Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko 78

 

78

 


…….Itama dakatar da itan abinda tai niyyar sake faÉ—an da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai É“ace. “Wai miye haka kuma ban son Æ™aranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”

 

MiÆ™ewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miÆ™e babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama’ar É—akin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taÉ“e baki Æ™asa-Æ™asa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin Æ™arfin halin rashin jin daÉ—in jiki Baba ya balbale Dada da faÉ—a, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki…..

 

Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buÉ—e musu suka shiga, gaba É—aya kayan na’a hannunsa har handbag É—inta ma. Har É—aki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daÉ—in abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taÆ™aice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata É—ayan nan bazata so a wulaÆ™antashi ba dan itama dai da taje gidansu ba’a wulaÆ™antatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.

 

Shima a can wankan ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya zaÉ“i shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai taÉ“a wulaÆ™antata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa’i da wutri yayi sannan ya fito. Shayi ya haÉ—a a kofi biyu ya nufi É—akin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta Æ™urama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana haÉ—iyar busashen yawun daya tokare maÆ™oshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo Æ´ar saman rigar data ajiye gefe ta É—ora akan wadda ke jikinta dan Æ™arama ce ma da kaÉ—an ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miÆ™a mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciya da faÉ—in, “Thanks.” kansa kawai ya É—an jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da faÉ—in, “Kayi haÆ™uri da abinda Dada tayi, ni ban faÉ—a mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da faÉ—a ne sosai”.

 

Murmushi yay a karo na farko, sai kuma ya É—an kafeta da idanunsa da suka canja launi kaÉ—an. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi faÉ—a kenan?“. Hararsa tayi da É—an murguÉ—a baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban É—auki abinda tai É—in komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya É—an tattara mata game da case É—in yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smart tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiÆ™e. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai É—in ba ta É—ago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido É—aya. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai lumshe idanunsa.

 

Komawa tai ta zauna da faÉ—in, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da É—akko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu daidaiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma Æ™asan maÆ™oshi, tare da faÉ—a mata dokokinsa akan yanda yake buÆ™atar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har Æ™asa ya sata dubansa cikin tura baki ta ce.

 

“Hijjab har Æ™asa? Ni ce zan saka hijjab har Æ™asa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure bane balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a Æ™arÆ™ashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunta juna. Ni harka ma É“atamin rai na”.

 

Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tashi tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buÆ™atar abinda zai É“ata mata farin cikin data samu yau a wajen Æ´an uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana faÉ—in (akwai Æ™ura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitane da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai….

 

WASHE GARI ta tashi da É—okin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case É—in nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban Æ™amshi take zubawa dan ta baza turaren nata. Tana Æ™oÆ™arin É—aura igiyar takalmanta ya shigo É—akin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har Æ™asa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin Æ™ofar ya jingina tare da harÉ—e hannayensa a Æ™irji ya zuba mata idanu kawai. Ƙin É—agowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta É—ago É—in ma kallo É—aya tai masa ta É—auke kanta tana miÆ™ewa. Da ga sama har Æ™asa ya sake Æ™are mata kallo. Yayinda ita kuma ta Æ™arasa tattare kayanta ta nufo Æ™ofar kanta tsaye. Kallonsa tai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.

 

Maimakon amsa mata sai ya É—an kauda idanun nasa a kanta ka É—an batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take buÆ™ata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da É—an kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.

 

Cikin husky voice ya ce, “Idan baÆ™yason rasa shari’ar ko makarar go and change your dresses. Na faÉ—a miki duk abinda bakina ya furta shine nake buÆ™ata kuma bana canjawa da ga ra’ayina akan duk abinda na riga na tsara.”

 

Cikin É“acin ran da ya fara yunÆ™uro mata ta ce, “Aliyu!!…”

 

Hannu ya É—aga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buÆ™ata to bana buÆ™atar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.

 

Jitai jiri ma na neman kamar É—ibarta. Amma sai batace komai ba tai masa wani irin kallo mai Æ™unshe da abubuwa masu yawa ta juya kawai ta ajiye kayan hannunta a saman gadon. Komawa tai wadrobe ta É—akko hijjab zata saka kawai, amma sai ta tsinkayi muryarsa yana faÉ—in, “Kayan duk zaki canja zuwa wasu, bana son wannan turaren kuma idan zaki fita, idan zaki saka a gida fine ko zakiyi wanka da shine ba babu damuwa a gareni. Sakawa a fita ne dai bana so dan haramunne ma a gareki ba faÉ—a ta bace.” bata tanka masa ba, sai kayan data É—auka ta nufi toilet dan taga baida alamar fita, ita kuma taci alwashin bazata kulashi ba a yanzu saboda abinda ke a gabanta. Tsaf ta sake shiryawa cikin wasu kayan ta saka hijjab É—in ta fito, sai ya samu kansa da kafeta da ido. Dan tayi Æ™yau matuÆ™a a cikin hijjab É—in fiye da waccan ranar. Shi da kansa ya É—ibar mata kayan yay gaba tabisa a baya tana taunar lips na danne masifar dake cimata zuciya. Baya ya ajiye mata kayan tare da miÆ™a mata hannu alamar ta bashi key É—in motar dake hanunta.

 

Rai a É“ace ta ce, “Bana buÆ™ata”.

 

“Kema kin san aikina ne ai hakan”. Ya faÉ—a babu wasa shima a tattare da shi. “Aina faÉ—a maka na kore ka”.

 

“Ban koru ba, dan bake kika É—auke ni aiki ba ai ko”. Ya sake bata amsa a dake yana zare key É—in tare da jan hanunta ya tura ta kujerar kusa da driver ya maida ya rufe. Zagayawa yay shima mazaunin drivern. Koda yaje gaban gate sai da ya fita ya buÉ—e sannan ya zo ya fita da motar ya sake komawa ya rufe gidan sannan. Tunda suka É—auki hanya babu wanda ya tankama wani, gara shi ma ya miÆ™a mata Æ™aramin flaks da ya haÉ—a mata tea a ciki. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tana harararsa. Murmushi kawai yay batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga tuÆ™insa. Kai tsaye office ya kaita, inda suka samu abokan aikinta suna tsaiwar jiranta duk da safiya ce sosai. Motar na shigowa suka shiga mata marhabun su Zainab na mata spry da Æ™yalkyali mai Æ™amshi da ga shi har ita. A take aka shiga musu murnar auren. Kamar yanda ya dake yana amsawa itama sai ta dake tana amsawa. Sunci kusan mintina goma a wajen kafin Zainab ta kwashi kayanta suka wuce office, shi kuma sai ya fito bayan sun É—an yi magana da security É—in nan da a yanzu suka saba sosai ya samu napep ya shiga ya koma gida………✍️

Post a Comment for "Furar Danko 78"