Bakar Ayah 34
Page 🖤34🖤
Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka.
“Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan”
Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa.
“Wacece matar,tana waje har yanzu?”
“Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi”
“To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi”
“Wani kallon mai kuke Æ™ullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta É—ora dacewar”
“Wani kam iyani mai kuke Æ™ullawa da wannan matar ne kam,kardai kicemin dama wani abu zakuyi da ita shiyasa kikaxo,naga tunda kikazo garinnan ko gidan su iyah bakijeba,in kuka fice a gidannan da safe bakwa dawowa sai dare,gashi kince jibi zaku tafi”
“Ahhah bakomai fah karki damu,yau dama zan shiryah naje musu,har gidan Addah Sa’ade zanje”
Daga haka tayi saurin kawar da zance tayi É—aki,inda Hajiya zeenah take.
Tana shiga ta maida labulen tareda ƙarisawa inda Hajiya zeenah take zaune da sauri.
“Hajiya an kawo wasiÆ™a,inaga fah daga wajen Bombee ne”
Tafaɗa tana miƙa mata wasiƙar.
Karba tayi cikin sanyin jiki ta buÉ—e.
_Na amince da aikinki,saidai bisa sharaɗin nan masu zuwa. Maimakon miliyan ashirin zaki bani miliyan Hamsin,sannan kuma ba wata shida nake buƙata ba shekara gudan nake buƙata,idan kafin sannan nafitar miki ita daga gidanki contarct yaƙare daga nan,idan kuma na haura shekara guda ban fitarta ba nan ma contract ya rushe,zan kuma maido miki da kuɗinki.
Inkin amince da sharaÉ—ina gobe za’a É—aura auren a address É—in dana rubuta,wata masallacin juma’ar garinnan.
Waliyyin É—anki yazo gobe za’a É—aura auren bayan sallar juma’ar,akwai wanda nakeso yaji aurenne,kekuma bakida haÉ—i sa hakan tunda ba garinnna kike ba.
Bayan É—aurin auren Hilyaan zasuje itada khamees suyi duk abinda nakeso wajenda zan zauna yakasance.
Niba yanzu zan biku ba saina gama wani abun,kuma yarona bashida kafiyah a yanzu ,baxanyi tafiyah dashiba_
Wannan shine bayanina inkin yarda akwai takarda a ciki kiyi sign,akwai nawa sign É—in a jiki,idan kuma baki yarda ba karkiyi sign ki dawomin da takardar haka.
From BB
Ajiyar zuciyah Hajiya zeenah tasake tareda miƙawa iyani takardar itama ta karanta.
“Inkinada biro kawomin zanyi sign”
“Hajiyahhh wai kin yarda da abinda tace,miliyan hamsin fah kuma kiji wasu sharudda kamar uwar mutane”
“Ki miÆ™omin biro kawai na amince dasharaÉ—inta,sa’a tace dana samu ta amince,idan bata amince ba inaji a jikina ciwo zuciyah zai kamani na takaicin lubna,wanda inna kwanta in miliyan É—arine ma zan cinye ban warke ba. Dan haka ki miÆ™omin biro da kuma wayata,zan Æ™ira alhaji kan batun waliyyin Jabeer É—in”
Daga haka iyani batasake cewa komai ba,sai miƙowa Hajiya abinda ta buƙata din.
Allah sarki bawan Allah da bai É—auki duniyah a bakin komai ba,yana zaune akan kujerar sa bayan Madeenah ta gama Kawo masa maganinsa yasha bayan ya karyah.
Wayarsa ce tayi ringing,yana dubawa yaga sunan matar tasa,murmushin manya yayi kafin ya ɗauki ƙiran.
“To mai kuma yafaru uwar yara”
“Sai abu ya faru kafin na Æ™iraka,yajikinnaka,ina fatan dai suna kulada maganinka akai akai”
“Ko kinannan ma dama ai suna kuladashi sosai,ya abinda kikaje nema,kinyi nasarane”
Eh ta amsa masa a hankali,dan tasani sarai ya É—agota ganin Æ™iranta yanzu,sabanin yanda take kirannnasa sai dare kawai tun zuwanta gembun”
“Nayi nasarar samun amincewarta,yanzu aure za’a É—aura gobe,kayiwa Baffansu magana akan yin walin,inyaso saisu taho a jirgin dazaizo É—aukar mu”
“Ahah Karki saka Abdullahi kan wannan maganar taki,kinfi kowa sanin yanda abin zai kasance,kedai ki bari akwai wanda zan turo goben idan jirgin zai taho. Saidai har yanzu kina ganin yin wannan auren shine mafitar wannan matsalar? Kaman yanda kika faÉ—a nabar miki ragamar abin,na zuba miki idone naga wanne irin gyara zakiyi?…”
“Komai yana tafiyah daidai, na tabbatar komai zai tafi yanda na tsara”
“To shikenan Allah ya baki sa’a,kin faÉ—awa shi É—annaki abinda yake faruwane na aurennasa gobe?”
