Acikin Gidana 12
⚡️A CIKIN GIDANA ⚡️
(SEX,ROMANCE,RUNS)
📝FATIMA ZAKARIYYA
EPISODE1️⃣2️⃣
Kanta ta danna a pillow tanata ihu ,ta shiga Rudami matuka,bata tuba tunanin Zata iya tsintar kanta a wannan situation din bh ,Kai !!! Aliyu ! Aliyu dai mijinta baban yarana ,masoyinta ,Wanda nake Alfahari dashi , hasbunallahu wani’imal wakeel ,Allah ka sanyaya min zuciya tah ,Allah kaine Allah ,Allah ka taimakeni ,Allah kana gani ,Allah kaga abun Dana gani ,Allah zuciyata babu dadi ,Allah Dan Allah ,Tana fada tana kuka ,ta rasa inda zata saka rayuwarta ,kuka take Tana buga hannunta agan bed site drawer ,hannunta saida ya kumbura sbd bugu ,wannan wace irin duniya ce ta fada a ranta ,mene abun dadi a wanann rayuwar,Ina akeso mutum ya saka kansa ,me kuma zanyi a duniyar nn ,sai kuka ,a daki take Amman haka ta tashi Tana zagaye dakin nn Tana kuka ,bakin cikin mh ta rasa daga inda yake fitowa ,Jin karar motar Aliyu ne yasaka tayi sauri ta fada toilet ,motarsa ya ajeyi Ko kofar bai rufe bh ya tafi yana sauri ,sama ya hau dan bai ganta a kasa bh ,yana zuwa kofar dakin sai kuma ya tsaya ,dan idan ya shiga baima San me zai ce mata bh ,Allah ya gani bai tabajin kunyar tah bh irin na Yau ,baisan tanada kwarjini bh sai yau ,ya Allah ya zanyi ya shiga tambayar Kansa,ya tsani Kansa bayason mh ya tuna abun daya Faru ,dakinsa ya koma shima ya fashe da kuka hardasu bare Baki kaman wani yaro,kuka yake sosai dan gabaki daya ya rasa me zaiyi ya samu sukuni ,bai taba sanin shatu Zata gansa a irin wannan situation din bh ,Mirror ya kalla yaga har yanzu bakinsa da red lipstick,Zara ido yayi ya shiga gogewa da rigarsa kaman zai cire bakin ,pillow ya dauko ya dinga bugawa a kasa yana kuka ,wanka shima yaje yayi ,bayan ya fito ne ya yanke shawarar yaje yaga shatu yaga ya ake ciki ,yana zuwa kuwa ya murda kofa ,ganinta yayi akan sallaya tanata sallah ,zama yayi daga gefe yana jiran ta iddar ,ita kuwa tunda taga shigowarsa ta dinga sallah taki dainawa ,sallah kawai takeyi dan batason mh yace zai mata magana ,a yanzu ba maganar sah takeso bh,ya barta kawai taji mah da abun dayake ranta ,ganin bata da niyyar iddar wa ne ya tashi jiki babu kwarai ya fita ya koma dakinsa ,yana fita kuwa ta iddar ,ta zauna tanata gayawa Allah Tana kuka ,zama tayi Akan gado Tana tunanin abun da zatayi next ,tashi tayi ta bude wadrobe ,ta dauko wasu kayanta na Atamfa Masu kyau ta saka ,dauri tayi simple ta shafa powder hardasu saka kwalli ,red lipstick ta dauka harta shafa sai kuma ta tuno yanda taga red lipstick a bakin Aliyu ,sai ta hau gogewa,pink ta dauko ta shafa ,ta zauna tayi azkar ta saka counter a finger dinta ta fita tanata ambaton Allah a ranta ,kasa tayi ta kira jummai tazo ta tayata hada dinner ,favorite food din Aliyu tace zasuyi ,tuwo ta masa da miyar taushe me dadi ,kamshi duk ya cika gidan, dinning takai ta hada masa , Akwai zobo datayi da safe a fridge ta dako masa then ta hada masa tea dinsa as usual,ta koma parlour taje ta zauna ta daure ta kunna kallo,ba kallon take bh Amman dai ta kunna kallon ,Addua take