Duk karfin Izzata Book 1 Page 29
Episode 2️⃣9️⃣*
Zaune yamma tan Ammi suke a palon sama na É“angaren Ammi, suna ta hira hiyana na duba takar dun ta na boko diyana na kallon awayar Zahra amrat na karatun qur’ani, Zahra da lamrat suna kallo a makeken Tv dake manne a bango,
da sallama yaya Khalid ya shigo palon, har suna haÉ—e baki wajen amsa masa sallamar kariso wa chiki yayi ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1 murya kasa kasa hiyana tace “ina wuni yaya Khalid ya mai jiki, kakalo murmushi dole yayi kafin ya amsa mata da “lfy sister ya shirye shiryen koma wa makaranta ina fatan kungama shiri, hiyana zatayi magana Zahra ta rigata “ina wuni yaya Khalid, dawo da kallan sa kan Zahra yayi kafin ya amsa da “lfy sis love ykk, sunkuyar da kai kasa Zahra tayi dan jin sunan da ya kirata yau ta tashi daga Auta ta koma sis love.
Yaya Khalid ya mai jiki chewar diyana “jiki da sauki sister ya aikin kai coffee, sai lokachin diyana ta É—auke blue eyes nata daga kan wayar Zahra ta mai da kallonta izu kan yaya Khalid “hmmm ai inayi ku jiyama na kai masa kuma.. bata karisa maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna abun da yaya Aryan yace mata akan idan ta kuskura ta faÉ—a wa wani abun da baa tambaye taba to sai ya É“allata,
ganin tayi shiru ta kasa karisa maganar yasa yaya Khalid É—an sakin murnushin kaÉ—an dan yasan Aryan ne ya mata gargaÉ—i kuma hakan ba karamin daÉ—i ya masa ba dan diyana tana sakin layi dayawa
“To ku shirya fa gobe zaku koma school kunji daman abun da nazo faÉ—a muku kenan yana kai karshen maganar ya miÆ™a ya nufi hanyar fita, har suna haÉ—e baki wajen chewa to,
Abangaren Ahmad kuwa
Zaune Aryan yake a gefen gadon da Ahmad ke kwanche yana kallon face nashi “bro zaka chi wani abune, É—aga ido sama Ahmad yayi alamar a’a “why bro, why ba zaka chi abinchi ba tunfa jiya da rana baka chi komai ba haba, É—aga ido sama Ahmad ya kuma yi alamar aa ba zai Chi komai ba, Aryan zai sake magana sai ga Bgs ya shigo tare da wani likita
zama Bgs yayi kusa da Aryan Dr kuma ya fara kokarin sakawa Ahmad ruwa dan ta taimaka masa tun da baya chin komai,
“Yallaboi ko dai zaku gwada maganin gida ne tun da na asibiti yaki chewar Dr yayi Maganar dai dai lokachin da yake É—aure hannun Ahmad dan neman jijiya,
wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace “Allah ya kyauta abawa É—an uwana wan nan dattin, zan nemo kwararrun likitochi daga kasa da ban da ban suzo su du bamin shi, “Allah ya baka hakuri sir, Chewar Dr ya karisa maganar dai dai lokachin da ya gama sawa Ahmad ruwan, ya tattara kayan aikin sa ya nufi waje
Kallon Bgs Aryan kafin yace “bro wai yanzu menene abun yi, shiri Bgs ya É—an yi kafin yace “ban yi tunani a kai ba amma muje zuwa anjima dole musan abun yi ya karisa maganar yana mikewa, mikewa Aryan ma yayi suka fita tare
Misalin karfe 2 na rana gaba É—aya family sun haÉ—u a palo dan chin abinchin rana ban da Bgs Aiman Fahad da kuma Ahmad, shiru palon ba abun da zakaji sai karan spoons
“My daughter ya kama ki koma gidan ki yau kinji, chewar Abba yayi maganar yana kallon Aunty farida, Mardiya salma Maryam dukka ku shirya kuma kuwuche gidan mazajen ku, “Abba daman gobe in Allah ya kai mu zan koma nariga na faÉ—awa dady’n junior ma chewar Aunty farida, chikin dashe war murya wadda da kaji kasan tasha kuka har ta koshi Aunty salma tace “Abba pls ka barni na kara koda 2dys ne sai mugani y jikin Ahmad É—in zai kasanche “a’a Salma ban yar da ba gobe idan Allah y kaimu kafin karfe 1 kowache ta koma gidan mijin ta, wai ma idan kuka zauna kara masa lfy zakuyi ne? Akoi waya duk abun da ake chiki zan sanar daku ai addu’a kawai yanzu ya ke bukata awajen ku bawai kubar gidan mazajen ku, kuzo ku zauna kusa da shiba,
