Furar Danko Book 2 Page 64
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣
*SCHOLARSHIP, 3 DAYS CLASS*
Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni
Class ze fara ranar jumaa insha Allah
WhatsApp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA
WhatsApp 08144147273
👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Mexico Tour visa 1 month, Slovakia Job seeker visa
____________
.........Awannin da suka gabata sun tafine da sautin bugawar zukatan waɗan nan ahali. Kafin kowa ya samu nutsuwa a dalilin farfaɗowar Lulu. Ba'a bari an shiga inda take ba sai Smart kawai. Dan shikam a ranar ma tare suka kwana. Ko yaya ta motsa ya dinga tambayarta minene damuwarta kenan har saita sakar masa murmushi. Sai washe gari ƴan uwa da abokan arziki suka samu ganinta. Daddy ji yake kamar ya haɗiyeta dan farin ciki. Duk wani masoyinsu da uban gayyar sai yau suka samu nutsuwar kallon baby's. Yayinda aka koma kuma taya juna murnar samun ƙaruwa.
Salim shi Smart yasa yayma yara huɗuba a kasancewarsa babba. Itama Lulu sai a ranar ta samu ganin abinda ta haifa. Cikin ƙarfin hali da magana ƙasa-ƙasa take faɗin, “Mr A wannan karon ma kamin wayo, su duka kai suka biyo”.
Murmushi ya sakar mata yana wani ɗage gira sama da amsa mata da cewar, “Hakan na nufin na fiki jarumta a filin yaƙin ƙasa da ƙasa kenan. Next time ma ƴan uku zakiyi in sha ALLAH”.
Da sauri ta kauda kanta gefe tana faɗin, “Ai kai dama ba'a hirar arziƙi da kai. Mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kake wani kira masa haihuwar ƴan uku”.
Dariya ya sanya mata Nadiya na tayashi. Dan duk tana ɗakin suke wannan taɓarar... Dada da ciwo ya sake fidda tsufarta ta taƙarƙara da ƙyar tazo asibitin da duba Lulu. Lokacin da taga ƴan tagwayen nan sai da hawaye suka cika mata ido. Dole abubuwa su rincaɓe musu dan rabon yaran nan kaɗai ya isa ya zama sanadin kaudasu a duniya. Gashi nan cikin shekara biyu da rabi a auren nasu Lulu nada yara uku...
Alhmdllh Lulu ta samu kanta sosai kasancewar jikinta mai ƙyau ne baya riƙe ciwo. Kwananta shida aka sallamesu suka koma gida. Dan ta matsa akan ita a sallameta ta gaji da zaman asibitin nan bata son warin. Haka aka sallamota suka nufi gida. Sai dai maimakon gidan Abba sai taga an wuce da ita katafaren gidan da mijinta ya gina batare data sani ba. Duk da sun taɓa wucewa ta gaban gidan kasancewar a anguwarsu ta hotoro GRA ne har taita santinsa. Ashe wai nasu ne. Koda ta jiyo tana kallon Smart sai ya kama kunnesa yana wani ɓata fuska kamar AA na fushi. Murmushi kawai tayi tana mai sinne kanta dan suna a tsakkiyar mutane ne.
Gida bai sake rikita kowa ba sai da suka shiga cikinsa. Abun ba'a cewa komai kawai. Lulu na son keɓewa da mijinta sai dai babu dama. Dan gidan cike yake kasancewar su Ammah sunce fa sai anyi taron suna. Washe gari aka raɗama ƴan biyu suna. Inda sukaci sunan *_Ayshatul-humairah da Hafsatul-Ikram_*. Ƴan biyu Aysha da Hafsat sunyi goshi matuƙa. Dan kwai da kwarkwata na dangin Lulu da Smart musamman ƴan FURAR DANƘO C-BOX. AREWABOOKS, ZAFAFA FANS dama ƴan bayan katanga masu karatun bati sun zo a gayyar SOƊI🤣🥱 (A daure azo a biya 400 ne, duk 1k babu yawa bama son halin dangin Sulaiman Tsule ƴan bati. Dan nidai babu ruwana biyana za'ai🤪😜). An raƙashe an ƙwalle a wannan taron suna yayinda amaryar jego da jariranta sukasha ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon badaga baya ba kam. Munci hinkafa iya hinkafa. Munha zoɓorodo harda kajin gidan gona masu tsokar gaske. Ga halawa da biskin duk an bimu da su a ledoji. Kai al'amarin dai ba'a cewa komai dan an nuna halin girma. Sai muce ALLAH ya raya Ayshatu da Hafsatuwa....