tayi a ranta ,da taji zatayi kuka saita daure ,Aliyu ne yaga zaman dakin bazai masa bh kuma yaji saukarta kasa yasa ya sauko kasan ,ganinta yayi a parlour tayi kyau Tana kallo ,saida yaji gabansa ya fadi ,daurewa yayi yazo ya zauna a kusa da ita,har zuciyarta saida taji ciwon zama a kusa da ita da yyi ,dan ita har ranta bataji tanason zama a kusa dashi kuma,basarwa tayi ta cigaba da kallonta Tana murmushi a zuwan kallon da take ne yake bata murmushi,gyaran murya yayi ya dan kalleta ,gani tayi kaman magana yakeson yi sbd haka tashi tayi cikin style Tana masa murmushi ,tashi kazo Kaci abincin kh ,I cooked your favorite,dinning ta wuce ta zuba masa Sannan ta hau sama ,binta yayi da kallo dan shi dai jinsa yake kaman a prison ,so yake tama bude Baki ta masa maganar abun daya Faru ya bata hakuri ya gaya mata abubuwa Amman taki bada room mh ayi maganar ,shi wannan wace irin masifa ce,gabaki daya ta kullesa da ransa ,binta yayi da kallo sanda ta hau sama yaga Tana tafiya majestically Tana Danna wayar hannunta ,hardasu cin chewing gum ,shi dai Yau yaga ta Kansa ,wayarsa ya dauko ya shiga browsing “if your wife caught you cheating “, duka answers daya gani shows mata sunayin spark ,suna kuka ,wasu mh suna guduwa su tafi ,anayin hauka ,su kuma maza suna bada hakuri su lallaba su hada da karya duk dan matan su huce, duk cikin wannan babu Wanda shatu tayi ,kunya mh yaji da tace masa Wai ga abincin sah can ,da Ana shiga zuciyar mutum da ya shiga yaga me take cewa me take gani Akansa ,shi gabaki daya mh tsorata sah takeyi ,kaman ba shatu bh ,duk ya firgice yayi zuru zuru,dinning din ya lalaba yaje ya zauna yanason cin abincin nn Amman kadan ya iya ci ,ga abun mamaki ya cika masa ciki ganin babu abun data fasa masa ,infact favorite dinsa mh tayi masa ,duk abun da yakeso shi tayi masa ta kawo ,shi dai ya shiga uku yace ,Ina zai saka kansa ,me zai cewa shatu ne ,taki basa fuska,he want to talk to her Amman baisan ta inda zai fara bh ,baima San me zaice bh ,dama da zatayi magana ne sai yasan abun fada ,to taki masa maganar ,saman ya sake binta ya tsaya a kofar dakinta ,tanajin karar sah ta dauki waya ta fara wayar karya ,shima ji yayi tana waya kuma yaji tanata dariya ,Chab di yace a ransa , what is really going on ,kasa shiga Yayi ya koma dakinsa ,itama data tabbatar ya tafi wayar ta ajiye ta cire daurin ta,sama take kalla wasu sababin hawaye na zubo mata ,lallai Aliyu mayaudari ne ta fada a ranta ,tun yaushe yake mata karya yake yaudarar tah taketa tambayar kanta ,sai a yanzu maganganun hidaya da Rahama suka dinga fado mata ,wato this life never trust a man ,ka yarda da Allah kawai , and abubuwa zasu iya chanza maka any moment ,shiyasa akeson ka zama cikin Addua kullum ,yanda Ko abun tashin hankali ne zai sameka idan yazo saiya zo maka da sauki ,Yau abun da takeji a film a littafi gashi ya faru akanta ,so he was kissing a girl ,wato ita bata iya kiss din bh kenan ,yanzu duk abun da take sbd aurenta Ashe a banza Aliyu yake gani , kuka ne me karfi ya kwace mata ,Allah ya isa Aliyu ta fada a fili Tana kuka ,Allah ya isa ,Wayyo Allahna Ina zan saka kaina
