Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bakar Ayah 11


Page 🖤11🖤

 

Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba.
Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun É—a,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen.
Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi.
Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin sasu manta lalurar tasa.
Daneji ce a cikin ɗakin madafah tana girki,tun jiya take jinta wani iri,amma haka ta daure,dayake ansan mace da dauriya da kuma murƙushe kanan nan ciwo da laulayi.
Doyar da take dafawa zatayi sakwara ta buɗe,saidai ƙamshinta yana bugunta taji amai ya taso mata.
Da sauri tayi waje tana ƙoƙodon amai.
Inna laari ce ta fito daga É—akinta domin ganin mai yake faruwa.
Ruwa ta debo mata ta gyara bakinta tareda yimata sannu,suna cikin hakanne shima Malam Ahmadu ya shigo gidan ya dawo daga wajen É—aurin auren daya fita da safe.
Inna laari yafara tambaya mai yake faruwa,saidai kafin ta bashi amsa Daneji tacigaba da aman da takeyi,saidai takai ga ta amayar da duk abinda taci da safe.
Kafin lokacin ƙalilan ta galabaita ta fita hayyacin ta,kamata inna laari tayi suka shiga rumfah ta zaunarta,inda shikuma malam Ahmadu ya fita ƙiran ƴar mai ganye,dake tsallaken gidansu,domin ta duba taga mai yake faruwa.
Basu daɗe ba suka shigo tare,takalmanta fantala fantala zani a tsangale,sai jijjiga kai take ƙanƙanin. Hannun danejin ta kama tayi shuru,kafin tafara wasu ƴan dube dubenta,can ta waigo ta kalli mlm Ahmadu tareda cewa.
“Iyyyeeee Alhandu alhandu,Yarinya ciki gareta,Æ™aruwa ce ta samu sai kuyi murna ku godema Allah”
Tun kafin tagama maganar Mlm Ahmadu yafaɗi ƙasa yayi sujjada,tareda fashewa da kukan murna.
“Daneji É—iyar arziÆ™i,allah shi miki albarka,haÆ™ika kin sakani farinciki dana daÉ—e ban shiga ba a rayuwata,Allah ya saukeki lafiya. Inna Æ´ar mai ganye kinada kyauta ta musamman na wannan albishir É—in,yanzu dame dame take buÆ™ata kenan”
“Babu abinda take buÆ™ata,illah tarage yawan aikace aikace amma ba wai kartayi ba,sannan a kulada abinci masu gidan jiki sosai,nagode nagode mlm Allah yayi albarka,ni bari na tafi toh Allah ya raba lafiya,zan aiko yaro da ruwan saiwoyi ya kawo mata ta dunga sha”
“Shikenan iyah mai ganye mun gode”
Duk abinda ake iya Iyah mai ganyece da kuma Malm Ahmadu,inna laari bata ce komai ba itada Daneji,wacce take ɗan sauƙar da numfashi a hankali.
“Sannu mai zakici toh,bari a nemo miki Kwankwason akuyah a dafa miki”
ÆŠaga masa hannun Daneji tayi alamar yabari,amma mutumin ko kallonta baiyi ba,sai ma fita da yayi da sauri bajam bajam da babbar riga.
Binsa inna laari tayi da kallon kafin ta jijjiga kai tayi É—an murmushi.
“Zaki iya isa É—aki ko kuma na rakaki? Zan Æ™arisa abinci”
“Ahah zan iya Adda laari nagode da kukawarki”
“Babu komai kisamu hutu sosai jikinki yayi laushi,bari yakawo naman saina dafa miki,Allah ya sawwaÆ™e ya raba lafiya”
Daga haka Daneji ta ƙoƙarta tashige ɗakinta,ita kuma inna Laari tacigaba da aikin abincin data bari.