Har suna haÉ—a baki wajen chewa to Abba Allah ya bashi lfy, gaba É—aya palon suka amsa da amin
shiru palon ya sakeyi ba mai magana kowa kawai tsakuran abin chin yake dan kamar magani suke jin abinchin ba dan daÉ—i suke chiba sai dan kar yinwa ta musu illatasu,
“My daughter kayan nan sun miki kyau Chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana, daman kamar jira take tafara surutu “Abba ai yaya Aryan ne ya bani ji, daman tare ya kawo mana da su Zahra shine ya kulle nawa chikin jaka, sai jiya ya buÉ—e min kuma Abba kaga wata dan kareriyar sar…bata karisar da maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna yaya Aryan yace idan ta faÉ—awa wani sai daketa, jin bata karisar da maganar ba yasa Aryan sauke wata nauyayyar Ajiyar zuchiya wadda yasa Abba É—agowa ya kallesa, kuma sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa diyana ta dakata da maganar bata karisa ba.
saboda jin baki irin na Abba sai yace
“My daughter ya kika dakata da maganar, a sukwane Aryan ya É—ago yana kallon Abba, harara wasa Abba ya wurga masa, da sauri ya mai da kai kasa yana É—an murnushi dan ya gano abun da Abba ke shirin yi, “babu komai Abba kawai dai na manta me zan faÉ—ane diyana ta faÉ—a tana satar kallon yaya Aryan,
mamakine ya kama Abba daman ya tambaye tane dan yaji shin diyana tayi hankali ne ko kuma dai da saura, abun da ya bashi mamaki kuma shine yau diyana che da karya abun da bata taɓayi ba tab lallai na yar da yanzu kam diyana na Son Aryan daman zargi kawai nake Amma bari dai na sake gwada su.
“My daughter ina malamin makaranta kun nan daya taÉ“a chewa yana Son kin nan?
ÆŠaure fuska diyana tayi ta É“ata rai ta turo baki ta fara magana “to ai ni Abba bana son shi soja nake so kuma ai ni tun ranan ma ban sake ganin sa ba wata kila ma ya bar makarantar, kila kuma mutuwa yayi waya sanin masa, gaba É—aya mutanen palon sai da sukayi mamakin É—aure fuskantar da diyana tayi har shi kanshi Aryan dan tun da suke da ita basu taÉ“a ganin ta É—aure fuska ko ta É“ata rai ba ita ko dukan ta akayi tana gama kuka zata koma dariya
“My diyana menene abun É—aure fuska kuma? Ai ba wan da zai miki dole mijin da ki ke so shi zamu baki chewar Aunty farida “to ai Aunty farida ni bama wan da nake So sai yaya Khalid a sukwane gaba É—aya jama’ar palon suka É—ago ido suna kallon ta musamman ma Aryan da atake idon nasa suka sauya zuwa jaa saboda kishi, itakam diyana bata ma san sunayi ba ta chigaba da magana “yaya Khalid yaya Yusuf yaya Aryan yaya Bello Aunty Zahra Aunty mardiya Aunty salma Abba Ammi Ummi Aunty amarya hiyana lamrat da amrat da ke Aunty farida sai Bappa na da Inna ta, ku kaÉ—ai kawai nake so aduniya, wani ajiyar zuchiya Aryan ya saki, ya duÆ™ar da kai ya É—auki wayar sa dake gefen hannunsa kan table É—in, yashiga latsawa
“Hiyana karfe 3 dai dai ki dama fura ki ka womin fada Chewar Abba yana magana faÉ—in hakan ya miÆ™e ya nufi waje,
NmiÆ™ewa Aryan Khalid Yusuf sukayi a tare suka fice daga palon, “haidar muje mu duba jikin yaya Ahmad ko Chewar Umar “eh ya kamata kam ya kai karshen maganar tare ta mikewa, mikewa haidar É—in ma yayi suka nufi waje, a tare Aunty Salma da Aunty mardiya ma suka miÆ™e suka fice daga palon, Aunty maryam Aunty amarya suma tare suna mike suka fita, Ummi da Ammi kuwa betroom É—in Abba suka miÆ™e suka shiga, palon ya rage daga aunty Farida sai su diyana.
