Duk karfin Izzata Book 1 Page 17
Episode 17*
Ganin Aunty Maryam yasa diyana ta fasa ihu tana faɗin, dan Allah Aunty Maryam kiyi hakuri karkisake bugu wlh yanzuma chiwo kaina kemin, ” a zafafe Aryan yamike tsaye yana faɗin sister kibata wayar kinitsu” ina
diyana batama jinsa ihu kawai take tana surutai ” zama Aunty Maryam tazo tayi a gefen kadan nasu tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya ” hiyana ma jin diyana tayi ihu tana faɗin kar Aunty Maryam tabugeta yasata tafito daga toilet da gudu, ” Zahra ma mikewa tai tana kallan Aunty Maryam ɗin ” da gudu nurse nasuma tafito daga nata ɗakin tashigo nasu, tsayuwa tai daga bakin kofa tana kallan’su ” amrat da lamrat kuwa rungume juna sukayi suka rufe ido ” sai magana Aryan keyi tacikin wayar amma shiru dan diyana tama chire wayar daga kunnen’ta ” ina wanchan dan iskan ya kaiku jiya da’baku kwana a gidan nanba chikin tsawa tayi maganar ” tsagaita kukan da take diyana tayi tunda taga Aunty Maryam ɗin bata fara bugunsuba, san nan murya na rawa tafara magana asibiti ya kaimu, ” shiru Aryan yayi yana sauraron maganar tasu” waye jiya a chikinku yasanar da Aryan na bugeku” har suna haɗa baki wajen chewa wlh bani bace bani bace ” shoothup idan baku kukagaya masaba taya akayi yasani ” shiru sukayi gaba ɗayansu ” ke tashi kije ki wanke toilet’s ɗin bangaren Aunty amarya dukka san nan ki wankemin kana nan kayan dana chire ɗazun inkin gama ki wuche kitchin ki shiryamin abun buɗa baki tayi maganar tana nuna diyana ” mikewa diyana tayi san nan ta’ajiye wayar Zahra dake hannunta, tanufi hanyar fita tana faɗin to ” itama Aunty maryam ɗin mikewa tai tana hararar su hiyana tai waje ” girgiza kai kawai Zahra tai tana hawaye ” hiyana ta tako a hankali tazo ta zauna kusa da zahra tashiga rarrashinta ” chikin ɗakin nurse ɗin nasu ta karisa shigowa itama ta zauna, suka fara sharewa Zahra hawaye ” dan Zahra akoi saurin kuka ” amrat da lamrat ma suka dawo kan gadon suka zauna ”
Shiru sukayi kusan 30 mnt ” hiyana tana kokarin mikewa ke nan sai ga diyana tashigo ɗakin ” da mamaki a fuskar Zahra ta mike lfy diyana kika dawo, kodai har kingama aikin ne, zahra ta tambaya murya na rawa ” aa nidai kawai ina wankin toilet ne, saikuma Aunty Maryam ɗin tace nabari natafi ɗaki, shine nadawo ” baki buɗe zahra tace kai to ya akayi tace kidawo, anya kinji metace ta kyau kuwa ” eh mana Aunty Zahra naji wlh diyana tabata amsa ” hiyana dake tsaye tace to saikutashi muyi sallah ae tunda kin dawo ga lokachi ya kure ” mikewa sukayi baga ɗayansu har nurse nasun ” diyana tashige toilet nasu” lamrat kuma tafito tanufi toilet na ɗakinsu ” zahra kuma tanufi toilet na ɗakin Ammi ” hiyana kuma ta ɗaukoh dadduma ta shinfida dan ita already tariga tayi alwala tun ɗazun ”
Washe gari misalin karfe 3 na yamma gaba ɗayansu suna zaune a ɗakinsu ” hiyana dai karatun Al qur’ani mai girma take ” diyana kuwa sarkin kallo, kallon film take a wayar Zahra, ita da lamrat ” amrat kuwa tayi barchi abunta , Zahra na hira da nurse ɗinsu ” sunyi nisa chikin abubuwar dasuke,” sukaji diran motochi chikin gidan nan, take jiniyar motar yan sanda ya karaɗe ko ina na gidan ” da sauri Zahra tamike tana faɗin Aunty farida oyoyo, zata nufi waje diyana tariketa tace Aunty Zahra ya akayi kikasan Aunty farida che idan kuma