Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Amatulmaleek 3

 Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar


3

Maamah Bata taba yin qasa ko sanyaba akan tsaro da tarbiyarsu kaman yanda babansu ya dage ya tsaya kafin rasuwarsa duk da ta Wani bangaren dukansu har ita suna cikin hadari a gidan Dan ita kanta ansha shigowa bangarensu da dare da niyar a afka musu ko ita ko AmatulMaleek din Amma dai Allah na tsaresu shiyasa duk tsanani basa fitowa fitsarin dare gudun a keta musu haddi basuda abin yi Dan duk Wanda aka Bata gidan bayan hakuri Babu abinda zaiyi bawai Kuma Dan baa San masuyi din ba kawai dai bakada iKon magana ne ayita rigima da iyayensu ana Allah ya Isa da tashin hankali karshe dai cuta ce anriga an cuceka.


Maamah Bata taba Dana sani da damuwar aure a gidan taro me tsanani ba irin wannan sai yanzu sbd illarsa tafi dadinsa da albarkarsa yawa,

Amma dai tinda Allah yasa rabonta na 'yaya anan yake Babu yanda zatayi da kaddara bayan dagewa.


Ko islamiyya Bata barin AmatulMaleek tafiya ita kadai kullum tare suke zuwa lokacin tashi nayi taje su dawo tare duk da ta Dan girma Amma dai hankalinta baitaba Kwanciyar tabarta taje ita Daya ta dawo ita Daya sbd yawun da samarin gidan suka hadewa 'yartata Dan haka tasan ko a hanya zasu iya binta.



Ita kanta AmatulMaleek tasan rayuwarta a gidan tana cikin hadari Dan haka take kiyayewa tareda kame kanta Babu inda take taba zuwa Dan haka wasu da yawa a kauyen Basu Santa ba sbd Bata fita koyaushe tana dakin maamah ana tsaronta kamar wata gwal me tsadar gaske.



Abdulhameed Daya kasance qaninta shi Kuma sai ya zama kowa shi ya sani sbd shi Kam yawonsa yake zuwa yi tinda bara yakeyi duk da Shima Maamah din na kokari akansa Amma dai tafi Maida hankali akan Amah,

Yaron ya kasance Yana so da shaawan karatun Boko Dan haka kullum saiyaje makarantar bokon kauyen ya shige cikin Yara

Wannan dalilin ne yasa ake yawan kawo kararsa ga kawu bello sbd sunyita korosa Amma Baya Dena zuwa Dan haka kawun keji Asmaun da 'yayanta sun ishesa Daman kuka aure yakeson qarawa duk da manyancinsa sosai Dan haka so yake Asmau ta tattara tabar gidan ya samu bangaren sbd ya aje yar bazawarar da zai auro.



*****

Asmau tayi shekaru sosai rabonta da Abeeda a idanuwanta sedai aike Wanda Wani lokacin har mantawa akeyi dasu kafin su samu Wanda daga Yan Aiken ne da aka aje duk wata sukai musu abinci Amma Sam basa kaiwa sai bayan watanni watanni suke kaiwa ganin madame din Bata qasar sai Suma suke tasu zalamar.


A yanzu da AmatulMaleek tafara zama yar budurwar yarinya tini hankalin maamah yabar jikinta Bata bacci Batada nutsuwa kowane dare Bata iya baccin kirki sbd tsoron rayuwar da 'yarta zata shiga a yanzu da samarin gidan da babu nagari zasu iya cewa suna son aurenta kuma tasan batada abinda zai Bata damar hanawa tanaji tana Gani zaa lalata mata rayuwar 'yarta gashi kowannensu yaga budurwa tafara tasawa a cikin gidan sai suce sunaso gashinan da qananun shekaru sunata Tara mata daga me mace biyu Se uku sbd suna cewa sunaso akeyin wuf ayi auren sbd karfafa zumuntar da Babu so ko jin qai a cikinta.



******

Iyalan ASH TALBA sun sauka a kasar Nigeria a bazata sbd rasuwar mahaifin mom Aysha wanda yake tamkar mahaifin ASH din Shima Dan haka dolensu suka dawo Nigeria.


Saukarsu da labarin rasuwar tasa yasaka Maamah shiryawa dole itada 'yayanta sukai Shirin tafiya duk da batada kudin mota Amma hakanan ta siyar da akuyoyinta guda biyu datake ta Reno sbd auren AmatulMaleek idan zaizo kafin lokacin sun qara hayayyafan da zasu isheta yiwa AmatulMaleek din Wani abu.