“My diyana daga yau idan kinje É—akin yaya Aryan karki sake daÉ—ewa kina jina koh? Chewar Aunty farida, “to Aunty farida ai shi yake chewa in zauna muyi magana ta karisa maganar tana turo É—an karamin bakin nan nata
“eh ko yache ki zauna kiche kina jin barchi sosai, jiya fa har karfe 10 ina É—akin ku ina jiran dawo warki, amma baki da wo ba, kamar zanzo na kiraki sai kuma nache bari na bari da safe sai na miki faÉ—a, “to Aunty farida ba ke ki kache idan naje É—akin na rinÆ™a koya masa surutu ba tun da baya magana kuma kinche ni bazai bugeni ba ko na masa surutun “eh daaa ni nache hakan amma yanzu na fasa saboda idan namiji da mace suka keÉ“e to na ukun su sheÉ—an ne,duk da zan iya shedar kanne na a ko ina, amma dai daga yau kina kai masa coffee É—in ki dawo kinji, “to Aunty farida kawai na daiii na kai masa coffee É—in mana tun da hakane “aa karki dai na kai masa ki chigaba da kai wa kinji amma dai da kin kai sai ki dawo, “to kawai diyana tace tare da miÆ™ewa ta nufi hanyar fita “kutashi muje Zahra, chewar Aunty farida, gaba É—ayan su, suka mikewa a tare suka nufi waje,
Karfe 3:5
Da sallama hiyana ta shigo fada hannun ta riƙe da kyakkyawar kwarya ta rufe shi da pai pai, ta sanya zumbulele hijabi har kasa ajikin ta fari tas, fiskar ta sai kyalli take bawani make up da tayi asalin kayan tane kawai,ga ɗan bakin nan nata pink sosai kamar tasa jambaki, geranta kuwa kamar tayi caving, idan mutun yaga hiyana zai rantse da Allah tayi make up, amma haka fuskar ta yake,halittar Allah ne duk da kwayar idon ta Blue ne amma idon nata farine tas manya manya kamar ball, kuma idan ta kalleka kache tasa kwalli amma ba ta saba haka idon yake gata da bakin kwanche cin gashi mai tsantsi a gaban goshinta ga wani baki haɗadɗen saje a kwanche a gefen kumatun ta dogon siririn hanchin nan nata kuwa baa magana har baka yake, duk lokachin da tayi murmushi sai wani haɗaɗɗen dimple irin na Bgs ya lotsa, ga hakoranta farare tas sai wani ɗan siririn wushirya a tsakiyan hakoranta na sama
a hankali take takawa kamar mahauniya, gaban kujerar Abba taje ta duÆ™a kasa ta, dukar da kai chikin ladabi da girmama wa tace “barka da hutawa Abba, wani murmushi Abba ya saki dan shi har chikin ran shi yana kaunar hiyana sosai akoi ta da ladabi da girmama na gaba da ita ga sanyin hali bata son hayaniya son addini ga sun katun boko da arabic dukka,
Da fara’a Abba ya amsa mata, san nan ta juyo kasa kasa ta kallin in da Bgs ke zaune tace “ina wuni yaya prince, bai amsa ba kuma bai ko kalli in da take ba saima latsa wayar sa da yake,chikin kwanchiyar hankali
Hiyana bata damu da rashin amsa gaisuwar nata da Bgs yayi ba, dan in da sabo sun saba da halin sa, “Abba ga furan ta faÉ—a tare da É—ago kai ta miÆ™awa Abba kwaryan dake hannun ta,
