Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Amatulmaleek 8

 Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #




AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar



8

Koda su Husnah suka dawo gidan take masu aikin gidan suka sake shiga taitayinsu sbd mum Aisha da Sam Babu sauki a lamarinta Dan kuwa ko barin kaya baa da iKon yi zaka iya rasa aikinka a gidan Dan kuwa itace me fada aji,itace me iKon zartarwa akansu.


Husnah ma kusan halayenta tafi dauka Dan itace tamkar madubinta Kuma yar lelenta Dan haka kusan halayenta ne Husnan ke dauka duk da yanxu ne take zama Yan mata Amma dai halayenta a Fili suke Tin yanzu.


Koda maamah taga dawowan Husnah sosai ta shiga farin ciki sosai da ganinta ta rungumeta tana ambatar sunanta cikin tsananin kaunarta tana tambayarta ya gajiyan hanya.


Amsawa Husnah tayi tareda gaida maamah din Dan kuwa duk Wanda yake tareda mahaifiyarta Kona sati ne saiyasan maamah a bakinta da matsayinta a zuciyata Dan haka tasan wacece Maamah din a gurin mommynta.


Maamah datake farin cikin ganin Husnah itace da kanta ta gyare mata dakinta fes yanda takesonsa tareda komawa kitchen aikinta,


Ta sanar da AmatulMaleek da Abdul 'yarta Daya ta dawo wato Husnah.


Dayake Abdul shi dinma dayake qanqani yasan sunan Husnah a bakin maamah hakama shi a farko ya dauka da gaske ita din 'yar maamansu ce sbd yanda take fadarta har cikin zuciyarta da gaskiar kaunar datake mata.


Amatu da Abdul sunji farin cikin dawowar Husnah dan haka suka kwana da Shirin da safe zasuje su mata sannu da zuwa kamar yanda maamah tace.



Washe gari maamah din da kanta sukaje tare takaisu suka gaisa da Husnah wadda Babu laifi ta Dan sake musu din Su Daman ba saurin sabo ne dasu ba Suma Dan haka suna barowa dakinta gurin mommy Abeeda sukaje suka gaidata itama cikin kulawa da kauna ta amsa musu kafin suka fito suka tsaya gurin Haydar Amatu ta shiryasa bayan Maamah tai masa wanka Yana ihun bayason Amatu ta shiryasa sbd kada ta gansa ba kaya Amma hakanan suka dannesa itada Abdul harta shiryasa suna masa dariya ya fito yaci abinci Suma anan suka ci abincin dole sbd mommy Abeeda din da Husnah suna kan dining hakama Haydar Dan haka dole akace Suma suzo su zauna.


Dayake Amatu nada hankali sai Bata Wani sake taci sosai ba kamar yanda Abdul ya saki ciki yaci ya koshi Shida Haydar suna wasa da dariya Wanda Hakan ne ya Dan raya gurin daga tsit din Daya dauka.


Suna Hakan mum Aisha ta fito take suka nutsu Amatu tayi saurin gaisheta tana sauke kanta qasa daga kallan dataga mum Aisha din na mata Wanda ya Sakata Jin jikinta na sanyi.


Husnah ce ta gayar da ita tana sake fuska sosai.

Itama mum din murmurshi tayi tana sake fuska tafara amsa gaisuwar Husnah kafin ta amsa ta Amatu data cire tsammanin zata amsata.


Abdul kuwa Sam baima San da ita ba saida tayi musu magana cikin yar tsawar data Saka Abdul sauka daga kan dining din Yana dawowa gefen Amatu idanuwansa akan mum Aisha din wadda kyanta da fadan datakeyi suka sakashi yin shiru tsoronta na shigarsa.


Daga wannan lokacin suka nutsu sama sama suka qarasa suka koma inda suka fito.


Bayan tafiyarsu Babu Wanda yace komai sai Haydar Daya gama Shima ya sauko khaltume ce tazo ta tafi dashi zuwa inda driver ke jiran fitowansa ya shiga mota aka tafi dashi zuwa school.



Koda suka koma daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya fadawa maamah abinda ya faru saima zamansu da sukai daki suna abubuwansu.