Shima tunda ya shiga dakin ya kasa zaune ya kasa tsaye ,ya Dora hannu akansa ,ya bubuga hannunsa a wadrobe,yayi ball da abubuwa a dakinsa but still zafin da yake ji karuwa yake ,he want to hug his wife ya bata hakuri Amman baisan ta inda zaiyi bh ,sake fita yayi yaje kofar dakinta ,knocking yaga yanayi wanda shi Kansa baisan Meyasa bh ,before kai tsaye yake shiga dakinta but Yau ya tsaya knocking ,Tana jinsa ta gyara daurinta ta goge face dinta ta dauke wayarta ta fara dannawa , “wanne ?” Tace , da kyar ya iya cewa “Nine “ ,shigo tace masa ta cigaba da dannna waya dan har ranta batason ganin Aliyu batason sakasa a idonta ,kusa da ita yaje ya zauna a kasa kaman wani maraya ,shiru kowa dakayr ya iya fara magana ,Sugar dama inaso zamuyi magana ne , kanta ta juya Tana kallon kofa dan batason hada ido dashi ,Aliyu magana kuma ,nasan kah gaji Yau kayi aiki dayawa kaje ka kwanta ka huta kaji ,karka damu da wani Yimin magana ,harbawa yaji kirjinsa nayi ,wani irin aiki kuma ya fada a ransa ,shi dai ya shiga uku yaga ta Kansa ,Tama tsaya ya mata bayani taki ,daurewa yayi ya sake ce mata ,ni babu wani gajiya da nayi ,pls sugar ki taimaki ne ki taimaki rayuwata ki tsaya muyi maganar da zanyi miki,wlh tlh bazan miki karya bh komai zan gaya miki ,Allah Aliyu babu wata magana da zamuyi ta fada tana masa murmushi ,pls respect my decision go and sleep kaji ,ko akwai abun da zan kawo maka ?,Akwai abun da kakeso ne ?, Kai ya gyada mata jiki babu kwari ,tashi yayi yana tafe yana juyawa yana kallonta wace taketa danna waya ,yana fita yayi dakinsa ya dau waya ya kira Mubarak,Mubarak yana kan hanya zaije yaga karima ,dan yace shifa duk abun da zatayi sai yaga matarsa Yau dinnan ,kiran Aliyu ne ya shigo yayi sauri ya dauka ,” how far “ Aliyu ne ya fara magana kaman zaiyi kuka ,”Mubarak kana Ina ne ?” “Gani nn a hanya zanje inga karima batada lfy ,zan daukota mu dawo gida,lfy naji muryarka kaman zakayi kuka “,”kukan ya saka masa,Mubarak saida yayi parking Jin Aliyu na kuka ,lfy Ali mene ya faru “,Aliyu ne yace ka tsaya a inda kake ganin nan zuwa ,fita yayi yaje ya tarar dashi a bakin titi yayi parking yana jiransa , Mubarak na ganinsa ya fito da sauri dan ya matsu yaji mene ya faru ,shi ya dauka mh wani ne ya rasu , hawaye ya tarar yanayi ya shiga gaya masa abun daya Faru ,jikin mubarak yayi sanyi sosai sbd haka cewa yayi tada motar kah ,Nima Bari na kunna tawa mu tafi gurin kamal ,danni tsakani da Allah mh bansan me zan ce maka bh ,Nima yanzu haka tawa matsalar nake son zuwa na gyara