Ansa Abba yayi zai yi magana Bgs ya mike yana faÉ—in “Abba zanje É—aki sai da daddare, “aa Safras dawo ka zauna ai ban sallame kaba, ba don yaso ba hakan ba ya koma ya zauna dan ba yadda zai yi da Abba ne kuma ba zai iya yiwa Abban musu ba
dawo da kallon sa Abba yayi kan hiyana dake duƙe kanta na kallon kasa
“My daughter jeki kawo wa yayan ki nashi furan kinji, to kawai hiyana tace san nan ta miÆ™e da sauri ta nufi waje
“Abba nifa bazan sha wan nan abin ba Chewar Bgs É—in ya faÉ—a yana yamutsa fuska kamar wadda yaga kashi, “Allah sai ka sha, na dai faÉ—ama ni ba santin furar bane ya jani har nabi Ammin ku Yola na kasa samun kwanchiyar hankali sai da na Aure ta, kuma ita ta koyamin sha dan nima da bana sha É—in, “to Abba ai kai kache ba ni ba ni kam bana so kyama yake bani “koma me yake baka Allah sai ka sha na dai faÉ—ama ka, kasani ma ko daga sha…. Sai kuma Abba yayi shiru bai karisa maganar ba, dan yasan in ya karisa to wlh ko ya zai yi Bgs ba zai sha furar ba, shi daman Bgs ba wani sauraron maganar Abba yake ba kasan chewar yasa blooth a kunne É—aya,
Da sallama hiyana ta dawo fada hannun ta riÆ™e da kwayar nono da ta damawa Bgs, har gaban sa tazo ta duÆ™a chikin ladabi da girmamawa tace “yaya prince gashi nan, wani dogon tsaki yaja chikin tsawa yace “dole sai na ansa ne bazaki ajiye a kasa ba,
“mikomin nan my daughter Abba ya faÉ—a yana miÆ™a mata É—ayan hannunsa joyowa tayi wajen Abba a hankali ta miÆ™a masa kwaryan muryan ta har rawa yeke saboda tsoro tace “Abba zan iya tafiya, “aa my daughter zoki zauna a kujeran nan kema muyi hiran dake yayi maganar yana nuna mata kujerar kusa da shi da ido.
Ba musu ta miƙe ta koma saman kujerar ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa,
miÆ™awa Bgs kwayar nono Abba yayi yana faÉ—in “ansa kasha idan nima bazaka ansa a hannuna ba sai naji, rai a bace Bgs yasa hannu ya ansa kwaryar,batare daya kalli Abban ba,
ajiye wayar sa a gefe yayi, yasa hannu yachire pai pai da aka rufe kwaryar, kara É“ata fuska yayi lokachin da green eyes nashi yayi arba da damammiyar nono,
yaji fura ga kwakwa da dabino,amma duk da haka Bgs sai É“ata fuska yake, a hankali ya É—auki ludayin ya É—ebi nono ya kai baki sa sai wani tsuke hanchi yake wai dan kar yaji warin nonon.
….Duk abun da ya keyi Abba na kallonsa, a chikin zuchiya sa yana faÉ—in ai yau sai kasha nonon nan.
a sukwane Bgs yayi wurgi da kwaryar nono ya miƙe da sauri kafin ya kai bakin kofar fada ma ya fara kwarara amai,dukawa yayi kasa,kawai ya chigaba da Aman,
da sauri hiyana ta mike jiki na bari a zuchiyar ta tana faÉ—in, nashiga uku wayyo Allah yanzu shike nan na sashi yin amai nasan sai ya hukun tani.
