Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bakar Ayah 16

Page 🖤16🖤

 


 

 

Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki.
“FaÉ—amin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baÆ™ar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu.
Kunkoroki munyi miki komai amma kinÆ™i barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki”
“Zulaiha ce taÆ™arisa faÉ—in hakan,Æ™anwar bello abokin sule.
Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi alfarmar a maidata primary 5c.
To shiɗinma ajin su Zulaiha ne ƴan anguwarsu,duk yanda Bombee take iya koƙarinta wajen ganin ta ƙauracewa masu cutar da ita,abin yaci tura,kullum cikin fuskantar ƙalubale take.
Fatarta tayi baƙiƙƙirin,banda tabon izayar da mutane sukeyi mata babu komai a jikinta,tun tana kuka tana kaiwa Danejo kukanta har ta daina,ganin babu wanda zaima dubeta ballantana yaji kukantan ko kuma tausayinta.
Mata biyune a tsawon rayuwarta suke dubanta da idon rahama,daga Inna shatu mahaifiyar muruje sai kuma Innarta. MURUJE shine wanda takejin daÉ—in zama a kusada dashi,to shikuma yatafi boarding karatu,shekararsa biyu kenan da tafiyah.
ÆŠago fashashshiyar fuskarta tayi tana kallon zulaiha,wacce tsayah akanta da hijabinta a É—aure a kunkuminta tana rawar masifah.
“Ƴar gidan mayyah,daina kallona da wannan idanuwannnaki,kurwa ta kur in faÉ—amiki”
Tashi tayi tafara kaÉ—e uniform É—inta tareda sake kallon Zulaiha.
“Menene kalmar mayyar nan da kowa ke bina dai tane,wane yaro naci a garinnan da wanann sunan yadace dani,hmm ke innayi zo mu tafi gida kar a ga mundaÉ—e bamu dawo ba”
Kama hannun innayi tayi wacce take tsaye da jakkunnasu a hannunta,ita ajinta biyu a primaryn,dan haka duk abinda ake bata saka baki,duk da itama wani lokacin tana karbar nata dukan,a matsayinta na ƙanwar Bombee.
“Idan kika kuskura kika bita,kema saina miki duka,inaso ki kalli cikin idonta ki faÉ—amin wacece Bombee”
Hannunta ta cire daga na Bombee tareda kallon idonnata.
“Uhm mayyace”
Zaro ido Bombee tayi jin sunan da ƙanwar tata taƙirata dashi itama,abinda tunda take bata tana zaton zataji ba,tun tasowarta bata san komai ba sai soyayyar ƙanwarta ta,a ganinta ko kowa yaƙita ita bazata juya mata baya,saboda ita jininta ce,shiyasa wani lokacin idan yara sunayi mata tsiyah fuk yanda zatayi takan kare ƙanwartata,amma kuma yau abinda taji daga bakin ƙanwartata ya kwance mata ƙwalkwalwa fiyeda tunanin mai tunani.
“In…..nayi kema …..mayyah kike ganina kuma …..dodanniyah?”