kikaje ba itabace Aunty Maryam che zata komafa ” Aunty farida ne dan kuwa ita kaɗaice mai zuwa da kiniyar motar yan sanda, Aunty Maryam kuma da busar gidan sarauta take zuwa, ki gane bambanchin mana , Aunty Maryam ɗan sarki take aure, Aunty farida kuma ɗan tsohon gwamna kuma gwamna mai chi yanzu take aure, zahra na gama faɗin hakan tanufi waje da gudu ” da sauri su diyana’ma sukabi bayanta amma banda hiyana da nurse nasu, dan hiyana bazata iya wani dogon tafiyaba saboda jiri datakeji ,
Aguje Zahra ta tafi tafaɗa jikin Aunty farida dake tsaye tana kokarin fidda kuɗi daga jakarta, bazato ba tsammani kawai taji Zahra ta faɗo mata a jiki saura kaɗan su faɗi ” haba auta sokike ki kadanine ” dariya Zahra tayi san nan tace. To Aunty farida ae murnane yasa na faɗo jikinki, ina junior ” yana wajen baban’sa sai ranar Sallah zasu zo zata sake magana idanta ya sauka akan diyana dake tsaye murmushi ta sakarwa diyanar tare ta yimata alama da hannu a kan tazo ” da sauri diyana tanufeta itama tana murmushi ” haɗesu Aunty farida tayi ta rungume tana faɗin nayi kewarki my sister’s ” muma munyi kewarki wlh chewar Zahra ” sakinsu Aunty farida tayi san nan ta karisa wajen da lamrat ke tsaye, itama ta rungumeta tana faɗin kebazakizo kimin oyoyo ɗin bane ko dai kunyata kikejine, nifa ba surukarki bace ” inawuni y hanya chewar lamrat ɗin ” lfy lau Aunty farida tafaɗa tare da sakinta, ta chiro kuɗi masu yawa tamikawa security ta san nan ta rikoh hannun diyana suka nufi bangaren Ummi ” security na biye dasu da manya manyan trolley a hannu ” su Zahra suka rufa musu baya ” ina hiyana da amrat Aunty farida ta tambayi diyana tana kallan fuskarta ” hiyana na ɗaki tana karatu, amrat kuma tayi barchi , ” ok to meyasameki a baki naga bakin ki yakunbura kodai wajen rawan kan’kine kika fasa bakin ta karisa magamar suna kokarin shiga palon Ummi ” aa Aunty Maryam che ta fasamin ” Aunty farida na kokarin zama a kujera tace.what me ya haɗaki da Maryam kuma tayi maganar tana kokarin zaunar da diyanar kusa da ita ” nan fa diyana tashiga bata lbr abun daya faru tun ranar da Aunty Maryam tazo har yau sai da tafaɗa mata komai ” Zahra dai a tsorace take sosai dan yanzuma basu faɗawa kowaba, Aunty Maryam tace sun faɗa barekuma diyana tazo tafaɗa’ɗin ” Aunty farida ma shiru tayi kuma sai yanzune tagane dalilin daya Aryan yace tayi zuwar gaggawa, kuma batayi mamakin abunda Aunty Maryam ɗin tayiba dan tasan fiyeda hakama Maryam zata iya aikatawa ”
Am sorry my diyana kiyi hakuri kunji yanzu kutashi muje kurakani na dubo jikin hiyanar Koh ta karisa maganar tana mikewa ” suma mikewa sukai, tafita sukabi bayanta
Da sallama suka shigo palon kai tsaye ɗakin’nasu.suka nufa hiyana dai tana zaune inda suka barta, rike da qur’ani tana karatu ” ganin Aunty farida yasa tamike da kyar, tana faɗin sannu da zuwa Aunty farida” karisa shiga chikin ɗakin Aunty farida tayi taje ta rungumi hiyana, tana faɗin am sorry my dear y jikin “da sauki sosaima ” murmushi kawai Aunty farida tayi san nan ta saki hiyana, takama hannunta suka koma baƙin gadon suka zauna ” kin.sha maganin rana kuwa Aunty farida ta tambaya tana kallan fuskar hiyanar ” eh nasha ” ok to zaki iya tafi dan Ina san inje inyi wanka, kuma zanso mutafi tare gaba ɗaya, dan daga yauma har ranar dasu Ammi zasu dawo