Kamal ya fara bacci mh yaji Ana kiransa ,wayar ya duba yaga mubarak ,yana dauka kuma yaji ance fito kofar gida ,jallabiyarsa ya zura ya fita ,yana zuwa kuwa ya gamsu duk su biyon sunyi tsili tsili kaman Wanda aka yiwa mutuwa ,Aliyu kaman wani maraya duk ya fita hayacinsa,lfy ya shiga tambayarsu ,bude gate din yayi ku shigo ciki ,garden din gidansa suke wuce suka zauna ,Mubarak ne ya shiga gaya masa abun daya Faru ,tun kafin ya karasa gaya masa ya shiga gyada kai yana sallati ,kallon Aliyu yayi nasan za’a Rina ,abun dai da nake muku gudu gashi ya sameka,yanzu Aliyu ya zakayi ,Aliyu ne yace ni wlh bansan yanda zanyi bh ,taki min magana ,taki kuka ,taki zagi ,taki tsinuwa ,takeyin komai ,abincin Danafi so mh tayimin ,harda su drinks da tea ,tayi wankanta kaman wace Zata fita ,guys am stocked , ya zanyi ?ta Ina zan fara ?,me zan cewa matata ?,yana fada yana share hawaye,kamal ne ya fara magana ,Gaskiya Abu baiyi dadi bh ,da farko dai ,matarka is one in a million ,Ko a haka aka tsaya kaikam ka sami mata , ta burgeni karshe ,Amman taban tausayi ,is not easy for a woman ta Kama mijinta a hotel da wata Tana kissing dinta ,is never easy Ina tausayin halin da ka saka matar kah ,Aliyu ne ya fashe musu da kuka ,yanzu ya zanyi mata dan Allah ku taimakamin,wlh Ina son matata,banason ta daina sona ,banason ta daina ganin mutuncina ,da wani ido zan kalli shatu na mata bayani ,me zan ce mata ,Gaskiya safiyya Allah ya isa tsakani na da ita ,Ina zaman zamana yarinyar nn ta kirani ,kamal ne ya karasa masa , gashi kuma tanacan nasan tana harkokin gabanta ta sakaku a masifa kaida matarka ta sunna bah ,Kai bakasan kyautataa matarka kadai zai Kaika Aljannah bh ,mu maza idan ance Aljannarsu a kafan mu yake ,mu kuma kyatata musu may lead us to Aljannah ,mata sunada rauni abun tausayine su abun lallabawa ,na dade Ina gaya maka Gaskiya Aliyu bakaji ,me matan waje suke Baku Wanda matanku na gida bazasu iya Baku bh , Mubarak ne yace ni dama zata danyi maka ihu tadanyi zage zage irin yanda karima tayimin da ka dan samu hanyar mata magana kadan hada da borin kunya da karya ,Amman shirin nn da tayi maka Nafi tausaya maka ,kuma nasan she is in pain duk munsan wannan ,Amman dai da Zata taimaka kuyi maganar da abun zaizo da sauki ,Aliyu ne ya goge hawayensa ,ni yanzu abun danake so daku dan Allah ku taimakamin kuzo muje ku tayani bata hakuri da mata bayani ,kamal ne yayi saurin cewa wah!! ?? Bada niba Ali , Tana ganinmu da mutunci kasan dai yanda zaka janyo hankalin matarka ,kaje ka bata hakuri ,Amman Gaskiya you fucked up !! Yanzu shatu Ko ta yafe maka kasan mata da riko na masifa ,zatayi ta kallonka da abun ne ,wani kukan Aliyu ya saka ,yarinyar nn Tana ganin girmana Tana mugun ganin darajata ,Innalilahi waiinailahi rajiun,Zata Kara ganin girmana kuwa ? Allah rayuwata batada Amfani indai shatu ta daina sona ,shima Mubarak din cewa yayi badashi bh ,abokina kayi hakuri ,Be a man,ka daure kaje kawai kayi confronting dinta ,ka bata hakuri ,shatu Tana sonka ,idan Allah ya taimakeka Zata gane ,Amman fah sai kayi hakuri ,abubuwa sai a hankali zasu dawo daidai , Aliyu har yanzu kuka yake ,kuma rokonsu yayi Akan su taimaka masa su masa jagaba ,dan shi wlh tsoro take basa ,ya basu tausayi sosai sbd haka kamal ne yace tashi ka tafi kaje gida ka huta ka kwanta ,muyi waya gobe idan da Yuwar zuwa sai musan Abunyi,tashi yayi suka rakashi ,shima Mubarak ya shiga mota zai tafi gurin karima
