Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Amatulmaleek 14

 Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar



14

*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*

*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍

*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*


MAGANIN SANYI 

MAGANIN NONO 

MAGANIN HIPS 

MAGANIN SLIMMING 

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

SET MAIJEGO

MALLAKA 

SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI'IMA

BACK TO VIRGIN SET

INFECTION FLUSHER


08142800199

07068558096




**********

Husnah bayan dawowarsu komai tsayawa yayi a rayuwarta sbd duk yanda aka dauka zata iya riqe abin takasa sbd kanta da zuciyarta Sam basa iya daukan abinda Bata Saba gani ya faru a rayuwarsu ba Dan haka sai abin yafara yawa Yana bawa maamah tsoro da Haydar harma dasu Amatu Dan kuwa cikin kanta depression din yafara tabawa Dan kuwa a yanzu rayuwa ce sukeyi kamar mahaifiyarsu dai ta riga ta rasu Dan kuwa dukkaninsu sun saddaqar da ba tashin zatayi ba San haka take Jin ita mum din ma ta riga ta rasu.


Dad dinsu sosai ya Maida hankali akan kulawa da lafiyarta sbd kada abin ya taba kwakwalwanta sosai duk da yariga yafara tabawa Dan haka ya tashi tsaye Shida maamah ne suka tsayu a gun kulawa da ita da yawon ganin likitocin da aka ringa yi da ita harta Dan fara samun sassauci tukuna Dad din yakoma harkokin gabansa maamah ta ci gaba da kulawa da ita.


***Maamah ta zama uwa ta zama kusan Uba ga 'yayan Abeeda da nata yayan Dan kuwa Dad dinsu Bai fiya zama ba kusan youshe Yana hanyar zuwa dubo Abeeda duk da Babu Wani alamar nasara ko zata Tashi din Amma Bai cire tsammani ba kamar yanda yake Jin idan Abeedan ta tafi tabarshi zuciyarsa zata samu raunin da Babu healing har abada.


Babu abinda Ba'a wadata maamah da 'yayanta a yanzu da komai na ragamar gidan yake hannunta,

Babu duniyar da basa samu,


Lalurar Husnah itace Mafi wahalar da maamah Kesha a rayuwarta sbd tamkar me ciwon qwaqwalwan gaske Takoma mata Dan haka sai take Shan wahala da azabar kulawa da ita Dan kuwa itama abin sai yake Neman taba ta Dan ganin takeyi idan AmatulMaleek dinta ce Hakan ya sama duk abu Daya zata ji gashi kusan ayanzu marayu ake daukan su Husnah din.



Ahankali ahankali lokaci yaja sosai Husnah tafara samun lafiya sosai bayan lokaci me Dan tsayi data dauka a halin na wuya da tausayi,

Maamah nata yayan sun hakura sadaukarwa Husnah da ita Dan kuwa tin bayan shigar Husnah wannan halin maamah Takoma abin tausayi itama sbd kula da Husnah din,

Ta wahala iya wahala akan Husnah,

Wani tsufa da qanqancewa tayi sbd rayuwar data samu kanta aciki,

Daidai da rana Daya Bata taba Jin gazawa ko jin ba 'yarta ce ta jini take dawainiyar da ita ba,

Husnah da ita maamah din sun samu Wani irin shaquwa da bond me karfi dayasa AmatulMaleek dole ta barwa kanta yarda da Babu abinda zai wanke ko rage kaunar da maamah kewa Abeeda da iyalinta,


A yanxu Husnah data saddaqar ta rungumi rayuwa a yanda tazo musu ba magaifiya sai maamah da a yanzu itace take wa kallan uwa ta gasken gaske harka tana Jin kamar ta Fi Amatu so da buqatan maamah a rayuwarta Dan kuwa kauna da so me tsananin gaske maamah ta nuna make a babu sirk,


Haydar kuwa Amatu ce ta cike masa gurbin uwa,Kuma 'yar uwa harma da masoyiyar dayake fata a gaba Dan itama duk da karatun datake harta gama ta tsayu akan kulawa dashi da debe masa kewa da hanasa shiga kowacce irin damuwa itada Abdul Daya zama kamar twin brother dinsa Dan kuwa komai nasu a yanzu Daya ne Babu bambamci.


