Amatulmaleek 9
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
/
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
9
Su maamah na isowa gida babban tashin hankalin farko data fara cin karo dashi shine rashin gurin zama Dan kuwa tini kawu bello yayi Amarya ya Sakata a cikin sashen Dan haka suka rakube dakin inna lami data rasu cikin 'yayanta da jikokinta data bari a dakin gashi dakik a cunkushe yake Babu ko filin da zasu aje kayansu sbd kaya da hargitsin dakin.
Batada zabi bayan ajiye tulin kayansu waje a rumfar dakin inna lami din idan sunyo wanka anan suke shiryawa gashi yayanta sunyo Wani irin fresh da kyan Gani tini aka fara Saka musu Baki gashi ko bandaki Amatu zataje saita bita ta rakata Tayo abinda zatai sun fito tare sbd tsoro da fargaban abinda zai iya faruwa.
Amatun ma kanta samun kanta tayi da tsoron gidan da mutanen gidan sbd yanda kowa yake binta da Bakin jiki data Dan yi sbd batada jikin kiba ko kadan Amma ta Dan ciko tayi haske sosai duk duhun da fatarsu tayi ta rinewa ta wanke daga ita har Abdul maamah ce kawai ta Dan yi rama ta wahalar aikin datake sha Amma Kuma duk da Hakan itama fatarta tayi kyau sbd cima me kyau muhalli me kyau.
Kwanansu biyu da dawowa Akai addukar sati ta rasuwar Dan haka sai kowa ya koma sabgoginsa,
Mafarin Bude babin dawowan damuwar maamah shine sace kayansu da aka fara yi Daya bayan Daya Kuma batada iKon magana zaayita fada ana tashin hankali a gidan akan ta maqalawa yayan mutane satar kayan kunce da aka Bata tazo dasu Dan haka sai ta Dena magana ko sun duba sunga an sace musu abu shiru takeyi Bata magana hakama yayan nata Babu me magana.
Kudinta ma baa bari ba haka aka ringa sace mata su kadan kadan Dan haka ta tattara sauran canjin ta Siya abinci dashi ta aje Wanda zasu ringa dafawa da yayanta suna ci duk da tasan basuda ikom cin komai su kadai tinda tana dakin inna lami dole duk abinda zata nemowa yayanta suci Suma saita Basu.
Kawu bello Daya ga Hakan Saiya barta da lalurarsu ya zame Dan kuwa sauki ne ya zo masa.
Lalurar fara yiwa maamah din yawa tayi sbd ciyarda Yara da yawa bazata iyaba tinda ba Sanaa takeyiba gashi duk abinda tazo dashi din ya qare Dan Tama manta da anbude mata acct ansaka mata Koda Bata manta ba tayayama zata iya cire kudi tana cikin wannan kauyen dajin.
Tin tana boye gazawarta tana Fadi tashin ciyar da yaran duka har gazawanta ya bayyana Amma Kiri Kiri kawu bello yayi mata biris yabarta da 'yayansa tana wahala dasu Dan bazata iya samowa ta bawa nata yayanba su ta Hana musu Dan haka tinda tana zaune dakin mahaifiyarsu a rakube dole ta taimaka musu itama.
*******Tafiya tafara Nisa sun wayi gari ko suturar sakawa Neman gagararta da yayanta takeyi sun koma inda suka fito ga yunwa da azabar aikin wahala Dan haka ciwo yafara kokarin kwantar da ita.
Amatu data fara iya aikin wahalar sai tana kamawa mahaifiyar tata dasu suna samu suna Dan rufawa Kai asiri.
Duk halinda take ciki Babu Wanda ya taba ko kallanta da daraja a gidan bare a tausayawa rayuwarta a dubi marayun yayanta Dan haka take Dan sake dauriya tana dagewa Dan inganta rayuwar 'yayanta Amma jiki da jini dole Jikin ya fara kasawa sosai harta fara kwanciya ciwo kadan kadan saiga abu na Neman tsanani.
Amatu ce dole tafara fita da kanta Tana debo itace da zogalan da suke dafawa ana siyarwa.
Fara fitan Amatu shine yafi daga hankali da zuciyar maamah ba ciwontaba Dan kuwa tana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo Bata kaunar abinda zai tana daraja da rayuwar 'yarta,
Tinanin idan ta kwanta jinya me karfi Yaya rayuwar Amatu zata kasance acikin wannan gidan?