“Karka damu zan sanar masa a goben idan an É—aura auren,kuma ma aiba yinsa zanyi dan……..shikenan nan dai komai zaizo daidai”
Daga haka Hajiya zeenah tayiwa mijinnata sallama ta kashe wayar.
Kallon wayar yayi bayan takashe
“Hmmm idan na faÉ—amiki ki kwantar da hankalin ki bakyajin magana,yaronnan ya girma,amma har yanzu son zuciyarki ya hanaki kigani,muje zuwa,ina fatan wannan abin dakika É—akko dakanki yayi silar gane kurenki batareda wata babbar matsala na,nasan idan nahanaki yanxu damuwa zakisa a ranki dazai jawomiki ciwo……kai Allah ya kyauta”
Ƙara daga wayar yayi yasake ƙiran wani manager amininsa a company,wanda yasaka a boye ya dunga kulamasa da mai ake a wajen.
Magana sukayi akan yashirya zuwa gembun sannan kuma yazama waliyyin Jabeer ɗin a auren,Babu yanda zayyi,yasan idan yaƙi saka hannunsa yabarta taje tayi yadda taga dama,zata iya jawo matsalar dasai tafi bai saka hannunba.
A ranar su Hajiya zeenah basuje ko inaba,dan haka iyani ta samu damar fita zuwa ga danginta,itakuma Hajiya zeenah tasamu damar hutawa na zirga zirgar da tayi.
Washagari Ranar juma’a bayan an gama sallahr juma’ar ne mutane sukaji ana sanarwar É—aurin auren.
Sunan da aka ambata shiya girgiza mutane ba kaÉ—anba,wai Bombee zatayi aure,shikansa uban amaryar bai san da zancen ba sai dayaji an ambaci sunan.
“An É—aura auren JABEER ALIYU da kuma MARYAM AHMAD.kan sadaki Dubu hamsin”
Nan da nan kuwa kaman iska labarin auren Bombee yazagaya waje da dama,wasu sai murna suke zata bar garin tatafi. Yayinda wasu kuma har sannan basu gama yarda da lamarin ba.
A zaune take tana kallon window tayi shuru alamar mai tunani.
Hilyaan ce tashigo É—akin tareda cewa.
“An É—aura auren kaman yanda kika faÉ—a,amma miyasa ba aure bane normal kikayi shi cikin jama’a ba’a sirriba,mutane sai labarin auren sukayi”
“Saboda sonake kowa yashaida auren,musamman gidanmu,akwai wanda nakeso su sake ransu cewar na tafi,daga baya kuma saidai suga bayyanata batareda sunyi tsammani ba”
“Uhm toh shikenan yanzu kuma saime za’ayi,naji kince zamu farayin gaba kafin ki taho ko”
“Eh zakuje kuga wajen da tace zan zauna,inda matsala ku Æ™ira ku faÉ—amin,sannan ku saka duk abinda nake buÆ™ata,nan da kwana uku zan taho idan nagama abinda nake”
“Hmmm yanda suka bada labari kaman matarsa batada mutunci”
Ƴar dariya Bombee tayi tareda cewa.
“Wannan yana É—aya daga cikin abinda yasa na karbi aurensan,na daÉ—e bansamu abin nishadi ba kaman wannan,har na matsu naga abinda zai kasance,sannan kuma bayan lokaci mai tsayi finally zan koma garin Abuja”
Dan jijjiga kai Hilyaan tayi tareda fita zuwa É—akinta,saboda tattaro kayanta,dan an sanja tafiyar daga gobe zuwa yau. Babu zancen bata lokaci yanzu zasu tafi tareda su Hajiya zeenah.
Tafiyah yake a mota yana jin labarin da ake a gidan rediyo,hankalin sa yayi nisa wajen sauraron shirin da ake na Filin zamantakewar aure.
Ƙarar wayar sa ce tashashi ɗauke kansa daga kan hanyar ya kalli mai ƙiran.
Sunan Mommah yaga akan wayar,hakanne yasaka ta a jikin mota wajen ƙiran waya. Sallamar ta yaji ta doki dodon kunnensa,a ransa yace yau kuma koda wannne tazo?
“Hello Jabeer kana jina?”
“Eh ina jinki Mommah”
“Tamm Abbanku ya turo mana da jirgi É—azu,yanzu haka muna hanyar dawowa,na sanja dawowar sai gobe,kaje gida ka faÉ—awa su Madeenah dawowa ta,na Æ™ira wayarsu bata shiga”
“To shikenan dama ina hanyar gidan zan faÉ—amusu”
“Ohh bazaka tambayi ya abin ya kasance bane?”
“Mekenan dama ba fasawa kikayi ba,shiyasa zaki dawo?”
“Ka taba ganin nasa abu a gabana na fasa,ai ka kwantar da hankalin ka,nayi nasarar shawo kan matar danaje aura maka,yanxu haka an É—aura auren muna hanyar dawowa,ka fara Æ™irgawa ka kusa rabuwa da wannan jarababbiyar matar”
Bata gama faɗin bayanin datake som ƙarisawa ba Jabeer ya kashe wayar,saboda wani bugu da kirjinsa yayi batareda ya shirya ba.