A wulaqance aka siyesu sbd anga tanason kudin amma Bata damu ba sbd zuciyarta Sam bamai Saka damuwa bace hakama Allah yayi mata sanyin hali da tsananin hakuri me yawa Dan haka baka gane ko ka quntatar da ita sbd tana hadiye komai  da sanyin halinta.


AmatulMaleek da batajin dadin tafiyar tasu Sam Amma Bata nuna ba itama sbd kusan halin mahaifiyarta itace ta dauko sak na boye damuwa da hadiye kowanne bacin Rai da sanyin hali Dan haka itace da maamah din sukai wankin kayansu da zasuce tsumma ne ma Amma Kuma su suke dasu Dan haka dasu zasu.


Abdulhameed kuwa farin ciki yakeyi sosai sbd baitaba barin ko wajen kauyen ba bare zuwa babban birni ba dukda baimasan me birnin ke nufi ba Dan shi Kam asalin bafulatanin kauye ne.


AmatulMaleek din ma dai kana ganinsu kaga fulanin kauye sun fito Amma Kuma nutsuwarta ke Hana duhun kansu fitowa.


Ranar da zasu tafi gidan kaf murna sukeyi su tafi sbd bangarensu da kowa keso saikace ce musu maamah tayi bazata dawo ba,

To sukam Koda zata dawo din to idan ta dawo sedai ta koma zauren gidan da zama Dan kuwa duk Wanda ya shiga baida niyar fita idan ta dawo tinda Daman Neman ta tafin sukeyi,

Qalilan ne masu son zamanta gidan sbd AmatulMaleek dasuka qwallafawa Rai akan tana Isa aure zasu aureta su jefa cikin matansu.



Duk Wani Shirin tafiyarsu sun kammala Dan haka washe gari tinda asuba suka hau mashin Abdulhameed na gaba maamah da AmatulMaleek a Baya suka fita kauyen zuwa kauyen gabansu da acan ake Hawa motar zuwa babbar hanyar titi da acan Kuma zasu hau motar zuwa cikin state din kafin daga can su hau motar zuwa Abuja.


Tinda suka hau mashin din Abdulhameed ke washe Baki cikin tsananin farin ciki sbd Bai taba Hawa ko Keke ba bare mashin sai yau din.


Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa kauyen kurmawa,

Saukowa sukai daga kan mashin din maamah na ajiye jakar kayansu gefe 

Ita Kuma AmatulMaleek Abdulhameed Dake zare idanuwa Yana kallan koina ta kamo hannunsa suka dawo gefen maamah din.


Kudinsa Maamah ta Ciro ta basa na mashin ya juya Yana musu Allah ya kiyaye Abdulhameed ne kawai ya amsa da Amin cikin murna da farin cikinsa da Baya boyuwa.


Wata motar a Kori kura suka nufa wadda ita kadai ce Daman a kauyen take fita da mutane Dan haka kusan Tama cika Dan haka ba Bata lokaci aka kama su Abdulhameed din da AmatulMaleek aka Dora a sama kafin Maamah ta miqawa Amatu jakarsu tukuna itama ta tattara zaninta ta kama motar ta Haye ta zauna gefen 'yayanta suna Dan gaisawa da sauran mutanen Dake bayan motar a Bude kowannensu kura ta gama rife koina jikinsu kaman anyi juyen yashi a jikinsu sbd iska da akeyi.


Tafiya suka fara Babu me magana acikinsu sai Abdulhameed Dake kalle kalle har bacci ya daukesa a jikin AmatulMaleek wadda itama tafara komawa kamar bokanya sbd iska da qura Dayake Kara sauya kamannin kowa Dake motar.


Tafiya me tsayi Nan ma sukai sosai kafin suka iso babban titin hanyar shiga kauyukansu masu shegen Nisa.


Saukowa sukai kowa qafafunsa sunyi sanyi gashi zuwa lokacin Rana tayi Dan kuwa sha Daya saura Dan haka komai Basu tsayaba ruwa kawai da biredi kawai maamah ta Siya musu suka fada wata motar da zata kaisu state acan su samu shiga motar Abuja.


Babu Bata lokaci motar ta cika Dan haka suka sake daukan hanya.


Biredin data Siya musu ta rarraba musu suka fara cin abinsu hankali kwance.


Abdulhameed duk rawar murnarsa fara komawa ciki tayi sbd zuwa lokacinda suka Isa babbar tashar yola tsoro kamasa yayi sosai sbd Bai taba ganin mutane hakaba sosai da hayaniya anata ihun Neman passengers ta bangare daya ga masu talla takoina suna ihun azo a Siya abinda suke tallan,

Hakama a Wani gefen fada akeyi sosai a cikin tashar..


