Amatulmaleek 12
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
12
YAR UWATA TSAYA KIJI KAYANDA SISTER NA KE SAYARWA BAZAKI RASA ABUNDA KIKESO BA A CIKI IN SHA ALLAH 🙏💪
Sis Kinason siyen maganin Kara girman hips da breast kodai rama ce damuwarki❓kinaso kiyi kiba ki ciko kiyi kyau KO KUMA KAYAN GHT KIKESON KISIYA Na gyaran skin fatarki tayi kyau❓ko maganin infection ❓asthma ❓ ulcer ❓ rashin haihuwa ❓ hepatitis ❓ diabetes ❓ ko Kuma kiba ce da tumbi suke damunki❓ to tanada magani da yardar Allah ❓ga group link din sister na🥰 kiyi joining 👆👆👆👆Zaki samu fiyeda yanda kikeso Kuma kayanta nada sauki ga kyau tested and trusted 👍💪
Idan bakyason shiga group kiyi saving number dinta👉 https://wa.me/+2349038090328 👈kimata magana kice kinyi saving itama zatayi saving taki🥰 zaki godemin na hadaki daita danayi in Sha Allah 🤗
**********
Naufal dayaji mum dinsa Tayi shiru batace komaiba ya tabbatarda taji maganar Cynthia haka Kuma yasan yanda ta tsani mace ta rabesa sbd sam Bata masa shaawan aure batareda ya tsayu a cikin dukiyar data tsaya mata a zuci da ido Tim kafin ta haifesa ma.
Ajiyar zuciya ya Dan sauke a boye Yana basarda abinda mum din taji Yana cewa
"Mum ki bari zan kira anjima idan Aunt din ta farfado na mata ya jiki and I will call the grt ASH TALBA Shima na masa sannu da jikin nata"
Numfashi me zafi mum din ta hadiye randa duk ya gama Baci da daukan zafin halin Naufal din Dan haka Kai tsaye ta kashe wayar batareda ta amsa shi ba Dan kuwa zuciyarta zata iya kumbura a gurin.
Tana aje wayar ta koma dakin ta Tararda maamah data sha kuka Mai tsima zuciya da tausayin 'yar uwarta datake Jin inama wannan kaddarar Bata sametaba Amma ko yanzu ciwo ba mutuwa ba.
Cikin dacin zuciya mum Aisha ta nufi gurin zama ta zauna tareda jefa wayarta cikin lv handbag dinta Dake gefenta aje tana Jin zuciyarta na kasa hucewa Dan haryanxu Naufal ya kasa girman burin dataci akansa kwata kwata halin ubansa yayo bayan mace Babu abinda yake gabansu kamar Babu wata rayuwar bayan ta kusantar mata.
Tsoki data ringa saki Akai akai batareda tayi magana ba ya Saka maamah da idanuwanta sukai jajir dagowa ta kalleta itama batareda tace komai din ba.
Sai dare sosai suka dawo gida kuma har suka dawo Amatu batai bacci ba tana jiran dawowarsu cikin damuwa da tausayin Madame abeeda wadda ta San ciwon a jikinta yake Amma zuciyar maamah yake ci Dan kuwa maamah bazata sake walwala ba sai 'yar uwar tata ta samu lafiya.
Wanka kawai AmatulMaleek ta iya hadawa Maamah din ruwan zafi tayi Amma ko abinci Bata ci ba ta kwanta,
Bata iya cewa maamah din komaiba sbd tasan Babu abinda zata iya cewa bayan adduar data yiwa madame Abeeda ta samun sauki a bayyane.
Shima Abdul dayayi bacci ya Farka daga baya ya tambaya jikin Madame din Amatu tace yayi shiru kawai.
Husnah kukan datasha Jin ciwon mahaifiyarta Saida ta Saka maamah kuka itama sbd kasa riqe kanta tai Dan ganin kawai sukeyi mutuwa zatayi ta barsu.
Amatu komawa tayi Husnah da maamah din take kulawa dasu sbd halinda suka shiga ahaka Kuma take zuwa makaranta ga aikin maamah da dole itace ta karba tanayi tinda maamah din Takoma asibiti itace take jinya.
*****Kwana biyu madame tafara Jin sauki Dan tana Dan iya komai da kanta hakama maamah komai itace take mata bautarta da sadaukarwa ya ninku Dan haka dole Amatu ta dauke idanuwanta da zuciyarta daga Hakan Dan kuwa ta yarda ta sadaqar kaunar maamah din da Madame din bazata iya Hana maamah bauta mata duk abinda zatai sbd maamah ta riga ta sadaukar da kanta ga Madame din da duk abinda ya shafeta.
