Amatulmaleek 23
YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
23
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER
08142800199
07068558096
************
Cikin girmamawa da rawar jiki kaman zasuyi masa sujjada su kawu da manyan gidan gaba daya suka tarbi ASH TALBA ana masa barka da zuwa Dan haka tini Akai shimfidu na alfarma a babban kofar gidan Dan gidansu na cikin manyan gidajen kauyen.
Husnah cikin gida Abdul yayi da ita gurinsu maamah ta fada jikin Maamah ta qanqameta tana ko gaisawa basuyiba ta fara furta mata maamah Dan Allah ki bini mu koma bazan iya rayuwa ni kadaiba.
Numfashi me sanyi maamah ta sake ahankali tareda Dan sake rungume Husnah din tana Jin kewan Abeeda ita kanta sbd harda rashinta duk ya sakasu a wannan tsaka me wuyar tinanin abinda zasuyi.
AmatulMaleek dai na gefe tana yanka kayan miyan da za'a yiwa Faisal abinci dasu sbd bazai iya cin abincin gidanba sun sani ko tinawa da ita Husnah bayayi ba sbd Daman ita sbd maamah tazo Kuma komawan maamah dince burinta da nutsuwarta.
Ahankali Amatun ta Bude Baki tai mata barka da zuwa Wanda sai alokacin Husnah ta juyo ta amsa tareda kallan aikin da Amatun keyi sai alokacin tafara kallan gidan da inda suke cikin mamaki da rashin tauna zance da Bata iya ba tsoron gidan na Dan kamata Kai tsaye tace
"Maamah anan kika dawo kuyi rayuwa?
Tayaya kuka iya kwanaki anan?
Maamah bazan iya kwana anan ba tsoro nakeji Dan Allah mu koma yau.
Wani murmushin yaqe Maamah ta saki batareda ta iya cewa komaiba Dan kuwa Suma sunsan rayuwa anan din zata musu wuya kafin su Saba Amma Hakan yafi mata Dan matiqar suna can din AmatulMaleek na cikin hadarin Naufal.
AmatulMaleek dai na jinsu Bata iya cewa komaiba sbd tasan tata rayuwar Kwanciyar hankalin tazo karshe daga ranar da abinda ya faru din ya faru sbd batajin Koda maamah zata koma su kawu su bari ta tafi da ita,auren dasuka rufe ido sukai Niya shi zaayi mata Wanda ita kanta maamah tasan Hakan Dan haka take cikin matsanancin tashin hankalin Dan kuwa tasan qunci da damuwa me tsananin gaske tana daskare a zuciyar Amatu Amma Bata iya fadaba sbd zuciyar ta riga tayi nauyin da bama zata iya fadan ba.
Abdul zuwan ASH TALBA ba qaramin farin ciki ya Sakasa ba Dan zai iya Hana auren da akeson yiwa Amatu na rashin daraja da Kash rayuwa,tinda su kawun sun rantsuwa ga Faisal Nan Allah ya kawosa a daura dashi.
Ita kanta maamah abinda take fata kenan tinda sun rantse kodai ASH ya rokesu a fidda musu hatsin rantsuwar Kokuma ya amince a daura da Faisal duk da tashin hankalin Daya faru to Amma Kuma tanajin Husnah idan aka daura da Faisal zata iya shiga mummunan hali sbd mental health dinta Kuma tayi alqawarin bazata taba yin abinda zai cutatar da Daya daga cikin Amatun da Husnah ba sbd matsayinsu dayake Daya a gurinta shiyasa ma Tintini auren Faisal da Amatun ya fita ranta Amma ayau suna cikin tsaka me wuyar fita.
Acan kofar gida bayan angama gaisawa da barka barka maamah ASH ya buqaci Gani sbd magana da ita kafin komai.
Jiki na rawa kawu ya nufi cikin gidan kaman zai kife sbd rawar jiki da gaggawa.
ASH Kuma gidan uzaifa Dake maqale da Gidan aka Isa dashi har kan sabuwar tabarmar dake shimfide ta Barr Faisal.
Maamah tsayawa Kawu yayi akanta Yana tayi sauri Maza Maza me girma ASH TALBA na son ganinta yanzu.
Mayafi ta sauya babba akan Riga da zanin jikinta fuskarta tayi mummunan fadawa sbd damuwa data gama cinye zuciyarta da Kwanciyar hankalinta.