“Hhhhhh da alama bakisan mai Æ™anwar taki take ba koh,to koda kinje wani waje kin buyah ita take zuwa ta faÉ—amana inda kike,komai da saka hannunta,mai kike tunani zaki samu wanda sai kareki wai ……….ke ba mutum bace,babu wanda zai yarda dake,ko uwarki ma nasan ba sonki take ba,dan haka idan zakiso kanki kiso kanki”
Rufe ido Bombee tayi gam,lokaci guda kanta yafara wainawa,wani tururi mai cikeda baƙin duhu yafara tasowa daga cikin kanta zuwa sassan jikinta.
GabaÉ—ayah abubuwan da akayi mata tsawon rayuwar ta tafara tunowa,duk lokacin da aka zalunceta babu wanda taba rama mata.
“…..ni mayyace,babu wanda yake sona,dole naso kaina kuma na É—au fansa……..babu wanda zan ragawa daga yau koshi waye……..sai na É—au fansa…….saina rama”
Tunanin cikin kantane yafara cuÉ—anyah yana zama duhu,yayinda lokacin guda tunanin ta yatashi daga positive zuwa negetive.
Tafi minti biyar tana sauraron zugon da wata shaiÉ—aniyar murya take yima ta a cikin kanta,kana daga bisani ta buÉ—e idonta.
Sauƙeshi tayi akan Zulaiha wacce tayi shuru tana kallon ta tun sanda ta rufe idonta.
Zaro ido Zulaiha tayi ganin idon Bombee ya tashi daga Blue mai haske zuwa blue mai duhu,sannan kuma ga wani murmushi akan fuskarta kaman baƙin aljani yafito daga wuta.
Ja da baya tafarayi ganin tana tunkaro ta,cikin murya mai É—auke da muradin É—aukar fansa tafara magana.
“Bakince ni mayya ce ba,sannan kuma kinbani amsar dogon tunnain dana daÉ—e inayi a rayuwata,shine naso kaina babu mai sona.
Daga yau nafara son kaina,kuma babu mahaluÆ™in daya isa hanani É—aukar matakin duk abinda wani yayimin.kema …..kuma a yau banga shegen da duk faÉ—in gembu zai ceceki a wajena ba,saina yimiki Æ™asa Æ™asa anan wajen”
Daidai da lokacin data gama maganar ta iso kaman Zulaiha,tamkar ƙaramar baƙar kububuwa.
Hannun Zulaiha ta kama tareda juyata ta baya,babu bata lokaci kuwa Æ™ashin hannunta na dama yabada Æ™arar ‘Æ™arallll’
Bata barta iya haka ba ta bita duka ta ko ina kaman an aikota,tun Zulaiha tana kuka har ta daina sai nishi take kawai na wuyah.
Wani babban mutum ne zai wuce yakalli abinda ya faru,da sauri kuwa ya isa wajen ya dauke Bombee daga kan Zulaiha,wacce idonta ya rufe da muradin É—aukar fansa.
FaÉ—a mutumin yafara yiwa Bombee,amma ko kallonsa batayi ba ta fisge jakarta daga hannun innayi tayi gaba.
Baki ya saki galala yana kallon yarinyar da ko kaÉ—an bata É—aga ido,yau itace ta gallah masa harara hmmmm.
Juyawa yayi kan Zulaiha wacce take kwance sai zuba nishi take kaman mai shirin haihuwa.
ÆŠaukarta yayi a kafaÉ—a ya nufi gidansu da ita.

