Furar Danko 79
79
…….Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da zaman shari’ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta É—an taÉ“a aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security É—in nan ya dannama Smart
waya ya sanar masa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep É—in. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa’id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart yay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da Æ™yar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haÆ™ora. Fuska ta yamutse cike da izzarta ta ce, “Sanar mata tana da baÆ™uwa”. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.
Kallon gidan ta dingayi side by side tana taÉ“e baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa’id É—in ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani akwai kuÉ—in sai dai ko kama Æ™afarsu basu isa yi ba. Ƙofar da take Æ™yautata zaton falon gidan kenan ta nufa, cikin sa’a ma sai ta hango wata yarinya tsaye kamar tana kuka da alama mai aiki ce, isowarta kusa da ita ya sata daina kukan ta risina ta gaisheta. Sau É—aya ta amsa mata ta É—auke kanta. Yarinyar ce ta mata iso cikin falon, babbane sosai ya kumaji É—irka-É—irkan kujeru kamar bana dattijuwa ba. Kallo É—aya taima matar dake zaune a falon ta fahimci itace mamar mijin Hawwah É—in, dan ko’a ido ka kalleta kasan za’a zuba da ita kam. Zama tai kanta tsaye tun kan ma ace ta zauna, maman Sa’id dai kallonta take alamar rashin sani, duk da Lulu ta fahimci hakan sai ta basar, cikin É—aukar kan nan nata na isa da Æ™asaita ta ce, “Hajiya barka da rana. Sunana Barrister Mawaddat Isma’il JiÆ™amshi.”
Sai da zuciyar maman Sa’id ta motsa jin Æ´ar waye, sannan sunan kansa na Mawaddat É—in duk mai bibiyar harkokin mata a fanin fyaÉ—e dole zai santa, ita kanta dama tunanin ina tasan wannan fuskar takeyi. Lulu data lura da hakan ta cigaba da faÉ—in, “A yanzu haka matar Aliyu M. Idris Mawashi yayan matar É—anki dan bana tunanin kin halarci bikin sati É—aya daya shige”.
Gaba É—aya Mama duk sai ma taji ta daburce, dan tabbas Sa’id yata roÆ™arta zuwa bikin amma tace bazataje ba dan ba’a gayyaceta ba, koma an gayyacetan bazataje bikin matsiyata ba dan tasan dai bai wuce tuwo da waina da zoÉ“o ba. Harga ALLAH bata san É—iyar wa Aliyun ya aura ba. Da É—an jimami ta ce, “Da gaske kece matar Aliyun?”.
Lulu dake mata wani kallo a yamutse ta amsa da, “Oh baki yarda bane? Zaki iya tambayar É—anki ni yanzu ba wannan ne ya kawoni ba. Nazo nan ne game da case É—inki da Hawwah, kinyi Æ™oÆ™arin zuba mata mai dake saman wuta da nufin Æ™onata, ba kuma wannan ne karo na farko ba da hakan ta faru. Kinci arziÆ™in É—anki shiyyasa banzo da police ba a yanzu haka domin kamaki. Amma nazo da kalaman gargaÉ—i a gareki a karo na farko. Su iyayenta sun barki saboda jin nauyin karamcin É—anki. To ni kuma a matsayina na mai kare hakkin mata kuma matar Yayanta bazan iya barinki ba. Kin haifi Sa’id ba kin haliccesa bane, yana kuma da damar yin aure tunda bake zaki auresa bane, matsayinki daban matsayin uwa matsayin matarsa daban matsayin mata. Nan gidan aurenki ne, shi kuma nan gidan da aka haifesa ne, kina zaune da mijinki lafiya dan haka itama ki barta ta zauna da nata mijin lafiya. Wannan takardar da kike gani na tattara dukan abubuwan da