“Innalillahi Allah gani gareka shin wa nafi tsorone a cikinsu,Ummata ko kuma Matata,ga ………..”
Bai gama maganar ba yaji alamun yabuge wani abu a gabansa,da sauri yaja burkin motar,amma duk da haka daga yanda yaga mutane suna taruwa a wajen yasan akwai abinda ya bige.
Saurin fitowa yayi daga motar tareda ture mutanen da suka taru a wajen.
Bayan mace yake kallon sanye da milk É—in hijabi,kowa sai sannu yake mata,ita kuma ta sunkuyar dakai batace komai ba.
“Subahannallahi baiwar Allah bakiji ciwo ba dai koh”
Ɗago darara dararan idanuwanta tayi farare tasss ta sauƙe su akan fuskarsa,daga kallon zubin yarintar fusakarta bazata wuce shekara 17 ko 18 ba,kyakykywace ajin farko idan ana samun irinsu,ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke tareda sauƙe idanuwanta tana kallon hannunta wanda yake dauke da ciwo a jiki amma ba mai yawa ba.
Wani irin yarr haÉ—e faÉ—uwar gaban Jabeer yashiga a lokacin guda,wanda tunda yake bai tabajin yanayin ga Wata mace na,harda kuwa marigayiyar matarsa hafsah.
GabaÉ—ayah notin kansa ya kunce,baisan lokacin da yakai hannu kan inda ciwon yake ba,tana ganin hakan tayi saurin É—auke hannunta tareda cewa.
“Karka ta’bani”
Cikin wata murya mai ma’abocin taushi da sanyi.
“Jaleelah mai yasameki haka dama ke aka buge naga mutane,kinji ciwo sosai”
“Ahaha Fareeda ba sosai bane,mugafi gidamana kar dare yayi mana a waje”
TafaÉ—a tana tattaro litattafanta da suka zube akan titi.
Dogon hijabi ne har ƙasa,sannna kuma akwai rubutun larabci a jiki hakanne ya tabbatar daga islamiyyah suke.
Ko kallo dayah basu sake yiwa Jabeer ba suka kama hanyar zuwa gida.har sukayi nisa Jabeer yasaka motsawa bare yayi ƙoƙarin basu hakuri ko yimusu magana,tun lokacin da muryar yarinyar tashiga kunnensa.
Shawarar da Khaleel yabashi Kwana biyu da suka wuce ya tuna….
“”””Kasamu wacce zuciyar ka takeso ka aura,mai ilimi da tarbiyya,wacce zata kwantar maka da hankali idan suka tayar ma””””
ÆŠan murmushi yayi tareda shiga motarsa yafara bin bayan Æ´an matan………
Kashshshsshshshhsshh Makaranta,anan muka kawo ƙarshen littafi na ɗayah a cikin Labarin Baƙar ayah.
Domin Samun cigaban labarin da kuma tambayoyin da suke cikin kanku,ko kuma son jin wacce chakwakiya ce zata faru kaman haka
__Menene maƙasudin abinda yafaru da mahaifiyar Bombee?
___shin kuna zargin inna laari kaman yanda Bombee ke zarginta?
___miliyan hamsin bashine kaɗai abinda zai iya sakawa Bombee ta amince da ƙudirin Hajiya zeenah ba,sannan kuma ta buƙaci shekara guda maimakon wata shida meyasa toh?
_____Ga Luban….Ga Bombee…….Ga Jawaheer……sannan kuma ga zabin shi uban gayyar wato ……..Jaleelah!!!!!
Wacce chakwakiyace zata balle tsakanin wannann matan idan suka kasance ƙarƙashin inuwa guda,gasuda halaye mabanbanta???
Sannan waye uban É—an Bombee,shin Jaan family zasu yadda tazo musu da shege cikin gida???kuma shin zata iyah maganin Lubna kaman yanda tace………..
Masu magana sunce BAƘAR AYAH…….Itama cikinta farine. Shin wacece baÆ™ar ayah a cikin matannan,anya kuwa zata kasance farar kaman sauran BaÆ™aÆ™en Ayar???
Kaɗan kenan nasan daga amsoshin da suke cikin kanku,Amma karku damu duk zaku samesu cikin sauƙi idan kuka cigaba da bibiyar littafin a Arewabooks.
Ku sauƙe app ɗin kana kuma kuyi search littafin BAKAR AYAH zai fitomuku waral domin karantawa.
Ga wanda basu ganeba domin ƙarin bayani su tuntubeni ta wannan layin
09035784150
Wanda bazai iya karantawa ba a arewa book shima yayi min magana domin shiga group É—in littafin,idan an gama kuma sai ya siyah littafin document a wajena.
SADI-SAKHNA najiran isowarku makaranta❤❤❤❤ mu haÉ—e a littafi na biyu,ina yinku cikin carbi🤣🤣🤣
Alhamdulillah Alah kulli halin
Post a Comment for "Bakar Ayah 34"