Koda Rana tayi zaa tafi Kai Haydar Islamic school taredasu mommy Abeeda tace atafi su fara karatun kafin su tashi komawa.


Murna sukai sosai Dan kuwa Daman sunaso fita su Dan ga gari.


Su hudu aka tafi dasu harda Husnah wadda ta kwana biyu Bata zuwa sbd tafiyarsu.


A motar daga Abdul sai Haydar ne keta surutu suna farin cikin zuwan nasu makaranta tare,

Itama Amatun tana farin cikin zuwan makaranta duk da Babu Wani sakewa tsakaninta da Husnah Amma dai tinda gasu Haydar tasan batada kadaici.


Koda suka Isa makarantar tini akaiwa su Amatu komai Dan kafin zuwansu Akai wayar zaa kawosu.


Hatta uniforms da littafai da jaka a makarantar aka Basu sai gasu sun saje da sauran dalibai 'yayan masu fada aji.


Dayake sunada karatun addininsu sai Basu Wani muzanta ba a cikin mutane aka Basu ajinda yakeda daidai da karatunsu 

Abdul cikin saa aka basa ajinsu Haydar Dan haka murnarsu ta Qaru,

Amatu ma ajinsu Husnah aka kaita.


Wuni Amatu tayi a makarantar a kame sbd rashin sabo da shiga mutane sabanin Abdul da kamar Daman anan yake Dan kuwa Haydar tini ya jonesa da abokansa suka ringa murnan samun sake.



Koda yamma tayi sosai aka tadasu driver na gate Yana jiransu Dan haka suka shiga mota suka dawo gida.


Koda suka dawo maamah taga yayanta cikin uniform din makaranta Jin tayi jikinta yayi sanyi da farin cikin ganinsu a Hakan tana tausayinsu yanda suke farin ciki gashi dole zasu koma inda suka fito.


Da farin cikin da daddare suka ringa Bata labarin makarantar datake kamar a turai sbd kudinta da tsarinta.


Ita dai murmurshi kawai takeyi tana sauraronsu har dai aka gama dokin Abdul yaci abinci yayi bacci.


Amatu kuwa uniform din nasu ta nade musu ta tattara littafansa Daya barbaza ta mayar a jaka kafin itama taci abincin ta sukai sallar ishai da maamah ta kwanta 

Maamah kuwa ficewa tayi ta tafi gurin 'yar uwarta Dan sake nuna godiyarta akan abinda take mata.



********Ahankali su Amatu suka Dena dokin makarantar har suka fara sabawa yanzu Kam ba Doki karatu kawai Wanda kusan duk su biyun sunfi Husnah da Haydar kokari da Maida himma sbd ganin sukeyi sukam sun samu babbar sa'ar rayuwa ta zuwa makaranta bayan Basu tana Saka Rai da shiga kowace irin makarantar ba.


Husnah Sam babu Wani sabo sosai har lokacin a tsakaninta da Amatu Amma dai ta bangaren karatu hakanan take sakewa su koyawa juna ganin Amatu tafita saurin fahimtar karatun na islamiyya.




***ASH TALBA ya dawo kusan so biyu Yana sake tafiya Dan haka sudai su Amatu basuma San ya dawo gidanba harya komaiba sbd Basu taba ganinsaba Dan bayan 'yayansa da matarsa sai mum Aisha Babu me shiga bangarensa Dan haka ko maamah dataje suka gaisa Saida yabada damar Akai mata iso tazo har palonsa suka gaisa Kuma sun Dan jima suna magana duk da rashin son Jan zancensa Yana tsayawa Dana gida su samu lokacinsa.



Karatun su Amatu yafara daukan harama sbd karfin maamah da Abeeda taci akan komawarsu ba yanzu ba.


Kowanne dare a palon su Husnah suke zuwa su Hadu su hudu suyi karatunsu na islamiyya harma da karatun Boko dasu Husnah din suke koyawa su Amatu Dan haka sukam su Amatun suka Bude Kai suna koya Dan daga Amatun har Abdul din suna shaawan na bokon.