Tundaga wannan rana Daneji ta gagara lafiya,kullum cikin laulayi take,yau da lafiya gobe kuma babu,abinci kuwa kusan kowanne kala bata iya cinsa.
Tun malm Ahmadu yana É—okin magaji har zuwa yanxu abin yafara bashi tsoro da tausayi,inda yafara tambayar dama haka goyon cikin yake.
Inna laari ce take rawa take kidanta a tsakar gidan,ita kam daneji Ba sosai take fitowa tsakar gidan ba,in mutum ya ganta to zagawa zatayi makewayi ko kuma alwala.
Haka rayuwar tacigaba da tafiyah,da daÉ—i da kuma babu,har yazamto cikin daneji yayi girma sosai,ana saka ran ko yaushe zata iyah haihuwa. A lokacinne kuma aka dage dabata dan taimako,ita kanta inna laari ba’a barta a baya ba,takan samo mata É—an taimako daga wajen mahaifinta,dayake shima malamine.
Ɗakin Danejin inna laari tashiga da ƙwaryar magani a hannunta,magana tayi mata kasancewar ta juya bayanta bata kallonta.
“Daneji tashi kisha maganinnan ya tsumu sosai,karkuma yazo ya sane”
Duk maganin da Inna laari take bata a dole take sha saboda rashin dadinsu,saidai saboda karta nuna mata kazawarta a ƙoƙarin datake da ita yasa ta yunkura ta tashi. Alkhairin da inna laarin tayi mata bazata iya ƙirgasu,ji take a yanzu bata da kowa na kusada ita kaman ta,musamman daya kasance batada kowa a garin,ƴan uwanta tunda suka tashi batasan a yanzu inda suke ba.
Karbar maganin tayi dayake cikin ƙwarya takaishi bakinta tana yatsine fuska.
Da kyar tayi kurba uku kafin ta miƙamata ƙwaryar ta koma ta kwanta.
Cikin dare malm Ahmadu ya zabura ya tashi,jin ana jan bayan rigarsa daga ƙasa,lalumar fitilah yafara yi domin ganin mai yake faruwa,don yasan bazai wuce Daneji ba,don yana shashimawa yaji bata wajen data ke kwance ɗazu.
Yanzu haka haihuwa ce,yafaÉ—a a ransa,don dama tun shigar watan haihuwar tata inna laari ta lamunce masa ya koma É—akinta da zama,saboda kar haihuwa tazo mata cikin dare babu kowa a wajenta.
Baiƙi karbar tayinta ba,saima godiya dayayi mata,dan hakan baƙaramar dabara bace.
Haska fitilar yayi a wajen dayake jiyo motsin danejin,tana durƙushe ta kifa kanta da bakin gadon,ƙasanta duk ya jiƙe da ruwa yana ta malala mai haɗe da jini.
Salati malam Ahmadu yafara tareda buɗe ƙofar da sauri ya nufi ɗakin inna laari.
Tana bacci sai jin muryarsa tayi yana ƙiranta,cikin magagin bacci tafara tambayarsa.
“Lafiyah malam naganka a razane,ko haihuwarce kai tazo?”
“Ehh…..ehh itace ,maza kizo ki gani koda wani abu dazaki taimaka mata dashi”
Tashi inna laari tayi tabi bayan malm Ahmadu zuwa É—akin danejin,wacce take kwance har yanzu a inda yatafi ya barta.
Ƙarisawa wajenta tayi tana kallon yanayin da take ciki,saidai da alama haihuwar takawo kai amma kuma dasaura,don babu alamar tahowar ɗan har yanzu.
“Inaga har yanzu fah da saura,amma barina kawo ruwa a goge mata jikinta,sanann kuma tacire wannan riga da zanin,suma bazata ji daÉ—insu ba”
To kawai malam Ahmadu yace mata,domin aikinsa kallone kawai,bashida tacewa bayan hakan.
