Bakar Ayah 33
Page 🖤33🖤
Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa.
“Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu”
“Okay toh”
Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar.
“Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu”
Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar motah.
Tafiyah akayi mai nisa dasu zuwa wani waje daban wanda basu samu damar sanin inane ba,sauƙa akayi daga motar aka fara zansu zuwa wata hanyar. Nan ma saida akayi tafiyah mai nisa kafin aka basu damar tsayawa.
Jikin su Hajiya zeenah banda rawa babu abinda yake,dan sun saddaƙar gidan yankan kai aka kawosu.
“Yau nashiga uku nakawo kaina kabarina da kaina”
Hajiya zeenah tadaɗa a hankali,muryah murdaɗɗen mutum taji yana cewa.
“Mun iso ku ciremusu ƙyallen fuskarsu”
Kafin ya rufe baki sukaji an fizge yadin dayake fuskarsu,kamar za’a rana kansu da gangar jikinsu.
A hankali suke saita hasken wajen da kuma ƙarfin idonsu,babu wani haske a wajen,saidai saboda yawan ƙofofi da wajen yakeda shi,kai tsaye mutum sai ƙarewa abinda yake wajen kallo.
Wani irin ɗakine mai girman gaske,babu abinda yake jikin bangon ɗakin sai hotunan mutane kala kala anayi musu azaba salo salo.
Wasu irin winduna ne a cikin ɗakin ƙanana kuma a can saman silin ɗin ɗakin.
Ga mutane masu baƙaƙen kaya guda kaman goma a gabansu sunyi cirko cirko.
Kallon ɗaya mutum zaiyiwa ɗakim hantar cikinsa ta kaɗa,dan kana samunka cikin ɗakin karon farko zakayi tunanin ba a duniyah kakeba.
Wani na daga cikin mutanen ya matso gabansu ɗauke da zarto a hannunsa babba.
Cikin kakkausar muryah yafara magana mai amsa amo.
“Shin bazaku faɗamin maiyasa kuke neman shugaba ba,ku faɗamin wanene ya aikoku yanzu nan,kafin na gundule kan tsohuwa”
Kunna abin hannunsa yayi yafara ƙara,wanda kowanne ƙara ke sake gusar da ɗan nutsuwar zuciyar dake jikin su Hajiya zeenah.
Cikin karfin hali da tattaro dukkan jarumtarta tayi magana,wanda take ganin ita kaɗaice zata ceceta a halin da take ciki.
“Bada niyyar cutarwa muke neman Bombee ba,saboda wani taimako dazatayiminne. Sannna babu wanda aikoni,buƙatata ce ta kawoni wajenta”
Tsayawa yayi cakk jin abinda Hajiya zeenah tafaɗamasa,
“Shin kozaki faɗamana dalilinnaki?”
“Zaifi kyau idan iya nida ita mukayi maganar,abin bai shafi wani abin cutarwa ba,inzaka iya ka haɗani da ita akan maganar”
Suna cikin hakanne wata farar matashiya tashigo wajen,
“Khamees ka tsayah da wannan abin,Anty maryam ta buƙaci ganinsu a sashenta yanzunnan”
“Meee daga zuwansu har zata gana dasu…..”
“Haka tace na sanar dakai”
Sauƙe makamin hannunsa yayi yana kallon su Hajiya zeenah ƙasa ƙasa,juyawa yayi yabar wajen sauran ma suka bishi a baya.
Sauƙe ajiyar zuciya Matashiyar tayi tareda kallon su Hajiya zeenah tasake tattausan murmushi.
“Hmmm karku damu yanada saurin fushine,kuyi haƙuri da abinda yafaru….sunana Hilyaan,ko zaku iya biyoni zuwa wajenta”
Lokaci ɗayah Hajiya zeenah taji hankalin ta ya kwnata,saboda abinda yarinyar tafaɗamata.
Cikin sanyin jiki suka fara bin bayanta zuwa barin wajen,har sannann hankalin su bai kwanta ba.
Bayan sun fita daga ɗakin wata hanya sukabi wacce tayi hanyar wani ɗan ƙaramin gida a can gefen inda suka fitan.
Suna tunkararsa ƙyansa da kuma ƙawatuwarsa yana ƙara fitowa fili,babu wanda zai ce akwai irin wannan gidan a jejin inba gani yayi da idonsa ba.
Dan haka yakasance tamkar an ɗakkoshi an ɗorashi a wajen.
Suna shiga cikin wajen wani ƙyatacce ƙamshi yayimusu sallama a cikin wani mayalwaci falo.
Nuna musu wajen zama tayi kafi tayi wata hanyar da wani corridor yabi.
Bata dade ta tafiya ba wata mata mai dan shekaru ta shigo falon dauke da tiren kayan marmari a hannunta.