tare zamu zauna daku a ɓan.garen Ummi ” eh zan iya ” ok to kutashi muje, har sun mike zasu fita sai idan Aunty farida ya sauka kan nurse ɗin’su dake tsaye a gefen drawer ” wacece wanchan kuma ” juyawa sukayi suna kallan inda Aunty farida ke nunawa ” laaa. Aunty farida nurse ɗin.muce chewar diyana ” oh to itama tazo muje tare tunda daman kula daku take yanzu tunda zaku koma ɓan.garen Ummi itama ae dole tabiyo’ku dan kula daku, ” to sukace san nan diyana ta tashi amrat daga barchi ta rikoh hannunta ” ska tanufi waje ” Aunty farida na rike da hannun hiyana
Misalin karfe 6:45 Aunty farida tafito daga ɗakin Ummi a palo taisko’su diyana “suna ganinta suka fara gaishe.ta ” da fara’a ta amsa san nan ta ɗora dacewa kutashi kuje palon Abba muyi buɗa baki ” bamuyi azumibafa dukkanmu Zahra chewar Zahra ” eh nasan baku azumi amma ae zaku chi abinchin dare koh, bama wan nan ba dole muje kutayani chi abinchin ae ” har suna haɗe baki wajen chewa to Aunty Maryam ta hana’mu zuwa palon Abba ” dogon tsaki Aunty farida taja san nan tace.kutashi mutafi hai ” ba musu suka mike gaba ɗayansu ” Aunty farida takama hannun diyana sukayi gaba, su hiyana suka rufa musu baya
Da sallama suka shiga duk da sunsan babu kowa a palon.mamakine yakama diyana da sauri tace.Aunty farida yanaga table ɗin chin abinchin yazama biyu, kuma ankaro kujeru ” eh saboda sallah gaba ɗayan muna zuwane shiyasa, da sallah yakusa ake fito da ɗayan daman table biyune, kinga ae guda ɗaya bazai isshemu, mu dukka bakoh muna dayawa kuma kowani table kujera 12 to kinga ae kujera 12 yamana kaɗan ta karisa maganar tana kokarin zama ” zama gaba ɗayan’su suka zo sukayi ” Aunty farida tana faɗin my diyana kekam sai yaushe zaki daina surutune ” sosai diyana tai dari sai datayi mai isarta san nan tace ae nibana surutu ” Aunty farida dai bata kuma’chewa komai’ba ta kira masu aiki tabasu umarnin suzo su shirya musu abinchi ” chikin hanzari sukafara jeramusu a’binchin san nan suka shiga sarving nasu
Sunyi nisa chikin chin abinchinsu, ba wanda yake magana a chikinsu shiru palon sai dai karan spoon zakaji ” babu ko sallama ta faɗo chikin palon fuskar nan a tamke ” jin motsin anshigo palon yasa dukkan’su suka ɗago suna kallanta ” nan take hiyana ta kankame Aunty farida ” mai da kanta Aunty farida tayi tachigaba da chin abinchinta kamar ma bata san da mutun awajenba ” chikin tsawa Aunty Maryam tafara Magana “banache kada nasake ganinku a kowa bangare na gd nan ba, inba bangaren Aisha ba,” a sukwane Aunty farida ta ɗago kai jin Aunty Maryam tace. Aisha kai tsaye kallan’ta Aunty farida take sosai batare da tace uppan ba ” jin abun da Aunty Maryam tace yasa’su hiyana kokarin mikewa dan subar palo ” muryan Aunty farida ta katse’su dacewa ina kuma zakuje ” juyowa sukayi suna kallan Aunty farida kanta na kallan kasa tana chin abinchin’ta chikin kwanchiyar hankali, kana suka juyo sukaga Aunty Maryam dake tsaye tana jiran, suzo su fiche daga palon nan, ga fuskarta babu annuri ” sun rasa me ɗaya zasuyi kawai suka tsaya chirko chirko ” ganin hakan yasa Aunty farida ɗagowa ta dubi Aunty maryam a kausashe tace kifita a ɗakin nan Maryam ” kara ɗaure fuska Aunty Maryam tayi tace akanme zanfita ” a kan na isa inche kifita kuma kifita dole ” shiru Aunty Maryam tayi tana tunani bazata iya jayayya da Aunty farida ba dan kuwa idan tace zatayi hakan tofa gaba ɗaya gidan nan sai sun hukunta’ta “gashi kuma Aunty farida na neman kunyata’ta a gaban yaran nan, ganin Aunty Maryam ta tsaya shirune yasa Aunty farida chewa ” ke Maryam badake nakeba nace kibar wajen nan koh ” a fusace Aunty Maryam tajuya fuuu kamar wata kunfa tayi waje ” dawo da kallanta kansu hiyana tai tana faɗin ko zauna kuchi abinchin ku” ba musu suka zauna sukachigaba da chin abinchinsu
