Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bakar Ayah 21


Page 🖤21🖤

 

Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba.
“Inna……inannnaaaa”
Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa.
Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta hanyar baraxana akan ƴaƴannasu,dan ta kula mutanen agwagine,basu san komai ba sai soyayyar ƴaƴan su.
“Inna ki daina wannan damuwar haka,indai akan wannan aurenne ni zan iya sakawa a fasashi idan bakyaso”
“An zo wajen,ba auren dazai miki ne abin tashin hankali na ba,ke abinda zakiyi a aurenne abin tashin hankalina”
“Kaman yaya inna,taya zanyi shuru amin wai aure,wazai ganni yace nakai aure,ni babu abinda nasani akan wani aure,dan haka kuma bazanyi shi ba”
“Kinga koh,do wannan ne yasakani damuwa ba aurennaki ba,inkinason farincikina kuma ki daina ganin dakuwa ta,to ki dunga jin duk abinda babanki ya umarceki dashi,bana son kinayi masa musu akan abinda yasakaki”
“Hmmm nifah bawai inason yimasa gardama bane,kawai ni banson duk abinda nakeso shikuma yahanani,abinda bana so kuma kullum shi yake sakani,ni bana so ana shiga rayuwata irin haka,abinda ma yafi bani haushi shine,sai munyi magana dashi akan zanyi wani abu ya amince,daga baya kuma sai yaxo yacemin abinnan bai yarda dashi ba.
Taya inna kike tunanin zan yarda kullum yadunga yimin haka kuma……..”
“Saurin buge bakin Bombee Daneji tayi,tareda yin magana cikin bacin rai”
“Wani nikam yaushe zakiyi hankali ne kam,kullum kina girma kina cin ƙasa,wannan harkar maganar tantiran zaki zo kina min anan kina cije min baki,kuma wai duk da mahaifinki kike. Kenan bashida ikon sakaki abu komai koke nufi?.
Aure kuma saura naji kinyi wata tsiyar akai nida kene dan kinga ana ƙyaleki koh? Tashi ki bani waje,aure babu fashi”
Cune baki Bombee tayi tareda barin cikin ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Daneji tayi,tabbas dolene tayiwa tufkar hanci,idan tana son su shiryah da Bombee da kuma ubanta.
“Allah kayi mana maganin matsala”
Tafaɗa cikin kasalalliyar murya.
Shirye shiryen bikin Bombee aka farayi da GOJE ɗan gidan jauro,wanda suke wata Ruga nesa dasu kaɗan.
Goje mutum ne majanuni,saidai shi ƙarin tsiyarsa harda innarsa wacce take ɗaure masa gindi,kullum idan yayi abu sai tace bashi bane,daga kan satar gaji ya fara,har yaxo kan satar shanu suje su sayar.
Yanzu har ta kai yana haɗa baki da ƴan daba ayi babbar sata,wani halinsa ma na takaici shine har fyaɗe yanayiwa ƙananan yara,idan an kai ƙara wajen HARƊO sai ya shafe zancen,saboda maƙudan kuɗin da Goje yake bashi.
Tun Bombee tana yarinya goje ya ganta yace yana sonta,da jauro yazo ya samu mlm Ahmadu da zancen ya fatattakeshi,akan ƴar sa saliha babu abinda zatayi da wani goje. Haka jauro yakoma yafaɗawa ɗansa abinda mlm Ahmadu yace,duk da shikansa da farko dama yasan abin bayyi ba,DAYEE ce matarsa ta dameshi saida yaje,wato mahaifiyar goje.
Yanzu kuma kwatsam jauro yana wajen shanu saiga mlm Ahmadu yazo ya sameshi,nan yake faɗamasa cewar ya amince da auren Bombee da goje,abin yabawa jauro mamaki,saidai yayi shuru bai ce komai ba,a ganinsa koma menene bazai zafafa ba,dan burinsa shine ɗannasa yayi aure kozai shiryu yazama mutum.
Lokacin da aka faɗawa goje baƙaramin farinciki yayi ba,danshi saboda kyanta dakuma idonta yake sonta,dan dama shi mutum ne mai son kayansa yazama daban dana kowa,lokaci guda aka tashi gyaran ƙofar gojen wacce take cikin gidansu,yaransa kullum cikin gyara suke duk na zuwan amaryar tasa nan da sati biyu masu xuwa.