Ajiyemusu tayi cikin sakin fuska kafin tabar wajen.
Haɗiyar yawu iliyah yayi ganin yanda kayan marmarin suka nuna lutsa lutsa,tashi ɗaya sha’awar ya luma haƙoransa a cikin tuffan(apple) dayake gabansa ta taso masa.
Hannu yakai a hankali zai ɗauke,Hajiya zeenah ce tayi saurin buge hannunsa tareda yin magana ƙasa ƙasa.
“Wannan a kwaɗayinsa sai ya jawo mana abinda zai kashemu,wani inya ganshi zaicd bayacin kayan gabass”
“Ko ɗayah bazai mutu ba dan yaci wannan abin,shin a yanda kukaji labarina nayi muku kamada wacce zata sakawa mutum guba a abinci ta kasheshi……ahah ahah bana kaiwa farmaki ta baya kaman matsoraciyah ta gaba nake tunkarar koma waye,konayi nasara koshi yayi ni hakan shine nasarata”
Dukkansu ɗaga ido sukayi a tare suna kallon mamallakiyar muryar datayi maganar.
Fara ce sol amma ta sirka yellow bakaman fatar masu jan kunneba,tanada tsayi da kuma mulmulallen jiki wanda babu alamun tarin tsokar ƙiba a jikina.
Duk inda aka zayyano fulanin usul akan siffanta su da kyansu daidai gwargwado,ita baza’a cireta daga irin nasu kamanninba,saidai ita koma bayan su ,tana ɗauke da shuɗiyar ƙwayar ido,wacce tabata kamanni irinna turawan yamma,harma yafinasu yin kala da kuma radiating ɗin haske.
Idanuwannata dara dara ne farare,da suka samu baƙin ƙwalli da shudiyar ƙwaya,saita bayyana kaman ba daga duniyar tamu tazo ba.
Shuɗiyar doguwar rigace a jikinta,amma bata kamata har can ba,tana jingine a bakin ƙofar shigowa falon,da alama bata cikin gidan yanzu da shigo.
Ɗauke hannunta tayi daga bakin ƙofar inda ta dafa,kafin ta ƙariso cikin falon,a kan kujera mai ɗayah ta zauna wacce take facing ɗinsu.
“Sannunku,bansan ku suwaye ba,amma labari yazo kunnena tun lokacin da kuka buɗi baki cewar kuna neman Bombee a karo na farko. Lokacin danaji labarin wai wasu sunxo nemana nayi mamaki.
Mai kuke nema a gareni haka, dahar kukebin gari kuna nemana,koma menene nasan babban abune. Dan a lokacin da muruje yabaku labarina nayi zaton zaku haƙura kukoma inda kuka fito,saikuma kuka bani mamaki,dasafe ma sai aka ganku kunsake fitowa nemana”
Tsuru tsuru sukayi,lallai wannan matar taci wannan labarin da sukaji,wato duk yawon dasuke na nemanta tana sane kenan.
Har Hajiya zeenah ta buɗi baki zatayi magana kukan yaro ya ƙatseta,wanda Hilyaan ta shigo dashi tareda nufar inda Bombee take zaune.
Hannu ta miƙa ta karbeshi tareda tambayar Hilyaan ɗin.
“Mai yasameshi hakane,baya kuka irin haka akai akai,kuma likitan yazo ya dubashi kaman yanda nace?”
“Eh ya dubashi,inaga fah kaman ɗan zazzabine yake damunsa,sannan kuma kaman madarar da aka fara bashi jiyane yajawo hakn”
“A daina bashi madarar nan sai yayi wata shida tukunna,har yanzu bai girmaba,nidama nasan madarar nan rayiwa jikinsa girma,ki fita da ita daga gidannan,nafasa bashi ita,zan rage aikin zirga zirga na dunga shayarshi kawai,he need my time too,not only my matter”
Karban yaron tayi tana shirin fitar masa da mama,Hajiya zeenah ce tayi sauri bugar iliyah akan yabasu waje,da sauri kuwa yatashi bayan ya suri tiren kayan marmarin.
“Ohh sorry fah,banida manner ne sosai wani lokacin”
Bombee tafaɗa ko a jikinta lokacinda take sakawa yaron abincinsa a baki.
“Uhm ……uhm bakomai ne ya sakani tasowa daga inda nake nazo wajennan ba saidan wani taimako danake son kiyimin”
“Taimako wanne iri kenan kuma a guna?”
“Inasone ki auri ɗana na wani lokacin ƙayadadde,daga baya kuma sai a raba auren”
“Aure nikuma????? Kinsan mai kike cewa kuwa?”