A bangaren ASH TALBA kuwa a zuciyarsa Wani matsayi me girman gaske maamah ta samu da Babu abinda zai iya biyanta dashi har abada,

Itace ta tsaya akan gidansa da 'yayansa a lokacinda Babu Wanda zai tsaya masa,

Alokacin da 'yayansa suke buqatan uwa,

Alokacin da Shima yake buqatan macen da zata tsaya masa gidansa,

Ta sadaukar da rayuwarta da karfinta da lafiyarta harma da 'yayanta Bata bari gidansa ya shiga maraicin matar gidan ba,hakama yayansa Basu shiga maraicin da zai illata kuruciyarsuba, haka ma dashi kansa da itace ta tsaya tsayin dakan kulawa da duk wata lalaurarsa da komai nasa harya same qwarin gwiwa da zuciyar komawa kan qafafunsa ya tsayu a harkokinsa ya koma yanda yake a Baya,


Dan haka maamah itace jarumar rayuwarsu da bazasu taba iya biyan alkhairinta garesu ba daga shi har 'yayansa Dan haka matsayinta yake me girma a garesa.


Ta sadaukar da sauran karfinta da kuruciyarta ta tsufa karfi da yaji sbd wahalar data rataya akanta Dan bazaka kalleta kace tsaran Abeeda bace wadda itama aduk lokacinda yake dubata karyewa zuciyarsa keyi Takoma kamar ba itaba ciwo ya sauya kamanninta gaba Daya,Dan idan tanada Rabon tashi ba lallai ta sake komawa yanda takeba a Baya.



Mum Aisha datai tafiyar zuwa dawo Saida ta share itama lokaci me Dan tsayi kafin suka fara Shirye shiryen dawowa Dan Bata yarda ta dawo batareda Naufal da baiso dawowan ko kadanba shiyasa ta jira ya qarasa kammala takardunsa suka hada komai tareda Shirin dawowa gidan da zasu bude sabuwar rayuwa.




******AmatulMaleek tinda ta gama secondary Babu inda ta qara a karatun sbd Babu Wanda ya Tina da Hakan tinda Daman Madame abeeda ce take kula da lamarinsu Se mum Aisha datake musu komai da manufa Dan haka a gida take zaune tareda daukewa maamah wasu ayyukan gidan duk da ankawo masu aiki sunayi Amma wasu abubuwan kaman kulawa da sashen madame dana Mai gidan kusan yanzu itace takeyi tinda ko islamiyya ma ta sauke Dan haka Babu komai datake a rayuwarta itama yanzu bayan bautawa gidan ASH TALBA da Madame abeeda wadda suka fara shafe tarihinta duk da bawai ta rasu bane Amma a gurinsu kaman hakanne Dan kuwa ko su Husnah yanzu karatu sukeyi sosai kowa ya dangana ya rungumi kaddara hakama so Daya Dad dinsu ya taba zuwa dasu suka dubota sai yaga abin na tabasu Sai Bai qara barinsu zuwa ba.



******Ayau gidan ya Dan rayu da hayaniyar dawowar mum Aisha da Babban matashin Gidan ASH TALBA wato Naufal Talba Wanda dawowarsa qasar ya gama zubar da duk Wani farin ciki da burin rayuwarsa Dan haka Koda aka daukosu airport fuskarsa Babu alamar wasa ko sakewa acikinta,

Sanye yakeda black sweatshirt da sweatpants sai fcap da sunglasses.


Husnah ce kawai tayi murnar ganinsa ita data sansa sosai Dan haka rungumeta yayi ahankali Yana sake mata kyakkyawar fuskarsa Yana cewa


"Oh my gorgeous"


Dariya ta Dan yi tana dagowa daga jikinsa tace


"Sannu da dawo N Talba"


Dariya yayi sbd tinowa da shine ya koya mata kiransa da N Talba Dan Uncle din Yana masa Wani iri kamar tsoho.


Mum Aisha ta rungume itama tai mata sannu da zuwa cikin farin cikin ganinsu.


Ciki suke kokarin qarasawa Haydar ya fito daga geam dayake ta hanyar cikin garden Yana ganinsu ya qaraso Shima cikin farin cikin ganinsu ya rungume Naufal din Yana cewa


"Happy to see you Uncle, welcome"


Dan rungumesa Shima Naufal din yayi Yana kallan yanda Haydar din duka duka shekarunsa Basu wuce 18 ba Yanaga amma sbd geamin da yaron keyi ya Bude sosai kamar Wanda yayi 25 koma fiye gashi

Yana budewa kamanninsa da ASH TALBA na sake bayyana.


Ciki sukayo dukkaninsu zuwa palon mum Aisha da tini Amatu ce ta gyaresa fes Dan tin can tafison aikin Amatu Dan yafi nutsuwa da tsari Dan haka ko yanzu Amatu ce ta gyare mata palonta da bedroom dinta da toilet.


Shi Kuma Naufal sabuwar me aikinsu ce ta gyare bangarensa dayayi shekaru bayanan Amma ana gyarewa komai ya dawo fes kamar ranar aka sauya komai.


Ko zama Naufal beyiba a palon mum Aisha ya jiya yanufi bangarensa da already ankai kayansa can.