Ayau asibitin suka taho tareda Husnah dasu Haydar da ita AmatulMaleek din wadda harta San fada sbd ayyukan maamah data maye gurbin kusan rabinsu ita keyi.
Koda sukazo madame din tana zaune kan kujera maamah na hada mata ruwan wanka a toilet na dakin.
Shigowarsu ya Saka Madame dago idanuwanta dasukai haske ta kallesu Daya bayan Daya tana Jin tausayin 'yayanta da duk sukai sanyi tinda sukaji ciwonta.
AmatulMaleek ce ta nufi toilet din Mai tsaye cikin sanyi da nutsuwa bayan sun gama gaida Madame din da yi mata sannu Dan ta taimakawa maamah aikin datake ta yi a toilet din takasa fitowa.
Wanke toilet din takeyi Wanda baida komai fes yake sbd tsadan asibin tsaftansa na musamman ne bare su dasuke kaman vip room a can sama.
Kallan maamah din tayi tareda Dan lumshe idanuwanta ta qaraso ta Kai hannu ta kama hannun maamah din Dake goge ruwa da mopper sbd kada Abeeda ta taka ta zame.
Dagowa Maamah tayi ahankali ta kalleta da idanuwanta dasuka fada itama
Ganin AmatulMaleek ce ta saki Wani sanyayyan murmushi tana ambatar sunanta da cewa
"Yaushe kuka xo??
Numfashi mara sauti Amatun ta sake tareda karban mopper din tana sake kallan maamah da fararen idanuwanta masu maiqo aciki ta Bude Baki a natsenta tace
"Bari na qarasa kawai kije ki huta tareda su Husnah harma dasu Abdul mukazo."
Murmurshi maamah ta sake zatai magana AmatulMaleek ta girgiza mata Kai a hankali tareda lumshe idanuwanta ahankali tace
"Maamah zan qarasa kije ki gaisa dasu"
Murmurshin kaunar ta sakarwa Amatun cikeda kulawa tace
"Shikenan ki kula kada ki zame yanada santsi sosai"
Gyada Kai ahankali Amatu tayi tana kallonta harta fice toilet din.
Hannun doguwar rigar jikinta ta Dan nade kadan sbd kada ya jiqe ta fara mopping toilet din da maamah tariga ta gama wankewa.
Cikin nutsuwa takeyi gogewan harta gama ta Dan dauraye mop din ta ajiye gefe ta wanke hannuwanta liquid soap din dayake toilet din tafara kokarin hadawa Madame din ruwan wanka.
Wani qamshi ne da Bata taba Jinsa ba a ruyuwarta sbd fitarsa daban da Kuma yanda qamshin yake daban a hanci harma da yanda yake sauka a zuci,
Qamshine me sanyi da Dan haka ta Kalli kayan wankan madame Dake Jere a gurin tana Dan sauke numfashi me sanyi mara sauti sbd sanin wani abu daga cikin kayan wankan ne yake wannan qamshin,
Ruwan wankan ta qarasa hadawa tareda sauke wanke hannunta kafin ta nufi kofa ta Bude ta fito ahankali tana Dan warware hannun rigarta data janye.
Qamshin Daya shiga hancinta a cikin sanyi na nutsuwane tareda Jin tsit din dakin ya Sakata dagowa ahankali idanuwanta Basu sauka a koina ba sai akan the grt ASH TALBA Dake zaune tareda Abeeda a kujera Daya fararen dogayen yatsun hannunsa na sarke da nata tayi shiru a gefen jikinsa kwance.
Firgita da mamakin da Bata shirya musu bane ya Sakata shiga faduwan gaba da shock lokaci Daya sbd ba kowa adakin kowa ya fice hakama tinda ta taso a gidansa suke rayuwa a cikin gidansa yaune ranar farko data fara ganinsa gashi ga ta,Dan kuwa idan ma ya Santa to a iya Baki ya Santa 'yar Asmau takwarar matarsa Abeeda AmatulMaleek.
Rikicewa ta sake shiga sosai Dan Bata tsammanin fitowa Taga ba kowa ba Kuma Bata taba kawo tinanin zata fito ta ga the grt ASH TALBA a gabanta ba yau bayan ganin nesa Suka Saba masa hakama Wani irin zama ne sukai Shida Abeedan wadda tayi shiru a jikinsa da yanda shikuma nasa hannuwan suke sarqe da nata Dan haka duk ta sake rudewa cikin sauri ta nufi kofa tana furta Ina wuni batareda ta dago ta sake kallan inda suke ba.