kikai mata ne, tare da bincike mai yawa akanki a wajen Æ´an anguwa da Æ´an uwanki dana mijinki, kuma sun bani duk wani information a kanki har ma wanda bakiyi zato ba. Haka ma mijinki nayi waya da shi yanzu haka, dan haka kina da zaÉ“i biyu zaki saka hannu zan saka hannu Sa’id zai saka hannu hakama Hawwah da sharaÉ—in zaki fita rayuwar aurensu ki zauna a matsayinki na mahaifiyarsa, zakuma subar wannan gidan su koma nasu, sannan kije da kanki gidansu ki bata haÆ™uri ki bama iyayenta haÆ™uri. ZaÉ“i na biyu Æ™in amincewa da shawarar farko na shigar da wannan case É—in kotu mu zuba shari’a wlhy har sai na kaiki jail dan har video ke gareni na randa kika kusa kasheta a dalilin hankaÉ—ota daga saman upstairs gashi”. Ta É—aga mata wayar tana mai playing video É—in, jikin maman Sa’id ya fara rawa, Lulu ta sake shiga wani ta ce, “Ga kuma na randa kika watsa mata ruwan shayi harta Æ™one a wuya shima”. Sosai Lulu taga ruÉ—ewa a idanun Mama. Tai murmushi da kaÉ—a kanta cike da isa. “Ba waÉ—annan kawai ne ba, akwai wasu tari-tari kuma duk Hawwahn ke ajiyesu, bata nuna bane saboda mutuncin É—anki. Amma ni yanzu na shirya fiddosu a gaban alÆ™ali. Kin san dai mijinki siyasa yake yi har yana shirin fitowa takara a shekara mai zuwa ko, sannan yayanki a yanzu haka É—an majalissa ne, to a dalilinki duk zan iya tarwatsa wannan damammakin, dan bayan kasancewa jinin JiÆ™amshi jinin Alhaji Sufi Ado Garko nake kuma. Sai ki zaÉ“a na baki nan da kwanaki uku kacal. Na barki lafiya”. Ta faÉ—a tana miÆ™ewa murmushi É—auke da fuskarta ta É—aga mata yatsu biyu tai ficewarta. Sosai jikin maman Sa’id ke rawa da kakkarwa. Dan kuwa Lulu ta daketa ne a inda taji zafi sosai. Videos É—in nan sun matuÆ™ar tayar mata da hankali, har tana mamakin yaushe Hawwah duk ta É—aukesu batare da ita ta sani ba. Na biyu matsayin Lulu da hatsabibancinta akan shari’ar duk da ta saka a gaba. Na uku zancen siyasar mijinta da tai matuÆ™ar Æ™wallafama rai da buri a yanzu tare da matsayin É—an uwanta da shima take taÆ™ama da tinÆ™aho da shi a duk inda ta shiga. Idan wannan damar duk ta kufce musu ai ta shiga uku wlhy, dan za’a mata dariya matuÆ™a. Itafa dama kishiyar uwar yarinyar nan ce ke sake tunzurata akan tsanarta (Umma), duk da dai dama bata sonta kasancewarta Æ´ar talakawa, dan taso ace Sa’id yay auren kece raini ne na Æ™warya tabi Æ™warya. Amma ya Æ™are da auren Æ´ar malam shehu……
Lulu data fita da Æ™ayataccen murmushi a fuska ta shige motar tare da yin reverse tabar angur da gudu dan ita kam akwai wauta da mota. Mai Napep É—in nan dai na biye da ita. Ganin sun É—auki hanyar Nasara G.R.A yasa shi kiran Smart ya sanar masa. Koda suka iso gidan na Garko daka É—an nesa ya tsaya, yayinda ita aka buÉ—e mata gate ta shige ciki. Yau ma da mutane a gidan, sai dai kusan duk matan kawunan ta ne, suma É—in dai wanda basa fita aiki ne. Ta samu Baba na barci saboda allura da akai masa, hakan ya bama Dada dake cika na batsewa wa matan Æ´aÆ´an nata jan Lulu suka shige Æ™uryar É—aki. Dan fa ita tun jiya ranta a É“ace yake da batun zuwansu a napep. Balbale lulun tai da masifa, ita kuma ta tsaya tana kallonta da mamaki, sai da takai inda take so har tai shiru sannan Lulu ta taÉ“e baki. “To wai ni kuwa Dada dan ALLAH miye na damuwa anan, shiga napep É—in shi minene a cikinsa. Kinbi kin saka ma kanki damuwa”.