Ba Abdulhameed ba AmatulMaleek ma kanta tsoro ne da firgici me tsananin gaske ya shigeta Dan Basu Saba haka da mutane da wannan hada hadarba Dan haka dukkaninsu qanqame hijabin maamansu sukai ita Kuma ta riqe hannuwansu gam tana Basu kariya har suka samu motar da zata daukesu zuwa Abujan suka shiga ta rungume 'yayanta tanajin hakanan zuciyarta na karyewa da tafiyar Kuma a yanzu sbd so da dama duk halinda take ciki a kauyen sai tanajin yafi mata nutsuwa akan zuwa birnin duk da wannan tafiyar taji hankalinta ya kasu kashi biyu zatayi ne sbd magana da Madame Abeeda ta rage nauyin zuciyarta da quncin Daya dabaibayeta akan rayuwar AmatulMaleek da batasan Yaya zatai da ita acikin zuriar Sanda Fulde ba.



Shiru tayi tareda Nisa a tinanin rayuwarta tin kuruciya da irin gatan data samu a Baya da rayuwar data taso aciki har kaddararta ta sauya mata hanya zuwa kauye da auren kauye Wanda ayau ta samu kanta a tsaka me wuya sbd rashi na Miji Kuma uban 'yayanta Wanda da ace Yana Raye da bazata samu Kanta a wannan halin na kakanikayi da 'yayanta.


AmatulMaleek Dake jin tsoro me tsananin gaske a duk Nisan da suke qarawa na tafiyar shiru tayi jikin mahaifiyarta tana Jin zuciyarta na shiga yanayi na rashin murna da tafiyar dakuma yanayi na sanyi Dan haka ta rufe idanuwanta tana barin baccin datake ji daukanta.


Kallansu maamah ta sake bayan dukkaninsu sunyi bacci jikinta ta shafa kansu su dukan tana Bude zuciyarta cikin amincin Allah tace


"Allah ya kawo madaukakin haske da girma a rayuwarki AmatulMaleek keda 'dan uwanki,

Allah yasa ki zama tauraruwar macen  alfahari a duk inda rayuwa zata kaiki,

Yakuma Baki mijinda zai Miki Mafi girmamman so me tsaftan gaske..Amin"


Numfashi ta ajiye ahankali itama tana lumshe idanuwanta sbd zuciyarta Dake jin kaman tana gazawa da gwagwarmayar.



****

Tafiya yankin azaba kaman yanda aka fada,

Sai yamma lis suka sauka birnin Tarayya,

Daga maamah har su duka kafafunsu sunyi Wani irin nauyi da riqewa Dan haka daqyar dukkaninsu suka iya tsayuwa bayan sun fito motar zuwa lokacin Abdulhameed da AmatulMaleek sosai suke Jin tsoron mutane Dan haka a maqale suke da maamah wadda itama tasan bazata iya Kai kanta gidan ASH TALBA ba Dan haka numbern Madame Abeeda datake cikin kanta kamar hadda ta karanto aka kira musu ita cikin rashin saa akaita kira baa dagawa sbd basa daga bakuwar lamba Dan haka dole guri suka samu a tashar suka zauna ana sake kira lokaci bayan lokaci.


Yunwa da wahala ta Saka AmatulMaleek ringa Amai a gurin har Saida dole aka nemi guri aka kwantar da ita sbd take zazzabi ya rufeta.


Sanyi jikin Maamah yayi ga Abdulhameed Shima duk yayi laushi sbd azabar tafiya da yunwa Dan haka duk taji hankalinta ya tashi damuwa na rufeta ta zuwan nasu.


Sallar magrib ake kokarin shiga Wanda yaketa kira musu numbern ya ringa mata fada Yana cewa wayace suzo batareda sun sanar da inda sukazo din ba?

Basusan baa zuwa Kai tsaye gidajen manya ba batareda an sanar musu ba sbd basason damuwa da takurar talakawa da dangin kauye.


Shiru Maamah tayi sbd zuciyarta gabaki daya Bata mata dadi jikinta yariga yayi sanyi gaba Daya Dan haka batama San me zatace ba bayan sauke Kai kasa.


AMATULMALEEK

Regular 700

Vip 2k

0022419171 access bank Maryam sani

09033181070


#MAMUH#

#AMATULMALEEK

#ASH

#MADAME

#FRIENDSHIP

#LA HOT

#ROMANCE

#LOVE

#ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL

#MEERAH HERBS

Post a Comment for "Amatulmaleek 3"