Ajiye kwaryar nono dake hannun sa Abba yayi ya miÆ™e ya nufi Bgs dake duÆ™e yana ta kwarara amai kamar zai amayar da kayan chikinsa, dafa kafaÉ—arsa Abba yayi ta baya yana faÉ—in “sorry, my Son,
sosai bgs yayi amai dan sai da idon sa suka sauya sukayi jaa saboda wahala “my daughter bani ruwa a freij Chewar Abba, chikin tsawa Bgs yace “bana so Abba banson duk wani abu da yaran nan zasu taÉ“a da hannun su, kyamar su nake ji Abba shiyasa nache maka ni bazan sha ba, shiru Abba ya É—an yi kafin yace “to me tama ka da kake kyamar ta, “Abba ta taÉ“a zubamin jin… Sai kuma ya dakata yana yamutsa fuska “ok kawai Abba yace san nan ya wuche ya É—auko masa ruwan da kansa ya kawo masa
Chikin tsawa Bgs ya kuma chewa Abba kace ta bar É—akin nan ban son ganin ta, tun Abba bai yi magana ba hiyana ta fita da gudu tana kuka, shiru Abba yayi yana tunanin me yasa Bgs ya tsani hiyana haka har zai che baya son ganin ta
Kuskure baki Bgs yayi san nan ya miÆ™e ya nufi hanyar fita, ido kawai Abba ya zuba masa har ya fice daga fadan, Ajiyar zuchiya mai nauyi Abba ya sauke kafin yace “Allah ya shiryamin Safar ai ko me ta maka bai kamata ka tsane ta haka ba, yarinya bai war Allah, marainiya, bani da wani burin da ya wuche a che yau ka auri mace irinta shiyasa nake kokarin haÉ—a ku, Amma tun da hakan bazata yiwuba dole na samo maka wata matar dan tun da kafara furta ka tsaneta nasan da iya gaskiyar ka ka tsane ta, kuma idan nache zan haÉ—aku tofa ni da kaina zan kashe maraini yar Allah, Ya Allah ka sassautawa Safras wan nan zuchiyar tasa, yana kai karshen maganar ya juya ya koma kan kujeran sa, ya zauna, ya É—auko waya ya kira masu aiki akan suzo su goge amai da Bgs yayi da kuma nonon da ya zubar,
Ƙarfe 9:10 pm agogon Nigeria ta buga
Taku take ɗai, ɗai, kamar wata mahauniya, sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar riga abaya pink colour, ta yafa mayafin rigar a kanta, yau dai batayi kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai ɗan man baki da tasa a bakinta,fuskan ta sai kyalli take, tasa high heel pink tana rike da ɗan karamin plate mai ɗauke da cup, san nan ta rufe cup ɗin ma da wani ɗan ƙaramin plate mai shegen kyau, ta nufi part ɗin Aryan
ko sallama babu ta faÉ—a chikin palon kasa kai tsaye ta haye sama stair É—in ta shige palon sama nan ma ba ko sallama ta shige, kai tsaye betroom É—in sa ta shege, babu kowa a chiki, table É—in tsakiyar É—akin ta nufa ta ajiye cup É—in, ta juya da sauri dan gargaÉ—in da Aunty farida ta mata akan karta daÉ—e.
Dai dai zata fita taji an buÉ—e kofar toile É—in, da sauri ta wai go karaf idon ta suka sauka kanshi É—aure yake da towel a kugun sa.
ga jikin sa a jike da alama wanka yayi, wani kara ta saki ganin yadda kiran jikin sa yake afili, kafin yaya Aryan ya juyo tayi waje, da gudu, a sukwane ya bi bayan ta,
saboda high heel dake kafarta bazai bari tayi wani gudu sosai ba, a dai dai zata fita palon sama ya damko kugunta ta baya, sama ya É—aga ta da hannu É—aya ya juya da ita cikin É—akin, ihu diyana keyi, tana faÉ—in “yau kam na shiga uku yaya Aryan dan Allah kayi hakuri wlh na rantse maka bansa zaka fito ba kaya bane da bazan gan ka ba kuma ai ni, ban ganka sosai ba, shidai ko sannu bai che mata ba saman katafaren gadon sa yayi kurgi da ita san nan ya koma ya rufe kofar É—akin ya zare makullin ya nufi dressing room nashi,
shiru diyana ta kwanta tana kallon sama kasa kasa ta fara magana “yau kuma aljanun mugun tan yaya Aryan ne ya dawo ko?, to ni me ma na masa shiru ta É—anyi kamar mai tunani sai kuma ta chigaba da magana “kai lallai yaya Aryan ashe haka hannun shin nan yake kato kamar chinyar lamrat, kut lallai yana da nama sosai amma kuma shine yake saka riga ya É“oye wlh in ni ne shi bazan É“oye ba ai hannu mai nama sosai É—in yafi kyan gani, bari ya fito idan bai dake ni ba zan che masa ya faÉ—amin me yake chine hannunsa tayi nama dayawa haka nima inrinÆ™a chi ko nawa zaiyi, jin motsin shine yasa ta miÆ™e zaune tana zare ido
Fito wa yayi sanye chikin kayan barchi mai kyau da tsada gaban morrow ya tsaya yana gyara gashin kansa, Almost 10mnt ya É—auka a gaban mirrow san nan ya juya ya nufi saman sofa ya zauna, duk abun da yake diyana na kallonsa ta wutsiyar ido amma bata bari ya kamata tana kallon sa ba duk da chewa shi É—in ma duk abun da yake idon sa na kanta.