Yaya zata iya tsayawa ta taimaka gurin Bata kariya daga sharrin mazan gidan?
Komai zai iya faruwa da Amatu tana daga kwance Babu abinda zata iya yi...
Innalillahi wainna ilaihirrajiun,wannan tinanin kawai ke gigitata hankalinta yayi mummunan tashi harta Saka abin a ranta damuwa tayi mata yawa ciwonta sai qara gaba yakeyi.
Babu abinda yafara zuwa ranta da tinaninta sai komawa Abuja gidan Abeeda sbd Koda Allah yasa ciwonta bana tashi bane tasan tabar yayanta inda zasu tsira da mutunci su kuma su samu kariya da kulawa.
Wanna tinanin nata na sake komawa can din yake sake qarfafa a zuciyarta sbd Daman baaso dawowan nata ba ta dawo Amma Kuma babban abinda yake hanata zama acan din shine tayaya zataje tayi zaman dindindin gidan 'aminiyarta duk da ta Dade da zama 'yar uwarta tamkar jininta.
Wanna tinanin shine yake sake addabarta,takasa tafiya takasa Jin nutsuwar zama Dan haka abin ya taru ya sake mata yawa.
Su Amatu ma gaba Daya a tsorace suke da ciwon maamah din Dan kuwa a yanda suke ganin wainda iyayensu suka rasu a cikin wannan gidan almajirai suke komawa na karfi da yaji hakama lalacewansu yawa takeyi Dan haka tsoro ya kamasu Dan su tsoron ma irin wasu abubuwan Dake faruwa a gidan sukeyi sbd maamah datake Saka musu tsananin tsoron Hakan Tintini.
Rashin takamaimai shawara da madafa yasa suke cikin garari kullum Kuma suna waya sosai da Abeeda a yanzu sbd wayar data dawo da ita wadda aka Siya mata tin acan Amma bata iya fada mata halinda take ciki ba.
****Acikin wannan mummunan halin dasuke ciki kwatsam suka wayi gari da Kiran Husnah a wayar maamah din cewan Abeeda ba lafiya sosai.
Labarin shine Mafi tashin hankalin labarin Daya samu maamah sbd Abeeda Bata taba ciwon da harya kaita kwance ba Dan haka zuciyarta tayi nauyi da tsoron meya samu Abeedan,
duk da ita ma a kwancen take Amma ciwon Abeeda ya sata danne nata azaban ciwon ta fara kokarin Shirin tafiya Dan kuwa ita kanta Abeedan zataso ta farfado Taga Asmau acikin wainda suke zagaye da ita.
Halinda ta shiga na tsananin damuwa da kokarin boye nata ciwon akan son zuwa inda Abeeda da kwana biyu batasan inda kanta yake ba yasa Amatu shiga mummunan damuwa itama da tausayin mahaifiyarta datasan tana cikin nata mawuyacin halin Amma kaunar datakewa Abeeda yasakata dannewa idan ba ganin kanta tayi sun Isa inda Abeedan takeba bazata taba nutsuwa ba.
Acikin kwanaki biyu sukai Shirin tafiya Abuja,
Dayake batada lafiya yanda ya kamata da Kuma kudi da Babu a hannunsu dole tareda kawu bello suka taho har cikin garin Yola suka banki ta basa komai aka ciro kudi daga bankinta ya cire kudin da aka basu aro daga can na tahowa tareda nasa kudin komawar harma Dana Shan ruwa a hanyar komawa tukuna ya rakasu suka hau motar Abuja shikuma ya hau ta komawa kauye.
Koda suka dauki hanyar Abuja a mota shiru Amatu tayi tareda zubawa hanya idanuwanta dasuka fada kwana biyu sosai sbd jinya da kulawa da maamah,
Wannan tafiyar tasu kaman yanda maamah ta fada ba lallai me dawowa bace sbd tanason Koda zata kwanta tabarsu a hannun 'yar uwarta,
Meye makomarsu daga ita har Abdul idan maamah ta tafi kaman yanda take fada?
Daga dangin uwa harna Uba basuda takamaimai inane kaddararsu zata kaisu Dan haka take fata da adduar Allah yabarsu da mahaifiyarsu har girma da tsufa su rayu tare su mutu tare.