Ahankali ahankali sabo sosai ya shiga tsakaninsu duk da halin Husnah din akwai wuyar shaani Amma dai sanyin halin Amatu da zurfin cikinta yasaka take shanyewa zaman nasu na tafiya,


A yanzu Husnah da batada qawaye Amatun ce kawarta har islamiyya har gida Dan haka sai duk abinda ta cire na kaya ko abun buqata da bataso sai tana bawa Amatun tareda nuna mata sai tagama da abu take Bata Dan nuna itace a qasanta Kuma take cin alfarmarta Wanda duk lokacinda takewa Amatun Hakan Bata taba Jin komai ba ita sbd maamah Dake nuna musu Husnah da Haydar Yan uwansu ne datakejinsu a ranta kaman yanda take jinsu.


Kaf a cikin gidan mum Aisha ce wadda Basa zuwa ko inda tabi tabar kamshinta sbd tsananin fadanta da zafinta akansu musamman mahaifiyarsu Dan haka kusan Yan aikin gidan biyu ta sake sallama Dan haka maamah karfi da yaji ta koma 'yar Aiki a gidan Kuma aikinma Wanda ma'aikata uku zasuyi ita aka barwa tanayi.


Duk wannan wahalar da maamah din keyi haryanxu Bata taba Jin haushi ko bacin Rai ba,tsakaninta da Allah takeyi Kuma ko zatayi aikin dayafi wannan a gidan Abeeda batajin zataji Wani abu na dacin zuciya ko gajiyawa  sbd Abeeda ta inganta rayuwarta tin kuruciyarsu har yanzu dasuka manyanta gashi Kuma yanzu tana inganta mata ta yaranta.



Waya aka siyawa maamah tana waya da Yan can kauye tana Jin lafiyarsu da Kuma abubuwan Dake faruwa na zumunci da haihuwar da aketa sake yi a cikin Yan watannin da batanan

Ahakan ne katsam aka sanar da ita rasuwar uwar gidan kawu bello wadda take tamkar Yaya agareta Dan haka dole suka fara Shirin komawa gida.


Acikin gidan ASH TALBA Mansion Babu Wanda hankalinsa Bai tashiba da Jin maganar tafiyar maamah gida sbd baiwar data komawa kowa a gidan hatta masu aikin gidan aiki suke Sakata Kuma tayi,hakama tsaftar sashen Abeeda tini ya dawo hannunta hakama cimar Abeeda din,

Ta bangaren mum Aisha ma Amatu ce sabuwar me mata shara duk da Bata Wani iyaba Amma so take ta koya sbd a Qaru dasu Suma,

Su Husnah ma dasukai sabo da sakewa sosai ayanzu suyi wasa da guje guje harma da wasan ruwa a swimming pool dasu Amatun duk sai sukaji jikinsu yayi sanyi Dan haka suka roki mommynsu ta Hana maamah tafiya Amma dole saita tafi.


ASH Baya Nan zasu tafi Amma Kuma Saida ya Saka aka Basu kudin Daya bawa maamah tsoro sosai Dan haka aka Bude mata acct kafin tafiyarta aka Saka mata sauran suka riqe hakama Abeeda ta Basu kudi sosai itama bayan tarin kayan sawa da aka basu Wanda duk kayansu Husnah ne Dana Haydar aka bawa su Amatu itama an bata kayan sawa sosai Dan haka kaya Niki Niki sukai bankwana suka tafi ana kewarsu.



Bayan tafiyarsu har ciwo sosai Haydar ya kwanta kafin yaji sauki yakoma rayuwarsa ta Baya Babu abokin wasa Babu abokin fira bare karatu.

Itama Husnah bataji dadin tafiyar tasu ba duk da Babu abinda takewa Amatun a tarensu bayan Gori da nuna mata kamar komai na rayuwarta saita kashesa tagama dashi take bata.

#MAMUH#

For more pages follow me @Mamuhgee arewabooks 


*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee 

And

*_YANCI DA RAYUWA_*

By Hafsat Rano 

Na kudi ne

For more page ku biya

500 for littafi Daya

1k for duka books din biyu

 at👇

0022419171 access bank Maryam sani

09033181070

Post a Comment for "Amatulmaleek 8"