Har washe gari gidan nan cike yake da mutane. To su Xoxo anga hinkafar banza anƙi tafiya🥱. Huguma da Rano da Mamu kam harda rantsuwar su sai Lulu tai arba'in zasu wuce, yo anga gida ginin gilashi🤣. Nace kunji abin kunya Zafafa dai sai an nuna hali a ko'ina😏🚶, alhalin hinkafar nan fa dai kowa nada a gidansa, gilashi kuwa kowa akwai a windown gidansa. Amma dai bari mu bincika o'e da o'e kodai-kodai 🥱. (I love you Zafafa's😘😘😘❤️💞🙏).
Shatara ta arziƙi kam dai Lulu ta sameshi a wannan haihuwar. Dan Nadiya da Ummita da amaryar Baba Garko da Maryam amarya sune tsaye akan duk wani gift data samu. Tun a wajen hotuna bata sake saka mijinta a ido ba sai a daren na washe gari ya fidda kunya dai ya shigo har ɗakinta. Su Ummita dake baje suna buɗe gifts suka suka fara rige-rigen fita. Idanu Lulu dake da ga kwance AA na gefenta zaune yana fitinar a bashi Baby ta ɗago a hankali ta sauke a kansa. Shima ita yake kallo da yaransa guda uku dake gabanta reras. Lallausan murmushi ya sakar mata yana mai lumshe ƙyawawan idanun nan nasa da take kira na maciji tare da ɗaga kafafunsa a sannu-sannu ya cigaba da nufota cikin takun ƙasaita da kasala tamkar mai irga steps ɗin nashi. Dai-dai yana isowa ta yunƙura zata tashi zaune ya girgiza mata kansa yana mai kaiwa zaune a bakin gadon da kama kafaɗunta ya maidata ya kwantar yana kaɗa mata kansa. Bata da zaɓin daya wuce komawar ta kwanta. Baice da ita komai ba sai hankalinsa da ya maida kan AA. Cike da kulawa ya ce, “Waya saka Baban Ammah kuka ne?”.
Cikin shagwaɓa AA ya nuna Lulu, dan har yanzu shi maganar tasa sai a hankali ce. Dan ma ɗan zamansu a Nigeria ɗin nan ya fara samun bakinsa kasancewar gidan Abba gidan yarane. Balle shi da ko yaushe yana hannun yaran gidan kowa ji yake da shi saboda ƙyautatawar iyayensa. Kaɗan Smart ya ɗan waro idanu waje da faɗin, “Kai-kai Maah-maah ce”. Kai AA ya ɗaga masa yana wani sake ƙwaɓe fuska.. “Ayya Kakan Papa yi shirunka ƙyale Maah-maah kaji ko. Bazamu saya mata kayan daɗinmu ba ai ko?”. Nan ma AA ya ɗaga kansa dan yana jin magana sarai abinsa. Gyara masa zama Smart yayi tare da ɗaukar Hafsat dake a kusa da shi ya ɗauramasa a saman cinya, sai dai bai sakar masa ba tana a hamnunsa. A take yaron ya hau dariya yana nuna Aysha wai itama a ɗaura masa. Haka Smart ya biye masa itama ya ɗaura masan. Ita dai Lulu na kallonsu kawai, dan a yanzu tana sake fahimtar irin so da ƙaunar da mijin nata kema yara ta dabance. Sai da yaran suka ɗan jima a cinyar yaron sannan ya saukesu ya kwantar da su yace ya kwanta kusa da su ya musu wasa.
“Ni dai kada ya tsokale min idanun yara gaskiya. Har yanzu ban gama dawowa a hayyacina ba fa”. Lulu ta faɗa cikin shagwaɓa harda wani ɗan tura baki. Dariya ta bashi ma shi, dan haka ya juyo yana kallonta gira a ɗage ya ce, “Oh really?!”.