Yana Isa Bai tsaya Palo ba Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya jefar da wayarsa kan lafiyayyan gadonsa Yana sake numfashi a bayyane tareda zare duk kayan Dake jikinsa a tsakiyar dakin ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa.


Mum Aisha ma wanka tayi ta fito tayi salloli Dake kanta dayake safiya ce ko abinci Bata ci ba ta kwanta bacci sbd ta huta.

Shi kansa Naufal Yana Gamo wankan ya shafa abinda zai shafa na Mai da tirare ya Saka Wani tight short ya fada gadonsa hutawa yake buqatan yi.



Su Amatu kuwa mum Aisha kawai suka samu damar yiwa sannu da zuwa bayan ta tashi bacci da kusan yamma.


Kallan Amatu mum Aisha tayi ganin yanda a yanzu ta zama cikakkiyar budurwar da Babu abinda Bata rasa ba a jikinta na kyau da kyan jiki harma da jiri me kyau,

Sannan nutsuwarta data Saka ake Gani kaman sanyine da ita duk komai na nan saima abinda ya qaru ga uwa Uba kamun Kai ko a cikin gida ba kowane zece AmatulMaleek ta sake dashiba sosai.


Cikin gatse mum Aisha tana kallanta tace


"Amatu yanzu da aka gama makaranta Se aure ko tinda ba Wani karatun gaba zakiyiba"


Shiru Amatun tayi tareda Dan sauke boyayyan numfashi a boye kafin ta Dan saki kyakkyawan murmushi tana qarasa nade kayan mum din datake nadewa tana jerawa a wardrobe daga cikin akwatin Data dawo dashi batareda ta iya cewa komaiba.


sake maimaita tambayar tayi itama fuskarta a sake Dan tabbas zata so Amatun tayi aure da wuri tabar gidan tinda Naufal ya dawo idan batai taka tsantsan da Yan matan gidan ba masu aiki komai zai iya faruwa da wuri halinsa da Bazata taba yarda ASH ya saniba to zai sani komai ya lalace musu Dan haka dole zata Bude wuta ayiwa Amatu aure tabar gidan Dan gwara Yan aiki idan ya lalatasu zata Basu kudi ta sallamesu asiri rufe Amma AmatulMaleek sbd matsayin maamah a gun ASH zaa iya samun matsala.


Duk yanda mum Aisha din ta bugi cikin Amatu Dan Jin ko tanada saurayi Sam Bata samu Jin komaiba sbd zurfin cikinta dakuma saurayinka da batadashi.


Harta gama gyara kayan mum din Janta mum takeyi da fira daban daban itama ta San amsawa da Wanda ta sani Wanda bazata iya fada Kuma sedai murmushi kawai.


Kayan da zaa Saka cikin kayan wanki ta fito dasu basuda yawa kala biyu ne ma Dan haka ta fito dasu ta miqawa me aikin da zata wanke su.


Tana kaiwa kofar ficewa mum ta kirata tareda cewa


"Ki kawomin salad Amatu bazan iya cin white rice dinnan ba yanzu zata dameni"


"Ok mum" ta fada a natse da muryarta me dadi tana juyawa zata wuce ba zato tai karo da mutum da sauran kadan kirjinta ya Hadu da nasa tayi saurin yin Baya tana dago idanuwanta da Dan mamaki.


Naufal da sauran kadan numfashinsa yabar jikinsa sakamakon kamshin jikinta Daya shiga hancinsa sosai harma da Dan haduwar da jikinsu yaso yi sauke mata mayun idanuwansa yayi Yana kallan mamakin inda ta fito da inda zata,


Wani numfashi ya hadiye tarewa yawu ta maqoshinsa da Saida Hakan ya nuna a wuyansa Yana kallanta da dukkanin idanuwansa Dake qarawa mata sonsa.


Amatu dauke idanuwanta tayi daga kansa fahimtar waye shi Din

Sai tasake yin gefe kadan tareda Bude Baki a hankali ta furta 


"Yi hakuri ban luraba,sannu da dawowa."


Har lokacin idanuwansa akanta suke sedai lokacinda ta Bude Baki tana magana idanuwansa a bakinta suka koma daqyar ya Bude Baki zai amsa mata mum Aisha ta katsesa da cewa


"Amatu wuce kije"


Batareda ta gama fadar ba Amatu ta rabasa ta wuce tana Dan sake gyara riqon kayan hannunta dasuka zame batareda ko waiwayosa ta sake yiba.

#MAMUH#



*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee 

And

*_YANCI DA RAYUWA_*

By Hafsat Rano 

Na kudi ne

For more page ku biya

500 for littafi Daya

1k for duka books din biyu

 at👇

0022419171 access bank Maryam sani

09033181070

Post a Comment for "Amatulmaleek 14"