SAUDIA ✈️
Kwanche yake saman faffadar gadon’sa ya zubawa wayar hannunsa ido sosai yake kallan hoton’ta wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke ” a hankali da murya kamar mai’raɗa yafurta ke kyakkyawa’ce my sister ina kewarki sosai ina butatar, shan coffee ” takun tafiya yaji kuma ko ba a faɗamasaba yasan wan nan takun DON ne ” da sauri yafita wajen hoto ya kashe hasken, screen ɗin wayar ya ajiyeta a gefensa ” da sallama ɗauke a bakinsa yashigo betroom ɗin ” mikewa Aryan yayi zaune yana amsa masa sallamar ” kallansa Aryan keyi daga sama har ƙasa da mamaki yache inazakaje haka naga kasa kaki ” calmly DON yafara magana I need Ur prayer zan dawo jibi sai muwuche naija tare ” like how bangane U need my prayer ba inama zakaje yayi maganar yana kokarin sauka daga gadon ” London zanje yanzu kiran gaggawane, kar kafaɗawa’su Abba dan bansan hankalin’su yatashi ” no gaskiya sai dai muje tare ” aa Aryan taya zamu tafi tare kuma ae idan muka wuce tare dole su Abba su sani kawai ka tsaya ka taremin, insun tambayi ina nake kasan mezaka faɗa musu ” badan Aryan yasoba haka ya hakura yaraka,DON har airport san nan yadawo.
NIGERIA
Bayan sun gama chin abinchinsu ne Aunty farida tace to kutashi muje ɗaki muyi sallar mangariba da issha sai nabaku tsarabarku ” da murna suka mike Zahra na faɗin Aunty farida dan allah kinkawo’min lalle kuma zakimin koh ” sosaima kuwa auta ai daga jibi zan fara muku lalle mai kyan gaske ” da sauri diyana ma tace Aunty farida nima inasan lallen sosai zakimin” eh mana my diyana dukkanku zan muku ” jerawa sukayi Aunty farida na rike da hannu diyana ” sunzo zasufita palon ke nan ” jiri ya kwashe hiyana tatafi luuuu zata faɗi da sauri nurse ɗin tarike ta tana faɗin ” wlh yarinyar nan ta bugu sosai a kantan nan tana bukatar kulawa sosai ” a sukwane Aunty farida ta juyo hannu tasa ta taimakawa nurse ɗin suka rike hiyana sukayi bangaren Ummi,
A kam doguwar kujera suka kwantar da ita nan take nurse ɗin ta koma bangaren Ammi ta haɗo musu magungunar’su ta dawo ” ɗaya bayan ɗaya tabisu da kanta ta basu maganin sai da ta tabbatar sunsha san nan takoma kan nata kujerar itama ta zauna ” Zahra ki shiga chikin ɗakin ki ɗaukoh min babban trolley na ɗin nan kuje da diyana ta kama miki chewar Aunty farida ” to su’kace a tare suka mike suka nufi chikin ɗakin
Jim kaɗan suka fito da katan akwatin Aunty farida da kyar suke jan trolley ɗin ” a tsakiyar palan suka ajiye sai nishi suke kamar wayanda sukayi wani aikin wahala ” saukoh wa kasa Aunty farida tayi tazo ta buɗe trolley, ɗin nanfa tafara fitar musu da tsarabar’su komai iri ɗaya ta sai musu ” manya manyan lufaya na kanuri ta sai musu masu kyau da tsada kowa kala bibbiyu Pink da blue ” sai dogayen riguna masu manya manya mayafi kala uku² tabawa kowa da baki da ja dakuma porpul colour ” ga wasu manya manyan ribons na ɗaure gashi da manya manyan bit ” sai turare masu kanshi da kayan kwalliya sai takallama kafa uku 2
