fara zuwa school , cikin yan kwanakin nan wata shakuwa ce ta shiga tsakanin ta da husna duk da har ynxu husna bata san tahee na da aure ba, A kullum kuma tahee sai wani haske da fresh da fatar jikin ta take, gabaki d’aya kirjinta ya kara cikowa, duk lokacin da king zai kusanceta sai ya tanbayeta ganin yanda breast dinga ke cikowa tana kara murmurewa, wani irin soyayya suke wa junansu kamar zasu hadiye zuna, duk lokacin da d’aya bayanan toh daya zai kira yaji lapiyar daya , Tsantsan kulawa suke nuna wa junansu, musamman yanxu king da baya jin kunyar nuna soyayyarsa a gaban kowa .
Yau ta Kasance Friday, gabaki d’aya kowa na cikin family farin ciki ne dauke a fuskarsu , kowa Ka gani sai aikace ai kace yake, har wannan lokacin amrah bata yin gangancin haduwa da king sabida bugun mutuwar da yasa akai mata lokacin da zaki yakawo masa bayanin phone number din aka turo masa da text, ita kanta tayi na damar hakan sabida ga baki d’aya bata da sakewa yanxu ,kullum fargabar ta kar king ya ganta da warning din da yayi mata da babbar murya in ya kara ganinta.
Karfe 3:02 su ihsan suka nufi airport dan dakko su kabeer da haroon, wasu matasan samari ne chocolate colour suma duk da basu da haske babu mummuna a cikin su, ko wannan su ya aske gashin kansa da ya tara sai kadan da suka bari, kowa yayi farin cikin ganin su ganin yanda suka canza kamar basu ba, babu Wanda be nuna farin cikinsa ba sai aunty dake yaken dole, kowa aka dawo gida hirar Yaushe gamo aka kara kafun kowa yaje ya huta kasan tuwar dakinsu daya suma flat Dinsu da abeey ya bude musu, duk Wanda hidimar da ake tahee bata sani ba tana daki tana baccinta, sai da taje part din su dada ake fada mata dawowarsu, miran king ta gani a wayarta , kunyar daukan kiran take a gaban su dada ga abeey da ya shigo shima, sai da safe kawai tayi musu duk da kunya da tabi ta cika mata ciki, tana zuwa part din su ta tarar dashi sanye da bakar singlet da wando fari, wajan shi ta karasa zata rungumeshi tayi saurin ja baya, kallanta yayi alamun Menene “ banasan kamshin turaran nan”, da sauri ya kalleta alamun ta maimaita Menene bataso, ta bude baki zatayi magana taji wani irin amai ya ta so mata, da sauri ta nufi toilet din kasa har tana hadawa da gudu, system din gabansa ya ajje cikin tashin hankali yabi bayan babyn tashi, sosai tayi amai da ya sata galabaita, saida ya tabbatar data gama dakanshi ya wanke mata jiki sai faman kare hancinta take, yana ganin hakan sauri ya wa tsa ruwa kafun ya canza kayan jikinsa, be shafa komai ba ya nufi inda take a kwance,dago da ita yayi ta kara komawa luuu zata kwanta “ No !! Noo please , stay still , meke damunki, Menene ya saki amai” bakinta ta turo masa Nima ban sani ba kawai bana san kamshin turaran da ka sane ,ina shaka naji ina jin amai, kuma ni dan wake zanci da yaji”, idanuwansa king ya zuba mata, abunda yake fado masa arai yane yake so ya gasgata, “are you serious “, kanta ta daga masa dan ita dan wake take so taci, da wani irin sauri king ya kankameta a jikinsa , ya rasa Wana irin farin ciki zai yi, gabaki d’aya ya susuce ko magana ya kasa bayan rungumeta da yayi a jikinsa, cikin rawar murya ya soma magana “ thank you so very much dear, Allah yayi miki albarka, ya faranta miki kamar yanda kika farantamun, ke din farin cikin rayuwa tace da bazan iya musaltawa ba, I love you! I love you !!! I love you , I will now be a father , OMG”, ya karasa maganar tasa yana dora hannunsa d’aya akan cikin ta , bata gane me yake nufi ba shiysa take bunsa da kallo, wani irin tsantsan kaunarta ta hango a kwayar idanuwansa, a hankali ya kwantar da kansa saman cinyarta, ji yake komai na dawo masa sabo kamar yanxu abun ya faru, daukar damshi damshin da taji ne yasa tayi saurin dago da fuskarsa, hawaye ta gani suna sakko masa akan fusga, yayi saurin kneeling a kasa tare da yiwa Allah sujjada, bazai iya musalta farincikin da yaji ba, “ dady” ta fada itama kamar zatayi kuka Ganin hawaye akan fuskarsa, murmushin dayasa hakwaransa fitowa yayi kafun ta furta “ thank you zawj, I will now be a father, baby na ta girma she will be a momma “ har yanxu bata gane ba , shiyasa ta kallesa da sigar tanbaya, “ you’re pregnant “ ya furta mata, da wani irin expression ta kallesa ganin tsantsan farin ciki shin fide a fuskarsa, bata san lokacin da wani kuka ya kwace mata ba, da Sauri ya riko hannunta yana lallashinta har saida tayi shiru “ please inasan cikina “ ya fada mata a raunace duk da besan dalilin yin kukan taba, tausayi ya bata sosai, Inba me yin butulciwa WACECE ita da zataki Jinin dadynta, saukar hannunsa da taji akan cikin natane yasa ta kankame hannun nasa kafun ta rungumeshi ajikinta “ I love you so very much hayaty “ ajiyar zuciyar da har ita sai da taji yayi kafun ya rada mata “ I can’t expressed how much you mean to me maman unborn “, dan dago da fuskarta tayi tana kallansa “Ni fa sunana baby ba maman unborn ba” hancinta ya ja mata kafun ya furta “ you’re not a baby now , yanxu kin zama maman baby”, shagwabe masa fuska tayi kamar zatayi kuka “ wato tun kafun kaga dan Ka fara nunamun banbanci “, are you jealous “ ya furta yana zaro idanuwansa, kin magana tayi ta tashi sai faman kunbure kunbure take, wani irin sanyi ne yaji ya mamaye masa ransa , yayi saurin rungumota” Haba ke soyayyarki da bance ai, kadan zamu sanwa baby, kinga ynxu kinzama babbyn baby ko”, ita sai yanxu abunda tayi ma yasata kunya tayi saurin boye fuskarta. Jin kansa yake kamar a mafarki “I’m gonna be a father, Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah Ala ni’imatullah, Allah nagode maka,Allah ka albarkaci abinda ke cikin ta ka bata lapiya, Alhmdllh “ shine abunda king ke faman nanatawa aransa yana yiwa Allah tasbihi.
GIDAN AUNTY
Mss Lee 💖
07041879581
Post a Comment for "Gidan Aunty Book 1 Page 63"