Amsawa kawai Shima yayi da muryarsa me kauri da tarin nutsuwa da Kwanciyar acikinta batareda ya duba waye ba Dan kuwa gabaki daya tinaninsa da hankalinsa na kan Matarsa dayake Jin kaman ya bar qasar da ita a ranar.
Ita Kuma tana fitowa dakin Kai tsaye gurin da maamah ke zaune ta nufa ta zauna gefenta batareda ta furta komaiba,
Haydar Dayazo ya zauna gefenta Shima Yana kallanta cikin tsananin kulawa da kaunarta da Baya hadawa da komai sbd Allah ne ya Saka masa Hakan tin Yana yaronsa Amma yanzu daya fara zama saurayi Jin yakeyi kamar son dayakewa AmatulMaleek kullum qaruwa yakeyi batareda yasan wane so ne zuciyarsa ke kamuwa dashi ba tin Bai gama zama cikakken saurayi ba.
Jinsa a gefenta ya Saka Amatu juyowa ahankali ta kallesa da fararen idanuwanta Dake sakashi qure kallansa akanta koyaushe sbd kyanta dayake Gani fiyeda duk Yan mata tsaransa da wainda suka girmesa sosai kaman Amatun.
Ajiyan zuciya suka sauke atare tana dauke kallanta akansa sbd sai yau data taba ganin daddynsu a Fili ta fahimci daga Husnah harshi da ake cewa Yana yanayin mahaifinsa duk ba Hakan bane duk da kallo Daya tayi masa ta sauke Kai Amma a Hakan ma zata iya qararda Haydar ba Wani kama yakeyi dashi ba sosai sbd shikam ASH TALBA din batama San tayaya ake fassara kamanninsa ba.
Cikin kulawa Haydar ya sake kallanta yace
"Lafiya dai??
Sake juyowa tayi ta kallesa Dan itama har cikin ranta kaunar Haydar daban ce sbd jinsa takeyi kamar Abdul da uwa Daya Uba daya ya haifesu Kuma qarin girman kaunarsa a ranta shine yafi kowa Bata kulawa da tattali duk da Yana qasa da ita a shekaru Amma sosai yake nuna kulawansa akanta fiyema da Husnah Dan haka kaunarsu take da qarfi.
Bayan ta sake kallansa ahankali ta Sakar masa Dan murmushi tace
"Lfy kalau,Yaya Akai ne??
Ko mu tafi yanzu tinda dad dinku yazo babu me sake komawa ciki Seya tafi."
Kofar dakin ya kalla kafin ya Maida kallansa kan Husnah Dake waya da Uncle Naufal dinsu tin dazu ya dawo da kallansa kan Amatun yace
"Mu bari Dad ya fito mu sake dubata saimu tafi din."
Gyada Kai tayi tana cewa shikenan ba damuwa Allah yabawa mommy Abeedan lafiya.
Amin"kawai yace Yana kallan Abdul Daya dawo daga reception.
Zaman Jira suka fara suna Dan fira sama sama har kusan awa uku kafin ya Bude kofa zai fito.
Qamshinsa ne yafara gauraya gurin Wanda kowanne hancin dayake shaqan qamshin zai bambamta tsadan qamshin da wasu qamshin sbd Kai tsaye qamshin cikin sanyi me nutsuwa yake shiga ya wuce zuciya da itama qamshi me dadi ke isar mata.
Dayake Personal person dinsa Jameel na gurin Yanata waya Shima wanda kusan wayar duk ya harkar businesses na ASH dinne,
Shima ana Bude kofar ya kashe wayarsa ya qaraso kofar ya qarasa Bude masa Yana yiwa Madame sannu da jiki.
Fitowa ASH din yayi Haydar da Husnah suka bisa suka wuce Husnah na riqe da hannunsa Daya data kama Shima cikin kulawa yake Dan kallanta a da idanuwansa da idan ba iyalansa ba baayi kalla sbd tsananin kwarjininsu da haiba.
Maamah da ita ce kawai yayi magana da ita sosai kafin ta fito dakin su barsa ta miqe tafara komawa ciki kafin Amatu da Abdul suka bita.
Maamah Dake zaune har lokacin Amma da alama tayi wankan suka kalla suna sake mata sannun ta amsa tana kalla maamah da itama ita take kallan lura da jikin Abeedan din yayi sanyi idan Kuma ta canka abinda Abeedan take tsananin gudu da tsoro ne yake Shirin faruwa zaa dauketa daganan din zuwa Neman lafiyanta zata rabu da 'yayanta.
#MAMUH#
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Post a Comment for "Amatulmaleek 12"