“Kai ne shaida ai, tunda kai kafi kowa shan kuka”.
Kansa ya kauda gefe yana murmushi da faɗin, “Oh ni Aliyu. Na shiga tara kuma da gorin yarinyar nan. Ke da baƙya raye a lokacin ya akai kika san haka?”.
Murmushi ta saki mai bayyana haƙwara. Ta ce, “Likimo nayi fa duk ina jinka. Dan na sake tabbatar da wanene mijina. Ashe ragone shi a kan lamurana”.
Yanzu kam dole dariyarsa ta fita da sauti. Ya zuba mata mayun idanun nan nasa yana sakar mata wani murmushi mai sanyi da fasa zuciya. A can ƙasan maƙoshi yana mai dimtse hannunta cikin nashi da ƙyau ya ce, “Kin san kuwa matsayin da Mawaddat Jiƙamshi ke da a zuciyar Aliyu! Wannan sirrin ALLAH ne kawai yasanshi Baby luv. Kin fa gama mamaye ko'ina da ina baki ragema wata koda ƙanƙanin fili ba. Har tsoro nake ji kada wataran ƙaunarki ta fasa zuciyar ɗan bawan ALLAHn nan ma”.
Tuni ƙwalla sun cika mata idanu, zaune ta tashi tana mai juya kwanciyarta zuwa jikinsa. A tare suka saki ajiyar zuciya da lumshe idanunsu suka buɗe duk a lokaci ɗaya. Akan yaranta ta fara sauke nata kafin ta juyo gareshi hawayen da suka taru mata na sakkowa a hankali bisa ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Da sauri ya wara idanunsa zaiyi magana sai ta sakar masa murmushi da girgiza masa kan alamar kada yace komai.
“Aliyu!”.
“Uhyim Mawaddatan'warahmah!”.
“Kai ɗan aljanna ne da izinin ALLAH”.
“Tare ai zamu shige in sha ALLAHU”.
“Da'ace wani ɗan adam nada damar buɗema ɗan uwansa nan dana buɗe tawa ka ga matsayin ka a ciki” tai maganar tana ɗaura hannunsa a saitin zuciyarta. Idanunsa da sukai rauni sosai ya lumshe da sake buɗewa a kanta. “Kin mallaki Aliyu Hydar da komansa Mawaddatan'warahmah. Na jima da sanin kema kin mallaka masa zuciyarki. Sai dai ban san miyyasa kika zaɓi ɓoyewa ba baby luv. Salonki na azabtar dani matuƙa”. Dariya ta ƙyalƙyale masa da ita tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Sai ma sake matseta da yay cikin jikin nasa har sai da tai ƴar ƙara da faɗin, “Wash ciwona”. Da sauri ya saketa a rikice, ta ko kwashe masa da dariya tana masa gwalo. Sai ya ƙwaɓe fuska cike da shagwaɓa ya ce “Zan rama ne ai”.
“Sai dai wani karon wannan kam nayi winning”.
“Ba komai, ai da kai da kaya duk mallakar wiyane.” yay maganar yana mai lakace mata hanci. Ita kuma taja kumatunsa da faɗin, “Yaushe Aliyu ya fara ɓoyewa Mawaddat sirrikansa?” ta ƙare faɗa tana kallon ɗakin. Ya fahimci mi take nufi. Dan haka ya saki ɗan murmushi da kallon ɗakin shima. “Aliyu bai taɓa ɓoyema Mawaddat sirrinsa ba. Ya mata hakanne kawai domin supricing ɗinta, kuma Alhmdllh burinsa ya cika, wannan shine gidan Mawaddatan'warahmah da Aliyu da zuri'ar da zasu tara in sha ALLAH.”
Hawayene masu ɗumi suka gangaro a idanun Lulu dake kallonsa ko ƙyafta idanu batayi. Kallonta yay da sauri. Zai yi magana ta ɗaura yatsarta akan lips ɗinsa ta ce, “Shiii!!. Lokacin Mawaddat ne”.
Yanda tai maganar cikin raɗa sosai ya sashi sakin murmushi.....✍️
😁😁😁😁To nima bari na ɗan murmusa
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 64"