Yana nan zaune a gunta har inna laari ta dawo da ruwan dagama gyara mata jikin,sannan tabata fallen zani ta É—aura.
Kaman jira kuwa take tafara nishi da yunkuri,har wajen fitowar asslatu suna kanta,tana nishi amma babu haihuwa,saidai yafi na É—azu,tunda ana ganin kan yaron,aikinne dai har sannan da saura.
Yanda suka ga rana haka sukaga dare akan Danejin,wacce take fitar da nishi mai haɗe da ƴar ƙara na galabaita da gajiya.
A hanyar zuwa masallacine malam Ahmadu ya biya gidansu iya mai ganye,yake faÉ—amata abinda yake faruwa,aikuwa nan da nan ta shirya tanufi gidan,jiki yana bari taji daÉ—in kyautar da yayi mata wajen faÉ—ar haihuwa.
Sai bayan rana ta fito gadan gadan haihuwar ta taho,inna laari tana gogemata goshi,ita kuma iyah mai ganye tana taimaka mata wajen fitoda jijirin.
Kaman jira shima yake kuwa ya canyare wajen da kuka,har makwantai ana jiyoshi.
ÆŠago dashi iyah mai ganye tayi tana duddubawa,take kuwa tasaka guÉ—a.
“Ayayyyyyriririrrri malam Ahmadu yasamu É—iya mace,barkanki dazuwa duniya É—iyar Albarka”
Sai bayan tagama guÉ—ar kafin ta kalli Daneji wacce take maida numfashin gajiya.
“Sannu sannu Æ´ar nan,sannunku keda abokiyar zamannnaki,dole kisha wuya kam,yarinya tafarkallah mashaallah,ga tanan kuwa jajir da ita kaman uwarta,ta amsa sunan Æ´ar Daneji.
Laari saiki taimaka mana da daro ruwan zafin da zasuyi wanka itada yarinyar.”
“Ruwan kan daman an É—umama tun tazu,saidai ko na kaimuku banÉ—akin kiyi mata wankan,kafin ku fito itama jaririyar sai a gyarata”
“To shikenan hakan ma yayi sannunki da Æ™oÆ™ari”
Kaman yanda ta faÉ—a ruwan takai musu banÉ—aki,inda iya mai ganyen zatayiwa mai jego wanka,yayinda itama ta haÉ—a wani a baho zatayiwa jaririyar.
Shigo É—akin tayi da ruwan wankan ta ajiye,kafin ta nufi inda jinjirar take kwance a tsumman mahaifiyar tata,É—aukarta tayi a hannunta tareda yin murmushi,kana kuma tashare guntun hawayen dayake kan fuskarta.
“Allah sarki jinin Mlm Ahmadu ne a hannuna,ashe zanga jinin malm Ahmadu da raina,duk da cewa banice na haifa masa ba,amma nayi maka murna dakaga jininka”
Lokacin da su iyah mai ganye suak fito daga wankan inna laari na zaune a É—akin tana tsane ruwan jikin yarinyar,wadda tayi shuru a cinyar inna laarin tana jin É—umin dayake ratsata.
Iyah mai ganye ce tafara magana tareda cewa.
“HoÉ—an kiji yarinya tayi shuru kaman ba haihuwar yau ba,kokukanta bamuji ba na wanka”
“Ko kishi kike kai kinganta da juriyah zata Æ™wace miki kujera kai iyah”
Inna laari ta amsawa iyah mai ganye cikin sigar zolaya. Suna cikin hakanne kuma kaman an tsikareta ta canyare da kuka kaman ansaka a speaker.
Nannaɗeta tayi a zanin tareda miƙawa daneji ita akan ta gwada bata nono.
Itama iyan mai ganye ƙara ƙarfafa mata gwiwa tayi cewar tashayar da yarinyar,musamman da sukaga tana kauda kai akan yarinyar tana nuna halin fulani.

 

……………ShuÉ—iyar Æ™wayah kuma(blue iris),kodai bata gani kai………daneji da faÉ—a a ranta.

 

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

 

Post a Comment for "Bakar Ayah 11"