Dayake akwai kofar dazata shigar Dake tsakar gidan uzaifan ta cikin gidan Dan kusan ma a hade gidan yake kawai dai shi yayi wata kofar ne ta waje Dan yanason kebe kansa da amaryarsa, ta Nan sukabi tana tafe Husnah na bayanta kaman qaramar yarinya Dan qasar gidan ma Jin takeyi tana tsoron takawa Dan koina gidan ba Wani kyan Gani.
Suna shigowa madaidacin tsakar gidan Yana zaune kan tabarma gabaki daya qamshinsa ya cike iskar gidan har can cikin gidansu iska ke Kai qamshinsa duk Yan gidan suka rude da son ganin me girma ASH TALBA da aketa fada a redion kawu bello tinda gwamnan jaharsu zaiyi.
Kallo daya maamah tayi masa ta kasa tareda sauke idanuwanta daga kansa kaman yanda ta Saba Bata iya kallansa ko a bayan sbd kwarjinsa da tsananin haiba.
A mutunce ta qaraso tayi gefe Daya inda aka shimfida wata tabarmar bayan wadda yake Kai shi Daya ta zauna cikin sanyi ta Bude Baki ta gaidasa tareda masa barka da zuwa.
Shiru yayi na mintina kafin ya Bude Baki Bai kawo mata zancen tahowar datayi batareda ta jira dawowansa ba yayi mata uzurin tashiga Wani hali ne Mai wuyar tsayawa kayi tinanin Daya kamata Dan haka bazai dawo da zancen ba Kai tsaye hakuri ya Bata akan abinda ya farun Dan shi kansa Baya kaunar dawo da zancen dayake kamar tabon baqin ciki ne ga kowa na abinda yakusan faruwan.
Yana gama Bata hakuri ya Dora mata da zancen auren Naufal da zasu daura da AmatulMaleek tareda komawarsu ayau din duk gaba Daya.
Ba maamah ba hatta Husnah shock ta shiga sbd tasan maganar aurawa Naufal Amatu zai lalata maganar komawan maamah taredasu.
Da sauri ta kalli maamah idanuwanta na cikowa da hawaye masu tsananin dumi da tashin hankali batareda ta Saka Baki a maganar ba Dad din dayake gurin Kuma shiga zancensa idan bashine ya baka dama ba.
Ita kanta maamah din wasu hawaye ne suka tsinke mata wanda ya Saka ASH dauke kansa sbd ganin Kai tsaye alama ce da Bata aminta da Hakan ba.
Zai sake magana a karon farko a rayuwarta data fasa kuka a gabansa mara sauti sosai sbd baqin cikin dayake ranta yayi mata yawa batasan Yaya zatai da rayuwartaba.
Husnah ma kukan ta fashe dashi tana rarrafawa gurin Dad din cikin tsananin kuka tana cewa
"Dad Dan Allah maamah batason yaya Naufal ya auri AmatulMaleek,
Dad Yaya Naufal bayada halin kirji ko Daya wlh,
Babu ranarda ya kwana a gida tinda ya dawo kwanakin dayake yi a gida a kirge suke......
Abdulhameed Daya shigo sbd tashin hankalin Daya barke acan waje ma akan maganar Neman auren Naufal da AmatulMaleek su kawu sun buga hannu a qasa sunce Basu amince ba bare da Faisal cikin tashin hankali ya zayyano halayen Naufal din Babu na arziki hakama su kawu na Jin shine yayiwa Amatun qaramar kisa da fyade Dan haka wlh sun gwammaci bawa yayansu ayita ta qare kowa ya huta.
Faisal na Jin Hakan ya bayyanar da kansa Shima tareda bayyanarda manufarsa ta zuwa Shima take acikin iyayen Wasu sukace Shima ai sun tozartasu akan aurensa da Amatun Baya.
Rikici da hayaniya ce suka kaure a waje kawu bello ne kawai ya tsaya akan idan ASH TALBA yace Naufal zaa daurawa to wlh shi zaa daurawa Dan haka sauran Yan uwa sukai kansa Shima.
Abdulhameed ne ya sanar da ASH abinda yake faruwa a wajen Wanda dole ya Bada umarnin aka shigo cikin gidan uzaifa sbd sirrinta abin.
Bayan shigowarsu ganin irin kukan da maamah keyi yasa zuciyoyin kowa harziqa kawu bello ya kalleta Yana cewa
"Kuka kikeyi Asmau sbd zaa rufa Miki asiri a aurar Miki da 'ya bayan abinda yafaru?