Sai murna suke sunamata godiya musamma ma diyana nata murnan daban ne dan an kawo mata kayan kwalli kit guda sai dariya take ” daukoh turare mai tsada da dogon riga mai kya Aunty farida tayi taba nurse ɗin, ansa tai tanata godiya
To kutashi ku kai kayan ɗaki ku ajiye sai rananr sallah yanzu jibi zamuyi lalle raanar Friday kuma zanmuku gyaran gashi dan gashin kun nan bazai kitsuba yayi tsantsi dayawa shiyasa na sai’muku wayan nan bit ɗin dan namuku kitso guda biyu a gaban goshi kawai nasamuku bit ɗin nan, sauran gashin kuma ayi parking ta baya ” sai murna suke har suna haɗa baki wajen chewa to tare da mikewa gaba ɗayan’su kowa rungume da kayansa zasu fita ” Aunty farida tace. Inakuma zakuje ” dakinmu zamu kai kayan zahra tabata amsa ” aa ae nafaɗamuku sai Ammi ta dawo zaku koma bangarenta dan haka kuzo ku kai ɗakin Aunty mardiya ku ajiye, kuma a nan zaku rinƙa kwana ” ba musu suka juya suka nufi ɗakin Aunty mardiyar suka ajiye kayan nasu chikin sip san nan suka dawo Palo
YOLA
Abun duniya ya ishata yau anwayi gari babu komai na chi a gidan ga azumi ba abun chi idan anyi buɗa baki, zama tayi tana tunanin yazatayi, chankuma tayanke shawarar ta ɗaukoh 1k a chikin kuɗin data ajiyewa boka tayi chefanen abun da zatachi, Allah barshi kafin lokachin komawarsu wajen bokar sai tanemo wani kuɗin tachikasa da wan nan tunanin tamike tanufi ɗakinta ” ɗaga gadon chiyawarta tayi ta ɗaukoh kuɗin ta chiri 1k ,ta maida sauran, ta ɗauki mayafita tayi waje dan zuwa yin chifene
KANO
Ku tashi kushiga ku kwanta dare yayi kunji chewar Aunty farida ” to kawai suka amsa mata tare da mikewa gaba ɗayansu har sun kai bakin kofar betroom ɗin Aunty mardiya” Aunty farida tace. aa to ae gadon yamuku gaɗan diyana da amrat suzo mukwana a ɗakina itakuma nurse naku taje wan chan ɗayan ɗakin ta kwana, tana gama faɗin hakan tamike tanufi hanyar fita ” harta kai kofar fita tsaikuma ta juyo tana faɗin diyana kuashiga ɗakina keda amrat ku kwanta ina zuwa zanje wajen Maryam ” to kawai sukache san nan suka nufi ɗakin nata itakuma tayi waje, su Zahra ma nuka shige ɗakin Aunty mardiya nurse nasu kuwa tawuche ɗakin da Aunty farida ta nuna ”
Da sallama Aunty farida ta shiga palon Aunty amarya babu kowa dan haka kai tsaye tawuche ɗakin Aunty Maryam da sallama tashiga kwanche ta isko ta tana latse latsen ” ko amsa sallaman ma batayiba bare ta ɗago kai ” Aunty farida bata damu da hakanba wuche tayi ta zauna a bakin gadon a nitse tafara magana ” tashi inasan magana dake ” mikewa Aunty Maryam tayi zane, a kausashe tace to me kikeso yanzu kuma ” daure fuska sosai Aunty farida tayi san nan tafara magana ” meyasa kika bugi yaran nan mesuka miki ” dogon tsaki Aunty Maryam taja san nan tace abun da kikazo jike nan to na buga kuma babu abun da sukamin kawai naji inasan bugun’sune shiyasa na bugesu, ko zaki rama musune ” juyowa Aunty farida tayi a fusace ta ɗauke Aunty maryam da mari tana faɗin ni sa’ar kice dazaki zauna kina faɗamin magana ” a fusace Aunty Maryam ma ta ɗaga hannu..✍️✍️
More comments pls 🙏🙏
💖The Talent Troupe Writer’s 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*
Post a Comment for "Duk karfin Izzata Book 1 Page 17"