Kofar gidansu karima yaje ya kuma aika yaro ,Aunty Huda ta fara bacci mh ,tashi tayi tace wane yazo mana gida Acikin Daren nn ,karima idonta biyu tanata tunanin duniya amman Jin aunty Huda ta tashi yasa ta maza ta rufe idonta ,lekawa tayi taga Mubarak ,lfy Mubarak a Daren nn ,Kai yaketa sosawa ,aunty Huda dama zuwa nayi in dauki karima , hmm aunty Huda tace ,toh zauna Ina zuwa ,shiga tayi ta samu karima ta tasheta,karima mijinki fah ya sake dawowa ,yace ki shirya ki tafi gida ,tashi karima tayi ta gyara zama ,Aunty Huda inason in fada miki wani Abu , dan Allah kimin Alkawarin babu Wanda zaiji , Karki gayawa mama bare baba ,wannan Amanata ne dake ,Kai ta daga mata babu komai karima a duniyar nn babu abun da bazan iya miki bh ,Ke yarinya ta ce kuma kanwa a gurina ,banida Wanda ya fiki ,gani nake Nafi kowa son farin cikin ki ,mene ne gayamin,aunty Huda ance Wanda ake jin cikinsa aikinsa baya baci ,kuma sai anfi sanin yanda za’a taimaka maka ,Ina cikin wani Hali bansan ta inda zan fara bh ,aunty Huda ki gayamin abun da zanyi ,labarta mata abun daya Faru tayi ,aunty Huda babu Kaya fah a jikinta ta fashe da kuka ,aunty Huda kanta saida ta mata kwalla ,dan ita akwai tausayi Abu kadan ne zai sakata kuka ,lallai karima dole kiyi Zazzabi ,Amman Ina fatan kin gayawa Allah ba iya kukan kika tsaya bh ,Sannan karima ni banza taba saki dole bh ,a yanzu dai idan kinason komawa bazan hanaki bh idan bakyaso mh bazan hanaki bh ,duk abun da kika zaba toh zan tsaya na tayaki,Sannan kinyi min daidai da kika Zane Shegiya,gobe idan akace taje gidan matar aure bazata kuma bh ,kin koma burgeni da kika zaba wanann abun ya zama sirri ,tabbas wannan sirrin ki ne da mijinki , kuma kema Alkah zai rufa miki asiri duniya da lahira ,shiyasa kenan naga tun safe yake sintirin zuwa munafuki ,to mene yakeson yace miki? karima ce Tana kuka tace aunty Huda tsoro yake dan kar mamansa taji,yanzu haka wannan zuwan dayakeyi so yake ya rokeni karna gayawa kowa kada mamansa taji ,Tana fada tana kuka , kiyi hakuri karima ,kiyi hakuri ,kowa a duniyar nn da nasa jarabawar,kowa kika tambaya Yanda tasa Matsalar in one way or the other ,wani ta miji ,wasu na yara ,wasu na kishiyoyi,wasu mh na iyaye ,wasu na gurin aiki ,rayuwar nn is full of challenges,from dis to this ,Kowa da kika gani gidan aurensa hakuri yakeyi ,anajin dadi a aure Amman still Ana hakuri , karima nasan kinyi hakuri gaskai Amman na barki kiyi tunanin sosai kiga abun daya kamata saiki gayamin na Baki shawara ,Sannan zan bayar gobe ayi miki sauka , zanyi sadakar shinkafa da wake akai Wancan makarantar malaman ,Sannan ki daure kiyi istikara kiga abun da Allah zai nuna miki , zakiga Addua idan da Alkhairi zamu gani ,idan babu Allah da Kansa zai Watsar da abun ,yanzu ai ba’a dole ,ki Mika lamuranki gurin Allah Kisha mamaki ,shi kuma yanzu dayake ta min sintiri Bari naje na samesa ,fita tayi tagansa yana nn tsaye a kofar gida ,bata rai tayi sosai dan har ranta haushinsa takeji,Mubarak ka wuce ka tafi bazaka samu ganin tah bh batajin dadi ,Mubarak saida ya daga ido ya kalleta dan yanda yaji tayi sounding kaman ba itace