A hankali ta zuro kafafunta kasa san nan ta sauko daga gadon ta nufi inda yake, gaban sofar da yake zaune,tazoe ta sugun na, Murya na rawa tace “yaya Aryan dan Allah kayi hakuri kaji,
“laifin me ki ka min da kike bani hakuri, da sauri ta É—ago kai, “laaaaa yaya Aryan da gaske ban maka laifi ba, kallonta kawai yake dan yanzu tama dai na bashi mamaki, “yaya Aryan in tafi É—aki ta Tambaya tana kallon face nashi yayin da shima ita yake kallo “a’a tashi ki kawomin coffee din kizo ki zauna muyi hira “aa yaya Aryan Aunty farida tace na daina daÉ—e wa a dakin ka “me yasa zaki dai na dadewa a dakin nawa, dariya diyana tayi kafin tace “Aunty farida tace idan namijin da mace suka keÉ“e to wai na ukun su sheÉ—an ne, a sukwane ne Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallonta, ganin ita ko ajikin tane ma yasa yace “ok to dauko coffee din ki kawomin sai kizo ki buga game kaÉ—an da wayata kafin ki koma É—akin na ku, da sauri ta nufi table din tana murna ta É—auko masa coffee ta kawo masa, ya ansa ya mika mata wayar sa shi kuma, gefensa ta koma ta zauna tana latsa wayar.
“Yaya Aryan kasan me, batare da tajira amsar sa ba ta chigaba da magana, Allah ko kwanan nan ina tunanin yaya bello sosai ina kewar sa
, wani tarine ya sarke sa coffee din ta haura masa kai sosai yake tarin, asukwane ya ajiye cup É—in coffee É—in ya dafe kansa da hannu É—aya yana tari,
da sauri diyana ta ajiye wayar ta nufi freij ta É—auko masa ruwa, ta dawo ta mika masa, bai ansa ruwan ba sai yasa hannu ya damko wuyar ta ya fisko ta da karfi ta faÉ—a kan faffadar kirjinsa, sosai yake tari ya kasa magana, ita kuwa da sauri ta É—ago kai daga kirjin nashi, jin yadda yake tari, chikin tsoro tace “yaya Aryan ka sakeni in É—auko maka ruwa dan Allah, da kyar ya iya faÉ—in “babu ruwan ki da ni ki bari tarin ya kashe ni “dan Allah yaya Aryan kayi hakuri Allah bana son ganin ka kana tarin kaji pls, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, “aa ba ruwan ki dani nache maki koh “hannu diyana tasa ta toshe masa baki tana girgiza tana faÉ—in “dan Allah yaya Aryan ka daina faÉ—in haka mana wlh akoi ruwana da kai kuma har da tsaki na, hannunta ya chire daga bakin sa, chikin dashewar murya saboda tarin da yayi, yace “tashi min ajiki kuma ki fitamin a É—aki karki sake zuwa, yayi maganar in a serious matter, “yaya Aryan me na maka to? “Ban sani ba ki tashi ki fita nace, yayi maganar da É—an karfi
Nan take diyana tafara hawaye tana faÉ—in “yaya Aryan to dan allah ka faÉ—amin me nayi maka da kache kar na kara kawo maka coffee, kuma ai nasan kana son coffee din, wani irn raÉ—aÉ—i yaji a zuchiyar sa saboda kukan da take, slowly yasa hannu ya É—ago haÉ“arta suna fuskantar juna runtse ido tayi ganin yadda yake kallonta, calmly ya fara magana “me yasa kike kuka kuma?, Chikin shesshekar kuka tace “to ba kai ne ba kaki ka faÉ—amin me na maka, “ya isa to kiyi shiru baki min ko mai ba kinji, da sauri ta buÉ—e idonta tana kokarin tashi daga jikin nashi kara firgota yayi ta dawo kirjinsa har sai da kanta ya bugi gemunsa.