“Haba gaji haba gaji,yau ki duba kigani,wai abinci kike rabawa,nan Robar kashice yara sunyi ba’a zubar ba,suma kuma ba’a wanke musu ba.
Ga Æ™wanukan wanke wanke tun safe Æ™uda yake bi amma ba’a wanke ba,sai yanzu da za’a raba abincin kafin ake wankewa ra ruwan ana zubawa.
Wai yaushe zaki gyara ne idan baki gyara yanzu ba?”
“Haba mlm nifah ka dameni ehe,kullum faÉ—an yau daban na jiya daban na gobe daban,baka ganin banida lokaci ne iyae,dawa zanji,dakai zanji ko kuma da Æ´aÆ´an ka koda sana’a ta.
Da ciyar damu ya ishemu mana,idan ka wadatar damu aiki ya ragumin saina gyara,amma aikin banza babu zuciya sai shegen surutu,to karka dameni ni”
Tana cikin masifar ne kan gari ya gari sukaji sallama a wajen.
Mlm idi dama neman hanyar zillewa masifar Gajin yake,dan haka da sauri ya fita wajen.
Bai daɗe ta fitaba sai gashi ya shigo hannunsa riƙeda Zulaiha rai a hannun Allah yana salati.
“Ya ilahi gaji kinga fah,yanzun nan wani bawan Allah yaganta a hanyar makaranta Æ´ar gidan mlm Ahmadu ta hau kanta sai dukanta takeyi.”
“Naaa shiga uku ni gaji,yau mai zan gani haka,ai wanann mayyar yarinyar,ko ba itaba kai?”
“Eh itadai,da farko nima saida nayi mamaki,yarinyar dako magana bata cikayi ba,wai itace tayi wannan aikinta.
Sai yacemin dayayi mata magana ba harara ta zabga masa tayi tafiyarta”
“Kai malm dubafah hadda karayah tayi mata,kan ubancan ni kuwa zanga shegen dazai rabani da su,shari’ah daga nan har gaban sarki,banza na haifawa Æ´ar dazata mata wannan aika aikar”
Tunda suka kamo hanyar gidan Bombee batace komai ba,itama Innayi bata kulata ba,tunda taga abinda tayi koh jerawa da ita taƙiyi.
Lokacin da suka shigo gidan ma Bombee batayi sallama ba,iya Innayi ce kawai tayi a ƙasan maƙoshinta.
Inna Daneji ce take rarraba abinci,yayinda inna laari kuma ta fito daga banÉ—aki É—auke da buta a hannunta,shikuma mlm Ahmadu yana alwala zai tafi masallaci.
“Yau ma faÉ—an kuka sakeyi koh,waye kuma ya dakeki yau”
Daneji ta tambayi Bombee tana cigaba da aikinta,kana ganin fuskarta zaka hango tsagwaron tausayin Æ´ar tata,amma kuma bata da ikon yin komai akai.
“Ahah ba wani ne yadake ta ba,itac……..”
Tun kafin innayi taƙarisa magana Bombee ta ɗauketa da mari tassss.
“Munafuka kawai,dankinga nayi shuru ban kulaki ba shine har kika samu bakin magana koh,kisake cewa wani abu saina yimiki fiyeda nata,kuma daga yau kika sake yin munafurcina a ko ina ne saina yanke miki baki”
Tana gama faÉ—in hakan tayi hanyar É—akinsu tareda barin innayi a tsaye a tana kuka ta dafe kuncin.
Kowa daga cikin mutanen gidan,baƙaramin kaɗuwa yayi ba da abinda yafaru,babu ma yah Daneji wacce take ganin shikenan ta faru ta ƙare,komai ya gama faruwa.
“Ke innayi mai ya faru faÉ—amin”
Saurin jijijjga kanta tayi jikin yana karkarwa.
“Baba bazan iya faÉ—aba,tace zatayimin irin abinda tayiwa Zulaiha,baba wannan ba addah Bombee bace”
“Naji to kekuma mai kikayi mata taÆ™iraki da munafuka uhm”
Nan ma shuru innayi tayi kanta a sunkuye,da alamar rashin gaskiya a fuskarta.
“Ki fadamin mai yasa tace miki munafuka”
“Uhm dama…..dama….nice nake faÉ—awa su Zulaiha inda Bombee take idan suna neman ta”
“Meyasa kike faÉ—amusun toh,waye yace ki dunga faÉ—amusu,sune suka sakaki”
Girgiza kai innayi tayi,tareda ƙara sautin kukanta,hsr mlm Ahmadu ya buɗe baki zayyi magana inna laari tayi saurin katseshi tareda yin magana,dan dama tun sanda Bombee ta mari innayin tafasa shiga ɗakinta.
Tabbas kana kallon fuskarta zata tabbatar bataji daÉ—in marin da Bombee tayiwa Æ´ar ta ba,amma haka ta daure tareda cewa.
“Mlm yanzu dai duk wannan bashine abun yi ba,yakamata aji ita tabakin Bombee mai yake faruwa,saboda bata taba shigowa gida a haka ba.
Ke kuma innayi shiga É—akina ki sanja kayan,karkije inda take yanzu saita huce.
Jijjiga kai mlm Ahmadu yayi tareda numfasawa,da alama ya yarda da abinda inna laarin tafaÉ—a.
Duk abinda ake Daneji batace komai ba,ta lume cikin kogin tunani,sai daga bayane ta tashi ta nufi hanyar É—akin su Bombee.

………mai zata gani??!!!!!😲😲😲.
Ku biyoni muje mugani gobe…….

 

 

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

Post a Comment for "Bakar Ayah 16"