“Ya bazan sakama kaina damuwa ba Mawaddat. Kamarki ace kina hawa Napep. To ai ko uwarki datai irin wannan Æ™addararren auren naki bai kai naki watsewa da lalacewa ba. Shi wai cikakken É—an iska ma, an bashi abinda zai riÆ™eki har yace baya buÆ™ata. Ke anya kuwa yaron nan ba asiri yay miki ba kuwa?”.
Dariya Lulu ta kwashe da shi a karo na farko, ta ce, “Ho Dada tamu, Aliyun ne zai min asiri. To wlhy bara na faÉ—a miki ma shi ustazu ne. Dama cakikai girman kai ya hanashi amsa sai na yarda. Amma ba asiri ba. Yo ni koma asirin ne ina ruwana ma, iyakaci lokaci na cika zan Æ™ara gaba babu abinda asirinsa zaimun ballema ni nasan ba asirin bane. Kuma nidai ki daina zagar min miji dan nima Æ´an uwansa basu zagan ba sai ma girmamani da mutuntani da nuna min soyayya sukeyi”.
Dada data saki baki tana kallonta ta ce, “Iyyeee a lallai Mawaddat kinyi baki, harni kike gayama wannan zantukan. To inba asiri ba ubanmi zai kaiki auren yaron dake matsayin driver É—inki. Ko Æ™yan nasa ne ya ruÉ—eki da waÉ—an nan shegun idanun nasa kamar na Æ´an maye. Dubeki fa wai kece da saka hijjabi yau kamar wata tsohuwa. Yo koni dana haifi uwarki na ninkaki shekaru bazan saka wannan abun har Æ™asa na fita ba”.
Baki Lulu ta taÉ“e tana miÆ™awa, “Dada bazaki gane ba ke dai. Ya kike so nayi? ya rantse in ban saka ba bazan fito ba gashi inada shari’a mai muhimmanci. Wlhy taurin kan Aliyun nan ya wuce duk yanda kike tsammani. Bar ganinsa yana wani sissine kan nan shegen kansa ne.”
“A to lallai na sake yarda yaron nan asiri yay miki wlhy, ke yanzu duk yanda na sankin nan da rashin É—aukar raini har kece taurin kan wani É—a namiji zai girgiza ki ko ya baki tsoro da saki laushi haka a cikin sati É—aya kacal. Dolene na miÆ™e tsaye dan wlhy koma miza’ai sai na rabaki da shegen yaron nan dan baza’a sake maimaita abinda ya faru akan uwarki ba. ALLAH dai yasa baki miÆ™a masa kanki ba ya lalube shegen”.
Dariya Lulu tai harda kwanciya, sai kuma ta É—ago cikin dariyar dai ta ce, “Ke kam Dada inda ace a zamanin baya kikazo irinku ne bakwa musulinta da wuri ga riÆ™e gaba har Æ™arshen numfashi. Indai aurena ne ki kwantar da hankalinki bamai daÉ—ewa bane, sati biyu ya rage ana uku na koma free. Sannan kina damuna da habaici akan Daddy na da Mamana, idan na tambayeki kuma kiÆ™i faÉ—a min, kin kuma hana kowa gayamin. Mi Daddyna yay miki ne kike jin haushinsa haka, idan dan yaÆ™i baki riÆ™ona ne ba gashi yanzu na dawo kina ganina ba”.
“Ke ni Æ™yaleni shashasha ba ganewa zakiyi ba. Ni ina tambayarki wani abu ya shiga tsakaninku ne? Sannan kince nanda sati biyu, kin fa sani a duhu”………✍️
Post a Comment for "Furar Danko 79"