“Goje ana maka sallama a waje”
“Wanene?”
“Bansani ba yace dai jauro yake nema,to da nace masa baya nan saiya ce kazo kai ɗin”
“Buge Indo yayi ƙanwarsa wacce tace anayi masa sallamar kafin ya fita waje”
Hayaniyace ta fara tashi a wajen,kana jiyo muryar goje dakuma wani daga cikin gida.
Inna dayee ce tayafa mayafinta tareda nufar ƙofar gidan.
“Kai goje mai yake faruwane,kaida waye haka,kace musu jauro bayanan yatafi Gassol jiya”
Idonta ne ya sauƙa kan wata yarinya a bayan wata mata,shikuma namijin sunata magana shida goje.
“Zakace haka mana ka bata mana yarinya,gatana ai bazata yi maka ƙarya ba,ka musa idan bakayi mata fyaɗe,aradu daga nan wajen jauro zan wuce nayi ƙararka”
“Ƙara akan me naji ana zancen ƙara kuma,wani akayi maka,kayanka akaci Mlm?”
“Ina kayana ɗanki yaci ai da sauƙi,ƴata ya lalatawa rayuwa,in baki yarda ba kata ki tambayeta,kaita lungu yayi yai mata fyaɗe,sannan kuma ya gargaɗeta akan kada ta faɗa.
Jiya yarinya tafara amai ashe ciki gareta,saida nabata azaba kafin ta faɗamin gaskiya. To bazan yardaba aradu sai anbimin kadu.
Kuma yarinya dole ya aureta tunda ya lalata ta”
Dariyar rainin hankali inna daayi tayi,tareda tafa hannaye.
“Heeee sai yanzu ka sosa inda yake maka ƙaiƙayi mlm,kace kawai ƴar ka tagama yawon dambaɗewa kanason mannawa ɗana ita saboda kaji zayyi aure,to ahirrr dinka munfi ƙarfinka munfi ƙarfin wanda ya tsaya maka ma.
Ba wajen jauro zaka kai ƙaraba ka kai cikin gari ma idan kanaso,haka kawai kowa sai yazo yana laƙawa yaro sharri,dan kawai kunga yayi farinjini yaki auren ƴaƴan ku,duk ina sane da abinda kuke ai,kowa so yake ƴarsa da auri goje saboda ta haifamuku ɗa namiji kuci dukiya,toh aradu baku isa ba.
Kaikuma ka bacemin daga ƙofar gida,ko kuma nacewa arɗon kunzo har gida kunyimana sharri.
“To shikenan tunda haka zakice,kowa a rugar nan yasan tsiyar da ɗanki keyiwa Al’umma,amma saiku danne kurufe,saboda kuna da hanya a wajen Manya,babu komai a akwai Allah,zakuga yanda zaku ƙare dashi.
Lalatacciyar uwa mai boye laifin ɗanta,zaki samu wanda zai yi maganinsa kuma babu yadda zakiyi”
Mahaifiyar yarinyar ce tafaɗawa inna daayi cikin muryar kuka,hannunta rikeda dana yar tata wacce itama take kukan.
Dan takaici shi uban ko magana bayyi ba,sai turasu dayayi suka tafi. A hakan ma daayi bata barsu ba tana iyowa daga bakin ƙofar gidanta.
Sai bayan sun ‘bacene Inna daayi ta juya takalli goje wanda yake yangara hakora yana hura hanci,shi a dole an bata masa rai,amma kana ganin idonsa kasan bashida gaskiya a lamarin.
“Yanzu duk yanda nayi dakai akan kadaina wanann halin yanzu aure zakayi baka daina bako,a hakan kake tunanin zasu baka auren idan suka san haka kake?”
“Na nawa kuma ai sun riga sun sani,a tunaninki haka kawai zasu bani aurenta tana hankali, hmmmm itama tantiriyace lamba ɗaya.
Saikiyi shirin karbar tantiriyar suruka inna”
Zaro ido inna daayi tayi tareda jan ajiyar zuciya.
“Kuma kasan hakane ka nace saiak aureta,yanzu duk ƴaƴan dana kawo maka ka aura kaƙi,dama dan ka auromin irinka ne cikin gidannan,aikuwa zan saita mata zama,dakanta zata bi yanda kowacce mace take a gidan aurenta”
“Hhhh a tunaninki zan kawo matata ki dunga yimata izaya ina kallo,ba iya son Bombee ne yasakani aure nan ba,saboda naga yanda zatayi dake a cikin gidannan ne,baki san halinta ba sunanta kikeji,amma kije ki buncika ki gano da kanki”
‘Dama hakane ?’ ta faɗa a ranta.