me lallabasa bh dinann , kasa daurewa yayi ,Aunty Huda dan Allah kice mata tayi hakuri ,wlh Ina son naganta ,itama kasa daurewa tayi tace kanason ka ganta ka bata hakuri kada mamanka taji abun daka mata ko Mubarak ?saida zuciyarsa ta buga , kunya ce ta kamasa sbd haka kasa yayi da Kansa ya fara magana ,aunty Huda na rantse da Allah nayi nadama ,naji banason mamana ta sani Amman wlh itama inason ta yafemin ,inason matata wlh Allah dagaske nake miki ,inason tazo mu koma mu cigaba da rayuwa ,na rantse da Allah aunty Huda na tuba ,wlh Allah dagaske nake miki ki taimaka ki tayani bata hakuri ,aunty Huda Ko mene takeso zanyi mata ta yafemin,aunty Huda ce tace kaji matsalarka Mubarak,wato Ko mene takeso Ko ?an gaya maka kudi ne kawai so ,kodan kanada kudi shkkn zakayi abun daka ga dama ,dan kanada kudi zaka bawa yarinyar mutane wahala toh abun ba haka yake bh ,kadai a tunanin kudinka zai maka wani abun a duniyar nn ,dakai da kudinki ba komai bane ,kaji tsoron Allah kawai shine abun dazai taimakeki kudin naka mh suyi Albarka ,tsakanin kh da karima kuma babu ruwana,babu abun da zan iya cewa ,duk abun da taga dama rayuwarta ce ,ni kuma na mata Alkawarin zan tsaya mata a duk decision da Zata yanke ,yanzu karima ta girma babu Wanda zai mata dole ,sbd haka gaka gata ,tsakani ku ne Amman kaji tsoron Allah ,wlh kaji tsoron haduwarka da Allah ,ku Ko tsoron cututukan zamani nn bakwayi ,kuzo kuyita saka yaron mutane a wahala ,duk abun fah da kayi sai anyi wa naka ,kanaso Yau ace ka haifi yarinya tayi aure mijinta na kula wasu a waje ?,har zuciyarsa saida yaji babu dadi ,Kai ya gyada mata yayi Alamun nadama sosai ,ikon Allah yace a zuciyarsa ,lallai abun nn ya bata mata rai yanda ta kwarkwaresa rokonta ya shigayi da ta barsa yaga karima badan halinsa bh ,tafiya tayi ta barsa a gurin ,gani Yayi bazai iya bh gidan ya shiga shima sai ganinsa sukayi,baima San inda zaije bh muryar aunty Huda ya ji ya fada dakin sai ganinsa sukayi akansu ,aunty Huda ce kawai ta fita ta barsu, karima na kan gado zazaabi ya rufe ta sosai , matsawa yayi kusa da ita ,tashi tayi da sauri ta nuna maaa kofa ,tashi ka fita ,zai fara magana ta cilla masa pillow tashi ka fita nace ,mazinaci kawai Wanda baya tsoron Allah ,na tsaneka na tsani ganinka ka fita nace maka ,tashi yayi yaje ya rike mata Hannu yana rokonta ta taimaka ta yafe masa wlh ya daina ,gani yayi tayi kasa bata magana ,wuyanta ya taba yaji shiru fita yayi da guda ya kira aunty Huda itama da gudun ta shigo Tana ganin karima a kwance tayi kanta ,ta taba wuya nan mh shiru ,zaro ido tayi tace SUMA tayi Mubarak ,da karfin gaske ya dauketa suka fita sai asibiti ,tun a wajen asibitin yake kwallawa nurses Kira ,da sauri kuwa akazo aka karbesa, an dade akanta kafin ta far fado ,doctor ne ya shiga duba result dinta da abubuwan da akayi mata ,shigowa dakin yayi ya tarar dasu a tsaye a kanta ita kuwa bama tasan inda kanta yake bh andai kara mata ruwa ,doctor ne ya kalli Mubarak yace masa CONGRATULATIONS your wife is pregnant….
Post a Comment for "Acikin Gidana 12"