Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 63

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲






  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣



.......Washe garin da aka miƙa Maryam gidan miji Mawashi family suka tashi da tashin hankali biyu. Na farko shine gano Huwaila ɗauke da cikin shege na watanni biyar. Tashin hankalin bayyanar wannan ciki kuma yasa Ummah yanke jiki ta faɗi. Inda faɗuwar tata ta zama sanadin samun paralysis. Smart na masaukinsa yana barcin gajiya Lulu a jikinsa ya samu kira da ga Salim. Dole ya shirya ya nufo gidan da Lulu data dage bazai barta ita kaɗai ba. Sun sami gida a rikice. Ko Ummah ba'a ɗauka ba zuwa asibiti sai da yazo ya fara faɗa. Bayan ankai Ummah asibiti suka samu tabbacin ta samu shanyewar ɓarin jiki gida suka dawo da ita bisa shawarar doctor bayan anyi treatment ɗinta yanda ya kamata. Ummah dai an tafi, dan babu abinda ke motsi a ɓarinta na dama sai ido da kai. Amma daga wuyanta zuwa yatsanta ma ƙafa komai cak. Sai ɗayan ɓarin haggun kawai. Babu abinda take sai hawaye. Dan bakin ma idan tayi magana ba'aji sosai sai yawu ke fita babu ko ƙyawun gani.

       Smart da Salim suka tsare Huwaila. Zata musu wani kwana-kwana tasha maruka a hannun Smart. Salim ya rufeta da duka da ƙyar aka tsaida shi saboda lalurar dake a jikinta. Wahalar da tasha yasata faɗin gaskiyar cewar saurayinta ne ya mata lokacin suna tare da Umma a gidan Kawu Jibirin, idan tace ta tafi makarantar islamiyya sai ya ɗauketa a hanya su tafi hotol ko ɗakin abokansa. Ran kowa ya ɓaci Abba harda hawaye yana jama Umma ALLAH ya isa da jin nadama bisa nadama akan aurenta. Dan bai tsira da komai ba sai baƙin ciki da tashin hankali tun daga ƙuruciya har zuwa yau. Garama yanzu da Smart ke ƙoƙarin dawo da su Salim a hayyacinsu. Dan a yanzu haka jira yake a kammala bikin nan ya gyarama Salim shagunansa da suka ƙone. Smart yasa an nemo wanda yayma Huwaila ciki tare da iyayensa. Da farko ya musa harda cewa shi baima taɓa ganin Huwaila ba, sai da Smart yay masa jan ido harda maruka biyu a gaban iyayensa babu ko kunyar idonsu sannan ya faɗi gaskiya, amma yace ai bashi kaɗai bane tana kaima wasu. Huwaila ta sanya kuka da rantsuwa da shi kaɗai take tarayya, hasalima shine ya fara saninta ɗiya mace, tana ma da shedar hakan. Ansha rikici sosai har sai da Huwaila ta kawo recording na wayar da suka dingayi da ta dinga ajiyewa sannan fa shegen yay laushi. Inda aka tsaida magana da zaran ta haihuwa za'a ɗaura musu aure. Sauran ƴamatan gidan kuma ya basu tabbacin nan da wata uku kowacce ta kawo mijin aure in ba hakaba shi zai zaɓo musu. Hakan ya saka iyayen jin kwanciyar hankali. Dan sai ga Mama sarkin ruɗiya yau na sakama Smart albarka. Saboda ba ƙaramin tayar mata da hankali batun cikin nan na Huwaila yay ba, dan itama tana da ɗaya a ɗakinta mai rawar kan tsiyar da giggiwa. Haka ta tasa ƴaƴanta gaba wanda basuyi aure ba tana roƙonsu ALLAH Annabi su taimaka mata su rike mutuncin kansu karsu kasheta tun lokacinta baiyi ba kamar yanda Huwaila ta zama sanadin Ummanta. Sun daiga yanda tarbiyyar ƴaƴan Ammah a gidan ta jawo musu alkairi.....


     Samun lafawar ƙurar biki ta bama Smart nutsuwar fuskantar ƴan uwansa. Yayinda ya nutsu wajen nemawa ƴan uwansa maza da matan ma abinyi. Tare da zagaye dangin mahaifiyarsa dana mahaifinsa kaf yay musu alkairai masu tsoka da yaketa samun albarka shida zuri'arsa. Shine har dangin Mama dana Aunty Amarya, dan ita Umma danginta sune dangin Abba sai dai na ɓangaren mahaifiyarta. Gefe ɗaya kuma ya samu damar gina wasu manya-manyan mall guda biyu da kafa business daban-daban. Tare da yin amfani da ƙungiyar Lulu ya tallafama yara da ɗan yawa akan karatu. Masu shaye-shaye a ciki ya kaisu rihab. Dan Nadiya dake ta lallaɓa rayuwarta a yanzu tare da Ummita tsaye suke akan ƙungiyar. A cikin wannan halin bikin Ummita da Usman ya tashi suma. Haka Lulu taita ƙoƙari nan ma akayi komai da ita. Ta kuma bama Nadiya shawara akan ya kamata itama ta samu miji mai irin ciwonta suyi aure tunda yaron data haifa ya rasu. Ranar Nadiya tayi kuka sosai, tare jerama Lulu da Smart har ma da su Uncle Yousuf addu'oi. Dan yanzu ta koma gidansu a dalilin sanya baki da baba Garko yayi a zancen, babu kuma wanda take ganin mutunci da kima yanzu a duniya sama da Lulu da Smart. Amaryar Baba Garko ma ta shigo cikin tawagar masu kula da ƙungiya. Hakama Tajuddeen da a yanzu ya sakama kansa haƙuri game da al'amarin Lulu yana bada gudunmawa. Shima dai an saka bikinsa da ƙanwar amaryar mahaifinsa. Tunda ya lura yarinyar na masifar sonshi mahaifiyarsa da su Baba Garko suka bashi shawarar ya aureta kawai ya rufama kansa asiri, dan yanzu ba gida duka bane zai nema aure a bashi saboda tabon da mahaifinsu ya bar musu a cikin al'umma. Kowa ya zata Dada zataƙi. Sai gashi babu ko ja'in ja ta amince harda bada gudunmawar ta...