_____*_____*_____*___

“Ungo karbi kisha yanzu nan”
“Wannan ɗin menene inno?”
Bombee tafaɗa tana yamutsa fuska
“Kinci gidanku banace karki tambaya ba,ki shanyeshi yanzu nan,wacce zatayi aure ai saida gyara,kuma gobe ma ki tabbatar kin dawo,sannan dama na riga na hanaki bin Shugabannki jeki,karki ƙara yin tsalle tsallen nan bana mata bane”
Duk abinda inno tak faɗa Bombee tana jinta,ba abinda takeyi sai dariyah ƙasa,ita mantawa ma take da zancen sai anyi maganar tukunna.
Haka gidama tashi ga tafita,sunata aikin shirye shiryen biki. Jiya fitowar ta takalli ana shigowa dakayan gado cikin gidan,babu abinda take ayyanawa a ranta sai irin kuɗin dazasuyi idan ta siyarsu.
“Lahh inno gwanda dakika tunamin,dama fah inason naje nayi ɗan bincike akan shi wannan gojen”
“Ahah karki je dakanku,ki bari Mlm yasaka ayimiki,wai sau nawa zan faɗamiki ki daina hakane kam,tashi ki tafi gida ma ya isa haka,sai gobe kuma”
Tashi Bombee tayi batareda tayi musu ba takaɗe rigarta,wajen da yayi ƙasa.
Hanyar ƙofar gidan tayi batace komaiba ta kamo hanyar barin jejin.
Jijjiga kai inno tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,duk cewa batayi mata musu,amma hakan bashi ke sakawa tayi abinda tasakata ba. Tasan ko tsafi take da zaba Bombee bazata haƙuraba sai tayi binciken dakanta.
Haka take wata irin murɗaɗɗiyar yarinya ce itah,da kaɗan kaɗan tsoro sai barin cikin idanuwanta yakeyi,a hankali take sauyawa zuwa wata macen taban.
Da farko abin kaman ƙuruciya,amma kuma tana girma tana ƙara fitar da halayyarta na tsayawa akan ra’ayinta.
Duk da kasancewarta ba mai sabo da mutane ba,amma haka kawai Allah ya haɗata da jinin Maharbi Uwaisu,shida matarsa inno,basuda ɗa ko ƴa shiyasa sukejin Bombee har cikin ransu,duk su kansu sunsan batada daɗin sha’ani.

Hasashen inno bai tashi a banza ba,maimakon Bombee takama hanyar tafiyah gidansu,saita kama hanyar da zata kaita rugar su goje a ƙafa.
Tana tafiyah tana ƴar waƙa,irin wanda takeji a gidan rediyo,harta isa ga rugar.
Lokacin anyi magriba duhu ya kawo kai,wani mai gasa masara ta haɗu dashi a bakin hanyar yana da aikinsa.
Tsugunnawa tayi kaman abin arziƙi tace.
“Uh dan Allah bawan allah idan bazaka damuba tambaya nake”
“Allah yasa na sani toh”
“Inaso ne ka faɗamin duk abinda kasani gameda Goje dake rugar nan,kama daga mugayen halayensa harma da abinda yake aikatawa”
Kallon bakida hankali yayi mata,tareda yin dariyar rainin hankali.
“Mai yasa kake dariyah,bazaka faɗamin ba ko kuma kana tsoro”
“Tsoro? wazanji tsoro,tambaya ma kike akan meyasa bazan faɗamiki,dallah tashi ki bani waje tunda bakida hankali”
Kama bakin tiren gashin masarar tayi kaman mai shirin watsa masa garwashin a jikinsa.
“Ke me kike haka?”
Rashin hankalin nakeso na nuna maka banida shi kaman yanda kake tsammani,shin zaka faɗamin ko kuma sai na gasaka kaima da abinnan.
Zaro ido yayi tareda cewa.
“Keee ki bari aradu ina tsoron faɗamiki,zance yadawo ace a wajena kikaji”
“Tom tunda tsoro kake sai zabi na biyu,kwatanta min gidansu”
Kwatancen yafarayi mata batareda musu ba har ya gama.
Tashi tayi zata tafi,maganar sa ce ta ƙatseta ta tsaya catt.
“Mm….me zakiyi a gidansu,yarinya bazai ƙyaleki bafah idan wani abu kike nufinsa dashi,sannan kuma innarsa ta ɗauremasa gindi,ko ƙara kika kai baza’a saureriki ba”
“Wow kaga ka bani amsoshin tambayoyina dayawa,karka damu ba wani abu zanyi masa ba,kawai zanje gun innarsa ne na tambayi waye shi,dan nasan tafi saninsa fiyeda kowa”

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Post a Comment for "Bakar Ayah 21"