…É—ago kai tayi suna fiskantar juna pink lips nata har kerma suke, zata yi magana, yayi sauri É—ora yatsan sa a kan lips nata yana girgiza Mata kai, sauko da kansa yayi ya haÉ—e fuskokin su yana kallonta,Wani irin farin chiki da nitsuwa ya keji tana ratsa zuchiyar sa,
lunshe ido tayi dan ba zata iya haÉ—a ido da shiba, goga hanchin sa ya fara yi a jikin nata hanchin, kasa kasa yace ” menene tsakanin ki da Bello?, da sauri ta buÉ—e ido tana faÉ—in “yaya na ne kuma shine idan Inna ta hana mu abin chi yake zuwa ya karÉ“o mana wajen Adda hasana,
“shike nan alakar dake tsakanin ku, “eh shike nan “to amma me yasa ki ka che kina kewar shi? “To ai yaya Aryan kaga yana da kirkine kuma idan na samu kuÉ—i zan saya masa mota da gida dan shima ya dawo birni, “to idan Abba yace zai Aura miki shifa? dariya diyana tayi kafin tace “nifa idan ba soja ba to bazan yi aure ba soja kawai bake so.
Wani dogon nunfashi Aryan ya ja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin ya sake ta “tashi ki tafi É—aki to tun da Aunty farida tace karki daÉ—e, da sauri ta miÆ™e har tana kokarin faÉ—uwa,key din É—akin ya miÆ™a mata,
Ansa tayi, ta nufi bakin kofar tasa key ɗin ta buɗe kofar ta fice da sauri, miƙewa shima yayi ya nufi kan katafaren gadon sa ya kwanta ya lumshe ido yana mai da numfashi,
Washe gari misalin 9 na safe zaune suke a palon Abba kamar yadda suka saba dan yin breakfast.
Ammi ta dubi diyana tace “ke diyana jeki É—auki abinchin babban yayan ku a kichin ki kai masa, a sukwane Aryan ya É—ago dan yasan halin diyana yana son ya hanata zuwa sai dai kuma bai san surutan Aunty amarya dan yasan yana hana diyana zuwa sai Aunty amarya ta sa shi a gaba da tambaya, meke tsakanin su.
Da sauri diyana ta mike Abba na kokarin ya dakatar da ita amma ina har ta fice, kichin ta nufa ta É—auki abinchin nashi already an gama shirya masa fitowa tayi ta nufi part nashi.
Bb ko Sallama ta faÉ—a palon babu kowa kai tsaye ta haye stair É—in ta shiga palon saman nan ma babu kowa kofar da ta gani chikin palon ta nufa ba ko sallama ta shiga,
tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin Black jeans da t-shirt blue, bakarin kyau kayan suka masa ba,kamar dan shi akayi su, jin an buÉ—e kofar É—akin yasa ya zubawa kofar green eyes nashi ta chikin mirrow, ganin diyana che yasa ya É—aure fuskar nan kamar wani zaki ya kau da kallonsa daga kanta
“Kai mai kama da hiyana ga abinchin ka nan anche na kawo maka, a sukwane Bgs ya juya dan jin sunar da ta kirashi kuma har da che masa kai, chikin tsawa yace “get out, diyana ko tsoro tsawar ma bata jiba ta É—an ja tsaki kafin tace “dan ka samu ma na kawo maka abinchi wlh ba dan Ammi ba bazan…. Bata karisa maganar ba kamar wata walkiya ta gefar da kwandon abinchin tayi waje a guje, da gudun gaske Bgs yabi bayan ta sai huchi yake
To masu karatu sai mun haɗu ranar Monday idan Allah ya kai mu, ina masoyan diyana? tofa yau masoyiyar ku ta taɓo gidan rina ato ku tanaji ruwan zafi gasa mata jiki idan ma ta saura da ranta kenan
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
More comments an like pls
*💫STAR LADY💫*30
💖The Talent Troupe Writer’s 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*
Post a Comment for "Duk karfin Izzata Book 1 Page 29"