       _______★


      Hutun Smart ya ƙare zasu koma England sai dai Ammah tace bada Lulu ba. Dan a gida zata haihu wannan karon itama taga gatan da kowace ɗiya ke samu. Ba haka yaso ba dan haka ya dinga fushi. Ammah ko ta tattarashi ta watsar da faɗin yama fashe mana. Mawaddat ce dai babu inda zataje sai ta haihu tunda watan gobe ne haihuwar. Har kawo zancen AA zai shiga makaranta yayi amma Ammah tayi mirsisi da shi. Sai ma tace masa ya tafi da AA ɗin su zauna Lulu ce dai babu inda zataje. Babu yanda ya iya haka ya tattara rai a jagule ya tafi Lulu na faman masa dariya da gwalo. Dan ita farin ciki take da barinta a wajen Ammahn ta. Tana so da ƙaunar baiwar ALLAHr nan a rayuwar. Itama kuma Ammahn na nuna mata ƙauna mai tsayawa a rai. Idan ka gansu tamkar ba surukai ba. Wannan soyayyar tasu daga ALLAH ce kawai za'ace..


     Bayan wucewar Smart babu jimawa aka ƙarasa masa ginin katafaren gidansa da mutane keta magana akansa duk da basu san kona wanene ba. Dan hatta Lulu bata sani ba. Ammah da Abbah da Ahmad da Coach sai Uncle Yousuf ne kawai suka san gidan na Smart ne. Kamar abinda Lulu ke jira kenan ta fara naƙuda. Hankalin su Ammah ya tashi dan cikin dare al'amarin ya tasar mata. Gashi Ammah ta fahimci Lulu nada masifar tsoro ga kuma ta da Naƙuda mai wahala. Dole suka wuce asibiti a daren nan bakunansu da addu'a. A wannan karon ma dai cs aka shirya yima Lulu. Tunda Asma'u ta kira Smart ta sanar masa hankalinsa ke'a tashe. Tun a daren nan ya fara neman mafita dan ya tabbatar bazai taɓa iya haƙuri ba sai yazo Nigeria. Da ƙyar ya samu aka masa alfarmar kwana goma. Aiko babu ɓata lokaci ya shiga shiri...


      Alhamdullah an samu nasarar cirema Lulu yara biyu mata masu kama da mahaifinsu tamkar AA. Zokaga farin ciki da murna a wajen familyn nan guda biyu da suka zama tsintsiya maɗauri ɗaya a yanzu. Sai dai murnar tasu ta taƙaita ne kasancewar Lulu na cikin wani yanayi mai ban tashin hankali. Dan har Smart ya iso bata dawo hayyacinta ba. Hakan ya tada hankalin kowa da bada mamakin kasancewar a yanzu ansan cs ana yinsa ne ma idon mutum biyu. Koda Smart ya iso shi bata yaran yake ba, ta matarsa yake yi. Dan baiji nauyin kowa ba ya durƙushe a gaban gadon da take kwance samɓal kamar wadda ta mutu ya saki wani irin kuka mai ban tausayi. Yanda ya kife fuskarsa akan tafin hannunta yana kuka hawayensa suka jiƙe mata hannu. Haƙuri likitocin keta bashi dace masa addu'a take buƙata. In sha ALLAH kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci numfashinta ne kawai yay nisa. Ba Smart kawai ba hatta Daddy hankalinsa a tashe yake. Dan yana tuna a dalilin haihuwarta ya rasa mahaifiyarta itama. Baba Garko da Abba ne suketa lallashinsu da basu baki. Har dare babu wani bayani akan Lulu. Ga Smart ya kafa ya tsare ko nan da can baya gusawa, salla kawai ke tada shi a ɗakin. Cikin amincin ALLAH gabannin asubahi Lulu ta farfaɗo. Rikicewa Smart yayi dan farin ciki. Ya rungumeta jikinsa na rawa ga hawaye..

       Cikin ɗaga idanunta da kyar da shafo fuskarsa murya ƙasa-ƙasa ta furta. “Mr A!”.

   Rikicewa yay da farin ciki yana tattaɓata da rungume hannunta a ƙirjinsa hawaye fal idanunsa ya amsa da “Na'am Mawaddatan'warahmah!”. Wani irin murmushi mai tsayawa a rai ta sakar masa tare da maida idanunta a hankali ta sake lumshewa, hannunta ya saki a hankali. Wani irin ƙara Smart ya saki yana mai girgizata da sambatun faɗin, “Dan ALLAH kar kimin haka Mawaddat, karki tafi ki barni, kece rayuwar Aliyu kece farin cikinsa. Ni nake fata na rigaki mutuwa bake ki rigani ba. Ki tashi dan ALLAH na roƙeki”.

     Kukansa da sambatunsa yay matuƙar tada hankalin kowa a wajen. Dan Daddy ma luuu ya tafi zai faɗi sai da aka taroshi. Da ƙyar aka fiddo Smart a ɗakin likitoci suka rufu akan Lulu........✍️



      🙉🙉🙉Munga Boni





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 63"