Kawu ashiru ransa yagama Baci har Wani zafin kunnuwa yake ji sbd takaici yace
"Kuka kikeyi zaa bawa 'yayanmu aurenta ko kuwa Dan zaa daurawa Wanda ya lalatota din ita?
Asmau bansan me kikeso ki mayar damu ba, mutanen banza kika dauke mu ko me?
Bamu Isa da yayan naki bane?
To wlh rantsuwar aure ta Nan ba fashi a yau ma zamu daura mata aure wlh kowama ya huta da wannan tashe tashen hankalin.
Kawu ma maimaita rantsuwar yayi ta sai an daurawa Amatun aure yau kowa y huta musamman me girma ASH da yazo bazaiyi zuwan banza ba aure kaman anriga an daura da Naufal.
Faisal da Shima ya hankalinsa ya tashi matiqar gaske ganin Yana Neman rasa Amatun a gaban idonsa.
Shiru ASH yayi kowa yagama fadan nasa kafin ya sake buqatan a basa guri da maamah.
Maamah zuwa wannan lokacin kuka takeyi sosai ta dago cikin mawuyacin halin ta Kalli ASH bayan kowa ya fice daga ita sai shi dai husnah,
dukkaninsu sai abinda yace zaayi cikin tsananin kuka ta rasa abin fada a karo na farko Daya jefa mata tambayar Kai tsaye da cewa
Kinada Wanda kikeso a aura mata din??
Numfashi me nauyi ta sauke Babu Wanda yake ranta bayan Faisal Wanda ita kanta tana kunyar ambatar sunan Faisal din a gabansa da husnah.
Hakama itama Husnah Dake cikin tsananin tashin hankalin ganin Faisal zai iya auren Amatu tasan shine a ran maamah Wanda tana fada Dad zai iya daura auren,idan Hakan ta faru zata iya zaucewa,Dan haka gwara a daura da kowa Amma Banda Faisal,
Idan Kuma baa daura da Faisal ba duk Wanda Amatun zata aura a kauyen maamah bazata taba barinta a kauyen ta tafi tabarta ta shikenan ita Kuma ta rasa maamah......
Wani kukan Husnah ta fasa itama tashin hankalinta na qaruwa da duk abinda zai faru ayau din bazata iya barin AmatulMaleek ta auri Faisal ba kaman yanda bazata iya tafiya tabar maamah ba rayuwarta zata lalacewa zata iya qarewa daga qarshe asibitin hauka Dan ciwonta bazai bari ta iya karban wannan rayuwarba.
Maamah datasan kuka da tashin hankalin Husnah Menene a ranta itama abin a kirjinta ya tsaya tsananin quncinta na qaruwa
shiru sukai dukkaninsu bayan kukan husnah Mai cikeda damuwa da qunci Babu sautin dayake tashi,
Shi kansa ASH din shiru yayi sbd yasan a daidai wannan Gabar shi kansa baisan Menene mafitartaba,
A yanda yayiwa Husnah alaqawarin zai dawo da maamah gidansa
hakama itama yayi alqawarin bazai tilastata ba ko yin hukuncin da zai quntata mata sbd halaccinta dakuma cutatar da Akaiwa yarta.
Rarrafawa Husnah tayi zuwa gaban Dad din ta zube kusan kukanta ma ya Dena fita rawa jikinta keyi sosai tana son magana ta kasa sbd shaqewan datai na kukan maamah da Faisal.
Maamah ahankali ta dago idanuwanta jajir batareda ta iya ambatar sunan Faisal ba ta Bude Baki tace masa
duk hukuncin Daya Yanke zata bi Kuma duk Wanda ya aurawa Amatun ta amince Amma Banda auren Naufal wannan shine kadai adalcin da zai mata itada 'yayanta sbd tayi imanin zai tsayawa Amatu yayi mata adalcin abinda Akai mata tareda wanketa daga baqin fentin da Akai mata da bazai goguba har abada ga duk namijinda zata aura zai ci gaba da tinawa da goranta mata antaba kwatanta illata rayuwarta da fyade.
Miqewa tayi a hankali ta juya ta koma cikin gida.
#MAMUH#
#LA HOT
#AMATULMALEEK
#MARRIAGE
#HOT LOVE
#ROMANCE
#TALBAs
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Post a Comment for "Amatulmaleek 23"