“Ehh aure,karki damu babu abinda zai haɗaki da ɗana idan shi kike tunani,aikin dazakimin ba akansa bane,akan matarsane”
“Hhhhh nikuwa nasan ba abinda zai haɗani da danki,a labarin da aka baki da kuma wanda kika gani,kin shaida inada ɗa batareda aure ba,babu uwar dazata yarda ta haɗa ɗanta da mace irina,dole akwai abinda kike buƙata gameda kalmar auren.
Karki ɗaukeni jahila kaman yanda kikaji labari,wancan a dane ba yanzu ba,ki tafi kaitsaye ki faɗamin me kikeso”
Taƙaitaccen labarin lubna Hajiya zeenah tabawa Bombee,da irin ƙarfin ikon ubanta da kuma abinda take aikatawa. Sannan kuma taƙara da cewa.
“Ta hanyar aurene kawai zaki iya min maganinta,kasancewar ubanta yanada babban matsayi a kotu,idan abu kikayi mata ta hanyar kishi baza’a zargeni da komai ba.
Tana da ƙarfin hanya ta kowacce siga,idan nace zan turasashi yasaketa kuma tayi masa asirin dazai mutu a ranar,dan haka nayi bincike naga ke kaɗaice nakeda wacce zaki iya yimata abinda dakanta zata nemi sakin batareda matsala ba”
Ɗan guntun murmushi Bombee tayi,danta fahimci inda zancen Hajiya zeenah ya nufah.
“Hhhhhhh kuma a yanda kika ban labari sai kikaga nayi kama da wacce mutum zai taso yazo yasakani abinda yake so na matsalarsa na magance masa,shin kama nayi miki da mai taimakon gyara aure?”
“Ba taimakona zakiyi kawai ba,aiki na kawomiki,auren iyah Wata shidane kawai,ko kuma gwargwadon yanda kika karya lagwonta,sannan zan baki Miliyan Ashirin idan kikayi min aikim”
“Hhhhh miliyan Ashirin?? Kibar wannan zancen,nizan tsara komai yanzu,shin na yarda da zanceki ko kuma akasin haka.
Hilyaan zata karbi bayanan komai danake buƙata gameda lamarin,zanyin bincike nan da gobe.
Ki saurari aikana daga nan zuwa goben,na sallameku zaku iya tafiyah idan takarbi bayanin danake so”
Daga haka Bombee ta ɗauki ɗanta tayi wata hanyar daban.
Bayan tafiyar tane Hilyaan ta zauna da labtop ta karbi duk wani abu daya shafi Lubnah da kuma shikansa Jabeer ɗin.
Mota Bombee tasaka aka maida su Hajiya zeenah inda aka ɗaukesu,inda suka shiga gidan da jiran tsammanin sako daga Bombee ɗin.
“Wai amma fah Hajiya tanada kyau sosai,yanda aka bada labarinta kuwa haka take”
“Hmm kyan ɗan maciji ba,kyanta bazai ruɗeniba kamar kai, tana gama abinda zatayimin zata ƙara gaba,kasuwanci ne zai haɗamu kawai. Na kula shima shegen ɗannata irin idonta ne dashi”
“Wai Hajiya anya kuwa bazaki kai tashin hankali ba gida,karki manta fah da ɗanta zataje,sannan yanda iliyah yafaɗa tana kyau,kar aje a samu matsala fah da Yallabai(Jabeer).
“Kumin shuru ko karen haukane yaciji ɗana mai zayyi da wannan matar,bayan haka ma anayin wananan ma zai aure wacce tun farko tadace dashi ai Wato Jawaheer,wannan bakomai bace illah Mai aiki wacce aka ɗakkota damin tayi a biyata. Mujira dai muji mai zata ce gobe,koma menene ni bazan fasaba daga kan ra’ayina”
……ku garzayah arewabooks domin Samun Cikekken labarin da kuma yawan pages fiyeda wanda kuke samu nan.
_*Sadi-sakhna ce*_
Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
_Mashaallah A yau Allah ya ara mana lokaci mun gama littafin BAƘAR AYAH na farko._
Ga duk ɗaukacin masoyana ina godiya sosai.
Gobe in allah ya kaimu zan fara post littafi na biyu a AREWABOOK.
Sannan kuma a ranar zan buɗe group a whatsapp.
Duk mai buƙatar littafi na biyu zai turo Naira *300* ta Wannan jaddawalin kamar haka.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Masu turo da kati zasu tura katin mtn ta nan
09035784150
Mutanen niger zaku tura *300f* ta wannan layin.
+227 97 21 16 15
Mai ƙarin Bayani ya tuntubeni ta layina
09035784150
Ko direct whatsapp message
https://wa.me/message/MAPXUDCCPXCGP1
______________****_______________
Post a Comment for "Bakar Ayah 33"