Kaman yanda sukasha wahalar hanya wancan Karan wannan ma sunsha sedai wannan da sauki sbd sunsan Daman tafiya ce me Nisa zasuyi ba kaman na farkon ba da basusan Nisan tafiyar ba.
Sai bayan ishai suka sauka Abuja Dan haka Kai tsaye driver ne yazo daukansu harda Husnah wadda itace tazo da driver din sbd ta matsu su maamah din su iso.
Tana ganinsu jikin Maamah ta fada tareda fashewa da kuka sbd tanata Neman Wanda zatai kuka a jikinsa Amma Babu Dan kuwa duk kauna da gatan da mum Aisha ke nuna mata ita Bata Jan Yara a jikinta ga mommynta akwance kwanaki batasan inda kanta yake ba.
Ita kanta maamah Jin tayi idanuwanta na cikowan da hawaye na tsinkewan zuciya Amma hakanan ta daure tana boye nata ciwon suka nufo gida.
Dayake dakinsu na Baya Yana Nan Babu kowa a cikinsa anan suka sauka bayan duk masu aikin gidan sun tarbeta tareda mata sannu da zuwa harma da gyara mata dakinta da wanke toilet da komai.
Basu zaunaba sai da sukaje har palon mum Aisha suka gaisheta tareda mata jajen jikin Abeeda din.
Sama sama ta amsasu tana kallan yanda duk suka sauya ba kamar yanda suka bar Nan din ba musamman Amatu data rame sosai.
Abdul ne ma dai take Dan sakewa Dan haka shi ta ringa tambayar Yaya kauye da karatu Yana amsawa har suka fito suka koma inda suke.
Wanka sukai dukkaninsu suka gasa jikinsu musamman maamah da jikinta yayi nauyi sosai na ciwo da gajiya.
Abinci aka kawo musu Saida sukai salloli suka ci take kowannensu bacci ya kwashesa a qasan tiles din sai maamah suka barwa gadon sbd rashin lafiyanta.
Washe gari Babu tinda Babu abinda sukeyi bayan cin abincinsu da mum Aisha zata asibiti ta tafi da Maamah gurin Abeeda din sbd yanda duk maamah tayi zuru zuru Babu baccin arziki sbd rashin sanin menene yake damu abeedan.
Koda suka Isa babban private asibitin me tsadan gaske suka Isa sama har dakin da Abeedan ke kwance baa Wani shiga sbd baa son motsi me yawa ko karfi.
Ahankali maamah ta iso har bakin gadon Abeedan tana kallanta da idanuwanta dasuka fara cikowa da wasu irin hawaye masu dumin kayewan zuciya na ganin mace kamar Abeeda a kwance gabaki daya kamar ba itaba a cikin qanqani lokaci Allah ya Maida ita Hakan,
Tayi Wani irin haske tayi fayau kamar wadda Babu jini ko kadan a jikinta hakama fatarta kamar wadda aka shafe da yar farar Hoda.
Kasa riqe hawayenta tayi suka fara gangarowa tana Sauke idanuwanta daga kan Abeedan tanajin kaman zuciyarta bazata dauka ba sai kawai ta fashe da Dan kuka mara sauti tana Jin halinda Abeedan ke ciki har cikin zuciyarta.
Ita kanta mum Aisha duk tazo Jin takeyi zuciyarta na karyewa sbd abu ne dayazo lokaci Daya hakama ASH TALBA yakasa fada musu abinda likitoci sukace akanta tin ranarda aka kawota asibiti zuciyarsa ke cikin Wani mummunan hali Amma qarfin halinda yaqi nunawa,
Abeeda wata tsoka ce a zuciyarsa dayakejinta musamman duk da baisan Menene so ba,
Idan Hakan shine so to tabbas Abeeda tagama zama sonsa qwal Daya da bayajin zai samu sassauci akan Hakan.
Kuka sosoi maamah Tasha a asibitin Wanda yasaka nata ciwon datake dannewa tashi sosai sbd Daman ita Kuma matsala ce ta zuciya datake kumbura tsaban kunci da damuwar datake ciki.
#MAMUH#
For more pages follow me @Mamuhgee at arewabooks or join vip
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Post a Comment for "Amatulmaleek 9"